Showing 249001 words to 252000 words out of 397328 words

Chapter 84 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70104

ya faru ranar ne ya sa kike hushi da ni har yanzu, to ki yi haƙuri, shiyasa ma na zo da kaina dan na baki haƙuri da kuma nuna miki dalilina na ƙin karɓan Yusrah a wancen ranar."

Taɓe baki Hajiar ta yi tana kallon ta sama da ƙasa tace" Dalili? Ina jin ki to? Me kika zo da shi? Amma ki sani idan akan maganar auren su ne kar ma kice za ki fara bani haƙuri, dan ba zan haƙura ba wallahi, ba ta yadda zan bar Bilal ya auri yarinyar nan alhalin na san wacece ita."

Kallon Hajia ta yi sosai, tabbas ta yarda akwai wani abu da ita ma ta sani, amma sai ta yi gaggawar ciro wayar ta tana neman vidion, ko da ta nemo shi ta taso daga kujerar ta tana kusanto Hajiar ta bata wayar tana cewa" Duba kiga Hajia, wannan na ɗaya daga cikin dalilan, ni nafi kowa sanin wacece Yusrah da uwar ta, ba na ƙi karɓan ta bane saboda son zuciya, na ƙi fitowa na faɗi dalilin ne a gaban kowa dan za'a ga kamar na mata ƙage ne, fisabilillah me zai sa ka kasa riƙe yara biyu ƴaƴan ɗan uwan ka? Ai sai dai idan baka da imani, ki yi tunani mana Hajia kiga ƙanin ta fa na asibiti kwance asibiti amma wai aka neme ta aka rasa kwana uku, ina ta tafi Hajia? Me ta je yi da ya fi ɗan uwanta mahimmanci? Amma cewa take neman kuɗin aikin shi ta tafi, bayan kuma ni mun yi magana da ita kan zan siyar da filin mu na gado sai na bata kason mahaifin su a mishi aikin, a haka fa kuma aka neme ta aka rasa, ita kan ta Iya abu dake tare da shi ai abun ne ya bata haushi shiyasa ta tafi ta bar shi, daga ƙarshe nan ta dawo mana da kuɗaɗe masu yawa wanda suka ninka wanda na bata fa, a ina budurwa za ta samo wannan maƙodan kuɗin a kwana uku kacal Hajia? Ai abun da ɗaure kai."

Ba ƙaramin muhalli kalaman Goggo suka samu a zuciyar ta ba da har ta ji e hakane fa, me ya sa ma ita tun farko ba ta yi wannan tunanin ba? Yarinya dan rainin wayo ta dinga nunawa uban kowa wai ta je neman kuɗin yi masa aiki ne, ko da ta dawo bata same shi ba, a cikin garin nan? Ki gagara leƙa shi ko sau ɗaya? Ai abun a duba ne wannan, hankali kuma ba zai ɗauka ba, dan haka ita sai ta ce Alhamdulillah da ba'a riga aka ɗaura ba bare raba auren ya fi yi mata wahala, wannan aure ba za'a yi shi ba har abada, sai dai kuma idan mutuwa ta yi... Kai ko yanzu ba ƙaramar rantsuwa za ta gittawa iyalin nata ba kan duk wanda ya aura masa ita ko bayan ran ta, to tabbas bata yafe ba duniya da lahira.

Jiki a saɓule ta miƙawa Goggo wayar tace "Wannan ai na riga ki ganin shi ma wataƙila, shiyasa na kafe kai da fata akan ba zan yarda Bilaluna ya auri wannan ƴar taku ba."

