Showing 393001 words to 396000 words out of 397328 words
ma da ya sauko daga makaranta nan aka sauke shi dan ya san su basa gida.
*10:38 na dare*
So yake ya ci gaba da aikin duba takardun dake gaban shi da hotuna da wasu ƙananan memoires dake ɗauke da wasu manyan hujjoji, sai dai rashin dawowar ta gidan nan da kuma Safwan da aka kawo shi kaɗai ya kuma tabbatar masa bata gidan Anna har lokacin sai hankalin shi ya fara barin gangar jikin sa, nutsuwar sa ta watse, ya rasa me zai kama a aikin nashi, ya yi tsaki ya fi a irga, ya buga table ɗin gaban shi sau ba adadi, shin me ya mata? Me kuma take niyyar aikatawa? Yaji kenan za ta masa? Bayan tasan bashi da wata bayan ita? Tasan ita ce komi nasa.
Alƙalamin hannun shi ya cilla kan table ɗin yana hautsina sumar kan shi ya rufe idanuwa, Safwan dake zaune da litattafan sa yana karatu ne ya dube shi yace "Dady, na kawo maka ruwa ne?"
Kallon shi ya yi a tausashe ya girgiza masa kai yace "A'a, thank u."
Da kulawa Safwan ya sake cewa "Dady ko kan ka yake ciwo? In kira aunty Yussy ta zo ta duba ka?"
Tsurawa yaron idanuwa ya yi yana kallon shi, sai kawai ya ji wani murmushi zai suɓuce masa saboda shawarar da yaron ya kawo, a hankali ya jinjina masa kai alamar e, da sauri Safwan ya tashi ya je ya ɗauko wata ƙaramar waya kamar ta wasa amma kuma tsaf take kira har bangon duniya, dama ya bashi wayar ne ya saka shi hardace lambar shi da kuma ta Yusrah da ta Aba, sannan ya saka masa layin sa a kira kai tsaye kawai sai dai a cire kuɗin a asusun shi, dan haka ba ya aika kira ace masa bai da kuɗi sai dai idan matsalar sadarwa ta yi ƙarfi, dan ko game da aka zuba mishi a tab yana yi lokacin hutun shi har waɗanda basa buɗewa sai da data yake da, kuma tsaf yake bugasu saboda gidan zagaye yake da wifi, ba na ciki ba ko wanda ke ƙofar gidan zaune yana anfanuwa da shi.
Tuni Safwan ya zurawa Yusrah kira, duk da zuciyar ta ta bata ko shi ya sa Safwan ya kira ta, amma sai ta dake ta ɗaga kiran tana danne duk wani abu dake ran ta na damuwar rashin mijin ta musamman da ya share ta bai sake kiran ta ba, da kuma rashin ɗan ta ɗaya a kusa da ita, gashi ta ƙi nunawa Manal da uncle Sul akwai wani abu bare su bata shawara, cikin dakakkiyar murya tace ma Safwan _"Babba, ba ka yi bacci ba har yanzu?"_
Safwan na takowa kusa da AA ya zo ya tsaya gaban shi yana bata amsa da _" Bamu yi bacci ba, aunty Yussy sai yaushe za ki dawo wai? Dady fa bashi da lafiya."_
Gammmmm! Gaban ta ya yi wata irin mummunar faɗuwa har saida ta miƙe tsaye tana dafe da ƙirjin nata tace _" Bashi da lafiya? Me ya same shi? Yana ina? Me yake damun shi Safwan? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"_
Duk ta yi maganar tana rushewa da kuka tare da jawo gyalen ta ta yafa, ta ɗauki abun goyon AA babba tana saka yaron Safwan kuma cike da wayo ya kai hannu ya taɓa wuyan AA da ya lumshe idanu yana son yin murmushi yana ayyana _'Nono ba kya yi farin banza ba, ko ba daga ni ka fito ba ai ka isa ɗauko halayena yaro, Allah dai ya maka albarka, Y. Turaki kuma kin ji kunya wallahi, ace ba ki da aiki sai ɗagawa miji hankali.'_
Safwan kuma da ɗaurewa ƙarya gindi sai yace _"Kan shi ke ciwo, kuma jikin sa ma kamar da zafi, aunty Yussy ki yi sauri ki dawo dan Allah."_
Da sauri ta amsa mishi da _" Gani nan zuwa Safwan, gani nan."_
A firgicen nan ta so tafiya ta yi tuƙi a daren nan ga kuma goyo, sai Allah ya taimaka uncle Sulaiman ya shigo, shine fa ya rarrashe ta tare da karɓan makullin motar ya tuƙa ta har gida, har farfajiyar tsakar gidan ya sauketa yana kallo ta shiga bayan ya ce ta je ta duba zai jira, idan da sauƙi sai ya tafi shima.
