Showing 279001 words to 282000 words out of 397328 words
dama su shiga inda suka ga dama, wai ta ce gidan can gaskiya gida ne na kowa da kowa, sannan uban jejin dake bayan nan da Aba ya hana su zuwa bata yarda da shi ba, gwara a saka yarinyarta a wajen da ya dace.
Ajiyar zuciya kawai ya sauke a tausashe ya ce" Ok Aba, idan muka fito daga gidan su Y. Turaki zan je asibiti in ɗauko son in kawo shi can gidan, ina so in shirya shi idan za'a yi zaman dan ya zamo cikin familly."
Aba ya yi murmushi ya ce" Ba damuwa sai kun zo jikan Anza." Daga nan suka yi sallama shi ma Aba ya ci gaba da harkokin gabansa.
A ɓangaren ƴan matan Anna Yusrah na komawa ɗaki suka haɗe suka taru suka sakata a gaba, balle da tana kukan nasihar da Aba ya yi mata ya zamo suna tsokanarta kafin Abrar ta rumgumeta a tausashe ta ce" Sister, kin san wani abu? Ki daina kuka, kin ji? Ni ina mai tabbatar maki zaren nan irin yadin ne, tabbas haɗin nan zuwa gaba kaɗan zamu gane ba haɗi bane."
Yusrah ta ɗan dago ta dubeta domin a cinyarta ta ɗora kai, a hankali ta ce" Abrar, hausar ki ta zamo kamar yaren bagwari a kunnena, ni na san haɗi ne wanda da wahala ya zamo mai daɗin da nake mafarki, sai dai duk rintsi zan yi biyayya, zan kyautata da dukkan ƙarfina da kiyaye abinda addinina ya koyar da ni."
Abrar ta yi murmushi ta riƙe hannunta mai ɗauke da jan lalle ta dubi Manal dake kallon su ta ce" Kin san bata san waye mijinta ba, kin gane bata san waye aka aura mata ba ko? Ko da yake idan yana dodon wasu a gabanta sai mu ga ba haka ba, dodo yake a sauran duniya banda ta Anna, ta Aba da kuma *taki*."
Da wani mamakin ta ɗago tana kallon su ta ce" Abrar, kina da tsokana, ni wa? Idan akwai wacce yake dodo a duniyarta nice, kin kuwa san vidion da ta yi sanadiyar fasa aurena da Bilal vidio ce da kawai aka ɗauka a cikin tunanin eh haka ɗin ne? Manal, a motar haya fa waje ɗaya ya rage da ya shigo yadda yake din nan ya buɗe ƙafafu, ta yiwu tsakin da na masa ne ya hassalashi ya kira ni da suna mai abin kunya wanda bana son maimaitawa, kin ga *Aswan* ko ? Sam baya wani tausayina."
Manal ta kama baki tana zaro ido, sai kuma ta yi dariya har yana dafe haɓa ta ce" Sunan nan da kika kama Aba kawai da Anna ke kama shi gatsau, shi ma idan ya ɓata musu rai ko suna nishaɗi, in bai ɓata musu ba suna kiran sa da jikan Anza ne, kin san me sister? A gaba za ki gane abinda muke nuna maki, amma ki yarda da abu guda, tabbas a duniya ke ce halitta ta *uku da yake tausasawa ko da bai so ba*."
Yusrah sai ta samu kanta da mamakin furucinsu, ita ai gani take yi kaf babu wanda yake nema da bala'i irin ta, gani take yi a duniyar gaba ɗaya babu wanda ya tsana kamarta, duk idan sun haɗu sai ya nemeta da fitina, ƙiri-ƙiri ya ce da ita baya tunanin zasu shirya a duniyar nan tunda bata jin tsoron Allah ta saki yaro ƙarami ta tafiyarta yawonta, yanzu dan bata da kunya take ihun faɗin ƙaninta a bata abinta, ai idan ta ce zata duba abubuwan da yake yi mata bata san ko zata iya dubansa ba gaskiya, wani abin ya fi ƙarfin ta faɗa sai dai ta yi shiru kawai.
