Showing 123001 words to 126000 words out of 397328 words
sun mayar da layin wajen bushe bushen su.
Ta zo zata karya kwana shi kuwa ya zo a mota daga bayan su, bai tsaya neman ba'asi ba ya nemi shigar samarin nan ya danne oda sannan ya afka masu, domin a yanayin da ya ga budurwar na gudu tana ihu su kuwa harda wuƙa ya tabbata mugun abu suke binta da shi.
Ɗaya ya samu ya yi gefe da gudun tsiya, ɗayan kuwa bai idasa yin gefen ba ya bige shi da abin madubin motar ya cin mata ya bude mata ya ce" Shigo baiwar Allah."
Kasantuwar tana gudun neman ceton rai a guje ta afka motar ta ja ta rufe tana haki haɗi da kuka faɗi take" Mu je mu je mu je, wayyo na mutu, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un! Na shiga uku, dama sai da Hajia ta faɗa min waje ta fi ƙarfin budurwa irina amma na fito ni kaɗai, na fito da daren nan wayyo na mutu na lalace."
Sakin zance take na tashin hankali shi kuwa tuƙi yake har sai da ya ɗauki hanyar da ta kusan kai shi gidansa sannan ya rage gudun sosai, dama fitowa ya yi nemawa Intisar ganda, har sun kwanta barci ta tada ballin ganda take so, da ya tambayi inda zai samu abokinsa ya masa kwatancen anguwar nan yace akwai wata mata dake yi mai daɗin gaske shine ya zo ya siyo mata yana dawowa ya ga wannan abin.
Furucin bakin yarinyar da irin firgicin da take ciki ya saka shi gane cewa wannan yarinya idan ma ta saba rashin jin ta ba na biye biye bane, ko da yake mutum na yau sai Allah dan haka ya dubeta ya ce" Ki ɗan nutsu dan ki faɗa min gidan ku in kai ki ko ki bani lambar iyayenki ko wani babba a gidan ku in neme shi in sanar masa abinda ake ciki sai a ɗauke ki."
Yusrah ta yi wani irin tsittt tana kallon wayar hannunta, sai kuma ta ɗaga ta dube shi muryarta a sanyaye ainun ta ce" Suna clinic Alheri , ka sauke ni a nan in samu adaidaita in tafi."
Agogon hannunsa ya duba, ya kalleta ya ce" Ayya! Sorry, basu da lafiya ne? To kin ga ni gidana kusa da nan ne sosai mu je in ba iyalina saƙonta kar barci ya ɗauketa tana jira sannan na mata bayani kar ta ga na jima hankalinta ya tashi, daga nan sai in kai ki, kin ga yanzu waje cike take da hatsari, da rana ma an sace mutane balle da dare, ki kula, ko menene bai dace ki fito daga gidanku da dare ba kin ji?"
Yusrah ta gyaɗa kai murya a sanyaye ta ce" To na gode Allah ya saka da alkhairi."
Bai kuma ce mata komai ba har suka ƙarasa gidan nasa, umarnin ta biyo shi ya bata, ta kuwa bin nasa dan duk da dare ne gidan da mutane waɗanda yanayin su ya nuna ba masu cutarwa bane sai dai a wani ɓangaren na daban, ita dai idan ma ƙwaƙwalwarta ta tushe ne saboda damuwa har ta iya bin namijin da bata sani ba haka ziƙau ne? To kuwa ta kunce ɗin, biye dai take da shi har ya buɗe falon ya shiga da sallama a bakinsa domin tuni mai aikinsu ta shige da kwanon gandar.
Ɗago da kanta ta yi tana amsa sallamar haɗi da ɗan shagwaɓe fuska ta ce" Baby tun ɗazu nake jira gashi wayarka bata shiga, hope lafiya?"
Murmushi ya yi ya ƙarasa ya zauna yana faɗin" Ke dai bari sweetheart, haɗuwa na yi da wata baiwar Allah wasu samari sun biyo ta tana ta ihu, shine na taimaketa, yanzun ma kaita zan yi asibiti ta ce iyayenta na can, shine nace sai na kawo maki sannan mu wuce, Ina kike? Shigo ku gaisa mu je." ya ƙarashe yana miƙewa dan Yusrah bata shigo ba tukuna.
Da yanayin tausayin da ya bayyana a fuskarta ta ce" Ya rab, yanzu ba security a wasu anguwanin sai addu'a kawai, bab Allah ya sa dai basu yi mata komai b... Yusrahhhhh?" Ta faɗa da ɗan ƙarfi tana miƙewa tsaye.
Yusrah ta dubeta da sauri ita ɗin ma, lokaci ɗaya ta zaro ido ita ma ta ce" Aunty Intisar?"