Wani farin ciki ne ya kama Goggo ta koma ta zauna tana haɗe farin cikin ta a sanyaye tace "Hajia wa zai ƙi nashi, ai sai idan lalacewar sa ta fi ƙarfin ka, kar ki so kiga yarinyar wajena da ta ga vidion nan, in dai ba yanzu ba bayan fitowa ta za'a samu cikin samarin gidan wani ya fatattake ta, kuka take yi ba ji ba gani tana faɗin wai ƴar uwar ta ce a wannan rayuwar? Ita fa ɗaya da biyu ta yi tagumi ta ce min _Mama wallahi Yaya Bilal nake tausaya ma da zai auri Yusrah bai san ko wacece ita ba_, ni kuma sai na ce mata Safiya ki tausayawa kan ki ke da baki da miji irin Bilal, sannan duk tausaya masan da kike yi bai san ma kina yi ba, babu ranar da bata min maganar nan har saida na tsawata mata kaɗai, daga ranar kuma bata sake maganar ba saboda Safiya duk cikin yara ni dai Alhamdulillah wallahi, shiyasa na ji tsoron haɗata wuri ɗaya da Yusrah, tunda budurwa ce idan tana ganin yadda take rayuwa wata rana abun na iya shiga kan ta."

Kallon ta dai Hajia ke yi saida ta dasa aya sannan ta taɓe baki tace" Ban ga laifin ki ba, ko waccen karon ma ai ni ba laifin ki na gani ba, kawai hargagin ki ne ya sha min kaina, kenan kina da ƴa budurwa?"

Washe baki ta yi har da wani rusunawa tace" E Hajia, sosai ma, ana can yanzu na san an tafi islamiyya."

Jinjina kai kawai Hajiar ta yi tace" Ma sha Allah."

Jin bata ƙara da komai ba ya sa Goggo faɗin" Hajia ko turo miki ita nake yi kika yadda ta fi ki damuwa da lamarin Bilal? Wallahi wai aka ce soyayya gamon jini, haka ita dai tun ranar da ya je gidana neman Yusrah sai ki ji ta ce yana bata tausayi."

Ɗan jim Hajia ta yi tana nazarin Goggon, ita kam idan da gaske ne ƴar ta na tausayawa Bilal ai za ta so ganin ta har ma ta aura masa ita, to ita dama duk faɗan ta da surukai ai akan rashin tausayawa yaran ta ne da ba sa yi, duk wacce ta ɗauko haukan ta sai ta juye a kan su, su kuma ba sa iya kaucewa buƙatar su kamar wani fadan Allah. A sanyaye ta jinjina kai kawai ta amsa da "Ba damuwa, sai ta zo ɗin."

Kamar Goggo za ta yi tsalle dan murna, amma sai ta haɗe kawai ta shiga yi mata godiya da sake kacancana maganar Yusrah har ta miƙe ta bar gidan, Hajia ma gyara zama ta yi da shirin ba wani kawu da zai hana ta ƙudirin ta, dan haka ta ci magani sosai. Da suka dawo kuwa Yaya Mubarak a bakin ƙofa ma ya tsaya tunda dai ba Aban bane ya zo, kawun ya shiga ya sanar da ita yadda sukayi, tsirarun kalmomi kawai ta faɗa masa cewa "Allah ya kawo shi lafiya."

Daga haka ba ta sake cewa komai ba, har kawun ya gama mata nasihar ta nutsu su fahimci juna idan ya zo, amma ba ta amsa shi ba haka ya ƙaraci zancen shi ya bar mata gidan.

Hajia Sa'a kanta dake uwa ta samu tarba yadda take samu, masu aiki sun aje mata abun ci da sha, sai kuma Hajia ta kunna mata vidion da sake faɗa mata zuwan Goggo da yadda sukayi, abun ka ga mata sai ta ji ita ma hankalin ta ya ɗauki maganar, sai kawai ta shiga cin kayan marmarin ta tana nanata "In dai hakane kuwa lallai Bilalu sai ya yi haƙuri, to yaushe za'a yi wannan katoɓara haka? Ai na tabbata Allah ya toni asirin ta ne tun kafin a ɗaura aure ta mallake mana yaro." Sai Hajia ta ji ta samu ƙarfin guiwar tsayawa kan ƙafafun ta, dan Hajia Sa'ar ce kaɗai za ta iya bata umarni kai tsaye ta bi, to kuma ta yi sa'a tana tsagen ta, yanzu me ya rage kuwa? Bayan Aba ya zo ta sanar da shi an fasa ba sa son Yusrah su kai kasuwa.


