Showing 231001 words to 234000 words out of 397328 words
da hannun babban ɗana, in sha Allah zamu kula da su kamar yadda muka kula da kanmu."
Aba ya ajiye maganar a tausashen dai, sannan ya bashi damar yin tasa maganar shi ma, ya jima kansa a kasa kafin ya ɗago yana duban Aba, ya jima rabonsa da garin nan, amma kafin ya bar garin ma ya san wanene Aba, ya kuma san halayyarsa na taimako da sauran su.
Maganganun Aba gaskiya ne cewar ina zai kai su? Ya so ya tafi da su dan ya samu nutsuwar tarkata komai nashi sannan su dawo gaba ɗaya, sai dai in suka tafin ba zasu samu kyakyawan mahalli ba? Ga rashin ƴanci da tarin tashin hankalin dake iya riskar su a kowani lokaci a can ɗin? Dan kuwa a abinda Aba ya sani a da yanzu ya ƙaru, sosai ake fama da tashin hankali kala daban daban na bambancin ƙabila, a sanyaye ya furta " Ya Allah, ya Salam."
Aba ya yi murmushi ya ce" Kar fa ka ɗaga hankalin ka ko kai idan ka zo kafin ka yi aure ai a nan zaka ringa sauka balle su da suke ƴan gidan, ka yi haƙuri kawai malam Sulaimana haka Allah ya hukunta, kafin ka tafi a ɗaura mata aurenta a kaita ɗakin ta, ka ga ko kana ina hankalinka kwance shi jikan Aliyu yana wajen babansa, ita kuma tana ɗakin ta."
Kunya ta saka Yusrah sake sadda kanta, uncle Sulaiman kuwa a dole ya yi dariya dan ko baya so dole zai sauko irin yadda Aba ke hiratarsa kan lamarin nan, yana faɗa masa gaskiya ne cikin sigar rarrashi da barkwanci, shi ma ya sani bashi da ja da lamarin nan fa, dole zai miƙa wuya, balle maganar aurenta ita ta fi komai daɗaɗa masa.
A tausashe yana dubanta ya ce" Daughter, kina son shi mijin da zaki kuwa?"
Sai da ta ɗan zaro ido ta sadda kai cike da jin kunya, kai inna lillahi! Kai jama'a in an gama da ita a sallameta mana ya ya za'a ringa sakata jin kunya haka? Dariya suka yi shi da Aban a tare, Aba yace" Kin ga tashi yi tafiyarki, kai kuwa bari a gyara maka ɓangaren Yayansu ka je can ka yi zamanka, idan da abinda zaka kwaso a inda ka sauka ka je ka ɗauko dan da gaske nake ko kai na riƙe ka sai na aurar da kai zaka zauna a gidan naka balle su, ina zuwa?"
Daga nan ya miƙe ya basu waje ya sauka wajen su Anna dan ya sa a gyarawa uncle Sulaimane can ɓangaren AA, ya kuma basu waje su ƙara tattaunawa, dukan su suka bi Aba da kallo da irin mamakin halayyar su ta son jama'a haka, wannan ai shine cinye du, su kowa riƙewa suke yi? Sun riƙe ƴaƴan yanzu kuma baban su?
Sosai ya ringa mata tambayoyi, kuma amsoshin da take bashi sun gamsar da shi, har albashinta da kuma kuɗin da AA ya bata check na fitar da Safwan da aka yi duka kaf, ya ji daɗin hakan ya kuma yiwa Allah godiya har ya dubeta ya ce" Hinda ta ji kunya, ko da yake, Allah shine gatan bawa, gwara da aka yi haka, da a gaban nata ku ke ta yiwu da yanzu tana can ta fara ɗora maki tallah tunda ba tsoron Allah a ranta, Allah shi kyauta, in sha Allah wata rana sai ta yi mangarin rayuwarki, ko a yanzu kin mata nisa kuma in sha Allah a hankali zata yi dana sani."
Ita dai bata iya cewa komai ba, a lamarin Goggo Hinda bata da doguwar magana sai dai ta yi murmushin yaƙe, bata da abun cewa sai ido a lamarin, Allah ai shi yake da komai, bai yi ƙasa a guiwa ba ya sake tambayarta Bilal ɗin na ina ne? Yusrah cikin jin kunya ta sanar masa ƙanin yaya Mubarak ne.