Tana shiga falon ba kowa, dan tunda Safwan ya gama waya da ita ya tashi a kasalane ya ce masa ya je ya yi shirin bacci ya kwanta, haka ko aka yi har ya kashe masa fitila ya mishi saida safe, shima ɗakin shi ya shiga ya tsala wanka sannan ya zauna daga shi sai towel akan kujera ya miƙe ƙafafun shi kan ƙaramin table ɗin dake ɗakin yana jijjiga ƙafafu cike da jiran ta zo a ci uwar sabada ko raini ya fita a tsakanin su, dan ba zai iya jurar wannan lamari ba, da wanne zai ji? Harkokin kula da kasuwancin Aba? Ko da aikin shi mai wuya da wahalarwa? Idan ba zai samu nutsuwa daga gare ta ba me kenan? Ya yi ya da rayuwar shi?
Ba ta tsaya duba ina Safwan yake ba kawai ta wuce ɗakin shi kai tsaye bayan ta aje AA babba kan kujera da niyyar za ta dawo yanzu ai, tana buɗa ɗakin da ƙarfin akan gado ta sauke dara daran idanuwan ta, amma sai duhun dake ɗakin ya hanata ganin komai, dan haka ta ɗan ƙara tako ɗaya zuwa biyu tana kai hannun ta inda fitulun suke ta kunna, take haske ya mamaye ɗakin sannan ta gan shi zaune nan yana kashe mata wani irin kallo mai kama da na warning da kuma za ki gane kuren ki...
Ƙasaƙai ta yi tana kallon gaba ɗaya jikin shi ta ɗan tako kaɗan da mamaki tace "Ya jikin naka? Da sauƙi ne? Ko dai lafiyar ka ƙalau?"
Sauke ƙafafun shi ya yi daga kan table ɗin ya ɗora guiwoyin shi sanan cinyoyin shi yana ƙare mata kallo yace "E, lafiyata ƙalau, haka kawai ɗana ya ji baya jin daɗin ganina a damuwar da mahaukaciyar Yayar sa ta saka mahaifin sa, shine ya ce miki ban da lafiya, ni kuma garas nake idan kika cire..."
Wata miƙa ya yi yana miƙewa tsaye yana faɗin "Ƙasan ne kawai ba daɗi, ƙaniya nake buƙata dan na horar dake akan hukunt..."
Da gudu Yusrah ta juya za ta bar ɗakin tana faɗin" In ka isa in zama miyar taushe ka sha ni, in yi yajin baka yi biko..."
Ita ma dai kalaman nata ne suka ƙare ɗiff saboda tuni ya carbota kamar ya riƙo kaza tare da ƙyalƙyalewa da dariya ya fara ƙoƙarin haɗa bakin shi da nata yana faɗin" Bari kinga yadda zan kurɓi wannan taushen kuwa, sha zan yi iya sha, kuma babu abi da za'ayi da jikan Anza."
Yusrah na neman zillewa ta fashe da kukan shagwaɓa tace" Allah ka sha shi cikin ka lalaewa zai yi, ka daina AA, uncle Sul fa yana waje shi ya kawo ni."
"To ya tafi mana, gayyatar sa nayi gidana? Shi ba sakamakon na can hannun ƙanwata ba da ya tabbatar mamu shima raya daren sa yake yi da ita ba, sai ni ne zan masa kara?"
Ya ƙarashe tare da sumbatar leɓunan ta ya ɗan dangware mata kai yace "An ji kunya Y. Turaki, wai a yi yaji gidan ƙanwar miji, anji kunya dai gaskiya, muje in miki wanka."
Kallon fuskar shi tayi tana turo baki kamar wata baby tace "Ni ai ba ni kaɗai na ji kunyar ba, AA da budurwa fa kake waya ɗazu ko? Wallahi dai ka ji kunya kai ma."
Girgiza mata kai ya yi bayan ya ɗauketa cimak suka nufi ban ɗaki yace "Ko kaɗan, wani aiki nake my lady, a da ma da bana tsoron mata ban kula su ba, bare yanzu da nake tsoron *mariƙiyar maraya*, ni naki ne ke kaɗai."
Maƙale wuyan shi tayi cike da jin daɗi ta biyewa mijin ta suka manta da AA babba ma dake falo yana bacci bare kuma wani uncle Sulaiman dake farfajiya yana jira ya ji wai ya? Za'a je asibiti ne? Za'a buƙaci taimakon shi ko ya? Da ya ga shiru ne kawai ya sake ficewa da motar ta Yusrah.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
12/07/2024, 12:06 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
~_*END*_~
*100*
Yau tun da ya farka da rigima ya tashi, yadda ka san cizonsa ake yi, ga aikin bincike ƙato dake gabansa wanda a yanzu AA baban jami'in tsaro ne shi bayyananne kuma ɓoyayyen mai binciken ƴan siyasa ne, wanda a haka yake cutarsu san kuwa ɗan su ne, a jikinsu yake, abokin aikinsu ne, kuma mai bincikar badaƙalarsu cikin ruwan sanyi ne, musamman ma da ya samu Aba ya cire hannun sa a harkar neman kujerar da ya so yi, sai hakan ya bashi damar shiga cikin su yake ragargazar su, amma kuma sai ya farka da son a yi rigima ko da waye yau.