Ire irin firarsu kenan tunda ɗaurin auren nan ya gabata, su dai sun san burinsu su ji ta ce eh na yarda zan yi yaƙi ko da baya so ya so, basu san dalili ba sun fi farin cikin ita ce matsayin matar jigon gidansu fiye da Nabihat, a jiya tagwayen Anna sun cika dare suna maganar auren nan da yaɗa farin cikinsu a junansu, kyautar da suka so yiwa Nabihat tunda safe suka samu Anna da maganar cewa ta yi kaɗan su dai sai sun ƙara, ita da kanta Annar sai ta basu goyon baya, domin barcin da ta yi a yau mai daɗi ne wanda ta jima bata yi irinsa ba, domin lokuta da yawa sai barcin ya fizgeta sai ta zabura ta zauna ta shiga tunani a kan lamarin yaron da gobe suke saka ran ya tallabe su idan sun yi doguwar shekaru, in kuwa sun rasu ya tallabi ƙannensa, rashin aurensa ko tunanin matar da yake iya aure na damunta ainun a rayuwa, takan yi tunanin idan fa ya samu wacce zata wargaza masa gida maimakun gyara masa? Idan ya auri wa ce zata nisanta su da juna fa? Abubuwa dai gasu nan kala kala da suke ɗaga mata hankali ainun, Allah kaɗai ya san irin addu'o'in da take yi a kan lamarin aurensa, a yanzu bata san dalili ba auren Yusrah ya saka mata nutsuwa da salama a zuciyarta.
Kusan ƙarfe goma sha biyu Anna ta shigo da masu aiki ɗauke da kayan abinci aka ajiye musu, da nutsuwa fuskarta ɗauke da fara'a ta ce" Idan kun gama ku yi jiran sallah, in kun yi ku kwanta ku huta saboda mai gyaran jiki da mak'up zasu zo bayan sallar la'asar dan taron yau, idan ku ba kwa jin barcin ku bar min ita ta huta saboda ina so a shiryata sosai."
Daga nan Annan ta yi tafiyarta ta bar su suna zuzzuba abinci, Yusrah kuwa ta afka tunanin wani taron kuma? Har da su mak'up? Su bikin gidansu haka ake ta kashe kashen kuɗi haka?
*AA ANZA*
Bayan sun dawo daga gaisuwar iyaye direct gidan AA suka sauka gaba ɗayan su, hular dake kansa ya cire ya nufi ɗakin sa yana faɗin" Arif, ni ya kamata a zo a godewa da na yi aure, amma shine aka sakani a gaba na je na gode ko?"
Arif ya ɗaga murya yana faɗin" To da kar ka je mana, da sai a hana maka ƴar Anna mai abin mamaki, namiji gama ka zo mu zanta."
AA ya dakata ya dube shi ya ce" Ba zan zo ba gaskiya, babu abinda zamu zanta, ka je kawai."
Arif ya masa ƙuri yana kallonsa har ya juya ya shigewarsa ya rufo ƙofar kafin shi kuwa ya gyaɗa kai yace" Za ka yi bayani ne AA, zaka yi bayani."
Wanka AA ya sake yi ya canza tufafinsa zuwa madaidaita sannan ya fito ya nufi asibitin uncle Hamat, da ya je ya samu uncle Hamat ɗaɗɗaure, an masa wani irin ɗauri yana ta ihun a zo a kunce shi sun ƙi kunce shi kuma sun ƙi ƙara masa allurar barci dan kar ta yi masa illa domin shekarunsa ba zasu ɗauki ire irin abubuwan nan ba, tana iya taɓa masa ƙwaƙwalwa ko zuciya, gashi zuciyar tasa ba lafiya ba, dole suka barshi a ɗauren nan suna jiran ƙarasowar Aba da matarsa ta sa a kirawo dan ita bata san ya ya zata masa ba, zagi da alwashin kisa ya yi mata har ya gaji, kallonsa kawai take yi, so take yi ya dawo hayyacinsa kaɗan ta sanar masa wallahi idan bai yi aniya da ita ba ita ce zata kai shi ƙasa, sai ga AA ya zo.