Da kula ya ce" Kina nufin matar nan da na ringa samu ita ce mahaifiyarsa?" Yusrah ta tabbatar masa cewa ita ce.
Mamaki ya kama shi ya ce" To amma, zuwana uku fa tana nuna min bata san zancan ki ba, kuma ance su suka riƙe ki, kuma gashi ashe har ɗan ta ne kuke soyayya, ko akwai wata Yusrah da suka riƙe bayan ki?"
Yusrah ta yi shiru ita dai bata iya cewa komai ba, shi kuwa ya shiga halin tunani yana ta tunanin anya? Kai bata gane ba ya dai kasa samun amsa yadda ya dace daga Yusrah sai ya yi haƙuri ya sakawa ransa zai ji ai, abu ɗaya ya sani shi dai ba zai taɓa iya ba da yarinyar nan inda zata sha wahala ba gaskiya.
Sai da suka gama fira ta masa sallama bayan Aba ya dawo ta je ɗakin ta ta yi wanka ta saka doguwar riga ta tarda ƴan matan Anna kicin dan yau tana fashin sallah ba zata yi sallah ba.
Nabihat kuwa ta bar gidan Anna zuciyarta cike da ɓacin rai, gashi dai farin ciki ya kamata ya luluɓeta cewa jibi jibin zata shiga cikin tarihin ƴan matan da aka kawowa lefe da sadaki na kece raini, miji na nunawa sa'a, auren gidan manya gidan a yaba ko da babu kyau balle ɗan buzaye jinin abzinawa, farin cikin da ya dace ace tun yau ta tantance ƙawayenta wacce da wace, taron da suka yi niyar ɗauko masu ɗaukan hoto da idan aka yi ɗaukan har ta su Tiktok sai an watsa, mahaifiyarta har ta tanadi mai ƙunshi da kitso da makup ɗin da za'a cancara mata dan murnar wannan rana mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali irin wannan rana, amma baƙin cikin cewa har yau magana makamanciyar wacce wancen banzar bazarar ke samu a wajen saurayinta ita bata taɓa samu ba ya hana mata rawar gaban hantsi da yadda wannan rana wa ƙawayenta.
Dreba ya sauketa da sha tara ta arziki, ta samu mahaifiyarta har ta fara tara baƙi a kan maganar sadakin da kayan lefe da zasu amsa jibi jibi, mahaifiyar ta ta ta tarbe ta da farin ciki sai koɗa ta take yi cewar ga ƴa ɗaya da ta fi dubu ga ƴar da zata wanke mata takaicin da wata haihuwar ta ƙunsa mata, ga mai ƙashin arziki ga dukiyarta, zanceceku dai ire irin waɗannan.
Da ƙyar ta iya ɗan jim kafin ta haye ɗakin ta ta watsa ruwa ta dawo da ɗaurin ƙirji ta zauna ta ɗauki IPhone ɗin ta ta shiga dp ɗin Manal, ai kam hoton Yusrah ne da Anna ƙarama inda Yusrah ta ɗaga Anna ƙaramar suka saka dariya hoton ya mugun kyau shine Manal ta ɗora saman dp ɗin ta.
Sai da ta ɗauki hoton cike da jin haushin Manal ɗin kanta a cikin zuciyarta sannan ta zauna ta yi ta tunanin ya ya zata yi da hoton? Ina zata bincika bayan yarinyar? Wato shekarun baya, abinda yarinyar ta aikata har ta taki sa'ar zama a gidan su AA da samun daraja irin wannan, haka kawai abin ya tsaya mata a rai, farin cikin yarinyar ya zamo yana damunta damuwa mai tsananin gaske, ƙarshe dai sai da ta yi block ɗin kowa na familly ɗin su AA sannan ta ɗora hoton a Tiktok wanda ya zama ruwan dare bayan ta rufe baby Anna ta ɗora sanarwa cewar duk wanda ya san wannan ya yi magana zai samu tukuicin million ɗaya, sannan ta rufe ta ajiye wayar ranta duk na ƙuna.
