Showing 108001 words to 111000 words out of 397328 words
matakan, sannan bayan duk wannan dole idan za ka fita da shi ma ku tafi da nurse wacce za ta dinga kula da ɗawainiyar sa acan, a irin wannan aikin haka ƙa'idar take."
A shashance AA yace" Ba zamu iya ɗaukar mai kula da shi ɗin ba a can?"
Murmushi Dr. Siddik ya yi yace" Su kan su tambayar farko da za su muku ita ce, ina rahoton lafiyar? Kafin su sake yi masa wasu gwaje gwajen, sannan su tuntuɓi ji daga bakin likitan da ya fara duba shi ko kuma nurse dake jinyar sa."
Sai kuma ya gyara zama yace" Wannan ba damuwa bane, kamar yadda nasan ba zai zama damuwa a wajen ka ɗaukar nauyin fita da mai kula da ɗan ka ba, idan kana so zamu iya baka nurse ɗin anan idan baka da."
Kallon Dr. Siddik ɗin ya yi ransa a jagule na cewa sai nan da sati biyu ko sama da haka zai fita da ɗansa nema masa lafiya, a taƙaice kawai ya tambaye shi da" Zan iya ganin shi yanzu?"
" E, bismillah..." Dr. Siddik ya faɗa yana miƙewa tsaye, tare suka fita suka kuma nufi ɗakin da Safwan ɗin yake.
Kamar yasan zai same shi yana fuskantar ƙofar ya buɗo ƙofar da murmushi a fuskar sa, Safwan ma dake zaune yana shan cream jin an taɓa ƙofar ya kalla, yana ganin AA ya saki murmushin dake nuna tsantsar farin cikin ganin sa, rashin ƙafafu ya hana shi saukowa daga kan gadon ya tarbe shi, amma saida ya aje robar cream ɗin ya ɗan jawo ƙugun shi kamar zai sauko yana faɗin "Dadyna..."
Wata irin narkakkiyar ƙaunar yaron ta sake huda zuciyar Aswan tare da ji har ƙoƙon ran shi kamar ɗan da ya haifa ne a cikin sa, da mugun sauri ya ƙarasa ya zauna bakin gado ya rumgume Safwan, cikin farin ciki yana shafa bayan shi yace "My lovely son, ya ka ke?"
Saida Safwan ya kalle shi kafin yace "Lafiya lau Dady, ka dawo? Ka zo lafiya? Ka yi nasara ko?"
Wani tattausan murmushi ya sakar masa jin tambayoyin da yake masa da ko babban mai hankali iya abinda zai iya yi kenan, jinjina masa kai ya yi yana shafo kuncin shi yace "Lafiya lau na dawo my boy, kuma addu'ar ka ta bini har gurin aikina."
Faɗaɗa murmushi Safwan ya yi bai ce komai, AA kuma ya tsura masa idanu yana kallon kyakyawar fuskar Safwan da sai yanzu ne hasken shi da kyawun nashi suke ƙara fitowa ka rantse ba'a gadon asibiti yake ba, a hankali ya ƙarewa jikin sa kallo da ma ɗakin, take zuciyar sa ta raya mishi lallai Aba da Anna sun riƙe masa ɗan sa amana...
Kamar yasan me yake tunani sai kuwa Safwan yace "Dady, yau Granny bata zo ba, sai anjima za ta zo?"
Da ɗan mamaki AA ya kalle shi yace "Granny?"
Ɗaga masa gira ya yi da ladabi yace "E, kakata, ita ta faɗa min ita ta haifeka, ni kuma jikanta, shine ta ce sunan ta Granny tunda ni ɗan ka ne."
AA dai ban da murmushin farin ciki babu abinda yake yi har ya dasa aya sannan ya laƙace hancin shi yace "Hakane wannan, nasan kuma anjima Grannyn ka za ta zo duba ka."
Murmushi ya yi na jin daɗi, sai AA da ya kalli cream ɗin da Safwan ɗin ya aje gefen shi, sai kuma ya kalli Dr. Siddik da har lokacin yake tsaye bayan AA yana murmushin ganin su a haka yace "Siddik, zaƙi ko sanyi ba zasu mishi illa ba?"
Girgiza kai Dr. Siddik ya yi yace "No, da yake ma ba ma yarda su bashi dangin abubuwan nan, yau ma ya nuna yana so ne, shine auntyn tasa ta roƙi alfarmar mu bar shi ya sha sau ɗaya ne ai."
Da mamaki ya kalli Dr. Siddik ɗin sannan ya kalli Safwan yace "Auntyn ka? Wacece? Ita take kawo maka?"
Da fara'a Safwan yace "Aunty Abrar ce, kullum sai ta zo da safe ta kawo min kayan daɗi, har da sandwich na makarantar su mai daɗi shi ma."