Ita da kanta da ta ga zuwan AA sai da hankalinta ya tashi, duk ba da irin zancecekun da uncle Hamat ke yi a kan maganar auren nan, shi yasa AA na shiga ɗakin ta bi bayansa ta tsaya a bayansa gabanta na dokawa sosai.
Tunda AA ya shigo ɗakin ihun da uncle Hamat ke yi ya tsaya cak, kallonsa yake yi ido cikin ido da wani irin duba wanda bai taɓa yi masa ba, kallonsa yake yi tun daga ƙasa har sama yana tunanin ko a zamanin da yake da ƙuruciya bai samu kyau, cika, tsayi, haiba da dukiyar AA ba, bai samu isa, cikar daraja gaba da baya irin ta AA ba, a yanzu da ya zo gangara bai san me yake da shi da zai ba Yusrah ta zaɓe shi a kan AA ba, wannan tunanin ya saka shi rintse idanuwansa ya saki wani irin huci mai zafin gaske.
Aswan ya ɗan ɗauke idanuwansa daga kansa ƙasa ƙasa ya ce " Me ya yi zafi haka har aka ɗaure shi? Mahaukaci ne shi?"
Matar uncle ta ɗan ƙaraso da ƴar inda inda ta ce" A'a, am, a'a, abinda yasa ciwonsa ya yi mugun tashi ne, shine yake ikirarin zai kashe ni, shi yasa suka ɗaure shi dan bashi da lafiya sosai abin ƙaruwa yake yi sosai."
Ɗan zuba mata ido ya sake yi kafin ya ɗauke dubansa ya ƙarasa inda yake kwance har da su abin fitsari suka jona masa suka ɗaure shi a asibitin da yake taƙama yake isa yake abubuwa a cikinta, a asibitin nan ne yau ya kai haka? Subhanallah duniya kenan.
Zama ya yi daf da shi ya saka hannunsa ya shiga kunce ɗaurin, da sauri ta dube shi ta ce" Kar ka kunce shi fa, wallahi abin nasa babba ne."
Bai ce da ita komai ba ya ci gaba da kunce shi, ganin haka ta juya da gudu ta je dan ta kirawo docter ɗin dake kula da shi dan ita tsoron AA take yi ba zata iya yi masa ihu ba, ba kuma zata iya kama shi da kokowa ba, tana fita AA dake kunce Hamat ya ɗago idanuwansa ya dube shi
Irin yadda Hamat ke yi ya saka shi sake zuba masa ido kafin ya ɗauke kansa.
Ƙarara yake karantar cewa yana cikin hayyacinsa, sai dai a yau ƙiyayya ce ke rinjayar soyayyar da yake ikirarin yana yi masa, da sauri docter ya shigo, cikin girmamawa ya ce" Sir, barka da isowa, kai ne ashe? Amma sir kar ka kunce shi baya cikin hayyacinsa, bamu san abinda ke damunsa da girma haka ba, sai magana yake yi a kan wata Yusrah, yana ta faɗin babu uban da ya isa ya aureta sai shi, to dai abin har da dukan madame ya yi ya shaƙeta, shine muka ɗaure shi muke yi masa treatment sannan muka sanar da oga, ina ga wani abu ya tsayar da shi da tuni ya ƙaraso dan mu ji abinda ya dace a yi."
Idanuwansa da suke kan docter ya sauke a hankali ya sake kaiwa kan Uncle Hamat, a nutse ya ɗago kansa ya dubi docter ya ce" Ka san Aba yana da matsalar hawan jini ko?"
Docter ya amsa shi da kula sosai, AA ya sake duban uncle Hamat zuciyarsa da nauyi sosai ya ce" Hakan ya sa, babu abinda zan yi ganganci da shi ni dai da kaina a kan lafiyar ubana, ka san idan ya ganshi a haka yana iya faɗuwa dan soyayyar da yake yiwa ɗan uwansa?"
