Showing 9001 words to 12000 words out of 397328 words
sannan ta fuskanci ƙanwar mahaifin nasu dake sanye da wata irin shadda ɗinkin babban riga, kallo ɗaya za ka mata ita da kayan kasan kuɗi ya jiƙasu, dan kuwa shaddar dake jikin ta kamar za ta yi magana tsabar kyau da yadda zanen ta y tsaru da kuma ɗinkin da aka zuba mata.
Ranƙwafawa Nawal ɗin tayi sai dai bata rumgumo auntyn nasu ba saboda sanin da ta mata yasa suke taka tsantsan da lamarin ta, tunda *Tidin* ta fahimci abinda Nawal ɗin zatayi wanda ta saba ta ɗan juyo mata fuskar ta kaɗan, hakan ya basu damar sumbatar kumatun junan su kowace fuskar ta a sake, sai aunty Tidin da ta ɗora da "Ya kike baby?"
Da fara'a ta amsa da "Ina lafiya aunty."
Da hannu ta nuna mata kujerar kusa da ita tace "Please, seat unjoing us."
Zagayawa Nawal tayi tana faɗin "Thank u."
Zaune tayi ta miƙawa Abrar hannu suka gaisa dan lokacin da zasu fito ita tana waya, haka ma ƴan biyun ta Mannal gaisawa sukayi tana faɗin "My half, how are u today?"
Da fara'a Mannal dake sanye da irin rigar ta sai dai ita kalar ta ta ja ce kasancewar ta fi son wannan kalar ta amsa da "Fine, ke fa?"
Lumshe idanu Nawal tayi alamar lafiya lau, lokacin ne ta kalli Yayan nasu da suke bi ma, yadda yake ta ɗaure mata fuska yasa ta miƙa masa hannu shima tana ƴar dariya kamar mai son sake ƙular da shi tace "Bro, smile now."
Harara ya sake watso mata yana kallon hannun nata fari ƙal wanda akaihun ta ke lulluɓe da jan lalle, kamar ya share ta sai kuma ya miƙo nashi hannun suka gaisa da harshen da ya fi iyawa wato buzanci yace "An ce kina waya, ke da wa yanzu da safe?"
Saida suka raba hannayen su sannan tana juya plate ɗin dake gabanta wanda ke rufe, sannan ta zura hannu ta fara ɗauko faifan wainar flawan da ta ga sauran duk suna ci da miyar hanta da aka yi ban da Anna dake tsaye har yanzu, babbar kwalban nutella ta buɗe ta saka wuƙar shafa butter ta laƙato tana shafawa wainar tana kallon Anna tace " *Sufayya* ce ta kirani Anna, ta min bayani game da makarantar su, gaskiya Anna na fi son zuwa Jericho ɗin."
Humed ne ya sake duban ta yace "Nawal, za ki iya zama New York?"
Kallon shi tayi tana ƴar dariya tace "Sosai ma Yaya, zan iya tunda ai ina tare da my Half."
Ta ƙarashe maganar da kallon Mannal da itama ta kalle ta, hakan ya sa aunty Tidin dake kallonsu tana murmushi cikin wata irin nutsuwa da ajin da jiƙa cikin kuɗi ya ƙara mata tace "Ya dai Mannal? Kin kalle ta, ko ba zaki je can ba?"
A nutse Mannal ta sauke ajiyar zuciya ta ɗauki wani golden cup ta kai jus ɗin ciki bakin ta sannan tace "Zan je aunty, dama ita na ba zaɓi, duk da dai ni Toronto na so zuwa."
Murmushi Nawal tayi tace "My half, za ki je Toronto in sha Allah, tunda mafarkin ki kenan."
Abrar dake sauraren su cikin nutsuwa ta kalli Mannal ɗin tace "Gaskiya sis ba ki iya zaɓi ba."
Kallon Abrar ɗin Humed yayi yace "Ni kuma sai naga gwara nata zaɓin da naki, ni ai sam Brazil ba ta birge ni, zan iya zuwa wani abu muhimmi, amma ban da shaƙatawa."