Wayar sa ya ɗauka ya zo falo yayi wani zama na neman fitina ya dannawa Mukhtar kira, Muktar na ɗagawa yayi sallama AA ya ce _" Wa'alaika salam, kai in tambaye ka?"_
Mukhtar ya amsa da _" Ina ji."_
AA ya ce _" Me yasa dan ka raina min wayo baka ce min Yaya?"_
Mukhtar yayi shiru yana jin sa kafin yace _" Yaya kuma?"_
AA ya ce _" Eh yaya, ba ƙanwata kake aure ba, ko zumuncin mu za ka datse ne dan iskanci?"_
Mukhtar ya dafe haɓa yace _" Tofa."_
AA ya wani karkace yace _" Ni ne tofa ɗin? Da ni kake?"_
Mukhtar ya gyara kwanciyarsa a hankali ya ce _" Allah ya baka haƙuri, in sha Allah ba zaka samu faɗan da kake nema daga wajena ba, to ta amarya na yi ko taka? Sai anjima aboki yanzu muna cikin fagen murza ƙaniya."_
Daga nan ya kashe kiran, AA ya ɗauke wayar daga kunnensa yana kallo ya wani nuna ƙirjinsa ya ce _" Muntari ni za ka rainawa wayo ko? Ba laifi Allah ya haɗani da kai, dan na baka ƙanwata ne ba zan je gidan ba in ba dan shi ba yau da sai na yi ƙasa ƙasa da kai."_
Yusrah dake can wajen diner tana gyarawa ta ƙara leƙowa ta ɗan zuba masa ido kafin ta taɓe baki ta ci gaba da aikinta,
_"Hello Arif, kana gidan uban wa yanzu?"_
Ya faɗa da ɗan ƙarfin da ya sa Yusrah ƙara leƙowa ta zuba masa ido, ta gama yarda cewar ta yiwu dan yaji yau zata tara baƙi ne zai tsiro da bala'i ko? Ai wallahi kallonsa take yi yau sai ta karɓi baƙin ta.
Arif ya yi wani sheƙeƙe ya ce _" Oga ka sha wiwi ne?"_
A zabure ya mayar masa da cewa _" Roci na sha, Arif roci na sha, ni za ka maidowa tambaya da tambaya?"_
Arif ya ɗan dakata da tafiyar da yake ya ce _" Ka ga, gaskiya in buru'uba ka ke so mu yi ba yau ba, na ɗirkawa ƴar mutane ciki dake mayar da auren mu, yanzu haka gani a hanyar chemis zirganiya ta sameni, abin sai ya min yawa ai idan na biye maka, sai anjima kawai ma haɗe a erea."_
Shima ya kashe kiran ƙit hakan ya sa AA rafka tagumi yana tunani, can ya danno lambar uncle Sulaiman ya kuma gyara zama, uncle Sulaiman na ɗagawa ya ce _" Barka da warhaka sirikina, fatan an wuni lafiya?"_
AA ya wani gyara zama ya ce _" Sulaiman nine za ka yiwa magana ba sallama? Ka san ai ƙanwata ka ke aure ko? Wannan ai wulaƙanta siriki ne."_
Yusrah ta ɗago a zabure ta zuba masa ido, la'ilaha illalah! Wannan mutum wannan mutum akwai fitinanne, to in taƙamarsa ya ba da ƙanwa shi uncle ai ƴa ya bashi, ludayin dake hannunta ta riƙo ta nufo falon a lokacin da uncle Sulaiman ya ce _" Ina ga yau ƴan mutuncin basa kusa, in ka dawo hayyacin ka ka zo in yafe maka, ni da nake da amarya ina ni ina faɗa? Sai anjima."_
Shi ma ya kashe masa waya ya ɗago a birkice ya sauke dubansa a kan Yusrah da ta tsaya tana jijjiga ta ce" Uban nawa ne kake kashewa bala'i haka AA?"
Aswan ya miƙe yayi tsaye ya ce" An kashe, aka ce an kashe Y. Turaki, ke dan cin zalin ba dan na ƙara maki wani cikin bane kike min faɗa kina cewa yaushe ma ki ka haihu? Kin ji kunya Y. Turaki kuma daidai nake da ke wabilahilazi, daidai nake da ke, ki min fitsara ki gani in kya je aiki nan da sati ma malama."
