Showing 135001 words to 138000 words out of 397328 words
Yusrah, ki zo dan Allah ki bar su suyi aikin su, zo muje na nuna miki wani abu?"
A dole Yusrah ta cire hannayen ta ta biyo bayan Intisar ɗin ba dan za ta nuna mata wani abun ba sai dan kawai ta rabata da aikin nan.
*Wata* uwar harara ta maka masa cikin faɗa sosai tana kumfan baki tace" Yanzu Mubarak dan na zama shashasha a gidan nan a ce har baƙuwa ta kwana anan cikin gidan amma ban sani ba, sannan da safe na ga an yi baƙi ɓangaren ku kuma kun jima kuna tattaunawa, amma babu wanda zai ɗaukeni da darajar da za'a iya sanar da ni, sai yanzu ne za ka zo ka zauna kana faɗa min hukuncin da ka yanke akan yarinyar? Wato ka ma gama yanke hukunci ko?"
Cike da ladabi Yaya Mubarak ya kalli mahaifiyar tashi yace" Wallahi Mama ba haka bane, lokacin da muka shigo jiya na tabbata kin kwanta dan ba dare kika kaiwa ba, da safe kuma bamu ko gama kimtsawa ba mutanen nan suka shigo, sannan abinda muka ƙudurta zamuyi bamu da tabbacin zasu bar mana ita ɗin, shiyasa ban saka ki a maganar ba, yanzu ma ba wai cewa nayi na yanke hukunci ba, a'a na faɗa muku duk abinda yake faruwa ne na ɗora da cewa idan an samu danginta kuma sun amince zasu bar mana ita, zaki zama ɗaya daga cikin shaidunmu Mama sannan ki tayamu riƙo, tunda ai yaro ba ya ɗaukar yaro sai dai rumgumar ni mu faɗi."
Wani irin jinjina kai tayi tana kau da kan ta tace" Da kyau, ya yi kyau Mubarak, ku ci gaba da yi mana yadda kuke so ku da matan ku, na tabbata wannan shawarar ta Intisar ce, dan ba zata yarda ka kawo mata budurwa a gida ta zauna ba alhalin bata san ta ba, amma ka sani wallahi babu ruwana a maganar nan, tunda har baku sakani da fari ba, to nima ba zan shiga ba, can kuje ku ƙarata."
Da jin ba daɗi sosai ya kalle ta yace" Mama, kin san yarinyar wacece kuwa? Ita ce fa yarinyar da Bilal yake so muke kuma tayashi nema."
Da sauri ta kalle shi, sai kuma ta kyaɓa fuska kawai ta fashe da kuka tana share hawayen da ko fitowa basuyi ba tana faɗin" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Shikenan ni *Hawa'u* na gama, shikenan ni ƴaƴana a bautar mata zasu ƙare? Shi ma autan nawa Bilalu yanzu ya fara bin bayanta kamar raƙumi da akala, oh Allah! Oh Allah wannan wace irin jarabawa ce?"
Gyara zaman shi ya yi ya dafa cinyar ta yana faɗin" Mama, dan Allah Mama kiyi haƙuri ki daina kukan nan, Mama ba fa abinda zai faru, dan Allah ki daina kukan ki gafarta mana idan mun ɓata miki rai."
Kallon shi tayi tana nunashi da mafificin hannun ta dan ita da ta kunna fanka ko ac gwara ta yi ta firfita a ganinta ta ragewa ƴaƴanta kashin kuɗi tace" Ka duba ka gani gidan nan muna zaune lafiya lau, rana tsaka ƙanin ka Marwanu, rana tsaka ya kira masu aiki aka shiga bige gidan nan aka fitar masa da ƙofa ta waje ya ware kan shi shi kaɗai, duba kaga sunan nan da akayi irin maƙodan kuɗin da ya kashe, a ce haihuwar mace amma a yanka saniya har da raguna ƙosassu guda biyu?"
Sunkuyar da kai Yaya Mubarak ya yi, idan da sabo ai ya saba da jin wannan ƙorafin daga bakin mahaifiyar su, Marwan kuma da take magana ita ce bata sani ba, amma Marwan yana ɗan taɓa harkar banza a waje wacce kullum yake masa fatan shiriya da yi masa wa'azi ya daina ba kyau, to dare yake cikowa sosai kuma Hajiar tana saka ido akan haka, duk in ya shigo sai ta tsare shi da tambayoyi, ba dole ya raba ƙofar shi ba tunda yasan matar sa dai bata isa hana shi ba. Kawai Maman nasu tana saka ma kanta damuwa ne, amma shi kanshi yanzu nan idan suka samu matsala da Intisar aunty Bilkisu ce ke musu sulhu ba sai iyaye sun ji ba, ita kanta Zahra'u da tsohon cikin nan sai da ta yi ikrarin barin gidan nan Maman bata sani ba, shi da Intisar ne suka lallaɓata da bata haƙuri da kuma yi masa faɗa, amma dake murmushin su ta sani ba kukan su ba, sai take ganin kamar duka matansu sun mallake su ne, alhalin aiki suke da ilimi wajen kaucewa ɓata ma iyayen rai ko saka su jin abinda zai dinga ɗaga hankulan su.