Da matsanancin mamaki Aswan ya maimaita sunan a laɓɓan shi "Abrar?"
Ɗaga masa kai Safwan ya yi alamar e tare da cewa "E Dady, da ita da su aunty Manal, da uncle Humed, dukan su suna so na, ba ma kamar aunty Abrar, kuma ko Dady, duka ƴan gidan ku masu kyau ne kuma farare... Amma dai..."
Sai kuma ya yi shiru, hakan yasa AA dakatar da tunanin da ya fara lulawa na cewa Abrar na zuwa nan kuma wai tana ƙaunar ɗan sa, anya hakan zai yiwu? Yarinyar da ta fito daga tsatson Goggo Tidin? Yarinyar da ina kwana ina wuni kawai ke haɗa su?
Maganar Safwan ta saka shi murmusawa da cewa "Amma me?"
Cike da kunya ya saci kallon Dr. Siddik sannan ya ma AA raɗa a kunne yace "Kafi kowa kyau."
"Da gaske?" Cewar AA yana masa kallon tuhuma, jinjina masa kai ya yi alamar e, dan haka suka rumgume juna da farin ciki. Dr. Siddik ne ya dubi AA yace "Aswan ni zan kom office, idan akwai wani abun sai ka tuntuɓeni."
Jinjina masa kai ya yi ya amsa da "Shikenan, na gode." Ya fice daga ɗakin ya bar su cikin nishaɗi kamar ɗa da uban gaske ko wanda suka kwashe shekaru tare suna ta hirar su.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*29*
Tunda Nabihat ta dinga noƙe kai alamar jin kunya sa'ilin da ta mata magana ko dai tana son Aswan ne? Sai kawai ta yarda e ƴar ta tana son babban mutumin da ba zata yarda ta ce ya fi ƙarfin ta ba, sai dai ta ce tabbas ta yi babban kamu da dole sai sun fara hayaƙi saboda magauta za su iya shiga maganar su ɓata.
Cike da tabbaci ta faɗa mata za ta sanar da Abban ta yau yasan halin da ake ciki, Nabihat kuma da take ganin kamar tarkon ta zai kama kurciya ne sai ta yarda da hakan har take ganin ai idan iyayen su ne suka shiga maganar bai isa ya musa ba zai karɓe ta a tsamayin mata ko ba ya so, ita kuma dama a shirye take ta zauna da shi ko yana son ta ko baya son ta, indai za ta wayi gari ta ga kyakyawar fuskar sa, sannan ta zama ita ce mafi sanin ƙololuwar sirrin sa, to dan so ba matsalar ta bane, shi ma so ɗin wata rana zai nuna mata shi.
Da fuskar damuwa ta sake duban mahaifiyar ta ta da ta ga kamar ma ta fi ta farin ciki da jin wannan labari tace "Mamma, ni fa matsalata da Yaya AA shi ko kula mutum ma ba ya yi, kuma kinga sai in je gidan amma har ka dawo ba ka gan shi ba, ni ban san ya zan yi ba."
Cike da kissa mahaifyar tace mata "Ke kwantar da hankalin ki, Aswan duk safiyar Allah in dai yana garin nan kuma a cikin hayyacin sa yake to rana bata fitowa bai je ya gaishe da iyayen sa ba, sannan rana bata faɗuwa har dare ya raba uku bai je ya musu sai da safe ba, dan haka ta nan za ki yaƙe shi."
Da rashin fahimta Nabihat tace" Kamar ya kenan Mamma?"
Da murmushin mugunta a fuskar ta tace mata" Gidan za ki je ki zauna na kwana biyu tunda ana hutu ne, jiya da mukayi waya da Hajia Asalama take sanar da ni tana asibiti ganin ɗan Aswan, s..."
Da alamar tashin hankali Nabihat ta zaro idanu tace" Ɗan AA kuma? Daga ina? Yake da bamu sani ba?"
Murmushi Mammar ta yi tace" Nima tambayar da na mata kenan, ashe wai adopten yaron ne ya yi saboda ba ya da kowa, kinga wannan yaron zai iya zama makamin da zaki yaƙi zuciyar shi, idan kika je gidan ki riƙe kowa da kulawa har da shi kan shi matsiyacin yaron da ya tsinto ya kawo, burinmu dai ki samu shiga fadar sa ne ai."
Dariyar jin kunya Nabihat tayi tace" wallahi Mamma shiyasa kike birgeni, ni dama tun ranar da naje gidan ai da na wa Abrar maganar sa naga kamar ita ma son shi take ko me dai oho, na yanke shawarar zan yaƙeta ta hanyar girmama duk wanda yake girmamawa kamar zan bauta musu, dan ita na kula banza ce."