*BAYAN KWANA BIYU*
A yau take babbar rana, ranar da za'a kai kayan AA da sadakinsa gidan su Nabihat, gidan Anna ya cika da jama'a sosai, duk kuwa da irin yadda ta nuna ba sai an yi taro ba a bari babbar ranar idan ta zo a yi taron, amma mutane sun zo ma sha Allah dan taya su murnar kai kayan babban ɗansu da kuma sadakinsa, musamman ma ƙannan Anna mata har da maza ma sun zo kafin suka wuce inda sauran mazan suke.
Aure ne da da yawa suka yi jira, aiki ake yi ka'in da na'in, ciki har da su aunty Furera,su Hajiar Jafar, su Fatila su Maryam da mahaifiyarta domin Yusrah ta sanarwa kowa kuma kowa ya zo shi yasa suke tsaitsaye suna ta tarban baƙi, gefe guda kuma an tanadi duk wani abu na ci da sha da za'a kai gidan su Nabihat, murna kawai ake ciki a yau har ta Anna tana cikin farin cikin ganin ranar nan duk da ba ta ɗaurin bace amma ta tabbatuwar ɗaurin auren ce in sha Allah.
Da yamma kusan ƙarfe biyar motoci suka fara ɗaukan iyayen suna nufa gidan su Nabihat da su, mazan kuwa dama ba a gidan za'a tarbe su ba waɗanda zasu tafi da sadakin. Ƴan matan Anna na cikin tawagar ƴan kai akwati, sun yi anko ɗin lafaya ja mai duhu da duwatsu rerass farare ƙarƙar, sai farar riga a ciki da ɗan kwali fari, idan ka ga shigar ƴan matan nan a yau babu ta yarwa, hatta Maryam dake bak'a a cikin su kamar ka sace ta ka gudu, wanka ne aka yi lafiyayye ya hau lafiyayyar fata da ƙira ga ƙamshi ana bazawa, sai ya zamo ma sha Allah ba dai ka kushe ba sai dai ka yi hamdalah ka ƙara kallo.
Lokacin da suka ƙaraso gidan su Nabihat a galleliyar motar da ta kwaso su suka bi layin manyan manyan motocin dake parke suka ajiye tasu motar, sun gama bidiyoyin su da hotuna sannan suka nufi baban falon su Nabihat wanda ba'a jima sosai da shiga da akwatunan da envelope ba, a lokacin da suka shigo sun tarar da mahaifiyar Nabihat wacce aka ba anvelope ɗin kuɗin ɗauke da kuɗin auren da kuma akwati saiti ɗaya jal aka sanar mata sune aka wakilce su su kawo ta yi shatakai tana kallon su da irin alamun abin dariyar nan ta yi murmushi ta ce" Hajia, wato angon nan salon sa daban ne, ya taho mana da zazzafan salo fa, sai an fara tsokanar mu sannan a shigo da akwatunan da kuma check ɗin kuɗin? Dan na tabbata kuɗin auren Elhaji Aswan Aliyu Anza ba zasu ɗauku a envelope haka ba."
Hajia ta ɗan dubi aunty Furera, da su Hajia A'isha maƙotan Anna, amma suka yi gum sai ɗaya daga cikin ƙannan Anna ce ta ce" Hajia ana wasa da lamarin neman aure ne? Abinda aka bamu kenan ko?" Ta ƙarashe tana sake duban su Hajiar domin Hajia babba bayan ta basu kuɗin nan sai da tace masu idan ma an ce kuɗin ne su ce eh su ɗin ne.
Wani irin abu ya so rufewa mahaifiyar Nabihat ido, abu ya tsaye mata a wuya, ba wani tsaye tsaye ta buɗa kuɗin ta duba da kyau ƴan dami damin jaka ɗari ɗari ne har biyar hakan na nufin jaka ɗari biyar ne aka kawo kuɗin auren Nabihat da AA?
Ƙawarta ce ta miƙe ta amshi kuɗin a hannunta ƙasa ƙasa ta ce" Kar ki manta ana ɗauka a vidio fa, ki yi haƙuri mu sallame su sai mu bi ba'asi mu ji abinda yake faruwa please."