Intisar ta ƙaraso da sauri tana faɗin" What, ke ce? Yusrah? Daga ina kike? babu irin neman da bamu maki ba, ina ki ka je ne? Ina Safwan ɗin? Ya rab! Bab ka ga Yusrahn Bilal ce fa, ita ce ka haɗu da ita?"
Yaya Mubarack da ɗan mamaki ya dubi Yusrah ya kalli matarsa ya ce" Eh ita ce, amma ita ta ce iyayenta na asibiti, kuma tana ta maganganu kamar dai mahaifiyar ta ta hanata fita waje ita kaɗai, Yusrah me yake faruwa?"
Yusrah ta yi tsuru tsuru ta kasa furta ko da a ne, Intisar ta kamo hannunta ta kaita wajen kujera tana kallonta ta ce" Yusrah, ko wajen Safwan ne kike nufin zaki je? Wace Hajia kike maganarta?"
Yusrah ta yarfar da hannu a hankali ta ce" Aunty Intisar iyayena sun rasu fa."
Intisar ta sauke ajiyar zuciyar cike da tarin tausayi, a hankali ta dawo gefen Yusrah ta zauna ta riƙo hannayenta tana kallon ta ta ce" I'm sorry dear, i'm sorry ƙanwata, na san sun rasu, na je na nemi labarin ki dan mun damu sosai, ki yi haƙuri kin ji? Lokacin su ne ya yi wanda mu ma du shi muke jira, idan ya yi ba tsumi ba dabara sai mun amsa kiran Allah, ki yi haƙuri kin ji?"
Yusrah ta gyaɗa kai hawaye na ɓalle mata ta ce" Dama, asibitin ce zan koma dan in ga in dreban da aka ce ya ɗauki Safwan ya dawo? Ko zai taimaka ya bani shi, shine ƴan daba suka biyoni."
Cike da tausayin yanayinta, da tarin ƙoƙarin hana kanta kuka ta ce" Yusrah yau kwana tara fa, ina kike tunda muka rabu da ke? Dama baki ga Safwan ɗin ba?"
Yusrah ta fuskanci Intisar da kyau ta ce" Eh, dama da muka rabu da ku ƙauye na je, baya wajenta sai na ɗauki hanyar Katsina zan je Funtuwa dan in je wajen ƙanwar Mamarmu ko ita ce ta zo ta ɗauke shi? Sai kawai a hanya na haɗu da wani ɗan ballaja'u ɗan iskan gari da ƙwaya ta gama rikita shi ya min shari ya sa aka rufe ni a cel, daga nan da na fito wani mai suna Jafar ya kaɗe ni shi da matarsa..."
Nan ta kwashe komai ta sanarwa Intisar har fitowar ta a yanzu da dalilin da yasa ta ga ba zata iya zama silar ciwon Hajiya ya tsananta ba bayan duk irin soyayyar da ta nuna mata har zuwa haɗuwar su da Yaya Mubarak.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*33*
Sosai ran Intisar ya ɓace, ta ringa faɗa da faɗin lallai ɗan ballaja'u kika haɗu da shi da ba ya tsoron Allah, lallai Tasneem bata da hankali da ta taɓa lafiyar Yusrah da sai ta rufe ta, Yusrah kuma ta mata daidai da ta bar masu gidan su ƙarata da Tasneem ɗin.
Yaya Mubarack sai a lokacin ya yi magana, cike da tausayin Yusrah ya ce" Madame, a'a fa, wannan ba shara'a bace, sam bai dace ba ace Yusrah ta bar gidan Hajia ba tare da sanin kowa ba, ko ba komai masoyi ai ba maƙiyi bane, kuma Hajiar nan ta ce bata da lafiya, shikenan tunaninku na mata ya raya mata in ta tafi shikenan Hajia zata samu lafiya? To ke ina ne kike da niyyar tafiyar da ban haɗu da ke ba yanzu?"
Kan Yusrah a ƙasa jikinta a sanyaye ainun ta ce" Ni a yanzu duk hankalina ba a kan abinda yaya Jafar ke nufi da ni ba yake, ga abinda yake faruwa shi yasa na gudu da nufin idan na je aka bani Safwan sai mu koma gida in samu masu gyara su gyara mana ɗaki ɗaya a cikin gidan sai in kama sana'a, idan kuma hali ya bada sai mu koma wajen aunty Fureira can Funtuwa."
