Showing 246001 words to 249000 words out of 397328 words
ma ana bada haya kuma restaurant ce haɗe da wurin.
Ƙaramar magana sai Hajia ta maida ita babba, abu kamar wasa sai ya zama gaske, dan kuwa buɗar bakin Hajia cewa ta yi maganar auren Bilal da Yusrah fa babu ita, ita dama hankalin ta bai kwanta da auren shi da ita ba, ta yi shiru ne kawai dan ba yadda za ta yi da su, amma yanzu da ta samu hujja akan yarinyar nan da ta nuna wacece ita, to fa sai inda ƙarfin ta ya ƙare. Da fari shashaƙai Bilal ya ɗauki lamari, amma da ya fahimci da gaske take sai kuwa ya murje idanu ya nuna sam ta ma bar wannan magana, ta kuwa san kwana uku ne ya rage auren su idan aka cire daren yau? Imran ma da ya zo gidan bai samu Zahra'u bane ya leƙo nan ya tarar da wannan lamari, kai tsaye shi ma ya faɗa mata "Hajia matsayin ki na babba ai bai kamata ki yanke hukunci daga ganin abu a waya ba, wayar nan fa yanzu babu irin abun da ba'a haɗawa da ita, kamata ya yi ki samu manya ki ji ta bakin su har ku suhulta, amma dakatar da aure yanzu Hajia gaskiya zubar mana da mutumci ne za ki yi a idanun mutanen nan, kuma auren Yaya Mubarak da aunty Intisar ma zai iya samun matsala saboda haka fa."
Shi kam kallon shi kawai ta yi, to dama a cikin ƴaƴa ma ai akwai wanda ke fita zakka, ta san ko ta ce za ta tanka shi zai kakkaɓe rigar shi ne ya bar mata wurin ma, amma sai ta ga har Yaya Mubarak yau shima ya sake jadadda mata abinda Imran ɗin ya faɗa mata tare da ɗorawa a marairaice da "Hajia, ki dubi girman Allah ki kwantar da hankalin ki, mu fara tabbatar da Yusrah ce a vidion nan, sannan mu bata dama ta faɗa mana abinda ya faru, wallahi bana jin yarinyar nan tana da wani mummunan hali da take ɓoye mana, ke babba ce kuma uwa da ta haifi maza da mata, idan aka ma ƴar ki haka Hajia ba zaki ji daɗi ba, an fara abun nan a mutumce Hajia kar mu bari wata matsala ta ɓullo daga gare mu, duk da abinda kika sa aka kai na auren ta bai damu kowa bayan an san mun fi ƙarfin shi, kar ki so kiga irin kai da kawon da naga Intisar nayi, wallahi akwai ɗaya daga cikin ɗinkunan da Yusrah za ta saka a auren nan da naji Intisar na maganar kuɗin sa a waya kusan kashi biyu a cikin uku na kuɗin da muka kai, kenan Hajia abinda muka kai bai dame su ba kuma a shirye suke da su kawota da ninki ba ninkin shi, yanzu idan muka zo da wannan kuma, shin ba zasu kallemu a matsayin masu son kansu marar sa adalci ba? Za ma su iya kallon mu kamar tun farko ba'a son auren kora da hali ne aka ma yarinyar, shiyasa aka kai wannan kuɗin sai suka nuna ba komai bane, yanzu kuma muka fito da wannan, dan Allah Hajia na roƙe ki kar kisa a kallemu da wasu idanu da ba na kima ko daraja ba, dan Allah Hajia?"
Ƙwarai maganganun shi manya ne, kuma hakane kam, amma fa wallahi ba za ta yarda ba, dan haka ita ma ta nuna musu ita uwa ce kuma ita ta haife su ta hanyar miƙewa tsaye tana duban su dukan su tace" To ku ji da kyau, idan kuka dage sai Bilal ya auri yarinyar nan, wallahi ni dai ba da yawuna ba, sannan a ranar da aka ɗaura masa aure ku kawo masa mata tare da nemawa kan ku sabuwar uwa, amma ba dai ni ba, dan daga ranar zan sallama ku dukan ku wa matan duniya tunda su na haifawa, sannan..."
Ta faɗa tana ƙyasta yatsunta tace" Daga yanzu ma kar wanda ya sake tunanin ni uwar sa ce har sai kun yi biyayya ga umarnina, ku sani ni ba mahaukaciya bace da ina kallo zan bari ya auri yarinyar da ta yi zaman magarƙama, sannan bamu da tabbacin ma auren ɗan ta'addan dake kan ta ya mutu ko takaba take masa, to mu zuba mu gani ni da ku."