*DR. HAMAT*


Lallai duniya ba ta da tabbas, Dr. Hamat, babban likitan nan da ƙwarewar sa a fannin sa ta ja masa suna, asibitin gwamnati da na wasu garuruwa suke alfahari da shi, yake kuma girman kai da isa da ƙafafa saboda haka, yau sai gashi kwance gaban Aba da bai san irin abinda ke zuciyar sa a game da shi ba, yana kwance numfashi ma sai da iskan oxygen yake iya yin sa, bayan haka daga bayan shi zuwa kan yatsun sa biyu da ƙirjin shi duk wayoyi ne dake nuna numfashin shi, bugun zuciyar shi, tafiyar jinin sa, da kuma babbar matsalar da likitocin suke son ganowa dan su sanar da Aba kamar yadda ya yi tsaye kan ba zai matsa ba maza maza su duba masa ɗan uwan shi su gano me ye matsalar shi, idan ba haka ba yanzun nan zai tashi jirgin da zai ɗauke shi zuwa wata ƙasa a babbar asibiti a duba shi.

Yadda likitocin ke tsaye kan ƙafafun su suna ta zirga zirga da shiga ɗakin da Dr. Hamat ɗin yake da fitowa, haka Aba ma yake tsaye yana ta safa da marwa sai waya da yake amsawa a kai a kai, Sk ma na bayan shi duk in taka ƙafa shi ma sai ya taka, idan ya ce Aba ya zauna ya ɗan huta sai ya nuna a'a ba yanzu ba, haka aka gama duk wani aune aune daga na bayan gari, fitsari, jini har da yawun shi kaf sannan aka shiga lab dan binciƙen ƙwaƙwaf.

AA da duk da baya jin daɗin jikin shi da yanayin shi haka ya damu rashin sanin ina mahaifin sa, saida ya kira Sk ya sanar da shi inda suke, duk haushin kawun da yake ji da irin tarin shirin da yake shiryawa a kan shi, da ya zo ya gan shi kwance miraran bawali ma sai a kwance yake yi sai hankalin shi ya tashi yana tuna ganin sa na ƙarshe da shi, shima sai ya shiga sahun a gaggauta sanar da su me yake damun sa ne haka? Bayan duk wannan tsawon lokaci dai likitan dake duba uncle Hamat ɗin ya zaunar da su dan shaida musu abinda ke damun shi.

Cikin tausasa harshe da fara musu da kalamai irin na kwantar da hankali ya fara, kafin daga bisani ya ɗora musu da faɗin "Yallaɓai, ina ga ko akwai wani abu da Dr ke so kuma bai same shi, hakan ya sa yake wahalar da zuciyar shi fiye sa kima wajen tursasa ta tunani, har ta kai lokacin da ta gaza jurar haka shine ta fara yi masa kumburi, yanzu haka zuciyar shi a kumbure take, ga bugawar ta da har yanzu ta ƙi daidaita yadda ya kamata a ce tana bugawa, sai kuma..."

Shirun da ya yi na daƙiƙu ya sa AA faɗin" Uhummm!"

Dan haka ya ci gaba da cewa" Sakamakon matsananciyar shan sigari, hakan ya masa illa a huhun sa, wanda zuwa yanzu bana jin... Ko da yake komai na Allah ne, shi ma in sha Allah zamu ci gaba da bashi kulawa har ya miƙe kamar bai yi ba."

Cike da damuwa Aba ya ɗan share ƙwallar gefen idanun shi yace" Kana ganin zai tashi kuma?"