Docter ya gyaɗa kai a tausashe da yanayin jimami ya ce" Hakane sir, sai dai yanayin jikin docter ne abin tashi ɗayan nan ya rikita mu, wallahi tun jiya na ba madame shawarar a je a yi masa roƙon Allah, kar aje wani ke son shigarsa ba'a sani ba."
AA ya yi murmushi mai ciwon gaske, mai tsananin ciwon gaske, wannan karon a kausashe sosai ya ce" Akwai mugun ice irin zuciya? Babu mugun nama irin zuciya, zuciya dafi ce Docter, shi yasa duk mai hankali idan yana addu'a farko farko addu'arsa zai nemi tsari da aikin zuciya ne."
Ya dire maganar yana kallon matar uncle Hamat da ta yi wani iri tana kallonsa kafin ya juya ya dubi uncle ya miƙe tsaye ya ƙarasa ya saka hannunsa ya kunce ɗayan hannun da ya yi saura, ai kuwa uncle Hamat da ya yi wani kiskirim ɗin gangan zuciyarsa ta gama yanke masa a yanzu da ake faɗin sunan nan idan ba haukan ya zuba ba ta yiwu da wuri yaron nan ya gane shi, shi kuwa so yake yi ya fita daga asibitin nan dan ya samu ya raba shi da duniyar baki ɗaya, ai sai yana raye zai iya anfanarwa Yusrah wani abin ko?
Ɗagowar da ya yi da ƙarfi da wani irin gurnani dan ya nuna haukansa ya saka AA saka hannunsa ya danna shi da ƙarfi ta yadda har sai da ya dantse harshensa da ya so fitarwa dan yin magana, ya haɗiye maganar da ƙarfi yana saka wani marayan ihu ƙirjinsa ya shiga dokawa fat fat fat muryarsa a haɗe ya shiga faɗin" Son, son? Yaushe ka zo? Kai da wa kuka zo? Son ka kaini gida, son ban da lafiya wasu halittu nake gani son, so suke yi su kamani."
AA ya yi murmushi ganin Docter ya rikice shi ma yana faman janyo ayatul kursiyu
Gefen leɓensa ya dantse bayan ya sake danna shi har sai da ya ji kamar zai kashe shi sannan ya sassauta masa ƙasa ƙasa sosai ya ce" Kai ka san na san lafiyarka ƙalau, a duka kaf garajanka ɗayan nan jal ne zaka yi in kasa kawar da kaina da jiran hukuma, ina mai tabbatar maka idan ka shiga ƙoƙarin taɓa lafiyar Aliyu Anza nine nan hukumar ka! Ka nutsu yau ba zai shigo ba zan tare shi, amma gobe zai shigo, *Hamat* idan ya zo ya samu irin haka wani abu ya biyo baya komai zai fito fili, ka kiyayi wannan zalamar a cikin zalamomin da zaka yi sune zasu kai ka ga halaka, ai ka san matar mutum ƙabarinsa ko?" Ya ƙarashe a saman leɓensa yana sake saka idanuwansa cikin na uncle Hamat dake zaro ido bugun ƙirjinsa na sake fin na da sosai.
Sakinsa ya yi yana ɗan ɗaga murya kaɗan ya ce" Docter, idan wani abu ya taso ni zaka nema ba Honorable ba, ƙwarai jikinsa ba daɗi amma a daina ɗaure shi, ba mahaukaci bane, a yi ta ɗirka masa maganin barcin kawai in ya kasa nutsuwa zamu je a yi ta roƙon Allah, ko me ye za ka ga zai nutsu in sha Allah, please daga yau kar wanda ya sake garajan shigowa ganinsa idan ba tare da ni muka zo ba."
Docter na kallon irin yadda docter Hamat ya yi wani kashangar, da irin yadda matarsa ke zaro ido ta haɗe da jikin ƙofa jikinta na rawa ya ce" Ikon Allah, ka ga wallahi ya kasa tashin kuwa, ka ga kokowar da muke sha da shi kuwa? Ya rab ya baka lafiya docter, in sha Allah mu je sir ka saka hannu saboda a bi ka'idojin asibitin, sannan maganar masu zuwa dubiyar har da Madame?"
