Showing 66001 words to 69000 words out of 397328 words
da abinda ke kanki jinyar masaki ba ƙaramin abu bane, Allah ya sawaƙa." Daga haka ta fice ta bar Yusrah tsaye tamkar mutum mutumi.
Ta jima a tsayen nan har sai da Safiya ta shigo ta yi mata wani kallo sheƙeƙe sannan ta ɗaga ƙafarta da ta yi mata wani irin nauyi ta juya ta fita daga gidan gaba ɗaya ta tsayar da ɗan adaidaita ta shiga, a hankali ta kifa kanta tana jin wani irin kewa na iyaye na neman bijiro mata, a yanzu har kewar na son dane farin cikin da ta riƙo na samun kuɗaɗen aikin auta, innalilahi wa inna ilaihi raju'un, Gwago na magana mahaifinta take hange a jikinta, sai dai kalamanta a hankali suka rikiɗe suka koma tamkar baƙin kumurci, a hankali kamannin Gwago suka yi baƙin ƙirin a idanuwanta, har ma da kuɗaɗen nan jaka ɗari uku kacal da ta bata matsayin shine kason su a million uku da ɗari ɗaya...
"Mun iso yan mata." Mai adaidaita ya sake faɗa yana juyowa gaba ɗayan sa dan ya jima da tsayuwar amma bata motsa ba.
Da ƙarfi ta sauke ajiyar zuciya tana kallon ƙofar asibitin ta ji wata salama na ratsa ta da nutsuwa, a hankali ta fito ta ciro kuɗinsa ta bashi sannan ta juya ta nufi asibitin cike da zumuɗin son ganin fuskar Safwan.
A nutse ta nufi asalin ɗakin da ta tafi ta barsu, ba na kuɗin nan ba kafin a mayar da su na yaku bayi madaidaicin kuɗi.
Tana zuwa ta samu wasu a ɗakin , hakan ya sa ta fito bayan ta tambaya sun tabbatar mata da suka zo basu ga kowa a ɗakin ba.
Da ɗan sauri ta nufi wajen likitocin dan a nan ne kawai zata samu bayanin ɗakin da aka mayar da su Safwan, tana zuwa ta samu likitoci uku a wajen, har da wacce Docter ya sa ta fitar da Safwan.
Bayan ta gaishe su ta tambayi shin an mayar da ƙanin ta da Iya wani ɗakin ne? Ta je inda ta barsu basa nan. Kallon kallo suka yi, sai kuma suka kalleta bata da datti a jikinta, amma kana ganinta zaka ga yanayin jigatuwa a tare da ita.
Inda inda ke neman wanzuwa a tsakaninsu har sai da wacce Docter ya saka aikin ta jajirce tana kallonta ta ce" Kina ji? Da aka wayi gari aka wuni aka kuma kwana baki zo ba inaga tsohuwar tafiyarta ta yi, bayan kwana biyu kuma Docter yace a sa kurma ya fitar da shi ko ni ya korenii a kan aikina, ni kuma na fitar da shi wajen masu gadi."
Yusrah dake kallonta da sauri ta ja baya, ta sake matsowa inda take muryarta na rawa tana nuno likitar ta ce" Kina nufin, tun jiya kuka fitar da Safwan can cikin titin cen wajen sauron cen? Kina nufin Iya tafiya ta yi ta bar Safwan kwana biyu bana nan?" Ta idasa da ƙarfi muryarta na fashewa alamun kuka zai ɓalle mata.
Baya likitar ta ja tana dubanta ta ce" To yaya kike so na yi? Kin san dai haka kawai ba zan ɗauki babban risk ɗin da za'a koreni daga aikin da na sha fama kafin in samu ba ko? Ni fa banda laifi a nan gaskiy..."
Da sauri Yusrah ta juya, wata juwa na son sarƙeta, ta shiga lalubar hanyar da zata sadata da wajen masu gadi tana jimƙar hijab ɗin dake jikinta har ta ƙarasa.
