Showing 72001 words to 75000 words out of 397328 words
murya yace "Ya kyakyawa, magana fa nake miki? Me zai hana ki kwana anan wajen mu? Kinga da safe sai ki wuce, kuɗin ki ma gashi sai na dawo miki da su."
A ɗan ƙufule ta kalle shi da yanayin zafafa ta ture shi da ƙarfi ya yi baya tace "Na kwana anan na maka uwar me? Dallah ni ka barni naji da abinda yake damuna, kuɗi ne gasu nan na baku an wuce wajen."
Ta ƙarashe da jan tsaki, kafin ya mata magana wani daga can bayan shi ya leƙo dan ganin fuskar ta yana faɗin "Ke wacece take ɗaga mana murya?"
Ƙarasowa ya yi sanda saurayin ke faɗin "Oga wannan ƴar ce, da wai ganimar yaƙin na so kawo maka matsayin abokiyar kwana, shine take mana wannan ihun."
Gabanta ogan ya tsaya yana ƙare mata kallo, duban saurayin ya yi yace "Ka samu wani abu wurin ta ne?"
Nuna masa kuɗin ya yi yace "E oga, cittar ta ma tafi ta sauran yawa."
Kuɗin ya kalla shi ma sannan y a kalli Yusrah da bata kallon su, sai kawai ya kalli saurayin yace "Ka cajeta da kyau, akwai fiye da haka a jikin ta."
Jin hakane ya sa cikin Yusrah ya ɗuri ruwa ta shiga daidai tsayuwar ta tana taɓa jakar dake ƙugun ta...Baya ta fara ja tana faɗan "Wallahi kar ka caje ni, idan ma cajenin za'a yi mace ta cajeni mana, ni ba wasu kuɗi a jikina iya su na baku..."
Tana maganar ne tana ciro jakar daga ƙugun ta, idan dai Allah ya so ka da rahama kana bakin kura ma sai ka fita ba kwarzane, hakane ta faru da Yusrah yanzu ma, dan kuwa tana danganewa ga jikin motar sai ta yi gaggawar cilla jakar ta ƙasan ƙafar ta, tana faɗuwa jakar cikin hargagin nan na ta ɗauki hankalin su ta ci gaba da faɗin kar wanda ya taɓa ga ta sa ƙafa ta ƙarasa jefa jakar ƙarƙashin motar, hakan yasa ogan yan daban ya kalli wata mata da ita ba dattijuwa ba ba kuma yarinya ba yace "Ke baaba dan Allah caje mana wannan ƴar..."
Sai kuma ya kalli Yusrah yace "I swear idan aka ƙara lalubo mana wani abu a jikin ki ba uban da zai hanaki kwana anan."
Da irin turo baki tace "Na yarda." Matar nan jikin ta na rawa rawa ta matso kusan ta, duk da goyon dake jikin ta haka ta shiga lalabe Yusrah, amma da bata samu komai ba ta kalle shi tace "Wallahi yallaɓai ban ga komai ba."
Wani kallo duk ya watsa musu, sai kawai ya kalli yaron nashi yace "Za su kaimu gobe?"
Ɗaga kai ya yi alamar e, dan haka ya kalle su yace "Duk ku ɓace daga nan."
Juyawa sukayi su dukan su suka fara tafiya, haka suma suka dinga shiga motar jikin su na rawa, sai Yusrah da ta zagaya ta baya ta duƙa ta jawo jakar ta, dreban kaɗai da ya ga haka ya shiga motar yana faɗin "Kin yi dabara, amma ko dan gobe irin waɗannan ba'a musu, ki dinga kula kin ji ƙanwata."
Ƙala ba ta ce mishi ba ta shiga motar suka ci gaba da tafiya, sai lokacin ne Yusrah ta shiga da addu'ar hawa abun hawa sannan bakin ta bai gushe ba tana ambaton Allah har suka isa ƙauyen su Iya Abu.
Saboda daren da ya jima da tsalawa ya sa Yusrah jimawa tana buga ƙofar su Iya, da ƙyar Goggon da baccin farko ne ya kwashe ta shiyasa ya mata nauyi ta taso ta buɗe gidan. Da ta ga Yusrah wallahi ta ɗauka ko dan ta wuni har ta kwanta da tunanin halin da suke ciki ne ya sa Yusrah ta mata gizo, to amma kuma da ta tuna ai ƙofa aka buɗe sai ta yi tunanin mafarki ne take gigin tsufa kuma ya taso ta.
Wani sheƙeƙe ta kalli Yusrah tare da kasshe fitilar hannun ta tayi niyyar maido ƙauren ta rufe sannan ta koma ciki, riƙe ƙofar Yusrah ta yi tace "A'a Iya, wajen ki na zo."