Da fara'a sosai yace" Me zai hana yallaɓai? Muna jira ne ma ya farfaɗo sai mu yi ƙoƙarin haɗa shi da mutanen da muka san suna da mahimmnci gare shi kuma mafi soyuwa, hakan zai taimaka masa sosai wajen cire damuwar da ke damun shi, sai kuma kuyi naku ƙoƙarin wajen gano abinda yake so dan a masa idan da hali, idan kula babu halin yi masa sai a tausashi zuciyar sa da haƙuri da maganganu masu daɗi har ya gane ba komai ake so ake samu ba."

Saida AA ya kamo Aba ya fito da shi daga ɗakin sannan suka sake tattaunawa da likitan tare da roƙon shi su yi iya ƙoƙarin su dan Allah, dan idan wani abu ya samu uncle ɗin to Aba ma damuwa za ta iya kwantar da shi, da ya fito ya so su tafi gida tare da Aban amma ya ce sam yana nan har sai ya ga farfaɗowar uncle ɗin sannan zai tafi, dan haka shima AA ɗin bai tafi ba sai ma ɗaya daga cikin escort ɗin Aba da ya tura ya siyo abinci mai rai da lafiya da lemuka da kayan marmari aka kawo wa su Maman Joli da mahaifiyar ta da ƙannan ta da suke nan, sai Goggo Tidin ita ma da bata jima da zuwa ba. Wannan zaman a asibiti ya sa Aba bai samu damar zuwa ganin Hajia ba, dan sai daf da magriba uncle Hamat ya farka, bayan sun yi sallah kuma Aba da Goggo Tidin kaɗai aka ba damar ganin shi, sune suka jima tare da shi suna ɗebe masa kewa, sai dai shi kallon su kawai yake yi da idanu amma abinda ke ranshi shine _'Ina wayar sa take? Ba ya so ya rasa wannan ɗaukar ta Yusrah, dan da ita zai yi anfani ya tilastawa Yusrah fasa auren Bilal sannan ta aure shi, dan ya san ba za ta so fitowar wannan vidio a duniya ba.'_

Suna nan zaune likita ya shigo ya sake duba na'urorin dake kafe a jikin shi, nan ya yi hamdala ya faɗa musu Alhamdulillah kumburin na ragewa kuma hawan jinin ma da sauƙi, shine kaɗai ya sa AA tisa Aba gaba ya ce ya je gida ya huta tun safe yana kan ƙafafun shi, tattare suka fito Sk ya buɗewa Aba mota ya shiga shi ma AA ya shiga tashi ya tafi, shi daga nan ya ratse wata hanyar saboda wani uzirin da zai je ya gabatar daga nan ya je ya ga Safwan, Aba ma saida sukayi nisa ya tuna da maganar su da kawu, dan haka ya umarci Sk da su juya gwanon motocin zuwa gidan su Intisar.

*Yau* rana ce ta farko a wajen Hajia da ya zama tasan duka yaran ta na gidan amma babu wanda ya ke zaune a falon ta, a yanzu da ba wani dare ya yi sosai ba, idan baka samu Yaya Mubarak anan ba to tabbas Bilal ne, su Uka kuwa dama ba cika shisshige mata sukayi ba, akwai mutum da za ka ga hakane Allah ya halicce shi komai son da yake ma jika ko ɗa ba ya iya sakin fuska da shi ka ga faran faran, haka take tsakanin ta da yaran, shiyasa suma ba sa zuwa idan ba da dalili ba, gashi ita ba ac take kunnawa ba, su kuma sanyin da suka saba da shi ya sa ba sa iya jurar dogon zama a wurin nata, amma matsalar yaran ma saida ta dinga ƙananan maganganu cewa hana su ne aka yi, wataƙila ma an nuna musu ba ta da daraja shiyasa suka rainata.