Shigewa ta yi ɗakin ta ta bar su cikin tsananin tashin hankalin da suka kasa fassara shi, sai dai Bilal ya fi su ruɗewa da shiga tashin hankalin, dan kuka na gasken gaske ya fashe musu da shi yana kiran wallahi fa su san yadda zasuyi da Hajia, amma shi gaskiya bai shirya yi mata biyayya a yanzu ba, dan wannan karon ta zo masa da bidi'ar da hankalin shi ba zai ɗauka ba, idan kuma bata ƙaunar shi ne ta faɗa masa mana, amma fa Yusrah ita ce farin cikin shi. Imran dai na kallon su bai iya cewa komai ba, sai ma Zahra'u da ta fito da goyon Yusrah ƙarama za ta tafi gidan ta jiki duk a mace ya miƙe ya bi bayan ta, Yaya Mubarak ne kaɗai ya dinga rarrashin shi da yi masa alƙawarin ba abinda zai faru in sha Allah, sannan suka tashi daga nan basu zame ko ina ba sai gidan ƙanin mahaifin su kawu Murtala, nan suka sanar da shi komai ya kuma yi musu alƙawarin da safe zai zo ya samu Hajiar.
Hakan bai ishe su ba saida suka wuce wajen Hajia Sa'a da take kamar uwa ga su Hajiar, duk da tsufan ta haka suka sanar da ita wannan lamari ta kuwa yi ta kwasar faɗa da cewa shin Hajia Habiba tana so ne akai matakin da ƴaƴan ta zasu bijire mata? Nan ta ce za ta sa a kaita gidan gobe Bilal ya ce shi zai zo ma ya ɗauke ta saboda tana da matsalar ƙafafu ga idanu ma ba sosai take gani ba, daga nan suka wuce ya ɗauki Intisar, amma duk yadda ta ga damuwa kwance a fuskokin su sam Yaya Mubarak ya ƙi bari ta sani yana so har su ga abinda gobe za ta yi da izinin Allah.
*WASHE GARI*
Kamar yadda dayawa suka ga wannan vidion na Yusrah da AA a saman tiktok, haka Safiya ƴar Goggo Hinda ta gani da asuba bayan gama sallar ta kafin ta yi shirin islamiyya, tana gani kuma a rikice sosai ta nunawa Goggon, ita ma ba ƙaramar kaɗuwa ta yi ba tana ta salati, daga baya kuma ta taɓe baki tana miƙewa dan fara sabgogin ta tace "Ba abun mamaki bane ai, da mamaki dama budurwa ta samo ɗaruruwan kuɗaɗe a kwana uku, Allah kaɗai ya san tsiyar da ta aikata tare da mutumin, hmmm!"
Fita ta yi dan aikin ta, sai kuma sheɗan ya shiga yi mata wasu saƙe-saƙe, dama fa ita tun farko Bilal ɗin nan Safiya ta so ma shi, amma ɗan iskan yaron nan ya jirgata baibai, tunda ya samu Yusrah kuma sai ya share babin ta ma a rayuwar sa, to amma kuma yanzu sai take jin kamar wata dama ce fa da Safiya za ta same shi ɗin, ko ba komai ai yana da mahaifiya, kuma idan dai ba gigin tsufa ya fara taɓa kanta ba, ai ba za ta so wannan aure ya ɗauru ba tsakanin ɗan ta da yarinyar da aka ma wannan terere haka.
Sai kawai ta yi amanna da wannan shawara, dan haka ta ƙwala ma Safiya kira kan ta yi maza ta fito ta kama mata su gama abinda suke yi duk safiya akwai inda za ta je ta dawo, daga ƙarshe ma da ta ga gari ya yi haske sosai, kuma sun ci ƙarfin aiki ga kuma kishiyar ta tsaye, sai kawai ta yi wanka ta shirya ta ɗauki hanyar gidan su Bilal dan bata manta gidan ba a zuwan ta na farko.
*Kafin* zuwan Goggo Hinda kawun su Bilal ya zo gidan, sai dai duk yadda ya so fahimtar da ita ta ƙi fahimta, sai da ƙyar ne tace "Shikenan ka je ɗin, abinda kawai nake so a tabbatar shine ita ce ko ba ita bace, in dai har ita ce a vidion nan to wallahi auren ta da Bilal ya haramta, in ko ba ita bace to ni da kaina zan bata haƙuri sannan a yi bikin nan lafiya."