Galala ya kalleta kafin ya girgiza kai ya ce" Yarinya ƙarama da ke zaki je ki zauna a gida daga ke sai marar lafiya? Ko baki da kowa a duniya ai ba za'a rasa na Annabi ba, baki san irin case ɗin da ake fama da shi ba ko? In dai aka gane mace ita kaɗai ce a gida an fara kawo mata wulaƙanci kala kala, ɓarayi ne, kwarata ne, balle ke da yarinya ce ai sai gyaran Allah."
Sai kuma ya gyara zama yace" Look! Bani lambar gidan da kika baro ko aunty Fureiran da kike magana in kira in sanar masu abinda ake ciki da hannun da kike, ba kuma zan yarda ki fita haka kawai ba Allah ya kiyaye wani abu ya same ki, bani."
Intisar a hankali ta ce" Bab, idan ka yi kiran su suka amshe min ita fa? Babu inda zata je, zata zauna da ni, zan samo mata aiki likita ce fa babba, zan zama ƙawarta in hanata kukan rashin iyaye."
A nutse Yusrah tace" Lambar aunty Fureira tun da na karɓo wajen Goggo nake ta kira ba ya shiga, wani lokacin kuma da ya yi ƙara sau ɗaya sai ya tsinke, sai dai ko lambar Fatila."
A dake ya sake cewa" Bani ita ɗin." A nutse bayan ya loda lambobin Fatila a wayarsa ya dubi matarsa ya ce" Sweetheart, komai na rayuwa a bi shi a tsarin da ya kamata ya fi alkairi, Yusrah tana da dangi, ta haɗu da mutanen kirki, zan sanar masu, kuma zamu nemi danginta,nd zan kai ƙarar dreban da ya ɗauki yaron nan idan ya min gardama, Yusrah ba yarinya bace tana da damar zaɓar inda zata zauna, zan nuna buƙatar a bani in riƙe in na ga danginta na nesa ko na fuskanci da cutarwa a zamanta da su kafin Allah ya sa takardar da nake nema ta fito, iyayen riƙonta zan gan su, domin ba zan so ta mana abinda ta masu ba, idan muka bi komai yadda ya dace zata zauna a wajen mu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa."
Ya dubi Yusrah da kula sosai ya ce" Ƙanwata ki yi haƙuri ki daina kukan hakanan kin ji? In sha Allah za'a ga ƙaninki kuma zaki samu nutsuwa bi'izinillah, but yanzu dole in miki faɗa, abinda kika yi tun farko bai dace ba, na san hankalin ki ba a jikin ki yake ba yanzu, amma idan abu ya faru da kai ya kuma faruwa sai ka gane, duniya abar tsoro ce, ke mace ce, killacewa ya dace da ke , tsaro ya dace da ke, kin shigo hanuna now, kar in ji ko in ga kin aikata irin abin nan da kika aikata yanzu, tashi ki je ki huta, yanzu zan yi kiran su Hajia, bab kaita ta samu waje ta huta."
Intisar kanta da shakku take kallon mijin nata balle Yusrah da shakkunsa ya cika mata ciki sosai har take ganin kamar Aba ya shiga rigarsa ya wanke ta, kuma sai a yanzu ta ga eh lallai bata fa kyauta ba, har suka shiga ɗakin da Intisar ta ja ta kanta a ƙasa, har sai da suka shiga ne Intisar ta kama kafaɗunta murya a sanyaye sosai ta ce " Yusrah ki yi haƙuri da faɗan da bab ya maki, ta yiwu akwai abinda ya ɓata masa rai a waje ko ya tsorata ne da kika fito bayan abubuwan da suka faru, kin ga bari in je in kawo maki abinci da kayan barci kafin Allah ya kaimu in je kasuwa in maki siyaya, ki zauna ina zuwa."
A sanyaye Yusrah ta ce" Aunty Intisar bana jin yunwa sai da na ci abinci da yamma kuma ban cika ci da dare ba."
Intisar ta ce" Ok, ina dai zuwa ko fruits kya sha, wannan ramar bana son ta, ina zuwa ƙanwata."
Daga haka ta bar ɗakin ta zo falo a lokacin yaya Mubarack na magana da Yaya Ja'afar, a nutse ya faɗa masa komai ya ƙarashe da faɗa masa ashe yarinyar ƙawar Madame ɗinsa ce da suke ta nema, ƙarshe dai sun gaisa da Hajia tana ta godiya tace in sha Allah a gobe gobe zata zo gidan, suka yi sallama bayan ya musu kwatance ya ajiye ya zubawa Intisar ido wacce ta je ta kaiwa Yusrah fruit salat da ruwa da kayan barci da sabon bruch da dai abin buƙata tace da ita tana zuwa ta dawo ta saka shi gaba bai gama wayar ba tana jiransa ya gama.