Dariya Mamma ta yi tace" Gaskiya ne, kuma kinga ai dama Tidin ba sa shiri da shi, idan dai ba dan matsiyatan kuɗi da yaron yake da su ba, bana jin akwai abinda zai sa Tidin ta yarda da auren su."
Cike da shaƙiyanci irin na yaran zamani Nabihat ta miƙe da gudu tana haurawa sama tana faɗin" Har na fara jin ina ƙamshin amarci Mamma."
Dariya ta yi ta bita da kallo tana ɗora ƙagfa ɗaya kan ɗaya ta ɗauki wayar ta da niyyar kiran Anna dan kawai su gaisa dan ita kanta bata ga ta zama ba sai tana kama ma ƴar ta ta ko zasu zama zama a fadar mutanen nan.
*WASHE GARI*
Washe gari, kusan ƙarfe tara Hajia ta fita da niyyar tafiya makarantar yaran Jafar da kuma biyawa gidan rasuwa ta yi gaisuwa sannan ta je gidan amarya ta ga ɗaki ta dawo, hakan ya sa ta tafi da dreba ta bar su Yusrah na faman shirya gidan.
Kusan ƙarfe tara na safe JAFAR ya zo ɗauke da akwatunan yaransa, kana ganin fuskarsa ka san barci dai sai dai ɓarawo in ya samu a jiya, yana zuwa Fatila ta ringa kai kayan ɗakin Hajia, Yusrah kuwa bayan ta gaishe shi ita ma ta gabatar masa da kayan karin da suka karya harda su shayi sannan ta koma kicin ta ci gaba da feraye doyar da take yi dan ta san Maryam gwanar cin doya ce, ita kuwa tun ɗazu tace ta fito dan tace dama sammako zata yi su sha fira kafin ta wuce gida.
Tana tsakiya da aikinta Fatila ta sauko da waya a hannunta ta ce" Yusrah, bari in leƙa ina ga Maryam ɗin ta ƙaraso, ki bar wa mai aiki aikin nan ki zo falon mana."
Yusrah ta kwashe doyar da ta zuba cikin mai dan ta soyu ta yi ɗan murmushi ta ce" Ai na ƙare fa, bari in juye sai in zo, ki tarbota sister."
Da to Fatila ta amsa ta wuce, ta so ta fito ɗin tun tana nan dan Yayansu ya jima da gama karyawar amma yana zaune bai tashi ba, kuma bai ce komai ba dai amma hankalinsa gaba ɗaya a kan kicin ɗin, ta tabbata da zai samu ganin Yusrah tabbas da sai ya aikata aikin da take addu'ar ya kasantu a tsakaninsu wato sharar fagen kasantuwa aminan juna a ƙarƙashin kulawar inuwa ɗaya.
Bayan fitarta a nutse Yusrah ta juye komai cikin flask sannan ta shiga ɗauka da ɗaiɗaya da nufin kaiwa kicin, domin tunda ta zo gidan nan ta gane mai aikin nan akwai aikata goshi, idan a gaban Hajia ne kamar ta goyi Yusrah, a bayan idanuwanta kuwa ita da kanta ta san ko aiki ta saka ta da wahala ta yi mata, shi yasa ba ma ta gigin sakatan, dan irin kallon da take bin ta da shi ma baya wani yi mata daɗi, ga kallo irin na wuce misali ga kuma kallon raini da take binta da shi.
Tana kai kular farko saman table zata koma yaya Jafar ya yi ƴar gyaran murya ya ce" Yusrah zo mana?"
Yusrah ta juyo ta ƙaraso ta dan duƙa dan bashi girma ta amsa, a nutse ya ɗan sake muskutawa ya ce" Nace ba, a wani mataki kike a makaranta ne? Dan ina son ki koma karatun ki, sannan ki shiga islamiyya ko kanwata?"
Yusrah ta ajiye ajiyar zuciyarta da take neman zame mata jiki, a hankali ta ɗan ɗago dan yin magana ta hangi mai aikin Hajia laɓe tana kallon ta, kai ta ɗauke a sanyaye ta ce" Yaya na yi karatun jinya, technicienne superieur ce na soin obsetrical , daga nan dai na tsaya."
Da mamaki ya ce" Wow! Ma sha Allah Yusrah, da ke likita ce? Likitar ma mai daraja? Likitar yara masha Allah ƙanwata ki ce zuwa gaba ƴaƴanmu ba sai mun kai su sun bi layin ganin likita ba?"
Maganar ta zo mata wata iri, hakan ya sa ta ɗaga da ɗan sauri ta kalle shi, daidai lokacin da su Fatila da Maryam suka shigo da sallama, haka kuma a lokacin su Arifa suka fito a guje suna faɗa, ganin mahaifinsu ya saka Arifa ƙarasawa da abin dukan dake hannunta ta ce" Abba, ka ga Mimi ta dake ni? Ta tsaya in rama ko in ci ubanta yau a gidan nan."
