Showing 228001 words to 231000 words out of 397328 words

Chapter 77 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69995

yin dariya sun zo daidai mota zata yi magana ta hangi Bilal na tahowa, dakatawa ta yi tana kallonsa haɗi da sakar masa murmushi kamar yadda yake ta ƙawata fuskarsa da murmushi hannayensa cikin aljihun wandonsa yana nufo su.

Nabihat ce ta ƙarewa fuskar Yusrah kallo, ta sauke dubanta har zuwa yan ƙafafuwan Yusrah, kai ta ɗauke ranta na cinkushewa ta juyar da dubanta ɓarin da Bilal ke ƙarasowa tana kallonsa har ya iso, irin murmushin da yake sakarwa Yusrah, laushin da idanuwansa suka yi a kanta, tarin ƙaunar da yake sakar mata a bayyane, irin ni'imar walwalar dake fita a fuskarsa dan kawai ya ganta suka saka Nabihat zuba masu ido da kunne ba ko ƙyaftawa dan tana son jin wace irin fira suke yi ita da shi idan sun haɗu?

A tausashe ya ce" Rayuwar Bilalu, ina zaki je ban ganki ba?"

Murmushi ta sake sakar masa a hankali ta ce" yaya Bilal kar a ji kana faɗin sunan nan fa."

Ya yi ƴar dariya ya juya wajen su Abrar da suka ƙi ƙarasowa suka tsaya daga can baya dan su basu fili ya ɗan ɗaga murya ya ce" Zaku tafi min da mata me kuke nufi ƴan matan Anna?"

Manal ta ce" Yaya Bilal ai bamu baka ba tukunan, kuma Anna tace ƙafar ta ƙafarmu."

Ya zaro ido yana faɗin" Ni me na yiwa ƴan biyu ne? So kike in haukace? Ke ina iya zarewa a kan yarinyar nan fa."

Wani irin bala'i da ya tokare wuyan Nabihat bata san lokacin da ta juyar da kanta ta saki wani tsinanen tsaki ta danna masu horn dan ky ɗin motar a hannunta yake tana tuƙi cike da yanga haka suka zo.

Da mamaki duk suka kalleta, yanayinta ya fassara abinda ke zuciyarta, har Nawal zata yi mata magana Abrar ta mata alamun a'a, suka nufi motar su dukansu, da kula Bilal bayan ya kalli motar ya taɓe baki ya ce" Ki bari in kai ki gida."

Yusrah ta ɗan sinne idanuwanta a hankali ta ce" Ka yi haƙuri, umarnin Anna yana da girma sosai, ba zamu take ba, sai mun yi waya Yayana."

Bilal ya ɗaga mata hannu bayan ya buɗe ta shige gaba, domin kusan su duka baya suka shige suka bar gaban ba kowa dan basa son irin yannayin da Nabihat ke yi ɗin nan, gashi ana ƙishi-ƙishin wai aurenta da Yayansu, hum lalle! Da sun bani a gidan nan, dan yanayinta ya nuna za'a kwasa da ita a kan abinda bai taka kara ya karya ba ma balle babban abu.

Baƙar abayarta ya gyara da kyau, sannan ya sake zuba mata ido a hankali ya ce" I love you so much."

Yusrah ta yi gaggawar ɗora kanta saman cinyoyin ta, ƴan matan kuwa suka kwashi dariya suna zuzuta abin irin dai suna ganin soyayya, ya dai shirya dan ƴar uwarsu mai tsada ce ɗin nan.

Motar ta figa ta yi waje ranta ɓace, wani irin tuƙi ta yi da su mai gudun tsiya, tana yi tana tsaki kamar ta hɗiyi tsaka har suka ƙaraso gidan, suna zuwa ta kasa riƙe ɗacin da ranta ke yi da ta buɗe zata fita ta ce" Aikin banza, ko ya ya ka yi da jaki sai ya ci kara, duk irin yadda za'a nuna mana wayayyu ake sai an ga ƙauyanci, wai soyayya, mu an nuna mana soyaya? Aikin banza ƙauyancin banza da wofi."

Ta gama faɗan ta ta mako ƙofar ta yi cikin gida, shiru ya ɗauki motar na ɗan lokaci, sai kuma Manal ta katse shirun tana faɗin" This girl bata da hankali ko kaɗan amma ko? Me yake damun ƙwaƙwalwar ta ne? Wani ya taɓota ne?"

Nawal da ita ma abin na Nabihat ya fara bata haushi ta ce" Wa kuwa zai taɓota? Ai ƙafar ki ƙafar ta tare muka je muka dawo, ina ga tana da damuwar maganar soyayya ne, ta ga soyayya ganin idanuwanta ne hankalinta zai tashi, in dai Akhi ne shi zai koya mata hankali, soyayya irin wannan kuwa bana tunanin zata samu da Akhi dan ban ga alamu ba, kamar fa in ta wuce taɓe baki yake yi kamar ya ga kashi."