Zazzaro idanu Bilal ya yi shi da Yaya Mubarak, dan su sun tabbatar ita ce, musamman da suka san labarin Yusrah da haɗuwar ta da wani mutum da bata sani ba ya yi ikrarin matar sa ce. Kawun dai ya tabbatar mata" Ko ta tabbata ita ce ba zaki hana auren ba, mutanen nan suna da dattako fiye da tsammanin ki, ko ita ce bana jin a gida irin wannan zasu iya zama da ƙasurgumar mai laifi irin wannan kuma ace basu ganota ba, dan haka ina so ki bi komai a hankali muyi bincike, zan je gidan yanzu na tattauna da Alhaji, Hajia bana so fa ki kai mutanen nan magaryar tuƙewa, magana ta gaskiya tun a auren Mubarak da ƴar su Intisar kike musu taka haye, wallahi karamcin su ne ya sa suke ƙyale ki, ki duba kiga ba'a fi sati biyu ba da muka je bikon Intisar, yanzu idan wani abu ya sake tasowa daga gare ki ko gidan nan bana jin Yayan ita Intisar ɗin zai iya kawar da kai fa."
Sai kuma ya miƙe ya kalli Bilal da duk ya zabge ya fita hayyacin shi daga jiya zuwa yau yace" Kai Bilal ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah babu abinda zai faru sai alkairi, yarinyar nan idan matar ka ce babu mai hana auren ka da ita, idan kuma ba matar ka bace to ka ɗauki dangana da haƙuri, dan babu mai auren matar wani."
Sai kuma ya dubi Yaya Mubarak yace" Muje, ko ba zaka je ba?"
A sanyaye ya girgiza kai yace" Kawu ka je kawai, ko kuma na raka ka dai, amma ba zan iya haɗa ido da kowa na gidan ba."
Jinjina kai ya yi yace" Muje to, Allah ya kyauta."
Da haka suka fita Bilal ma ya fita tare da su dan magana ta gaskiya Hajiar ma bai san ya zai ce mata ba ko ya zauna, gani fa yake kamar ba ta son shi ne ma, tunda suka shiga mota suka tafi ya sake komawa ɗakin shi ya hau sallaya ya shiga sake shaidawa ubangiji, dan shi kaɗai ya san girman tashin hankalin da zai shiga idan aka ce an fasa auren nan.
Hajia na nan tana ta ayyana ba fa za'a yi auren nan ba in dai ita ce, sai ta nuna wa kawun nasu ita ta haifi yaran, kuma ko mahaifin su ya dawo ta ce ba za'ayi ba to ba za'ayi ɗin ba sai dai duk abinda zai faru ya faru.
Kai tsaye aka mishi iso falon na Aba, saidai daga yadda ya same shi da alama yana daf da fita shi ma, dan haka ma bayan sun gaisa yake cewa "Elhaj ko fita zaka yi kar na tsayar da kai kuma? Ko anjima ina iya dawowa, dan na sani nima na maka sammako."
Murmushi Aba ya yi yana ɗan zama bakin kujera yace "Ah haba dai! Ai ba komai wallahi, nima da ban da niyyar fita yau ɗin saboda sabgar nan dake gaban mu, to yanzu ne matar ƙanina (uncle Hamat) ta kira take sanar da Annar su jikin nashi ya ƙiya tun da dare an sake mayar da shi asibiti."
Da kulawa sosai kawun yace" Subhanallah! Dama bashi da lafiya ne?"
Amsa Aba ya bashi da" E wallahi, tun lokacin da aka kai kuɗin auren shi babban ɗan nawa ai ba tare da shi ba, ya kwana kusan huɗu asibiti aka sallame shi, shine yau ma aka maida shi."
Da jimami sosai kawun yace" Subhanallah! To Allah ya bashi lafiya, ina ga Elhaj ko ka tafi asibitin, tunda ba'a san a halin da yake ciki ba ko? Idan ya so ko zuwa dare sai na dawo."
Girgiza kai Aba ya yi yace" A'a Alhaji, na zamuyi haka ba, tunda dai har ka zo a wannan lokacin, to na san magana ce mai mahimmancin gaske, ba damuwa kawai ka faɗa ina sauraron ka, fatana dai bai wuce a ce komai lafiya ba."
Numfasawa kawun ya yi ya ɗan sadda kan shi yana mai jin girman mutanen nan sosai, suna da karamci, suna da adalci, suna da kawar da kai, suna da kunya da yakana, amma Hajia ta ƙi gane hakan, so take har sai sun fito da kalar su an yi ba daɗi, numfashi ya sake ja mai nauyi sannan ya ɗan ɗaga kan shi yace "...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
07/06/2024, 18:12 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*62*
Numfashi ya sake ja mai nauyi sannan ya ɗan ɗaga kan shi yace "Elhaj, wani abu ne ya faru jiya da ya ɗan ɗaga hankalin ita mahaifiyar su Bilal, shiyasa na zo dan jin gaskiyar abun."
Gaba ɗaya Aba ya tattara hankalin shi ga kawu yace "Wani abu kuma? Wannan wane irin abu ne?"
Kallon Aba ya yi sosai yace "Elhaj, wata vidio ce ke ta yawo a kafar sada zumunta ta wannan...tiktok ne suke kiran abun ko me? Kuma yarinyar da ke cikin ɗaukar sak Yusrah ce tunda har da hotunan na aka ɗora, to tashin hankalin shine jami'ai ne suka kama su irin dai kamun nan na tozarci, sannan wanda aka kama su tare har yana ikrarin wai matar sa ce, shine fa abun ya ɗaga ma Hajiar hankali har tana cewa za'a dakatar da auren, nace a'a ba za'ayi haka ba gaskiya, shine nake so na ji ku ko kun san da wannan abu da ke faruwa? Ko kuma ma dai wata ce mai kama da ita yarinyar? Ko kuma shiri ne na wanda ba sa son auren ta da Bilal? Duba da har gida aka kai ma Hajiar waya sabuwa dal dan kawai a nuna mata wannan ɗauka."
" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil!" Shi ne abinda Aba ke ta maimaitawa yana kallon kawun hankalin sa a tashe.
Gyara zama ya yi yace" Ka ce a saman tiktok? In ga ɗaukar dan Allah? Yusrahn?"
Da irin yanayin nan na mantuwa kawun yace" Subhanallah! Ka ga kuma tashin hankalin maganar da Hajiar ta zo mana da shi ya sa ba wanda ya yi tunanin tahowa da wayar ko turawa, wallahi ban da shi anan."
Shiru Aba ya yi ya sadda kan shi yana nazarin abun, e tabbas Intisar ta faɗa musu, amma basu san anyi ɗauka ba, tsoron shi guda yanzu shine kar wannan abu ya zamar mata matsala a rayuwa, gashi basu san haka za ta faru ba dan haka basu nemi sanin mutumin da ya shafa mata wannan kashin kajin ba, ɗago kai Aba ya yi ya kalli kawun yace "Alhaji ba matsala, yanzu hankalina akan Hamat ne dake asibiti, in sha Allah daga nan asibiti zan je da kaina har gidan na samu Hajia da maganar, ni nasan vidion dan Yusrah ta faɗa mana komai, dama kuma anfanin faɗar gaskiya kenan, tabbas da a ce bata sanar da mu wannan ba, da ban san ta inda zan taro matsalar ba, amma idan na je zan fahimtar da ita in sha Allah." Cike da gamsuwa kawu ya amsa mishi sannan ya dinga fatan samun sauƙi ga uncle Hamat har suka fito tare Aba ya ma Anna sallama sannan ya fice.
*Bayan* fitar su Goggo Hinda ta zo gidan, kuma ba wanda ya san da zuwan ta dan lokacin ma Intisar ta yi sammakon fita zuwa saloon ita da yara za'a musu ƙunshi da kitso dan su rage aiki daga nan za ta wuce gida, dan haka ba wanda ya san da zuwan ta har ta wuce wurin Hajia, tana nan falo tana raya aure fa ba zai yiwu ba, dan har waya ta yi da wata a cikin dangin su ita ma ta goyi da bayan Hajiar, sai ga Goggon ta shigo.
Ba ta wani karɓe ta da sakin fuska ba ta dube ta sama da ƙasa tana faɗin "Kamar na san fuskar nan ko? Au! Au! Uwar amarya ko? To to! Da me kika zo min?"
Tsaf Goggo ta fahimci Hajia a sama take, dan haka tayi murmushi tana ƙara jimƙe wayar ta da ta sa Safiya ta tura mata vidion nan tace "Ba abinda ke tafe da ni sai alkairi Hajia, kiyi haƙuri akan abinda ya faru a baya."
Da zafi zafi Hajia tace "Alkairi? Ku har akwai alkairi a tare daku ne? Bayan mugun irin da kuka shuka gashi ya fara fitowa, mtsssssss!"
Dariya Goggo ta yi dan ta lura kamar dai Hajiar ita ma ta san wani abu game da su ko ta ce Yusrah, amma sai ta haɗe tace "Hajia, ni mai ƙaunar ki ce da iyalin ki baki ɗaya, idan abinda