Turo baki Abrar tayi tana kallon shi tace "Haba dai *couz* (cousin), kai wallahi kasan ba wurin da mutum zai ji daɗin shaƙatawa kamar Rio de Janeiro."
Murmushi kawai yayi da ya ƙara masa kyau a doguwar fuskar shi ya girgiza kai kawai bai ce mata komai ba, Anna *Asalama* da aunty Tidin da suke ta kallon su da farin cikin yadda suke jayayyar tsakanin su su dai murmushi kawai suke yi suna kallon kowane a cikin su, kafin Anna ta kalli Humed tace "Humed, jiya baku yi waya da *chairman* ba?"
Kallon Annan Humed yayi yana murmushi, haka kawai wanda ta ambata ɗin ya ji ya bashi dariya, girgiza kai yayi a ladabce yace "Anna, tun shekaran jiya rabona da shi a waya da ma zahiri, da wata matsala ne?"
Ɗan shiru Anna tayi na sakanni, Aunty Tidin ta kalla da ta ɗauki tissue tana ɗan goge bakin ta a hankali a hankali saboda bata so jan bakin ta ya goge tace "Tidin, ke ma baki da labarin shi?"
Wani kallo auntyn ta mata kamar irin hararan nan saboda jin wani saɓo da Annan tayi, ita ce take tambaya ko ta san inda chairman yake? Ita ɗin wai...? Ta yaya to? Ban da abun Asalama yaron da ko gaisuwar arziki ta ga tana haɗa su ne? Wani sahibin murmushi ta sakar mata bayan wannan kallon da ita kan ta Anna Asalama sai bayan ta mata ta gane abinda ta yi ɗin ta rusuna kallon ta irin kamar ta fahimci damuwar ta mana, cikin tausasa murya a wani gadarance da yanga tace "Ban gan shi ba tun shekaran jiya."
Daga haka ta miƙe tana aje tissue ɗin kan table ɗin tare da ɗaukar wayar ta dake kusa da plate ɗin da ta ci abinci, jakar ta ta ɗauka data saƙalata a hannun kujerar da ta tashi tare da wani ɗan yalolon mayafi irin ƙananun mayafan nan ta ɗora a kafaɗar ta ta dama, kallon su tayi dukan su da murmushin yaƙe tace "Ni zan wuce, sai na dawo."
Ba ta jira cewar kowa ba ta kalli Abrar da ta kasance ƴar ta ta shafi gefen fuskar ta tana mata murmushi sosai tace "My baby, sai na dawo."
Da fara'a Abrar ta amsa da "Bye Momma." A taƙaice ta juya tana faɗin "Bye."
Tun a falon farko wata jami'a mace ta fara take mata baya kasantuwar mai ba wa gwamna shawara ta musamman game da harkokin mata da yara, Humed ne ya kalli Anna yace "Anna ki zauna mana."
Girgiza kanta tayi tace "A'a Humed, fita zamuyi yanzu tare da Abban ku."
Da kulawa Manal ta dube ta tace "Anna, lafiya ko? Da wata matsala ne?"
Girgiza kai tayi dan su kansu basu da tabbacin ba lafiyar ba tace "Ba komai, idan na dawo zaku ji koma menene."
Humed kuma da ya san iyayen nasu basu cika shiga ciwon kai ba duban Annan yayi yace "Anna, ko dai oga ne?"
Nan ma girgiza kai ta yi, amma ba ta ce komai ba ta juya tana faɗin "Idan na dawo zamuyi magana, bana so Abban ku ya barni."
Juyawa tayi a nutse ta bi ta falo na biyu ta shiga ɗakin ta, nan ta ɗauki jakar ta da waya da kuma mayafi sannan ta bi ta ƙofar da zata sadata da ɗakin na shi. Ya so ta yi zaman ta, amma haka ita ma ta tsaya kan za ta bishi dan ta ji me ke faruwa, ta waccen ƙofar suka bi inda motoci manya guda uku masu kyau da masifaffiyar tsada ke jiran su, ɗaya motar dake tsakiya dreba ne sai wani escort dake cikin baƙaƙen kaya da baƙin glass da bindiga dake ƙugun shi da kuma ƙaramin abun saurare a kunne wanda yake sanar da sauran jami'an gidan duk wani motsi da shirin motsawa na gidan da kuma yallaɓan su kasancewar shi shugaban masu bada tsaro.