Yusrah ta ɗauke kanta daga maganar su ta buɗe motar ta fito cikin baƙon yanayin da ya ziyarce ta haka kawai take ji a ranta ai wannan ita ma bata dace zamowa sarakuwar Anna da Aba ba, mutane masu daraja mutum, masu son mutum, masu mutunci da karamci? Kai ba ta ga matar ɗansu a tare da Nabihat ba saboda irin yanayinta na wulaƙanci da ƙasƙanci da fitina kala kala dai, ko da yake, shi ɗin ma mijin nata ai baya jin magana, komai nasa dama ba irin na mutane bane, ire iren tunaninsa sam ba irin na mutane bane, dan haka sai ta basar tana duban su ta ce" Mu je please, kin ga cicin din da za'a yi da cake ni dai na zaɓi cake gaskiya."

Ai fa da wannan gardamar suka nufi falo suna ihun baki isa ba tare za'a yi, irin dai cacar baki idan an haɗu cikin ƴan mata, suna shigowa Anna na riƙe da tire shaƙe da kayan tarbar baƙi ta sakar masu murmushi ta ce" Ai fa, to sannun ku, Yusrah kama wannan maza mu je ɓangaren Babanku kin yi baƙo, ku kuwa sai ku je ku yi wanka ku shige kicin, girkin nan na Aswan ne sai ku maida hankali ku lalata wani abin ta yadda zai same ku, sannan ku fitar da abincin Goggonku tana hanya daga mission ɗin da ta tafi."

Su duka da kallo suka bita suna mamakin baƙo kuma? Dan a ganinsu yanzu suka baro Bilal a gida ai, baƙo kuma a kusa kusa shine kawai wanda zai zo nemanta kai tsaye, shi ne aka yarjewa ganinta shine aka ba ita.

Manal ta karɓi wayarta tana ɗaga kiran Maryam ta shiga amsawa dan a cikin su babu wanda bai san Maryam ba, sun saba da ita sosai, a ziyarar da ta kawo masu kuwa sun sha fira kamar ba gobe, dama a cikin su Nawal ce kaɗai bata da saurin sabo saboda ita ma tana da ɗan faɗa da saurin hawa, sai Yusrah, Yusrah kuwa ƙawarta ce ai ta zo ba zancan rashin sabo.

Ita ce a bayan Anna, bayan sun shigo ta kai tire ɗin ta ajiye sannan ta tsuguna ɓarin da su Aba suke sai a yanzu ta ɗago ta gaishe da Aba, sannan ta dubi baƙon da take ta tunanin baƙo kuma? Ita kuma?

Turus ta yi tana kallonsa ƙirjinta na dokawa, uncle Sulaiman? Ya Allah! Kamarsa da mahaifinta har ta ɓaci, shi ma farin hankicief ɗin hannunsa ya saka yana share hawayen idanuwansa, tunda ya zo ya samu ganin Aba suke zaune suna tattaunawa, jiya zuwansa gidan su Bilal na uku ne bayan Maryam ta kai shi gidan Hajia maman su Jafar kamar yadda ya buƙata ta fara kai shi inda aka fara riƙe Yusrah ɗin, Hajiar ta kai shi, suka taki sa'a Jafar na nan ya mayar da Maryam ɗin gida, sai shi kuwa suka zauna da Hajiar ya ji duka abinda ya faru har zuwa inda take, ya buƙaci a kwatanta masa gidan su Bilal saboda ya fara yiwa Yaya Mubarak godiya, sai dai ya ringa takar rashin sa'ar tarda Hajia ita kaɗai, ita kuwa ta nuna bata ma san zancan ba, yaronta kuwa baya nan, sai jiya da dare Allah ya taimake shi ya samu yaya Mubarak, tun a jiyan ya so ya kawo shi ya nuna masa dare ya yi amma yau sai su zo, shine ya rako shi tunda sassafen nan dan tunda ya yi sallar asubahi ya nufi gidan shine ya rako shi ya samu ganin Aba shi kuwa ya juya gida, shi ne suka zauna da Aba suke ta tattaunawa sosai da sosai a kan lamarin yaran har yadda aka yi AA ya samu Safwan da yadda aka yi aka ba AA Safwan matsayin ɗan sa da fitar da shi dai har zuwa yanzu.

Idanuwansa sun yi jajir dan hawayen da ya sha, yana kallon Yusrah ya miƙa hannayensa ya ce" Zo, zo nan ƴar papa."