A bayyane kuwa sai ta buɗa murya tana faɗin " Ma sha Allah, sharar fage kenan, sannunku sannun ku da zuwa ma sha Allah."
Ta ƙarashe tana sake mayar da ƙawar tata ta zaunar sannan ta maye gurbin ta ta ringa tarbar su da yin godiya mai ɗauka kuwa yana ɗauka, haka kuma ya fi kafe ƴan matan nan dake jere da abin ɗaukar nasa dan sun birge shi ainun.
Sau uku Manal da ƴar uwarta suna kallon juna na irin abinda mahaifiyar Nabihat ta nuna, gaba ɗaya hatta mai ɗaukan nan da zafi zafi ta kore shi, ƙarshe ma sai ta ɗauki jakarta ta haye sama ya zamo ta bar su da baƙi da ƴan uwanta da ƙawayenta, ƙasa ƙasa sosai Manal ta ce" Girl's, mu tafi an yi magariba kun san kafin mu isa an yi isha'i, gashi direban tamu bata gani da kyau da dare."
Yusrah ta fara jin sallama a ranta, dan duk ji take wani iri, gashi irin yadda aka cika saka masu ido abin saii ya fara damunta, babban abin da ya bata mamaki irin yadda aka ajiye kuɗin auren nan kuma su ɗin ko lemu ba'a basu ba, sai ya zamo suma manyan sun miƙe da wuri sun kuma kama hanya babu ko ƴar gudunmuwar nan da ake bayarwa idan an kawo kayan aure suka juya gida.
Suma a cikin mota suna tafe abin na basu mamaki, sai dai babu wace ta yi maganar gaba ɗayansu suka yi gum suka biya suka kai Maryam har gidansu dan Mamanta ta sanar mata ita ta wuce gida saboda dare kar ya musu, nisan waje da kuma tsayawa siyan pizza da suka yi ya sa suka kusan kaiwa ƙarfe takwas da rabi a hanya kafin su ƙaraso gida.
A lokacin da suka ƙaraso kuwa sun samu mutane duk sun watse dan gidan kamar ba'a yi uban taron nan ba, sai motar Yayansu dake parke a filin gidan hannunsa ɗaya ɗauke da Meem ɗayan kuwa yana jikin sitiyarin motarsa, ya fitar da ƙafa ɗaya waje, ɗayar ƙafar a ciki yana kallon motarsu da ta parka da tunanin su kuwa daga ina suke haka? Fitowa suka ringa yi su uku ɗauke da kwalayan pizzar, Manal kuwa da ky ɗin motar dan ita ce direban, suna ganin Yayansu su uku suka nufo shi da girmamawa sosai suka gaishe shi ban da Yusrah dake tsaye daga nesa tana kallonsa kamar yadda yake kallonta.
Amsawa ya yi a taƙaice, bai ƙure kowace da kallo ba ya ce" Daga ina kuke?"
Nawal cikin sanyinta ta ce" Daga gidan su aunty Nabihat ne Akhi."
AA ya ɗan dubeta ya ɗauke kansa ya sake maidawa kan Yusrah dake nesan nan tana dai kallonsa sai kuma ta ɗauke kai, ƙasa ƙasa ya ce" Auntynku ce?"
Su duka suka kalli juna da jin maganarsa suka sadda kai, har sai da ya sake duban su sannan ya ce" Akwai wani abun ne?"
Da sauri suka ringa girgiza kai kafin su yi ciki Manal ƙasa ƙasa ta ce" Yusrah ki gaishe shi mana kar ki sa mu yi laifi da daren nan ga gajiya ya tara mana wata dan ba girma da hukuncinsa ake yi ba."
Yusrah ta sake taɓe baki har ta juya zata bi bayansu dan bata yi niyyar zuwa ta gaishe shin ba, domin marabinta da shi jiya a asibiti faɗa suka yi, sai dai tuna wani abu da ta yi ya sa ta juya bata tsaya sanar da su ba ta ƙaraso inda yake zaunen yana kallon fuskarta har ta iso ta tsaya a ɗan face ɗin sa tana kallonsa ƙasa ƙasa ta ce" Ina yini."