Anna da Dad na fitowa yayi saurin ƙarasowa gare su yana sarawa, sannan ya ɗan danna abun sauraron dake kunnen shi ƙasa ƙasa yana sanar da jerin gwanon motocin cewa yallaɓai ya fito a motsa, da azama escort ɗin dake motar gaba da ta baya suka sara suma sannan suka tsaya, wannan babban escort ɗin ne ya buɗe musu murfin motar, Anna ce ta shiga ta nan ɓangaren shi kuma Dad ya zagaya ta baya wani escort din ya buɗe mishi ya shiga, sai lokacin babban escort ɗin ya shiga gidan gaba sannan suka fara tafiya. Dad da shi kaɗai ya san me yake ta tunani a zuciyar sa kallon escort ɗin nan yayi yace "Sk, daga jiya zuwa yau komai lafiya a gari?"
Da girmamawa ba tare da ya juyo gaba ɗayansa ba yace "Komai lafiya yallaɓai, ko a bincika ne idan da buƙatar hakan?"
A nutse ya ɗan girgiza masa kai tare da ɗan duba wayar shi yana danne danne, sun kai minti ɗaya kafin suka fita a harabar gidan a hakan ma wai ba tafiya suke a hankali sosai ba, suna fita Dad ya sake kallon escort ɗin nan yace" Sk."
Da sauri da kuma ladabi yace" Yallaɓai."
A sanyaye yace" Mu fara leƙawa ta gidan Aswan, dan mu tabbatar bai kwana gida ba."
Da girmamawa yace" To yallaɓai." Take ya sake danna yatsar sa a kunnen shi yana sanar da motocin dake gaban su da bayan su zasu tsaya nan kusa kaɗan a gidan AA.
Suna tsayawa SK ya fita da sauri ya sarawa basamuden sojan dake tsaye ƙofar gidan yana amsa waya ya tambaye shi ogansu, nan ya sanar masa bai kwana gida ba yana wajen aiki tun jiya, da sauri ya ƙaraso ya sanarwa Hon., hakan ya sake ɗaga masa hankali sai Anna da ta dube shi a nutse tare da ɗan dafa hannun shi dake kan kujerar motar tana faɗin " Please, kar ka ɗaga hankalinka mon Excellence, mu je CEN ɗin mu gani, na tabbata yana lafiya, ina ji a jikina yana lafiya."
Hannun nata ya riƙe shima a hankali bai ce komai ba sai kan shi da ya ɗan ɗagawa alamar to ɗin nan yana kallon hanya har suka ƙaraso compagnie suka samu shigewa ciki bayan sun samu girmamawa tun daga bakin ƙofa.
Da gaggawa aka ƙarasa da su office ɗin Chef, a lokacin da suka shigo yana tsaye ya tarbe su fuskarsa da matuƙar sakewa da walwala ya ce" Barka da zuwa abokina, amma me yasa ka ba kanka wahala ka fito baka tura na zo ba?"
Ɗan murmushin yaƙe Hon. ya yi ya gyara zamansa yana kallo suna gaisawa da Anna a mutumce, kafin daga bisani a nutse ya ce" Yaronka ne, rabona da shi tun jiya, na kasa haƙura dole na biyo baya na ji ko lafiya?"
Har ga Allah shi ɗin ma da zulumi ya kwana, dan ya san shaƙuwar Aswan da mahaifinsa, da ƙyar ya iya rintsawa saboda tunanin ya ya zai sanar masa yana cikin cel? Yanzun ma sai ya ji abin ya sake danne harshensa, amma bashi da yadda zai yi dole zai sanar masa dan ba za'a ɓoye masa ba. A tausashe bayan ya sauke ajiyar zuciya ya shiga sanar masa abinda ya faru, cike da tausarwa ya ce" A lokacin da ya zo gaba ɗaya kowa yana nan, an yanke masa wannan hukuncin ne ba da son raina ba sai dan ya zama dole mu bi ƙa'ida baki ɗayanmu, na rasa ta yadda zan sanar maka ne ya sa ban je ba."