Bayan a yi haƙuri Mama ba abinda ya sake cewa har ta gaji ta ce ya tashi ya bata wuri, haka ya fita jiki a sanyaye yana mai jin ba daɗi game da yadda mahaifiyar tasu take, bayan kuma tana da mata dake aure nasu gidajen ita ma, ba ta tsoron a musu haka?
Maman kuma yana fita ta ɗauki waya dan kiran aunty Bilkisu ta sanar da ita abin takaicin nan da Mubarak ya sanar da ita yanzu, sai kuma ta tuna ita kam ai ba ƴa bace, sai ta kora mata bayani ma ta ce to me ye Mama? Taimako ne fa sukayi, kuma yarinyar nan mace ce mai rauni, sai kawai ta shareta ta ce sai anjima za ta yi wa babbar Yayar su dake ƙasar waje magana, ita ai tasan za ta goyi da bayan ta, saboda halin ta ne sak *Asma'u* ta ɗauko, dan kawai yanzu ɗabi'un nata sun gauraya da na turawa ne.
*AUNTY FUREIRA*
Tunda aunty Fureira ta ga rana ta fara alamar faɗuwa ta fara shiri, ana idar da sallah magriba ta shirya tsaf abun ta, Aminu ne ma kawai da zasu tafi tare ya ɗan tsayar da ita tsaikon da bai fi minti biyar ba, amma a haka ji ta yi kamar sun yi awa basu tafi ba, haka suka kama hanya akan babur ɗin shi matar sa na ta musu fatan nasara suka nufi gidan Hajia.
Dake mai gadi dama yana tsumayin jiran su kai tsaye ya musu iso zuwa cikin gidan, tarba suka samu kamar an san su dai haka, sabuwar mai aikin da Hajia ta canza matashiya ta kawo musu ruwa da abinci, dan tun da abun nan ya faru Fatila ta faɗa ma Hajia mai aikin nan fa ta ta munafuka ce ita ce ta haɗa komai, dan haka Hajia ta sallame ta bayan ta cashe mata kuɗin ta ba ta bin ta ko sile.
Ruwan kaɗai duk suka ɗan sha shima dan Hajia ta matsa da su ci ko su sha ne, amma su bata wannan suke ba musamman aunty Fureira da ke ta wulƙita idanu tana fatan ko sun ga Yusrah, duba da yanayin aunty Fureira na zaƙuwa ya sa Hajia cike da dattako tace "Baiwar Allaj, ɗazu mun fita duka gidan, amma muna zuwa aka sanar dani nayi baƙuwa, kuma ta ce wai Maman Yusrah ce, shin hakane?"
Kallon Hajia ta yi a ɗarare tace "Hakane Hajia, ni maman ta ce."
"Ta ina? Ta ya ya kuma kika zama Maman ta?" Hajia ta tambaya kai tsaye.
Gyara zama aunty Fureira ta yi a sanyaye tace "Sunana Fureira, ni ƙanwar Maman Yusrah ce, ni nake bi ma Maman su Habiba, akwai kuma yayun mu biyu mata sai autar mu, dukan mu mata ne iyayen mu suka haifa, a can Funtuwa ta katsina muke da zama."
Da wani irin kallo mai kama da tuhuma Hajia tace "Idan hakane, garin ya ya baku gaggauta zuwa ba da abun nan ya faru? Nan da Funtuwa ai ba nisa tunda ba'a kwana a hanya idan aka duba da uzurin mutuwa ya fi komai."
Jinjina kai aunty Fureira ta yi tace "Hakane Hajia, rashin wayar Yusrah a wannan lokacin ya sa ma haɗarin da ya faru bamu ji shi da wuri ba, a ranar da za'a cika kwana uku ne muka ji hatsarin, Yusrah ta kirani da baƙuwar lamba take sanar da ni, a washe gari kuma na shirya tahowa ni da wani ɗan uwan mu shima, amma sai ƴata da nake goyo mai wata tara ta ƙone da koko, wannan ya sa tafiyar ta fasu da ni a lokacin dan saida mukayi kwana huɗu a asibiti kafin mu dawo gida a ci gaba da na hausa, to a wannan lokacin kuma ƴan uwana mata da wasu maza biyu sun zo har garin nan, sai dai basu samu su Yusrah da Safwan ba a ko ina, rashin sanin yadda zasuyi ya sa suka koma jiki a sanyaye suka sanar damu halin da ake ciki, dan haka ban zauna ba na nemi wanda zai ci gaba da kula min da ƴar tawa ni kuma a yau na kamo hanya na zo dan naji yadda ake ciki."