Zaro idanu Iya ta yi da matsanancin mamaki tace "Amm...Yasira kike? Au Yusrah, ke ce a daren nan? Ke daga ina kike haka? Jikin Safwan ɗin ne ya ƙiya?"
Wani kallo mai kama da hangen nesa Yusrah ta ma Iya, sai kuma ta raɓata ta shiga ciki tana juyowa suka fuskanci juna tace "Ban gane ba Iya, Safwan din na zo ki faɗa min wa kika bar wa shi? Na zo asibiti baya nan an ce wai wata mota ce ta tafi da shi, Iya ina Safwan yake dan Allah? Wajen wa kika bar shi naje na ɗauko ƙanina."
Tashin hankali aka ce da ba'a saka masa rana, lallai Yusrah ta rabka *WATA IRIN TAFIYA* da sai yanzu ne bayan doguwar hirar da suka sha da Iya tana faɗa mata yadda komai ya faru har ta baro shi ta gane yanzu ne ma za ta ɗaura ɗamba akan *TAFIYA* neman Safwan har ta riske shi...
Cikin sako da zafafan hawaye ta shiga girgiza kai tace "Iya me ya hana ki ƙara min wasu awoyi har na zo na karɓi Safwan? Iya ko da ace asibiti suna bamu kulawa a wannan lokacin ba majinyaci irin Safwan ake bari ba, wanda sai an ɗauke shi idan zai yi bahaya ko bawali, yanzu Iya ya zamuyi? Ina zamu ga Safwan? Wa ye suka ɗauke shi? Duk fa babu wanda ya san amsar waɗannan tambayoyin."
Sai kuma ta ɗaga kanta tana kallon sama tace" Ya Allah kar ka jarabceni da rasa ɗan uwana, shi kaɗai ne a yanzu nake da da zan iya kira da nawa halak malak, saboda tun bayan rasa iyayenmu mun fahimci gatanmu dama kai ne da kuma su, to yanzu ba sa nan, Allah ka bayyana min Safwan, Allah ka bayyana min Safwan."
Jikin Iya ya yi mugun sanyi sosai har ta dinga kuka ta rasa me za ta faɗawa Yusrah, saida ta kama hanyar fita ne Iyan ta riƙo hannun ta tana shasheƙar kuka tace" Ina kuma za ki je yanzu?"
Ba tare da ta juyo ta kalleta ba tace" Iya can zan koma na ci gaba da neman ƙanina."
Hanata ta yi tafiya kuma ita ma ta yarda ne saboda ba za ta samu mota ba yanzu sai dai kuma idan asubanci ta yi, ta dai shiga ɗakin ne saboda ruwa da aka fara, amma yadda ta ga safiya haka ta ga wannan dare ba ta rintsa ba sai kukan ta da take kai wa ubangiji ta hanyar yin doguwar sujada.
*AA ANZA*
*Kiran* sallah da aka ƙwala a masallacin asibitin ya farkar da shi, yana buɗa idanu kuma akan Safwan da ya zuba masa idanu daga kwance yana kallo yana ta tunanin da gaske yanzu shine baban shi? Kuma zai masa duk abinda baban shi yake masa? Gyara kwanciya AA ya fara yi kafin a hankali ya ɗauke kan Safwan daga damtsen shi ya ɗora kan filo yana masa murmushi yace "Son, ka tashi kenan?"
Cikin sanyayyar murya Safwan yace "Ina kwana?"
Laƙace hancin shi ya yi yana murmushi yace "Barka da safiya my prrince, ya jikin naka? Ina yake maka ciwo yanzu?"
Girgiza kai ya yi yace "Ba komai yanzu, kuma bana jin ciwo, amma ina so na tashi tsaye."
Kallon shi ya yi da tausayawa yace "Za ka tashi in sha Allah boy, likita ya tabbatar min da haka."
Murmushi Safwan ɗin ya yi, haka shima AA da ya gyara zama ya tayar da shi zaune ya jingina shi a bango bayan ya ɗora masa filo, riƙo hannayen shi ya yi suna kallon juna da tausasawa yace "My boy, wata magana zan faɗa maka, za ka fahimce ni ko?"
Gyaɗa kai ya yi yace "E."
Kumatunshi ya shafa yace "Good boy, ka san cewa baban ka soja ne?"
Zaro idanu Safwan ya fara yi da irin mamakin nan yace "Lah! Dama kai soja ne? Kana da bindiga kuma?"
Dariya ya yi har haƙoran shi suka fito yace "E, idan ka warke muka koma gida za ka gani."
Ɗan nuna kan AA ya yi da yatsa a tausashe yace "Shiyasa ka canza gyaran kan ka kayi irin na sojawan da nake gani."