Shiru ne ya fara ɗaukar wajen, a hankali Hajia Asalama ta ce" Kenan yanzu yana cikin prison? Ya salam! Allah ka sanyayawa Aswan zuciyarsa, ko me ya haɗaka da mutum ai ba zaka masa duka uwa d'anka ba, bale a tsofe ya tsofeka ai ana haƙuri da dattijo mai wuyar sha'ani dan shekarunsa ko? Allah ya sa idan ya fito ya ringa jin magana."
Da sauri Dad ya kalleta, sai kuma ya kalli Chef ya ce "Haba aboki, me yasa zaka ɓoye min wannan abin? Ai ba abin ɓoyewa bane, yanzu kwana ya yi cir a cikin cel?"
Jinjina masa kai Chef yayi alamar e a sanyaye, dan haka shi ma ya ɗan jinjina kai irin shikenan ɗin nan, sannan ya numfasa a tausashe yace "Ba laifi, a fito min da shi mu tafi gida, kuma ka san wani abu? Wallahi da ace zaka taimakeni da ka kore shi kwata kwata daga aikin soja, dan ni burina kenan ya bar aikin."
Ɗan tsai Chef ya yi yana tunanin yadda zai sake fahimtar da shi, a tausashe ya ce" Da ace ina iya fitar da shi da na fitar da shi tun jiya ya kwana gida, a yanzu da safiya ta yi ba zai taɓa yiwuwa na fita da shi ta gaban mutane ba, ka ga yanayin aikinmu ai son Excellence, dan Allah ka min uzuri cikin dare a zo a tafi da shi."
Gaba ɗaya sai Dad ya so rikice masu, dan so ya ƙiye masu ya so ya yi kira inda za'a bada umarnin a fitar da shi yanzu yanzu, Anna ce ta hana dan ita bata ga laifi a nan ba, daidai ne a hukunta shi shima, dama ita bata da irin ɗaurewa ɗa gindi ɗin nan, har sai da Dad ya yi fushi ya barta a office ɗin ya nufi motarsa sai da ita suka gama tsaida lokacin ɗauko Aswan ɗin ta fito ta shiga motar ita ma aka nufi gida da su.
Wunin ranar haka ya yi shi ba daɗi, ko abinci bai duba ba ya wuni ne cikin tunanin cel kuma? Da tunanin babu abinda zai maida yaronsa aikin nan, an yi kuma an gama in sha Allah sai dai ya yi haƙuri.
*Ƙarfe* biyu na dare ya shiga ɗaya daga cikin motocin Aswan ɗin suka fita shi da SK da wanda yake shugaban bada tsaron gidan Aswan suka nufi prison ɗin, motar baƙa ce siɗik wacce bullet baya ratsata, idan ana tafiya da ita ba'a jin kukanta sai wani suuu shima ba mai ƙara ba, gudun tsiya ne da ita , hakan ya sa nan da nan suka isa har suka shige suka ƙarasa cen wajen duhu suka faka motar. Tunda suka taso Chef ke fama da Aswan kan ya miƙe ya saka rigarsa yanzu za'a fitar da shi, amma Aswan da lokacin da Chef ya same sa ya yi nisa a wani tunani da sai lokacin ne ya ji yana neman ɗaga masa hankali, batun da Col. Garba ya yi na cewa an wuce da motar asibiti shaƙe da kuɗi kuma motar asibitin mahaifin shi, to me kenan? Wane irin kuɗi? Me ya sa kuma motar asibitin mahaifin shi? Ya yi tsaki ba adadi saboda wani takaici da ya sake lulluɓe sa na rashin wanda zai bashi amsa take, ga kuma wani sabon takaicin da abinda ya mamaye mishi jiki, wato shi da sanyi ba su da amana, sam ba sa jituwa da sanyi, yanzu haka ruwan nan da aka yi na sassafe tunda sanyin ya fara ratsa shi ya haifar asa da rikicewar yanayin sa, komai ƙanƙantar sanyi shauƙi yake saka shi, ko sanyin ac bai cika haye masa ba saboda yanzu zai fara haɗe ƙafafun shi yana damƙe filo kamar ya raba shi biyu. Yanzu da abun ya zo masa babu kaya a jiki, babu filon da zai rumgume ya ji sauƙi, sai ya fara haddasa masa harbawan jijiyoyin dqke kan shi, dan haka ya haɗa kai da guiwa yana dafe da kan nashi sosai. A wannan yanayin Chef ya same shi, amma buɗar bakin AA sai cewa ya yi shi ba zai zama ɗaya daga cikin masu take doka ba, tunda ya yi laifi an hukunta shi a bar shi ya gama cinye wa'adin shi ba zai fito ba, wannan lamari ya saka Chef jin kamar ya sumar da shi ya fitar da shi, amma ma ba halin hakan.