Yusrah ta zuba masa ido, ta gama karantar abinda yake nufi dan haka a nutse ta ƙaraso gabansa ta tsaya cikul a gabansa, ya ɗan ja baya ya ɗauko ɗan kwalinta ya ɗaura a tsatso yace" Bismillah ke in ban nanaki a ƙasa ba ki ce ba jikan Anza nake ba."
Ta kama haɓa tana kallonsa, wato bai samu wanda ya biye shi ba a tarin waɗanda ya kira, shine yake so ta masa garaje ya sumgumeta sai kan gado ya darji banza ko, ta yadda idan baƙin nata suka zo zasu shaida an mata ci wawu lega daga tafiyar ta, to ta Allah ba tashi ba, ita ma yanzu ai ta fara fahimtar shi ba laifi.
A hankali ta kama hannunsa a nutse ta nufi hanyar waje da shi tana kwance kallabin ta shi kuwa yana biye da ita dan wallahi sam bai ma gane waje ne zata yi da shi ba, ya zata irin abin nan na soyayya da ta saba masa ne in ta ga yana neman bala'i take kai shi dakin ya ci ƙaniya iya ci, shi yasa jikinsa yayi sanyi yana biye da mata yana kallon haja iya haja bai ankara ba, sam bai gane cewar cutarsa zata yi ba sai da ta kai shi ƙofar falon ta ja ƙofar ta ta kulle ta ɗaga murya ta ce" Aban Haidar da sadauki ka je ka samu a waje ku daku amma ba dai ƴar Turaki ba, kuma ciki da ka min kai ka sani an dai ji kunya a ringa ɗirkawa ƴar mutane ciki, Allah ya kiyaye hanya Rohi."
Wuri wuri ya yi da ya gano ƙofa ta kawo shi, ya kalli bayansa ya ƙara tabbatarwa ya ɗaga murya ya ce" Turaki ni zaki kora? In kin isa ki buɗe ƙofar nan yau ki ga yadda zan yi ƙasa ƙasa da ke."
Yusrah ta yi dariya ta yi masa shiru, ya ƙara ƙwanƙwasawa gashi ky ta murɗa da ya buɗe da emprinte ɗin sa ya ce" Yanzu ni zaki kora dan kin samu za ki yi baƙi ko? Ni zaki hanawa haƙƙina ko?"
Ta sake ƙyale shi tana sha'aninta ya ce" Yanzu dan kin ga Anza ya rasu ne kike min haka ko? Ba komai duk wanda ya shiga haƙƙin maraya ai shi da Allah."
Ya ɗan dakata ya ga dai shiru bata buɗe ba a dole ya juya yana harare harare ya nufi wajen motocinsa yana faɗin" Allah ya sa da mai ky a jiki, ina ma zan je to? Ta san dai ba zan je mu yi da Anna ba, tsaf Anna zata ci uban maraya dan ba ta son shirme, Aba kuwa ya jima da daina biyewa lakuru ya ce mahaukata ne mu, inna lillahi! Wa zan tarda wanda na fi ƙarfi?"
Motarsa ta sport kaɗai ke ɗauke da ky, ita ma dan za'a wanketa ne aka amso ky ɗin, kuma an fara wanke wasu ne yasa ba'a kaita ba dan haka ya buɗe ya shiga yana murmushi da ya tuna inda zai je ya yi wani aikin Allah.
Harbata yayi titi ya ɗauki hanyar gidan Hajia yana ta addu'ar Allah ya sa ya kama wani da wani laifin, da ya je ya samu samarin gidan Hajia sun tafi islamiyya, Hajiya ta tafi gidan suna sai ƴan matan gidanta kawai suna halin da suka saba wato zaman danna waya bayan ga aiki jibge.
Tunda ya zo gidan suka zabura suna masa sannu da zuwa, domin a zuwan da yake yi da wanda suka yi suka gama gane waye shi, duk da bai taɓa yi musu mugunta ba amma suna gudun ranar da hakan zai faru.
Kujerar tayani tsegumi ya ajiye a gabansu ya bi su da kallo ɗaya bayan ɗaya, kai ya cira bayan ya dantse leɓensa ya miƙa hannu ya ce" Ku bani wayoyinku?"
Da sauri suka ringa miƙa masa suna kallon juna, ya haɗe wayoyin ya ajiye a gabansa kafin ya ce" Ni ba malaminku bane, kuma ba zan iya maimaita muku abinda ake faɗa muku kullum ba, abinda nake so da ku shine maza ku tashi ku kwaso kayan ku kaf, ku fito da su nan sannan a tara ruwa mu wanke dakin."
Sosai gabansu ya faɗi, wanke ɗakin? Kan uba! Ta ya ya? Sai dai alamunsa ya gama