Dukda ƙananun shekarunsa tun suna yara in dai zai yi magana da su ta wayar mahaifinsu sai ya dage su ringa ce masa papa, shi yasa suke faɗa masa haka ɗin suma har suka saba, wai ace yana raye, a cikin duniya, a zamanin waya, ya rasa ɗan uwansa, da matar ɗan uwansa da ƴarsu guda Hinda ta ƙi sanar masa? Anya zai iya yafewa Hinda kuwa?

Yusrah da rarrafe ta ƙarasa ta jinginar da kanta ga ƙafarsa ta fashe da kukan kamaninsa da mahaifinta da kuma irin tarbar da ya mata, wacce ta sakawa ranta cewar tana ganin ba zasu taɓa ganin fara'a a fuskar dangin mahaifi ba, shi kuwa dama ta shafe shi a tunaninta, gani take yi wacce ke kusa ma ta ƙi su ina wanda ke tsinlurun wata ƙasa aiki? To ya so su ya yi ya ya da su? Hinda dake da sana'ar yi da kuma iyali ta nuna su ɗin wahala ce za'a ɗora mata ina wanda bashi da iyali? Shi yasa bata kawo shi ko kaɗan a cikin lamuranta dan ma kar ta sakawa ranta abinda ba zata taɓa samu ba.

Anna ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce " Daughter, kukan ya isa hakanan kin ji? Ƙanina ku yi haƙuri da kukan hakanan, Allah ya jiƙansu ya sa sun huta."

Sai kuma ta kalli Aba a tausashe ta ce "Aban yara, bari in je in saka a kai Nabihat gida, idan kun gama ka min magana please."

Aba ya bata dama sannan ya maida hankali kansu da kula ya rarrashe su har kukan ya yi sanyi, a hankali ya kama hannunta ya miƙar da ita ta zauna ɗan gefensa dan zai fi jin daɗi a haka.

A tausashe sosai yana kallonta zuciyarsa cike da tunanin ya ya ta yi ta iya kaiwa yanzu? Ya ya ta yi ta haɗiye duka wannan tashin hankalin? Ga maraici, ga wahalar neman abinda za'a yiwa ƙaninta aiki, ta samo ɗin ta zo ta tarda ƙanin baya nan, ta shiga kuma wahalar neman sa? Yau da ace bata haɗu da bayin Allahn nan suka taimaketa ba da yanzu tana ina tana me? Tabbas ƙadararta mai zafi ce, sai dai Allah na tafe da ita da sanyaya mata a duk inda ta faɗa.

A tausashe sosai ya ce" I'm sorry angel, i'm so sorry..." Sai kuma hawaye shar shar.

Aba ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Haba mana ƙanina, idan ka yi kuka ita ta yi me? Tunda na ji labarinta na yi kashedin kar wanda ya rayu da ita da tuna mata damuwarta ko ya ringa sakata a gaba suna yin kuka, Alhamdulilah ta samu ta tsallake abubuwa da dama, yanzu ba sai hamdalah ba? Tabbas an kai wajen hamdalah tunda ta san inda ƙanin ta yake kuma gata lafiya, ka yi haƙuri please kar ka tuna mata ciwon dake zuciyarta."

Uncle Sulaiman ya sauke ajiyar zuciya yana riƙe da hannunta dake cikin nasa muryar sa a shaƙe na abin kukan, sai dai da jarumta tare da ita irin ta maza ya ce" Yaya ka yi haƙuri, na jima da kukan nan a zuciyata, ban samu yi ba tunda na zo na yarda Hinda tana sha'anin ta da ƴaƴanta ta dube ni ta faɗa min rubish a kan ƴaƴan ɗan uwanta zuciyata ta yi nauyi, ta yi nauyi sosai, da ace ban samu mqmbar mai kantin da Yayana ke kirana da shi ba wani lokacin da har yanzu ban san takamaiman Yayana ya rasu ba kenan? Ni kam Allah ya isa...''

"Kar ka yi mata Allah ya isa, ka mata uzuri ka yi mata addu'ar shirya please, ai gashi Allah ya tsare su ko? Kuma Allah ya sa snna lafiya ko? Ka ga duk wani gata ai Allah ne ke yi ba mutum ba." Aba ya katse shi yana sake kwantar masa da hankali.

Ya jima yana ajiyar zuciya kafin ya dubi Yusrah ya saki murmushi ya dubi Aba a tausashe ya ce" Ban san irin godiyar da zan yi ba, gatanan cikin hayyacin ta, cikin shiga ta musulunci, tabbas tana hannaye masu kyau, kun min komai Allah ya saka da alkairi."

Aba ya yi murmushin shi ma ya ce" Amen ya Allah, ƙwarai wa'inda suka riƙe ta kafin mu ma sun yi domin Allah, dan da muka santa mu bata da matsalar komai, Allah ya ƙara mana masu tsoron sa a cikin duniyar nan."