AA da wani irin nauyi ya danne masa ƙirji tunda docter ya ambaci kalaman da uncle ɗin sa ke faɗi a kan Yusrahr da ya san ko wace Yusrah ake nufi da ƙyar ya iya buɗar bakinsa ya sake faɗin" Eh, har da ita, saboda lafiyarta."
Daga haka ya fice Docter ya bi bayansa da sauri dan tun shekaran jiya ya zo musu da maganar asibitin, da batun maida sunan mai riƙon ta a kansa, abinda ya ɗan tsaida su sun nuna masa dole sai da saka hannun Aba, Aban kuwa ne matsalar dan bai shirya tunkararsa ba, amma duk da haka sun san waye shi sun kuma san yana da hop ɗin karɓar asibitin a lokacin da ya shirya, shi yasa suka bashi haɗin kai suke kuma ƙoƙarin ganin an yi abinda ya ce ɗin, su da kansu mutum uku suna cikin farin cikin haka, masu kamawa Hamat wajen aikata aika aikar ne cikinsu ya ɗuri ruwa, duk da bai fito ya faɗi dalili ba, sun san akwai wani abin dake shirin faruwa, shi yasa gaba ɗaya yanayinsu a ɗarare suke, dalilin da yasa kenan basu wani damu da rashin lafiyar ogan nasu ba, ta kansu suke.
Suna fita Matarsa ta yi saɗaf saɗaf ta je wajen jakarta ta ɗauka ta sake leƙa shi dan ita duk tunani take yi ko ya suma ne? Sai ta ga idanuwansa a buɗe tarr, hawaye a gefe da gefe gashi tun dannewar nan bai motsa ba hannunsa a kan ƙirjinsa, wani irin baƙin ciki ke nuƙurƙusar sa, wannan shirun da ya yi tunani yake yi a kan irin hanyar da zai bi dan ya rama wannan cin kashi da wulaƙancin da yaron nan ya masa, inna lillahi Wa inna ilaihi raju'un, ace shi Docter Hamat yau shi ne ɗan zumuntar sa mafi soyuwa a duniyarsa ya masa haka? Abin takaicin ya kasa bambance a kan wani dalili ne cikin ukun nan? Dan ya kula yana son ɗagawa ubansa hankali ne? Ko dan ya san sirrikan sa ne? Ko kuwa wai dan ya ji maganar Yusrah ne?
Tabbas ya rasa gane wani dalili ne a cikin ukun nan, ya tabbata kowane na iya saka AA shaƙe wuyansa, ba ma kamar maganar babansa, baya haɗa Aba da kowa a duniya, ya tabbata saboda shi ne kawai... Amma kuma anya kuwa?
Kai zai tashi ya fita ne, idan ma menene zai gani, dan babu uban da ya isa ya hana shi fita daga asibitin sa, asibitin nan ai tasa ce babu mai iko ko ƙarfin da ya fi nasa a ciki, wallahi zai nunawa AA shine ubansa a komai, ya shirya ja da shi, kuma ba maganar kar a ɗagawa babansa hankali ya yi ba? zai ɗaga masa ta yadda hawan jininsa idan ya tashi musaki zai maida shi yana ji yana gani ana wadaƙa da dukiyarsa yana nisawa har ya mutu, banzaye yan iska kawai!
Buɗe ƙofar da vigil ya yi fuska a haɗe ya ce" Madame ki fito ki tafi bisa umarnin sir, kuma kar ki kuma zuwa sai an baki dama." Ya saka Uncle Hamat ɗagowa da sauri da wani mamaki ya kalli vigil ɗin ya kalli matarsa da ta zaro ido ita ma ta furta" To fah."
Haɗe fuska ya yi yana kallonsa ya ce" Kai kana da hankali kuwa? Matar tawa zaka yiwa magana a haka? Uban wa ye sir bayana a wajen nan?"
Wani kallo ya masa fuska a haɗe yana tabbatarwa ransa lalle ya haukace ɗin kamar yadda ake ta raɗe raɗi, gajeran wandon nan ne fa tun na jiya a jikinsa,