Sanin Aba ya zo gidan ya saka aunty Intisar tabbatarwa lallai akwai abinda ke faruwa kuma Yaya Mubarak ya sani ya ƙi faɗa mata ne kawai, dan haihuwa da rashin lafiya kaɗai ke kawo Aba gidan ta, amma yau gashi ya zo kuma ƙarfe tara har ta ɗan wuce, sannan bai nemi kowa ba ya dai gaisa da Yaya Mubarak ɗin da Bilal sannan ya wuce ɓangaren Hajia kai tsaye bisa rakiyar Yaya Mubarak, saida ya masa iso kafin ya bar falon dan baya so ma ya ji abinda za su tattauna, abinda ya sani ne kawai idan Hajia ta dage kan ba za'ayi auren da jibi ne ya rage ba, to gaskiya bai san da wane idanu zai kalle ta ba, zai ci gaba da yi mata biyayya, amma Allah ma ya sani ta tauye shi ta nan wurin, kuma da ya san haka ce za ta faru, wallahi tallahi da ya gaggauta dakatar da neman da Bilal ke yi wa Yusrah, gwara a ce ya hana tun farko da a ce saida aski ya zo gaban goshi za'a hana.

Duk irin zubar da Aba ya yi, ya kora mata bayanin ƙanin sa ne ba lafiya sosai shiyasa yake can asibiti tun safe, yanzu ma har ya ɗauki hanyar gida ya tuna ya nufo nan, a taƙaitacciyar kalma kawai tace "Allah ya bashi lafiya."

Aba ya amsa da "Ameen." Sannan ya ɗora da bayanin kawu na farko, kafin ya sanar da ita ainahin abinda ya faru, abun takaici da ya saka Aba yin jim ya kalle ta shine murmushi da ta yi mai kama da ita ce za'a rainawa hankali ɗin nan? Sai kawai Aba ya haɗe komai ya sake duban ta yace "Hajia, shiyasa na zo da kaina dan na sanar da ke wannan, Yusrah ta faɗa mana tun ma bamu san da ɗaukar nan ba, dan Allah kar ki dakatar da auren da aka gama shiryawa ake jiran safiyar jibi ta waye a ɗaura, yarinyar nan marainiya ce da bata da kowa sai Allah, a wajen Bilal ne take saka ran samun gatan da iyayen ta suke yi mata, sannan a wajen shine take da burin samun ƴar uwar ta da ta rasa, a tare da shi take samun farin ciki da kowane mutum ya kamata a ce yana samu, idan kika dakatar bamu san halin da yarinyar nan za ta shiga ba, wannan ɗaukar idan mukayi la'akari kamar masu son hana ruwa gudu ne suka same ta sannan suka yaɗa, idan kika yi duba da har gida aka same ki aka baki wannan ɗaukar, sannan ana tunanin za ki iya samar da abinda zai girgiza kowa, idan ba haka ba me ya sa mu ba'a bi ta kanmu an bamu ba? Dan Allah Hajia ki sassautawa zuciyar ki ki sakawa yaran nan albarka a wannan tafiya ta su, in sha Allah ba zakiyi dana sani ba."

Duk wannan bayanin ta bayan kunnuwan Hajia suka bi, gyara zama ta yi tana kallon shi tace" Alhaji, magana ta gaskiya ba wani ɓoye ɓoye auren Bilal da Yusrah ba za'a ɗaura shi ba indai ina raye, ko da rabo ya kasheni a yanzu ko a yau aka ɗaura musu aure a bayan ran nawa, to ku sani wallahi babu sa albarkata a ciki kuma ba da so na aka yi ba, dan haka kamar yadda nace ba za'ayi ba to kawai a bar ni a haka, da hankalina ba zan bar yarinyar da ta taɓa shiga magarƙama da laifin da ban san girman shi ba ta shigo cikin zuri'ata, idan nayi wannan ganganci ne da wauta, dan tana matsayin matar Bilal ma wani abu ya sake ɓullowa a sake zuwa min da tatsuniyar ai an san da labarin yanzu ne abun ya fito, dan haka kayi haƙuri dan Allah, Bilal zan lallashe shi ya dangana ya samo wata ko ni na samo misho, ita ma kuma Allah ya bata wani wanda ya dace da ita, amma tun asali ni dama ba wai ina son


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login