A sukwane ya ƙaraso ya sanarwa Dad abinda yake faruwa, shiru Dad ya yi yana jin har zufa na neman karyo masa, wannan naci da kafiya da Aswan ya yi ba na kowa bane sai nasa, sai dai Aswan ɗin ya dame shi ya shanye, ko da yake shima har da harkokin jama'a da yake yawanta yi wanda yanzu har ya kai yana neman matsayi a siyasance, ga kuma iyali dake gare ka, to wa za ka ma kafiyar? Ba kowane lokaci bane kake yin ta saboda nauye nauyen dake kan ka, shi kuma Aswan ko ƴar soyayyar nan ma ba yi yake ba, yanzu haka ya san in dai ba shi ya gani ba ba zai fito ba, dan haka ya sauko da farar jalabiyarsa ya bi bayan Chef suka nufi ciki suka ɗauki hanyar wajen da Aswan yake. Da ƙyar Dad ya ɗaga ƙafar sa ya ɗan haura da ita ta matakalar shiga ɗakin wacce ke yanayi da dangarama, kan shi a sama yake yana son a sakanni ƙalilan ya fahimci yadda ɗakin yake, sai dai Dad sai da ya ƙara cilla kan shi sama sosai kafin ya iya hango ƙarshen ɗakin da wata mitsitsiyar window a can manne sama, yana gama shiga ɗakin da salallamin da yake yi a zuciyar sa wani irin mugu mugun zafi ya masa marabar da ta nemi dakatar da numfashin shi na wucen gadi, da wani irin oder da ba zai i ya tantance na miye ba yake shaƙa a hancin sa. Kasa ƙarasawa yayi yana ta jujjuya kai yana kallon ɗakin, kwatsam sojawan dake cikin ɗakin masu ladabtar da fata irin ta su Aswan da ta saba da hutu suka kawowa Dad farmakin da sai da ya ɗan zabura ya juya tare da kai wa kunnen nashi tafi da niyyar bige abinda zai iya cewa a rayuwar sa ma idan ba a labarai ba ya manta rabon da ya ji sunan sa, to duk dare na Allah ba iya fadar sa ba kawai, gaba ɗaya unguwar tasu ta masu faɗa a ji ake fesheta da maganin sauro da ƙwari, ga ma'aikata dake kula da gida ba sa barin wata kafa da wani fitsararren sauro ma zai shigo musu gidan bale su ji kukan nasa.
A rikice Dad ya lalubo wayar shi ya haska fitila dan son sanin in da Aswan ɗin yake saboda duhun ɗakin, ƙaraswa ya yi kusa da AA dake zaune yana ɗan ɗago kan shi saboda ganin hasken fitila yana lumshe idanu, Dad da ya kula ya haske masa idanu yasa ya dan kawar da hasken fitilar, take Aswan ya gane wa ye gaban shi tsaye a ran shi yana ayyana _"Me ya zo yi nan?"_ Bai wani gyara zaman shi ba dan gaskiya ma kunyar miƙewa yake ji da yanayin nan nashi gaban Dad ɗin, sai Dad ɗin ne ya taka gaban sa da tsantsenin ɗakin ga kuma duhu ya isa gaban shi, da ƙyar