Sai da ta shagwaɓe fuska sosai ta ce" Bab, ya kamata ka mata uzuri, na san bata kyauta ba da ta fito daga gidan can, but ka duba fa ka gani irin haukar matar ɗansu, bayan wannan bab yarinyar idan ta samu nutsuwa sai na saka an yi mata therapy na psychisme, ta shanye abu da yawa dake iya buga zuciya ko taɓa ƙwaƙwalwa, inna lillahi wa'inna ilaihi raj'un! Ka duba ka gani dare ɗaya abin nan ya sameta, tana hannun iyayenta ana riƙonta lokaci ɗaya ta zama ita ce zata riƙe, dole za'a samu sake da aikin wasa da abu, kuma a haka ta yi faman nan ne dan ta ceci ƙaninta, ka dubi yarinyar nan, sai tana magana hawaye ya ɓalle mata, tana da buƙatar hutu, tana da buƙatar wa'azi nasiha ja a jiki, tana da buƙatar ƙawa, ƴar uwa, da kuma uwa duka a tare da ita, bab bata da buƙatar wannan fitinar da ta gani a gidan can da wani ƙoƙarin nuna mata za'a aureta ta ji da wasu ƴaƴan su uku da suka ɗauko tarbiyyar mahaifiyarsu, i'm sorry to say Yusrah ba maganin damuwarsu bace, a gaskiya ba dai yanzu ba, zuwa gaba in ta ji tana ra'ayin auren sai ta zaɓi wanda ya mata, but yanzu ba ma zan yarda a mata maganar irin haka ba! Please bab kar wanda ya ce zai amsar min ita, you see da ace danginta sun damu da yarinyar nan da tana tare da su suna neman Safwan, amma kana gani yarinya budurwa an saketa a fili tana fama da ranta, ta yi nan ta yi can babu inda zata ji sauƙi dan iyayenta basa raye? Ya Allah."
Sai kawai ta fashe masa da kuka ta kifa kanta a saman ƙirjinsa tana ɗorawa da" Ita kanta ban yarda da lafiyar ta ba, gini fa ya faɗa musu Bab, ya kamata mu sa a bincike mana jikin ta, dan bata cikin nutsuwar da ma za ta fahimci wani abun na mata ciwo, amma ni nasan da wuya a ce ba ta ji raunin komai ba ko da na nauyin jiki ne."
Murmushi ya fara yi, kafin ya saka hannayensa ya ɗago kanta yana dubanta ya ce" Bab, menene na kuka? Ki kwontar da hankalinki, na fi ki kwaɗayin riƙe Yusrah, zan bi hanyar da ta dace ne dan a bani riƙon yadda zai zamo ina da ikon zaneta idan ta gudu, na mata haka ne dan ta san bata rasa masu yi mata faɗa ba kuma in ta kama a yi mata gagarumin faɗa zan yi mata shi ne a kan gyaran kanta, kar ki yi haka mana tsoro ya shiga raina in fara tunanin anya idan muka samu riƙon kya kwaɓeta in ya kama? Kar ki yi kuka a kan abinda bai kai a yi kukan ba, kar ki ɗaga hankalin ki, na yi haka ne kawai dan in bi ƙa'idar da ta dace wacce ba za'a ce mun yi shirme ba, mutum ce sukutun Yusrah ba abin wasa ba, ba zamu kamata mu riƙe kawai dan mun isa ba, kin fahimta?"
Sai yanzu ta gane inda ya dosa, dan haka ta ringa gyaɗa kai tana sauke ajiyar zuciya, ya yi murmushi ya ce" Kin ci gandar?"
Sai yanzu gandar ta dawo ranta, kuma nan take ta ji yanzun bata da ra'ayin cin gandar, amma sai ta ɗauko ta buɗe tana faɗin " Eh na taɓa, na fi jin karyawa da shi, ko in zuba maka zaka ci?" Ta yi tambayar tana kallonsa dan ta san bakin inda ya ci abincin dare ya ƙare kuma da cin komai a bakinsa sai safiya ta yi.
Kai ya girgiza yana miƙewa ya ce" Bari in je ɗaki, please ƙara leƙota, ki tabbatar da ta kwanta ta samu barci kafin ki fito."
Ita ma ta ji daɗi da ya bata wannan dama dan ta so roƙarsa ta je ne ta ga yanayin Yusrah? Sai gashi da kansa ya nemi hakan dan haka ta miƙe hankali kwance ta nufi ɗakin da ta saka Yusrah, kasantuwar ɗaki ne da baya rabo da baƙi ya sa a share yake a gyare, shinfiɗa kawai ta canza mata ɗazu.
Tana shigowa ta tarda ita dunƙule waje ɗaya a saman gadon, alamu sun nuna ta yi wanka amma bata saka kayan