Shi ma ya amsa da amen, sai ya ɗan sarara a hankali yana sosa kansa ya ce" Aba, nace ba, anya kuwa shi Dad ɗin na Baban gidanmu zai bani shi kuwa? Dan so nake yi in tafi da su."

Aba ya ɗan dube shi da mamaki yana kama baki da kuma sigar wasa yace" Wai mu Baka me? Haba dai, to ai ba wai jikan Anza ya baka jikana ba, ko ni ba zan baka jikan ɗan Aliyu ba gaskiya, dan babar sa sai da ta faɗa min faran faran cewar a kan ƴarta tana iya yin komai fa?"

Shi ma yana dariyar da abin dariyar Aba dan a yanayin da yake yin maganar yana nuna kansa har ya gama sai kuma ya saka yanayin serieus ya ce" Ba kace baka gama ginin ka ba?"

Uncle Sulaimane ya gyaɗa kansa a tausashe ya ce" Eh Aba, amma abinda ya rage kaɗan ne, dan za'a iya zama ma idan ta kama dole."

Aba ya gyaɗa kansa a tausashe ya ce" Ka na da sha'awar zama anan ne gaba ɗaya ko?"

Uncle Sulaimane ya gyaɗa kai ya ce" Ƙwarai da gaske, harkar takalma da jakunkuna da nake yi nake so na kafa anan."

Aba ya gyaɗa kansa yana fahimtarsa sosai, sai kuma ya fuskance shi da kyau ya ce"...



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
06/06/2024, 09:22 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*58*



Aba ya gyaɗa kansa yana fahimtarsa sosai, sai kuma ya fuskance shi da kyau ya ce" Malam Sulaimane, zan so mu yi magana ta fahimta sosai, wacce idan mun yi in ka ga kana kan batun ka na yaran nan su bi ka, ba damuwa da kaina zan ga Jikan Anza, ko da baya so na tirsasa shi dan ya ɗauki yaron nan ya baka, ni kuma in haɗa maka da Yusrah, saboda ko ba komai kai ne shaƙiƙin su, a yanzu kaf duniya basu da kamar ka, ko wani irin gata za'a nuna masu kuwa bayan naka ne da ganinka a gefen su, kamar yadda na yi maka maganar ma-nemin aurenta ya fito, kuma na bada dama har ma mun yi magana da babar tasu da ke Funtuwa ta ce e zata shigo, dan nan da kwana huɗu muka yi za'a kawo komai mu saka rana, har na faɗa maka a yanzu da ka zo zaka sake ganin yaron da tushen sa ko ba komai kai ne maɗaurin aurenta tunda kana raye, sai hali na nesa da wani abin zai sa wani ya wakilce ka wanda ka amince, ka sani in ba dan yanayi ba, da babu abinda zai sa Aswa ya yarda da maganar yaron nan, to amma ni na san menene zafin rashi, na san kuma menene daɗin ɗan uwa kuma na fi shi shekaru sannan zan iya saka shi ko da baya so ya yarda, ka fahimta?"

Uncle Sulaimane ya gyaɗa kansa yana sake fuskantar Aba, Aba ya ɗora da faɗin" Bayan na yi shekara bakwai a aiki, na ajiye na je France na yi karatu na tsayin shekaru huɗu, a lokacin ina da aure, sai dai ka sani na sani in har mutum nada yadda zai yi kar ya je da iyalinsa to kuwa ya ajiye abinsa a gida a killace cikin mutumci da daraja, saboda irin ƙalubalen da muke gani a ƙasar nan dan kawai muna baƙaƙen fata, babba ba'a barshi ba yaro ba'a barshi ba, nawa suka rasa rayukansu a zuwan rashin sani? Nawa suka bar addininsu? Ban san irin yarda da ka yi da inda kake ba, amma na san meye cikin gari, abinda na sani shine ba zaka taɓa so ka je da yaran nan ba na lokacin da zaka ɗiba kafin kammala aikin ka kakaf, kuma ka nuna ba ka so ka bar su anan, idan ma ka ce za ka bar su tare da wa? Ko ba komai security ya yi ƙaranci a yanzu, ba zai yiwu ka bar budurwa ita kaɗai a gida ba, ko ba za ka aurar da ita ba?" Aba ya ƙarashe yana ƴar dariyar da ta saka uncle Sulaimane sadda kansa dan ya shiga tashin hankalin tunanin maganganun Aba.

A tausashe Aba ya ɗora da faɗin" Yara gasu nan, kai babansu ne, ko wani lokaci ka tashi ka zo ga inda suke, ga waya nan kana tare da su, idan har ka yarda ka bar su a hannuna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login