Da sauri Yusrah ta kalli yarinyar, hakama Maryam dake rage tsayi ta gaisar da Yaya Jafar, shi kuwa ganin kamar sun cika da baƙi ya miƙe ƙasa ƙasa yana faɗin" Arifa, ku daina faɗan nan, kuma ki daina zagi kin ji? Bari in je sai na dawo, me zan siyo maki?"
Ba addu'ar a dawo lafiya Abba ba komai suka shiga zayyane abubuwan da suke so a siyo masu, ba wai zayyanewar ake nufin laifi ba, ko ya ya mace kike da ƴaƴanki yana cikin yankin tarbiyyar da zaki ba yaro ki koya masa yiwa mahaifinsa addu'a idan zai fita, ki koya masa yi masa sannu da zuwa da gaisar da shi da amsar abin hannunsa, wannan kuwa idan ke kina yi ba sai kin saka yaron ba zai ɗauka matsayin abinda ya zama ruwan jiki, in ba'a yi ba har ba za'a ji daɗi ba.
Ita dai Yusrah kunya da nauyi suka sakata sunnar da kanta har ya fice bayan sun gaisa sosai da Maryam yana yi mata sannu da zuwa harda ƴar tsokanarta da cewa baƙuwarsa ce tunda ta Yusrah ce.
Yana fita da sauri Fatila ta ƙaraso tana dungure kan Arifa ta ce" Ke dilla ku je Ku yi wankan nan tun kafin in zane ku kun ji ko? Hajia Yusrah sai ki miƙe mu saka labule."
Irin cike da farin ciki da zumuɗi take son ji daga Yusrah, a lokacin da Yusrah ta miƙe suka rungume juna da Maryam dake yiwa Fatila dariya , daidai lokacin ne Arifa ta buɗi baki ta ce" Allah ya isa da kika dungurar min kai yar ƙaniya kawai!"
Ɗif falon ya ɗauka, mai aiki dake jira a sanar da abinda take jira dan ta yi kiran Hajia Tasneem ta sanar mata komai kamar yadda suka yi jiya da dare kafin ta tafi ta zaro ido it ama daga inda take ta juya ta je ta ɗauko abin tarbar baƙo ta fito ɗauke da faranti ta ga suna tsaitsaye ne tamkar an dasa su tashin hankali da mamakin furucin yarinyar da ta kai shekara tara ba yarinya ƙarama ba ba kuma mahaukaciya ba tsabar sangarta da rashin kwaɓa da yi a gaban yaro ya sa ta dubi auntynta ƙanwar mahaifinta wacce tana iya haihuwar ta da cikinta dan shekarunta sun kai ta haifeta ta bita da Allah ya isa ta ƙarashe da zagi.
Jiki a mace Maryam ta zauna dan sun kasa ce mata ta zauna tsabar firgici, ajiyar zuciya Yusrah ta sauke ta ƙarasa ta zauna daf da Maryam da ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana jiran hukuncin da zasu yiwa yarinyar dan wallahi wallahi idan basu daki hancin yarinyar nan ba yau ita zata daka sai dai a haɗata da hukuma.
Rai ɓace Fatila ta ce" Ni kike zagi Arifa?"
Yarinyar kuwa ido bushe da rashin kunya ta ƙi tafiya ta ƙi daina kallonsu ido cikin ido ta ce" Yo ba ke ce kika dakar min kaina ba?"
Fatiha ta gyaɗa kai tana kallonta ta ce" Dan na dungure maki kai shine zaki zage ni?"
Da ƙiririta ta tare Fatila tana faɗin"A'a ke ai ba babata bace, babata na gida gaskiya kuma du wanda ya dake ni sai na zage shi kuma..."
Har ga Allah Yysrah bata ga tashin Maryam ba sai saukar duka da ta gani Maryam na yiwa ƴar mutane, y'ar mutane jama'a ƴar da yau yau ta taɓa ganinta yanzu yanzu, hannayen yarinyar ta kama ta murɗe ta tafka mata duka mai zafin gaske da ƙarfi ta ce" Ke marar kunyar ina ce? Mu zaki saka a gaba kina zagi? Yau ga rashin mutumci, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, rufe min baki kar na karya ki a nan, sa'aninki ne mu? Ke marar kunyar ina ce zaki dubi wannan ki zageta? Ita ma ta haife ki tace ta haifi me? Risina min muryar ki a nan kar in karya ki, subhanallah subhanallah!"
A rikice Yusrah ta ƙaraso ta shiga kokowa da Maryam tana faɗin" Maryam saketa, ke Maryam."
Maryam ta warce yarinyar bayan Yusrah ta karɓeta ta kama kumatunta ta matse ta zaro mata ido ta ce" Ke, idan na kuma