Nan ma dariyar ya yi cike da kunya ya shafa kan nashi sannan ya kara riƙe hannun Safwan ɗin, saida ya daidaita nutsuwar sa ya sake ce masa "Boy, ina so zan yi *WATA TAFIYA*, but i promise ba zan daɗe ba saboda *kana raina*, ba zan iya yin nesa da kai ba a yanzu bare har na iya rayuwar jin daɗi ba ka kusa dani, addu'ar ka nake nema, ina tabbatar maka ina dawowa aikin fitar da kai ne kaɗai a gabana dan ganin ka samu lafiya."
Me Safwan zai yi? Sai ko ya kyaɓe fuska yana shirin fashewa da kuka, da sauri AA ya tallabo fuskar shi yace" Hey! Me na faɗa bai maka ba, zan janye yanzun nan."
Cike da shagwaɓa har yana shasheƙa yace" Za ka janye yanzu?"
Da tabbaci yace" E my son."
Turo baki ya yi yace" To ka janye tafiyar, bana so."
Da kulawa sosai AA yace" Saboda me boy?"
Da shasheƙa Safwan yace" Idan ka tafi kai ma, ba za ka dawo ba, ina bacci cikin dare na farka na ganni a asibiti, babu Babanmu, babu Mamanmu sannan babu aunty Hannah, kuma ina bacci aunty Yussy ta ce min ta tafi ta dawo, har yanzu bata dawo ba, haka ma Iya Abu ina bacci sai farkawa nayi ban gan ta ba, kai ma ina tsoron idan ka tafi ba zaka dawo gareni ba *Abba*."
Da sauri ya girgiza mishi kai da kulawa yace" Kar ka faɗi haka son, suma da suka tafi suka bar ka kuskure suka aikata da ba zai taɓa gyaruwa ba, son, ba zan taɓa barin ka duk abinda zai faru sai dai ya faru, kai dai ka min addu'a, na faɗa maka ni soja ne, wani aiki zan je mai mahimmanci da zai iya ɗaukata sati ɗaya ko sama da haka, ka wa Papan ka fatan nasara, ka ji ko yaron kirki."
Ƙyaƙyabta idanu Safwan ya yi kamar dai bai yarda ɗin nan ba, hakan ya sa haka AA ƙara shafa kumatun shi yace" Please son, ka yarda dani, ba zan taɓa barinka a halin nan ba."
Jim ya yi kafin ya jinjina kai yace" To, Allah baka sa'a Abba, Allah kawo kasuwa albark..."
Sai kuma ya yi dariya yana rufe baki yace" Wai! Allah ya sa Abbana ya zama babban soja."
Dariya AA ya yi yana jawo Safwan ya rumgume cike da ƙaunar yaron yace" Ameen boy, amma fa Abban ka ma ɗan kasuwa ne babba ma kuwa."
Da wannan farin cikin da jin daɗin amincewar ɗan nasa ya tashi ya shjga ban ɗaki dan yin alwala yana jin kan shi wasai ba nauyin nan bare wata kwaramniya.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*20*
*Asubanci* ta yi ta tafi, Iya kuma ta tabbatar mata ita ma idan gari ya yi haske akwai saurayin da za ta kira ya zo ya zauna da Baffa sai ta zo ta ga yadda ake ciki... Haka ta kama hanyar komawa zuciyar ta fal saƙe saƙe da tunanin ina Safwan, sai da ta kusa shiga garin kaɗai abu biyu ya zo ran ta, na farko shine ta yi cigiyar Safwan wajen Goggo da su Aunty Khadi, duk da tasan da wuya a ce Goggo ta ɗauki Safwan, musamman da aka ce a baƙar mota, na biyu kuma shine aunty Fureira, ta san halin ƙanwar Maman nata tana da zafi idan aka taɓa ta da kuma rashin son raini, tabbas ƙaramin aikin aunty Fureira ne ta ɗauke Safwan idan ta same shi a wannan halin a asibiti, da wannan tunanin suka sauka Yusrah ta yi farautar wayar aro wajen wani mutum ta saka kati, saida ta ciro jakar ta tana lalubawa ta kira lambar aunty Fureira aka ce ɗauki inda kika aje...
Tashin hankali sabo, nan ta shiga tunanin ina ta aje ta? Amma da ta ga ba zai fisheta ba sai kawai ta miƙawa mutumin wayar tana masa godiya, shi ma godiyar yake mata saboda kati ta saka sosai gashi kuma bata anfane shi ba. Adaidaita sahu ta ɗauka tana mai takaici koma wa ya ɗauki Safwan wallahi sai ta nuna masa ya mata ba daidai ba, ko dan kuɗin nan da take ta kashewa wajen neman shi ai tana ƙara rage kuɗin aikin ne, da wannan ta isa gidan Goggo Hindatu da tunanin yadda za su ƙare.