Fuskarta ya ƙurawa ido, kafin ya gyaɗa kai sai kuma ya yi murmushi ya ɗan girgiza kai ƙasa ƙasa ya ce" Ni zaki gaida dan kin raina min wayo? Faɗi abinda ke ranki kawai."
Yusrah ta sake zubawa leɓensa da yake maganar ido kafin ta ɗauke kanta bayan ta cunno baki sai kuma ta taɓe bakin ta sake kallonsa ta ce" Na rasa gane me yasa ka yi haka?"
"Me kuma na yi ni?" Ya faɗa yana sake kallonta, pizzarta ta ajiye saman ƙafarsa dake waje hankali kwance ta shiga nunawa da hannayenta ta ce" A kan me zaka sa Anna ta bada jaka ɗari biyar kuɗin lefen ka? Jaka ɗari biyar kuɗin katinka ne fa na ji su Manal na faɗa, kana cikin mazan da basa iya yiwa mata kyauta ne? Wato maƙo ne da kai ko?"
Sai da ya saki murmushi kafin ya ce" Haƙƙun, wannan haka yake."
Ta yi tsuru tana kallonsa again, sai kuma ta girgiza kai ta miƙa hannu ta ce" Bani pizzata in tafi, Allah shi kyauta."
Pizzar ya kalla, ya kalli hannayenta, harda su ƙunshi aka yi yau *mahaukaciyarsa*? Uhum! Ya basar yana faɗin " Ki saka hannu ki ɗauka tunda ba ni na ajiye a nan ɗin ba."
Pizzar ta ɗan kalla, ta ga inda ta ajiye ɗin ƙwarai tana iya ajiyewa amma bata tunanin in har tana iya ɗauka, a hankali ta ce" Dan Allah bani ka ji?"
Ya sake dubanta ya kuma dubi pizzar ya ɗauke kai ya ƙi cewa komai, haushi ya sakata juyawa ƙasa ƙasa tana faɗin" Sai ka cinye ai."
Shi ma ya rakata da kallo ƙasa ƙasa ya ce" Aikin banza, ko kyau baki yi ba."
Sarai ta ji shi ta masa shiru ta yi tafiyarta, tana shiga falon ta samu Anna ce kawai zaune, an gyara falon sumul sai tashin ƙamshin turaran wuta yake yi, Anna na ganinta da ƴar fara'a ta ce" A'a, ina kika tsaya ne?"
Yusrah ta ɗan yi jim kafin ta ce" Ina waje ne Anna, barka da watsewar taro."
Anna ta amsata da barka sannan ta bata damar tarda ƴan uwanta, tana zuwa ta same su baje sun buɗe pizzar sun haɗa da yogurt suna sha suna fira, ta cire lafayar nan ta yi zamanta suka haɗe suka shiga fira babu wanda ya tambayeta pizzar wajenta dan yanzu su sun fara mamakin ta sosai, irin yadda wasu abubuwa ke faruwa tsakaninta da Yayansu abin ya fara basu tsoro da mamaki, haka fa kwanaki a asibiti kawai suna zaune tare suna fira Yayansu ya kawo wani abu a wayarsa ya nuna mata ita ɗaya suka yi dariya tare ya komawarsa ɗaki wajen ɗansa ya zauna, abin nan sun jima suna nanata shi a tsakaninsu, basu da amsar dalilin da yasa suka ga haka sai ido suka kawo suka zuba kawai suka yi shiru.
Sun koro da shan fira Goggo Tidin ta yi kiran Abrar, Abrar ta amsa kiran mahaifiyarta ta sameta a ɗakin ta ta gama shafa mai da kayan barcin ta a jikinta, ita kanta haushin abinda suka kai ya gama cika mata zuciya, wallahi da ta ce ba za ta je ba saboda ba zata zama ɗaya daga cikin wanda za'a nuna ba, amma wata ƙanwar Anna da suke gane ma juna da wasu ƙawayen ta da ta gayyata suka takura kan ta je, idan ba ta je ba matsayin ta na uwa ga Aswan wa zai je? Sai da ta ji ina ma bata dawo daga mission ɗin da ta tafi ba? Ina ma ba za ta