Numfashi ta ja ta sauke sannan ta ci gaba da cewa" Gidan Goggon su Yusrah na fara zuwa, mun yi ba daɗi da ita sosai wanda bana tunanin wani abu zai sake haɗani da Hinda, daga nan kuma na zarce gidan su ƙawar ta Maryam, ita ce ma ta sanar da ni ai jiya warhaka ma tana gidan nan dan ta ce har bayan sallah isha'i sannan Yusrah ta mata rakiya, shine fa na tasota gaba muka zo nan ɗin, amma sai aka ce mana kun fita gaba ɗaya, har ma mai gadin yake ce min kun kwana da zulumin rashin sanin inda Yusrah take, amma..."
Sai kawai ta kalli Hajia sosai tace" Ban ji gabana ya faɗi ba sanda ya gaya min haka, shiyasa ƙarfin guiwana bai ragu ba akan zuwa nan ɗin dan jin ko da wata makama ce da zan riƙe da za ta kaini ga inda Yusrah take."
Ajiyar zuciya Hajia ta sauke tana murmushi ta kalli aunty Fureira sosai sannan ta nuna Aminu dake zaune gefen ta tace" Wannan, mijin ki ne?"
Kallon Aminun ta yi sannan ta girgiza kai tace" A'a, ɗan uwanmu ne shima, abokin wasa ne garemu, a wajen su Yusrah kuma uba yake, anan garin yake da zama shima, rasa wayoyi da su Yusrah sukayi a haɗarin shi ya kawo tsaikon jin mu wannan al'amari, da duk haka bata faru ba da izinin Allah."
Jinjina kai Hajia ta yi cike da gamsuwa tana faɗaɗa murmushin ta, kafin ta ce wani abu kuma Yaya Jafar ya sallamo dan dama sun yi akan ya zo dan su ga wane kalar baƙi ne zasuyi, makarar da ya yi ta sa saida Hajia ta gabatar masa da su sannan suka ƙara gaisawa sosai, daga bisani Hajia ta dubi aunty Fureira tace "Fureira, gaskiya ne Yusrah tana gidan nan jiya kwana biyu zuwa uku kenan, amma dalilin wata hatsaniya da ta faru ta matar ɗana sai daren jiya ta gudu bamu sani ba..."
Da sauri ta kalli Hajiar ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Yusrahn? Yanzu kenan ba'a san kuma ina ta nufa ba?"
Girgiza kai Hajia tayi a nutse tace "Alhamdulillah, Allah ya taƙaita mana wahala dukanmu, a cikin daren ta haɗu da wani mutumin arziki ya taimake ta ya tafi da ita gidan shi, a kuma daren Yusrah ta bashi lambar ƴata Fatila suka kirani aka sanar dani abinda ke faruwa saboda ta haɗu da ƴan iskan gari suna neman yi mata fajirci, a taƙaice dai Yusrah a can ta kwana da safe kuma shine muka same ta acan gidan, kuma wani abun farin cikin matar mai gidan tana matuƙar son Yusrah kuma sun san juna tun dama, hakan ya sa dai da naje suka ƙi bani ita da sharaɗin za'a nemi shaƙiƙan Yusrah na wajen uwa da na wajen uba, idan aka samu amincewar duka ɓangarorin sai Yusrah ta zauna tare da su har lokacin da za'a ga Safwan, haka dai muka tsaida, kuma na musu alƙawarin kai musu wasu muhimman takardun ta da ta bari anan da kuɗin da ta tara dan aikin Safwan."
Girgiza kai aunty Fureira ta yi tace" Ina! B a ma zai yiwu ba, na yi alƙawarin komawa da Yusrah idan har na same su ita da Safwan, Hajia ki faɗa min inda take daga nan zamu je can mu koma da ita gidan Aminu, zamu yi neman Safwan tare in sha Allah, da mun same shi ƙafar su ƙafata sai Funtuwa."
Ƴar dariya Hajia ta yi cikin dattako tace" Hakane, ban kuma ga laifin ki ba!"
Sai lokacin Yaya Jafar yace" Gaskiya ne Hajia, amma ni ina ganin da mu bari zuwa goben idan Hajia za ta koma sai ku je tare, kun ga sai a tattauna abinda ya dace a can inda take, sannan kuma a samu wani daga cikin dangin mahaifin ta, ko kuwa?"