Tana shigowa gidan na su Goggo dake safiya ce babu yara bare hayaniya, da kishiyar Goggo suka fara gaisawa da ta samu tana ma Goggon ɗaurin lemun siyarwa, ɗakin Goggon ta wuce tana sake yin wata sallama, bacci ta samu tana yi saman gadon ƙarfen dake falon nata, da ƙyar ta farka ta tashi zaune tana kallon ta tace "Yusrah, ke ce kuma? Me ya kawo ki da sassafen nan? Ba na baki kuɗin ki ba dan Allah?"
Ita ma yau da ke a ɗane take ɗan kawar da kanta tayi tace "Ba maganar kuɗi bace ta kawoni Goggo, na ɗauka Safwan yana nan."
Wani irin kallon jin haushi Goggon ta mata tace "Ah! Kin ɗauka yana nan ne? To ki sauke ɗaukar da kika yi, ke Yusrah wannan wane irin iskanck ne wai? Wane Safwan kuma da bai da lafiya zai zo nan, me zai kawo shi nan?"
Kallonta Yusrah ta yi tace "Goggo, Safwan ba ya asibiti, sannan Iya Abu bata san ina yake ba, tun jiya ta tafi ta barshi ina dawowa na samu baya nan."
Tsaki Goggon ta yi tace "To ku me ya fitar da ku daga asibitin har ku bar marar lafiya?"
Majina Yusrah ta ja saboda kukan dake son taho mata har muryar ta na rawa tace "Goggo dan Allah taimaka min da wayar ki na kira aunty Khadi na ji ko yana wajen ta?"
A tsaye ta bata amsa da "Khadija jiya har 11:00 na dare tana gidan nan kafin mijin ta ya zo ɗaukar ta."
A marairaice tace "To dan Allah ku bani na sake ɗaukar lambar aunty Fureira, na jefar da lambar ne ina ga a asibiti, sai na kira na ji ko yana can tunda mun yi waya jiya suka zo za su zo."
Wani banzan murmushi Goggo tayi tace "Au! Kin ma san da ta ce miki za ta zo shine kika zo nan neman shi? Ai kawai Safwan yana wajen Hure, tunda kinsan dama ba ƙaunar mu take ba, dan haka ba wani izinin mu za ta nema wajen ɗaukar shi ba."
Da lambar Yusrah ta so samu ta kira ta fara tabbatarwa, dan haka ma ta sake maimaita" Ku bani lambar tasu sai na kira na ji?"
Amma sai Goggo tace" Wayata jiya wajen dama kunu bayan tafiyar ki ta faɗa ruwa, yanzu haka fafutukar sake sabuwa nake."
Kallon Goggon ta yi, wallahi sam ba ta taɓa tsammanin haka zai dinga faruwa da ita ba, ran ta ya ɓace sosai ganin taimakon da bai taka kara ya karya ba amma Yar mahaifin ta ta kasa yi mata, juyawa ta yi a fusace da alwashin idan dai ba wani abun na da ya zama dole dole, gaskiya ba za ta sake kawo kan ta gidan Goggo Hindatu ba, ita kam za ta je gidan su ta ga me za ta iya samu wanda bai lalace ba, ta tattara ta ɗauki hanyar Funtuwa a safiyar nan, idan ta tafi kuwa in sha Allah ita da garin nan sai wani ikon Allah, amma sam babu alamar za su yi daraja idan ma suka zauna da Goggo anan.
Gidan nasu ta je, ta samu wata irin roba ce aka laulaya a bakin ƙofar, dan haka ta buɗe ta shiga tana kallon yadda gidan nasu ya zama kufai, falon ta shiga da bai ruguje sosai ba ta samu duk wasu kaya da aka ciro suna nan, haka ta shiga haɗa kayan ta da na Safwan ta kwashe duk wata takarda mai mahimmanci cikin sa'a kuma har da takardar gidan nan nasu tunda mallakin su ne, kuma a jakar kayan Babansu ta same ta, kawai ji take zuciyar ta na bata tabbas yana wurin aunty Fureira, tana haɗa kayan tana kuka saboda yau dai kam barin garin nan za ta yi gaba ɗaya, tana gama haɗa su a jaka ta hannu ta fito ba ta kula da komai ba ta fice a gidan, nan gidan Liman ta shiga ta musu sallama kan za ta je Funtuwa, haka ma gidan su ƴan biyu da duk inda ta san suna zumunci. Maryam kuma ta yi niyyar idan ta je ta nutsu ta samu waya sai ta kira ta, tunda ita tana da lambar ta a kai, daga haka ta ɗauki adaidaita sahu aka nufi tasha da ita.
Yau tashar a rincaɓe take da motoci da mutane wanda hakan bai cika faruwa ba, a yadda rana ta yi ɗin nan tuni wasu drebobin ma har suka kai mutane irin su Kano Katsina suna