Tana zuwa ta gaishe su a jimulce, daidai an buɗe ƙofa wata galleliyar motar ta shigo ɗauke, Bilal ne ke tuƙi sai Intisar gefen shi rumgume da baby Yusrah, duk da daren sunan yarinyar ne, amma cikon allurar ta ne za'a mata, Zahra'u kuma tana saloon shiyasa sai Intisar ta kawo ta, bata iya tsayawa sun amsata ba ta shiga tambayarsu da basu kwatance.
Sheƙeƙe tsoho mai gadi ya kalleta da alamun faɗa ya ce" Ke ja'irar gidan uban wanene? Kwana nawa yau da kuka gudu kuka bar yaron? Yanzun uban me kika dawo nema? Ko ajiyarsa kika bamu? Yaro ai Mani ya kula da shi, Mani ɗin kuma ya yi tafiya mai nisan gaske kafin ya tafi kuwa mu dai mun ga ya saka yaro a wata mota baƙa wuilik mai lambar Nigeria an tafi da yaron, yanzun ai kun huta an ɗauke maku nauyi, mu me ye namu da zaki zo nan kina mana tambayoyin rashin ɗa'a?"
Tunda ya fara magana jirin dake kwasarta ya tsananta, bugun zuciyarta ya yi tsananin gaske. A hankali ta buɗe bakinta tana jan numfashinta, da ƙarfi ta ɗaga ƙafar ta dan ƙarasawa wajen tsohon sai dai bata kai ga ƙarasawar ba ya juya yana nemo ɓotar sa yana faɗin" Yallaɓai kar ka ƙaraso nan, wannan ga dukkan alamu an faɗa sharin bariki za'a juye mana iskancin banza, bari ki gani."
"Kai, kar ka saki, kar ka saki ka daketa, domin da hannuna zan rama mata idan ka daketa, Yusrah." Muryar Bilal da tunda suka shigo idanuwansa suka sauka a fuskar Yusrah.
A birkice ya ƙaraso, da sassarfa Intisar ma ta ƙaraso lokacin kuma Yusrah ta kai ƙasa tana numfashi da bakinta idanuwanta sun firfito waje, muryarta haɗe da kuka ta buɗi baki bayan ta damƙi damtsen Bilal da ya riƙota ta shiga furta" Sssa... Safff... Ssssssa..." Ɗif ta ɗauke wuta, ɗauke wutar dake masu nuni da ta suma.
A haukace Bilal ya cirata, Intisar ta ɗauki silifas ɗin ta na soso da ta ƴar a ƙafar ta a guje, a kuma haukace suka nufi babban wajen emergency da ita suna ihun faɗin a taimaka masu suke yi, daga shi har Intisar ɗin dake ɗan gudu gudu saboda baby Yusrah dake hannun ta hankalinsu a tashe, ganin su waye da yanayin da suke ciki ya sa likitocin karɓar Yusrah H suka yi ciki da ita.
Kai kawo kawai suke yi, mintina ashirin tsakani aka basu damar shiga domin sun farfaɗo da ita daga doguwar summar da ta shiga.
Suna shigowa daidai lokacin da take sauko ƙafafuwanta daga saman gadon ta kama ta miƙe bayan ta cire ƙarin ruwan da aka saka mata da ƙarfi ta yi luuuu! Zata zube saman gadon, amma dan ƙarfin hali ta riƙe a birkice ta riƙe da ƙarfin ta, da ɗayan hannun kuwa ta dafe gaban goshinta dake sara mata sannan ta dago a rikice tana kallon Intisar da ta ƙaraso da sauri ta riƙo ta tana faɗin " Yusrah, innalilahi wa inna ilaihi raj'une! Subahanallah Yusrah, ji mana, saurara mana, kalli kin cire ƙarin ruwan nan jini na bin hannunki, subahanallah me yake damun ki? Ki kwanta ki huta dan Allah."
Yusrah ta zuba mata ido, sai kuma ta rintse idanuwanta lokaci ɗaya ta miƙe ta cire hijab ɗinta ta yar a nan, gashinta dake ɗaure da farin ribom ƙarami a kwance a gadon bayanta a birkice ta shiga ƙoƙarin kwance zaninta, hakan ya sa Bilal saurin juyar da kansa, kan nasa na sarawa tsoro na cika zuciyarsa, sai kuma ya juyo da sauri jin ta fara magana a lokacin da ta ciro ɗaurin da ta yi ta ɓoye kuɗin nan ta buɗe ta zazzago suka faɗo har da takardar dake ɗauke da lambar kawun ta da aunty ɗago kuɗaɗen tana nunawa Intisar ta ce" In huta? Ina na ga hutu? Anya kuwa zan huta? Bani da hutu, kin ga abinda na je nema, kwararo kwararo a ƙafafuwana dan in samo su, har roƙo nayi wanda ba ɗabi'ata bace hakan ba kuma tarbiyyar gidan mu bace, saboda in kawo a dubi ƙanina domin an nuna min ba za'a yi masa magani ba sai na kawo kuɗin nan, amma shine na zo yanzu aka ce wai ba'a san inda ƙanina yake ba, ba'a san inda Safwan yake ba? Sai ya nuna min inda ya kai Safwan, sai ya fada min inda ya kai min ƙanina, idan siyar da shi kuma ya yi sai ya haɗa mu ya siyar."
Tana gama faɗa ta juya a rikice ta fice ta gaban Bilal da ya yi mutuwar tsaye yana kallonta.
Da ihu Intisar ta ce" Bilal ka riƙota mana." A zabure ya ɗaga ƙafarsa ya juya, sai dai a lokacin da ya fito tuni an yi cincirindo a wajen hanyar babban office ɗin Docter.
Kokowa ake tafkawa da Yusrah da masu bada tsaro, a guje ya ƙarasa ya shiga janye duk wani wanda ya kawo hannunsa da nufin janta da ƙarfi yana hankaɗewa, ita ma ihu take tana faɗin sai an barta ta ganshi, sai an barta ta shiga.
A rikice Bilal ya riƙo hannunta da ƙarfi, sai dai bata bashi dama ba ta saka dukkan ƙarfin ta ta ture shi sannan ta ɗaga ƙafarta ta nemi kai masa duka ido rufe tana ihu tace" Wallahi sai na ganshi, sai na ganshi azzalumi fasiƙiiiiii kawai."
"Ke idan bamu jinyata ki ba shege nake, waye zaki gani? Oga ya bar ƙasar nan kuma ba kwana kusa zai dawo ba, ki daidaitu ko mu mayar cewa ke mace ce gefe mu kakkarya ki a kyauta." Ɗaya daga cikin masu gadin dare na wurin ya faɗa da ƙarfi yana wani cika da batsewa alamun tsaf suke iya rufa mata idan ta yi wasa.
Da sauri Intisar ta ce" Kai! Babu mai dukanta a nan, ku dakata babu mai dukanta, ina ya tafi? Me yake faruwa ne? Ku dakata!" Tana faɗa tana ta kiciniyar fitar da wayarta dan kiran uncle ɗinta, domin ta tabbata bai san da wannan rikicin ba, kuma ta tabbata ko waye ya taɓa Yusrah uncle ɗinta bashi da labari.
Yusrah da ta gama fahimtar ana nufin ya yi tafiyar da gaske kamar yadda masu gadi suka faɗa ne sai kawai ta juya, da sauri ta ƙarasa ɗakin nan ta duƙa ta haɗa kuɗaɗen nan ta mayar a ƴar jakar ta maida inda ta suke ɗazu ta warci hijab ɗinta sannan ta fice bata kula cewar ta ƴar da takardar nan mai ɗauke da lambobin su aunty Fureira ba ta kama hanyar waje idanuwanta na sake rufewa, jinin hannunta kuwa dan kansa ya dunƙule ya hana kansa zuba, duk ya ɓata mata jiki sannan hannun ya kumbura.
Tunda ta fito bakin titi babba su Intisar ke fama da ita, amma idanuwanta a rufe suke faɗi take yi Safwan zata je ta nemo.
A birkice Intisar ta riƙo ta da hannu ɗaya tana tallabe baby Yusrah a ɗayan tana faɗin" Ke wai lafiyarki ƙalau? Ki dakata mu yi magana mana, ina zaki je? Ki dakata ko menene a samu matsaya guda mana, haba Yusrah! Kin ga yadda kika fita a hayyacin ki kuwa, ki dakata mu nemi solution mana."
Dakatawar Yusrah ta yi tana kallonta, a hankali ta langwaɓar da kanta hawaye wani na korar wani, muryarta a sanyaye sosai ta ce" Dan Allah ki yi haƙuri ki barni in tafi, idan ban ganshi ba wallahi bugawa zuciyata zata yi, dan Allah ki yi haƙuri kin ji aunty Intisar? Na gode da kulawar ku a kaina, amma tafiyata *WATA TAFIYA* ce mai nisan gaske da babu tsayawa a jadawalina har sai nayi tozali da ƙanina, sannan *TAFIYATA* mai tsauri ce da tashin hankali, da wahala ki ji daɗin *LABARINA* balle har ki so kasantuwa a ciki, na gode da kula, amma ni na tafi."
Daga haka ta saki hannunta ta juya da gudu gudu tana tsayar da abin hawa, cikin ikon Allah na uku ya tsaya ta faɗa tana faɗa masa tashar motar da zai kaita wacce in da a hayyacin ta take ko me za'a bata ba zata je tasha dan shiga motar ƙauyen su Iya Abu a daren nan ba da ƙarfe 09:00 ta yi, sai dai niyyar ta a yau yau zata kama hanyar ƙauyen su Iya Abu dan ta sanar mata wa ta barwa ƙanin ta, tunda har ta iya tafiya ta bar marayan yaro ƙarami a halin rashin lafiya irin wannan, tabbas sai ta faɗa mata wa ta barwa shi.
"Ta tafi? Kika barta ta tafi? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une!" Bilal ya faɗa da ƙarfi yana duƙewa tamkar ba gansamemen saurayi majiyin ƙarfi da samartaka ba.
Hankali tashe Intisar dake share hawaye tana rirrigar baby Yusrah duk da ba kuka take ba ta ce" Bilal ya zan yi? Ya kake so na yi? Gaba ɗaya ta ƙi saurarana kuma ta ƙi fayyace min abinda yake faruwa da ita, faɗi take sai ta ganshi sai ta nemo shi, subahanallah! Innalilahi wa inna ilaihi raj'une! Wannan wani irin tashin hankali ne? Ka ga tashi, tashi dan Allah mu yi abinda ya kawo mu, tashi mu tafi, kuka zaka yi ba Bilalun Mama?"
Bilal ya rintse idanuwansa, da ƙyar ya iya tashi, sai dai ya kasa komawa asibitin, ya miƙawa matar yayansa ky ɗin ya ƙurawa hanyar da Yusrah ta bi ido hankalinsa gaba ɗaya ba a jikinsa ba, abu ne kamar da wasa yake son yi masa wani irin shiga mai tsananin da zai saka shi cire tsammani, domin yana ji yana gani ɗin nan irin yadda abin ya shigo ya koma sai ya ji tamkar da ruhinsa ta tafi, yana nan tsaye Intisar ta fito an yi wa baby Yusrah allurar ta ta fito da motar, saida ta tsaya daidai inda yake sannan ya buɗa ya shiga yana dafe kan shi, dake baby Yusrah kuma na sagale a ƙirjin ta bata damu da ya taimaka mata da wani abun ba, sai dai ta kan kalle shi lokaci lokaci.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*19*
Wani nutsatsen bacci ne ya ɗauki Safwan daga kan gadon nan, to ac ma daidai da yadda jikin sa zai ɗauka uban nashi ya daidaita masa, yanzu haka da AA ke kallon fuskar yaron yayin da yake bacci, sai yake jin wata ƙaunar sa na sake huda shi, tubarkallah yaron kyakyawa kuma gashi da fata mai duhu mai kyan gaske, yanayin gashin Safwan yana nuna masa kamar shi ma yana da nasaba da buzaye ne ko fulani, baƙi ƙirin gashin nasa sannan irin mai murɗewa ne da zaran ya taru.
Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya taɓe baki ya furta _"Hmmm!"_ Sai kuma ya shiga ayyana _" Mahaukaciyar banza da wofi, ba zaki ga da kyau ba tunda har kika rasa zuciyar da kowace mace ke ɗauke da ita, wato tausayi."_
Gyara tsayuwar da zai yi ta sa shi tunawa da wani babban uzurin da ya so gabatarwa tun bayan sallah isha'i, da sauri ya duba agogon hannun shi wacce aka ma zubi tamkar ta gold sai dai ba gold ɗin bane... Tabbas yanzu kam sai dai ya samu Isoufu Hassan a Park ɗin da yake zama, dan haka ya kalli Anna da yanayin gaggawa ya dafa kafaɗar ta a harshen buzanci yace "Anna, zan je wani guri na dawo yanzu, kar ku bar ɗana shi kaɗai, idan na dawo sai ku tafi."
Kafin ta ce wani abu ya juya fit ya fice a ɗakin sai da idanu kawai suka bi shi, ita kam Anna dama wannan sunan da yake ta ambata na ɗan shi ne bata gane masa ba kuma take son ya fayyace mata, amma tunda ya tafi ya zatayi da ya wuce shiru?
A park ya samu baristern cikin hayaƙin da ya tarawa kanshi na shisha, ƙa'ida ne dama kullum da dare yana nan wurin, zaune ya yi yana yatsina fuska saboda ƙarfin flavour dake cikin hayaƙin da yake shaƙa shi sam bai masa ba. Yadda idanun shi sukayi jajir kamar maye ya sa kawai ya dube shi yace "Magana na zo muyi?"
Da ƙyar ya iya buɗa idanu ya kalle shi sosai yana dakatawa yace "Ina jin ka chairman."
Ba tare da wani ɓata lokaci ba yace mishi "Me ye haɗin kuɗin da aka fito da su daga asibitin Aba zuwa gidan Muntari Buza?"
Wani warrr ya yi da idanu, sannan ya ƙara buɗa su ya kalli AA ɗin, a ɗan rikice ya aje shishar yana duban shi yace "Chairman, kwana biyun nan wasu tambayoyi ka ke min masu tsaurin gaske, me ye ni kuma haɗina da wannan tambayar?"
Kallon shi ya yi ba alamar wasa yace " *Ɗan Hassan*, bana son ɓata lokaci ko doguwar magana, ina so na san komai da yake faruwa, daga ina kuɗin nan suka fito suka zo asibitin? Daga cikin asibitin ake tara wannan maƙodan kuɗin? Ko daga wani wurin aka shigo da su zuwa nan? Sannan me ye na kai su gidan M. Buza? Ina so na san duk wannan, kuma an faɗa min kai kaɗai za ka sanar dani hakan."
Girgiza kai Isoufu Hassan ya yi ya gyara zaman shi sosai yace" Chairman, ka gane wani abu, ni fa gaskiya ba za ka iya jin komai daga bakina ba, wannan lamari ne dake da haɗari sosai, ba kowa bane zai iya jan wuyancin sanar da kai abinda kake son sani, kuma na tabbata wanda ya turoka wurina wallahi