Aminu ma jinjina kai ya yi yace" Wannan gaskiya ne, hakan kuma ya kamata..." Sai kuma ya kalli aunty Fureira yace" Ina ga ai daga nan muna iya wucewa gidan Hindar ko? Sai mu sanar da ita abinda ke faruwa."
"Kuma da ni? Kana tunanin zan iya sake taka ƙafata gidan ta?" Cewar aunty Fureira da faɗa faɗa, taɓe baki tayi ta kawar da kai, Hajia ce tace "In dai wannan Yayar Baban nata ce ban yi mamaki ba, amma haƙuri zamuyi yanzu ko me za'a yi a saka ta ciki indai ya shafi yaran, ba dan wani abu ba sai dan fita haƙƙin su na shaƙiƙan uban ta, ki sani duk abinda ya haɗa ku ko da kun ɓata dole shi zai sake haɗa kawunan ku tunda har akwai zuri'a, yau ko ba komai iya maganar auren Yusrah ma kawai idan ya tashi ku kaɗai dangin mamanta baku isa ku gudanar da komai ba dole sai da sahalewar su."
Jinjina kai aunty Fureira ta yi tace" Hakane Hajia, kuma ban yi musu akan haka ba, amma dai ni ba zan sake haɗa bakina da matar nan, Yusrah dama ta faɗa min irin cin zarafin da take mata tunda aka yi rasuwar nan, sannan ɓatan yaran nan duka sakacin ta ne matsayin ta na babba, dan haka gaskiya sai dai in kai Aminu za ka je amma ban da ni."
Murmushi sosai Hajia ta yi ta kalli Aminu tace" Ɗana Aminu."
Da tsananin ladabi ya amsa da" Na'am Hajia."
A tausashe tace" Ka min alfarmar nan, daga nan ka je gidan Goggon Yusrah ka sanar da ita abinda ke faruwa, dan Allah ka yi aiki da hankali kasantuwar ka namiji wajen shawo kan ta har ta amince gobe ko ni ce idan zan je sai na biya na ɗauke ta, ka ji ko?"
Da ladabi ya jinjina kai yace" In sha Allah Hajia, daga nan ba zan tsaya ko ina ba sai gidan ta, duk da ban san gidan ba za ta kwatanta min idan ya so ita ta koma gida a adaidaita sahu."
Da jin daɗi tace" Ya yi kyau, yanzu karɓi wannan saka min lambar ka..." Ta faɗa tana miƙawa Jafar wayar shi kuma ya miƙe ya miƙawa Aminu tana ci gaba da cewa" Yadda kukayi kenan sai ka kira ka sanar da ni."
"In sha Allah Hajia." Ya faɗa yana saka lambar sannan ya taso da ladabi ya kawo mata, da haka dai suka tsaida magana kuma Hajia bata bari sun tafi ba saida suka ci abinci, anan Aminu ya yi sallah isha'i tare da Yaya Jafar kafin suka bar gidan.
Daga nan Aminu gidan Goggo ya wuce, amma kai tsaye mai gidan ya sa a masa sallama da shi, shi ya sanar ma abinda ke faruwa kafin suka shiga tare ya sake jadadda ma Goggon, buɗar bakin ta da fari cewa ta yi ba inda za ta je, Yusrah kula dai ƴar ɗan uwan ta ce za ta sameta anan inda take, sannan kar wanda ya sake zuwa mata gida daga yau da maganar wasu su Yusrah, idan ta zaɓi shiga duniya ne a bar ta mana faƙat, idan kuma ta san suna da mahimmanci to zata dawo inda suke. Saida dai ran mijin ya ɓace sosai ya ɗan nuna shi ma namiji wani lokacin kafin ta ce za ta je ɗin, amma a zo har gidan ta a ɗauke ta, sisin kwabo ba za ta ɓata ba wajen neman yarinyar da bata jin maganar ta, haka dai Aminu ya tafi ran shi ɓace cike da haushi da takaicin Goggon, bai san aunty Fureira ta fi shi tsanar ta ba saida ya je gida yana sanar da ita abinda ya faru, haka ta yi ta kumfar baki tana faɗa mishi baƙaƙen halayen ta.
Dan haka dai suka ce a dai samu goben a samu matsaya, amma ko me zai faru sai dai ya faru ba maganar zaman Yusda Safwan tare da Goggo, idan aka samu inda zasu zauna cikin aminci, to kowa zai yi wuri ya aje ta ba mai sake shiga harkar ta tunda ba wata tsiya za ta wa mutane ba, su Yusrah kuma da ta raina take ganin kamar nauyin su ne za'a ɗora mata, da izinin Allah akwai ranar da za ta zo ita ce za ta neme su ba sune za su neme ta ba, tunda ai rayuwa ceba yadda ba ta juyawa.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV