Showing 366001 words to 369000 words out of 397328 words

Chapter 123 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70010

ta dawo, a nutse ya ringa duba msg ɗaya kan ɗaya na mutumin, har da lambar waya uku mutumin ya saka masa yana roƙonsa ya yi kiransa ko ina ne zai je ya amshi saƙon taimakon, sai godiya yake yi da addu'a dai, murmushi ya yi ya girgiza kai ya gyara zama bayan ya aika kira da baƙuwar lambar da ya buɗa Tiktok ɗin wacce ba zata shaida waye shi ba.

Kamar jira ake yi aka ɗaga kiran ana yin sallama, cike da basarwa ya ce" Wa alaika, dan gane da maganar saƙon ne, in zaka iya zuwa yanzu ka amsa kafin in yi tafiya, idan kuwa baka da time a barshi bayan na dawo sai ka zo ka amsa."

Har haɗe baki yake yi wajen faɗin" Ai ba abinda nake yi oga zan zo yanzu yanzu ko ina ne, a min kwatance kawai."

Aswan ya miƙe yana duban Yusrah da ta shigo da turaran wuta, ya sakar mata lallausan murmushi a hankali ya bashi kwatancen tsohon gidansa sannan ya datse kiran ya janyo ta jikinsa a hankali ya ce" Zan je wajen aiki in dawo Jaanu, ko baki gama dani ba?"

Yusrah ta kubce tana faɗin" Aban Safwan a dawo lafiya."

Dariya yayi dan sosai ta jigata jiya ma sai da suka yi ta kula da jikin nata ne har ta samu ta miƙe da asubahi, shi ne duk in ya zo ya matse mata waje sai ta gudu, raka shi ta yi har wajen ƙofar babban falo tana ɗaga masa hannu ya fice a nutse ya shige motarsa sannan ya ɗaga wayarsa ya dannawa masu tsaron ƙofar gidan can kira.

Suna ɗagawa ya bar musu sallahun zasu samu wani bargo yanzu yanzu, su jibge shi ba dukan mutuwa ba gaya nan zuwa, ai kuwa suka amsa da yanzu kuwa oga, shi kuwa ya nufi gidan hankali kwance yana tunanin daga yau dai zai cire hannunsa a binciken uncle ya barwa hukuma su ƙarata in sha Allah.

Dorina ya siya irin ta dukan raƙumin nan ya tafi da ita, yana shiga ya samu samari biyu an cire musu riga an basu wahala sosai ƙarti sai kuka suke yi ɗayan na yiwa ɗaya Allah ya isa da ya janyo shi dan son abin duniya suka faɗo gidan sojawa, shi ma yana yi masa rantsuwar ba nan ne zasu je ba, sun yi magana ne da wani mai sunan yaron gwamna zai je ya amshi kuɗi sun yi mistake ne ba gidan da zasu je bane suka zo.

Shi dai ya gama tsayar da motar ya ga yadda suka zubawa motar ido ya buɗe ya fito ya ɗauko bulallarsa yana gallawa sojan da ya ƙaraso ya sara masa harara ya ce" Daga cewa ku ɗan zane su sai ku fitar da su a hayyacinsu, me kuka bar min kenan? A nan in na taɓa su ai kashe su zan yi."

Da girmamawa ya ce" Oga wallahi son jikin tsiya ne da su, wancen ina ga ɗan daudu ne, ina taɓa shi fa ya fara kuka yana kiran mamansa wai, bamu wani gigitasu ba yan daudu ne dai kawai."

AA ya zarro ido ya ce" Ji jaraba, yau kuma ta haɗo mu da ƴan banzan gari? To ai shikenan mu je."

Ƙarasawa suka yi inda suke tsugunne ya zuba musu ido yana kallon yadda suke masa sannu da zuwa da faɗin wallahi sun faɗo gidan nan ne ba a sanin ransu ba wani gida suke nema suka zo nan, irin yadda yayi maganar ya sa AA dafe haɓa yana kallonsa ya ce" Kai wai namiji ne ko mace?"

Mutumin ya yi tsuru tsuru ya rasa amsar badawa, dan gaskiya yana daudu sosai da sosai, amma alamu sun nuna masa in ya cewa wannan ɗan daudu ne shi yana iya cin uwashi, AA ya dubi sojan nan ya ce" Wai ya ya ake yi suna iya ganin mata su yi abota da su amma kuma basa jin komai? Ko yanke ta ake yi?"

Sojan ya ɗaga kafaɗu ya ce" Wallahi oga ni da kaina ina mamakinsu, kai oga ya ce yaya aka yi kuke gauraya da mata kuma ba'a ganinsu da ciki?"

Ya wani langaɓar da kai ya sake fashewa da kuka, hakan ya sa AA faɗin" Inna lillahi, kai jama'a wannan kashe min imani zai yi ya sa in kashe shi a sakani prison Y. Turaki ta auri wani ta barni, gwara ya faɗi abinda ya sa na kirayeshi, nine yaron gwamna wannan vidion nake so ka faɗa min kana nan aka yi abin? Kai ne ka ɗauke mu ko kuwa wani ya sa ka ɗauka?"

Vidion ya kalla, lokaci ɗaya cikinsa ya juya, tashin hankalinsa ya bayyana, shi dai tunda ya ɗora vidion nan ya samu kuɗi da ita sosai, saboda wacce ta bashi aikin ta zuba masa kuɗi sosai daga baya da ta ce ya sauke ma sai da ta biya shi sosai shi kuwa ya yi block ɗin ta saboda dalilin vidion nan ya sake fasowa aka sake saninsa ya sake samun flowers sosai, bayanta ma wani ya biya shi wato Sulaiman dan ya san wanda ya bashi aikin, kuma kuɗi masu yawa, ashe ashe ranar a ci uwashi zata zo? Hankali tashe ya ce" Oga wannan vidion nima a duniya na ganta, ba ni na ɗauka ba, wannan ɗin ɗan daba ne aka kama da matarsa ƴar daba, kana gani sojawa suka tafi da su, daga wannan ban san koma.. "

Katsa masa marin da AA ya yi ya saka shi sakin ihu yana zubewa ƙasa ya dafe kumatunsa yana sake saka ihu yana faɗin " Inna lillahi zai kashe ni, wayyo kunnena ya doɗe, wayo zai kashe ni."

Bulalar da sojan nan riƙo ya warto ya dawo kansa ya ɗaga zai lafta masa ya duƙa ya rirriƙe ƙafafuwansa yana kuka yace" Oga zan faɗa maka, ka min rai wallahi wata ta bani aikin nan, ina da numbarta da sunanta, sunanta Nabihat ita ta ce in ɗora, wallahi daga wannan ban san komai ba."

AA yayi tsai yana kallonsa, da sauri ya kalli sojan nan ya masa alamun ya bashi wayarsa, sojan ya miƙowa mutumin wayarsa, jiki na rawa ya lalubo masa lambar a whatsup ya bashi, AA ya shiga ya ringa dubawa, da sunan, da hoton dp ɗin da maganganun su, da shedar trensfer na kuɗin da ta ringa tura masa da sauransu.

Idanuwansa sun gama birkicewa, ya dubi wannan mutumin ya duƙo yana dubansa ya ce" Wannan ɗan daban nine, wacce ka cewa ƴar daba kuwa iyalina ce, ni kaɗai nake da damar kiranta da wannan sunan, ni kaɗai nake da damar faɗi, zan je da wayarka dan in yi wani abin, in na gama zan ga in ka cancanci a mayar maka da wayar bayan ka fito daga aikin soja, domin daga nan zaka wuce gidan maza kai da abokin ka, a yi horo lafiya."

Daga haka ya miƙe ya nufi motarsa sojan nan na biye da shi ya shige motar ya fizgeta bai ce masa komai ba, sojan ya koma yana faɗin" Kuna zamanku ku ka biyo hanyar oga? Dama da mu ya barka da mun ɗan tausaya, kai dai ka mutu ka lalace kawai Allah ya sa ya baka horon da kansa." Wannan mutum kam zuwa lokacin babu baka sai ido, sai abokin tafiyar dake kukan ya shiga uku, aka shanya su a rana kamar kilishi aka ce kar su saki su tashi.


Aswan bai zame ko ina ba sai gidan Chef, a lokacin ƙarfe goma sha biyu ne na rana, ya zamo duk wani wanda ya kwana ya tashi a gidan yana falo daga ita har ƙannanta da mahaifiyarta, da ya zo ya zata Chef baya nan dan bai ga motarsa ta ma'aikata ba, bai san cewa motar na garage bane, shi kuwa Chef tunda ya gama abinda yake yi yau sai ya sauka ya je baya ya ajiye kujera da jarida dan ya shaƙi iskar duniya mai daɗi, hakan ya sa ya ga shigowar Aswan da kuma irin yadda ya ƙi fitowa daga motar.

A lokacin kuwa Aswan lambar Nabihat yayi kira da lambarsa ya ce da ita yana gidan, wanda hakan ya bata mamaki ainun, ita ai ta cire rai da ganinsa a gidansu da sunan wajenta ya zo, gaba ɗaya ma zata iya cewa ta cire wannan tunanin a ranta, a yanzu a halin da take ciki gaba ɗaya murnar auren ta koma cikinta, irin yadda Imran ke nuna mata so da kulawa ya zamo gaba ɗaya maganar aurenta ta fice mata a rai, sai dai ta san ko karan hauka ya cije ta bata isa ta nuna bata so ba, shi yasa ko jiya da ta ce ta tafi ta ƙara siyo wani yadi da take so a saka cikin ɗinkunanta dan kawai su haɗu da Imran ne, suka haɗu kuwa suka sha soyayyar da ta sakata kukan daɗi, ina ma ace zata samu haka a wajen AA? Tabbas da ta more, har tunani take yi ya ya zai yi kama a saman gado?

Cike da yauƙi ta fito, kanta ko ɗan kwali babu ta nufi motar tana yauƙin nan, mahaifinta har zai ɗauke idanuwansa a kanta yana murmushin ganin ashe wajenta ya zo, sai ya sake dubanta da mamakin ina gyalenta ko hijab ne ta fito kai buɗe tana tafe gaban namijin da ba muharraminta ba da matsatsun ɗinkuna? Amma mahaifiyarta bata ga fitowar ta ba ko? Zai kuma ɗauke idanuwansa ya ga AA ya fito rai ɓace ya nunata da yatsa a lokacin da ta ƙaraso tana niyyar buɗewa ya dakatar da ita murya sama sama ya ce" Ashe baki da hankali? Ashe baki da mutumci? Dama haka halayyarki yake?"

Wani irin faɗuwa da gabanta ya yi sai da ta kusa kifawa, tsoro ya kamata, tashin hankali ya kamata, kar dai aje ya san tsakaninta da Imran? Dama duk idan suna zance da shi in suka gama sai ta ce da shi ya goge komai saboda mahaifinta da mijin da zata aura sojawa ne, suna iya saka layinta a wani tsarin da zasu san wainar da take toyawa, abinka da marar gaskiya lokaci ɗaya zuciyarta ta ayyana mata asirinta ya tonu da maganar Imran.

Da sauri ta buɗe baki lokacin da mahaifinta ya taso ya nufo su dan ƙarara ya gane ba lafiya ba, muryarta na rawa ta ce" Yayanmu, Akhi dan Allah dan annabi ka yi haƙuri, wallahi ba abinda kake tunani bane, babu abinda yake tsakanina da shi, dan Allah ka yi haƙuri."

Mahaifinta da ya ƙaraso yana kallon ta ya ce" Subhanallah, shi wa? Ke lafiya? Shi wa?"

A rikice ta kalli mahaifin nata tana ja baya dan gadan gadan ya nufota ta ce" Inna lillahi, Aba ba kowa ba fa."

Chef ya dubi Aswan da ya yi tsuru yana kallonta cike da mamakin furucinta, yarinyar nan dama kana ganinta ka ga munafuka, Allah ne ya fitar da ita daga tsatson mutumin kirki amma halayyarta kaf ba na yarda a ciki, me take faɗa haka? Chef ya ce" Son, waye take magana a kansa? Hala da kuɗin aure a kanta take kula saurayi?"

Aswan da jikinsa yayi sanyi ya gaishe da chef a tausashe ya ce" Ba komai Aba, bari in tafi."

Chef ya janyo shi yana kausasa dubansa ya ce" Ki, sa'anka ne ni? Za ka faɗa min ko sai na saɓa maka?"

Nabihat jikinta ya riga da ya kwashi rawa tuni, Aswan kuwa ya ce" Aba ni ba abinda nake tuhumarta da shi ba kenan, nima yanzu na ji wannan ɗin."

Chef da mamaki ya dubeta ya ce" Ke, me yake faruwa, zaki gaya min ko sai na karya maki wuya dan ubanki? Kai ka sanar min abinda yake faruwa, Hajia, Hajia fito nan, saurayi yarinyar nan ta yi bayan da kuɗin aure a kanta dan ubanta? Ke kika ɗaure mata take wasa da dokar musulunci da kuma hankalin mu?"

Mahaifiyarta ta fito da sauri tana faɗin" Elhaji, lafiya? Wallahi ban san da zancen nan ba, ke Nabihat me yake faruwa?"

Aswan ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Aba, dama maganar wanda ya ɗora abin nan a Tiktok ne da ka ce in samo, ni shi ne ya kawo ni ban ma san maganar nan da take faɗa da abinda take nufi ba."

Daga ita har mahaifiyarta ido suka zaro, mahaifiyarta ta ɗora hannaye saman kanta, ita kuwa ta kama ɗage tufafin jikinta kamar zata zura da gudu tana faɗin" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."

Chef ya zuba masa ido yana kallonsa, a nutse ya ce" Ni duk ban gane ba, waye ya ɗora ɗin son?"

AA ya yi shiru na ƴan daƙiƙu, a hankali ya ce" Ka yi haƙuri Aba, ban san dalilinta ba, ta yiwu tana da ƙwaƙwarar hujja, gaba ɗaya ma abinda ya tunzurani tunanin me ya haɗata da mutumin da ya mata aikin, da irin maganganun da ta faɗa kamar ba musulma ba, sune suka tunzurani, ban ma san kana nan ba da ban zo ba."

Chef ya ƙure shi da ido ya ce" Kana nufin da saninta a kan wannan lamarin?"

AA ya ce" ita ce ta sa ya ɗora vidion."

Nabihat ta zube ƙasa tana faɗin "...



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
06/07/2024, 18:11 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍??🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*93*



Nabihat ta zube ƙasa tana faɗin" Shikenan, na mutu na lalace, nima korata zai yi ko ya kasheni, shikenan asirina ya tonu."

Chef ya zuba mata ido da shi da AA, furucin bakinta ya ƙara shiga zuciyar Chef tashi ɗaya, tabbas a kullum yana nadamar irin hukuncin da ya ɗaukarwa Fauziya dan kawai ta kawo mijin auren da bai masa ba, gashi yau har ranar da zai ji abin kai tsaye daga bakin ƴar sa ta cikinsa ya zo? Yana dubanta ya ce" Dama ke kika aikata haka? Amma me yasa?"

Nabihat ta ringa yarfe hannu tana kallon Mamanta, Chef ya dubi maman nata ya ce" Dama kin san abinda ta aikata kika rufe min?"

Da sauri ta girgiza kai ta ce" Ko ɗaya ban taɓa sani ba."

Nabihat ta zaro ido tana sake fashewa da kuka ta ce" Haba Mama haba mama, maimakun ki kama min sai ki juya min baya kamar lokacin da aunty Fauziya ke kukan ki rarrashi Abba kika ƙiya? Haba Mama nan fa na faɗa maki nice na kai gidan su surukan Intisar aka ba Hajiyarsu har ta fasa auren da Bilal kuma shine zaki ce baki sani ba? Wallahi Abba ta sani kuma ita ta ce kar a yi ka ji korarmu zaka yi daga gidanka."

Chef ya jima kansa sadde yana kallon ƙasa, har AA da ya yi mutuwar tsaye yana ayyana _'Kan uba, eh lalle wannan shugabar sheɗanun duniya ce. '_

Ya dube shi ya ƙaraso inda yake tsaye a hankali ya riƙe hannunsa a tausashe ya ce" Aba, please kar ka saka abin nan a ranka, tunda an ga wanda ya aikata kawai a rufe maganar, Allah ya kiyaye gaba."

Chef ya dube shi a hankali na kusan minti biyu, a raunane sosai ya ce" Ta yiwu a lokacin da Allah ya bani wacce ke kuka tana min biyayya na yi watsi da ita ne yanzu Allah ya bani wacce zan yi kuka saboda ita ko son?"

Aswan yayi tsuru dan zuciyarsa ke ayyana masa ya ce eh wannan hakane gaskiya, sai dai yanayin na chef ya saka shi dole ya tausasa a hankali ya ce" Ai ka yi nadama, kuma ka gyara, wannan ba komai bane kowa da irin rashin jin sa Aba, ka yi haƙuri kar ka kore ta."

Chef ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Babu asarar da ta kai na rashin dace da mace ta gari."

Da sauri maman Nabihat ta dube shi ƙirjinta na sake sarawa, a hankali ya ɗora da faɗin " Ai na yi alƙawarin duk rintsi ba zan kuma korar ɗa ba, ba zan koreta ba, amma kuma bincike tunda ya hau kanta zata je kotu dole ta faɗi dalilin da yasa ta yi haka, in bata da matsala a ciki babu abinda zai hau kanta, sai dai abu ɗaya na sani..."

Ya yi jim kansa a ƙasa ya ce" Ni dai ba zan so auren mai irin halayyanta ba, haka kuma na haramta maka aurenta, wallahi ko bayan raina na haramta maka aurenta, ta ginawa kanta ramin mugunta ta faɗa da kanta, a yanzu haka ina kyautata zaton tana da wasu samarin saboda furucinta, ko menene Allah ya sawaƙa, ka je son zan shigo in samu Elhajin dan wallahi na gama yanke hukunci ba zai hana ba."

A tsorace Hajia ta ce" Aban Nabihat, subhanallah! Wai me yayi zafi haka? Dan Allah kar ka yanke hukunci cikin fushi ka yi haƙuri mu je mu zauna, jibi ne fa auren nan, ya ya zamu yi da baƙi?"

Wani irin kallo da ya wurga mata lokaci ɗaya ta ja baya daga matso shin da ta yi,muryarsa a birkice sosai ya ce" Kar ki sa in duba tausar zuciyata da na yi niyyar yi in barki saboda ƴa] anki in


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login