Showing 234001 words to 237000 words out of 397328 words

Chapter 79 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70052

masa laifi ba? Ita kam da ta cire ko milyan goma ne a aljihun ta ta saka dan ta nuna masa ba ta son halin tsiya wallahi.

Murmushi uwar ta yi bayan ta gaisheta ta amsa tana kallonta ta ce" Kin ga kin sha wahalar banza ta bauta masa da ɗansa ko? Gashi yau an kai kuɗin aurensa sai ki maida hankali ki samo naki mijin dan wallahi ina kan bakana aurenki da shi ko ba zai haɗa ki da kishiya ba sai bayan raina balle ace wai ya fara auren wata ba ke ba."

Kanta a ƙasa, jikinta sanyi ƙalau ta ɗago ta dubi mahaifiyarta, a sanyaye sosai ta ce" Mama, ki yi haƙuri kin ji? Ina kyautatawa da girmama Akhi ne saboda Yayanmu ne baki ɗaya, ina son Safwan har zuciya domin Allah ne ba dan in birge Akhi ba, kuma in sha Allah nima na haƙura, ki tayani da addu'a Allah ya bani wanda zai so ni nima."

Mahaifiyarta tana kallonta bata ce komai ba har ta tashi ta tafi ta ɗauke kai tana taɓar baki ta furta" Gwara da kika yiwa kanki karatun ta nutsu, dan Aswa. ba mijin aurenki bane."

A falon ƙasa kuwa zaune suke Anna da AA suna zantawa a nutse, da kula sosai Anna ta ce" Ka ji basu saka rana ba fa, wai Chef ya ce Hajia ta yi kiransa ta ce idan ya je suka yi shawara sa yi maganar ranar taron."

Murmushi ya yi wanda ya saka Anna ƙure shi da kallo sannan ta ɗauke kanta, a tausashe sosai ya ce" Anna, zan je, ina so na tafi in ga son kafin in je gida, yau dai Anna za'a yi barci mai daɗi na cika maki burinki."

Anna ta ɗauki ƙaramin fulon kujera ta ƙwala masa tana faɗin" Aswan ka kiyayeni."

Dariya ya yi ya ajiye pizzar nan bayan ya sake kallon sama ya ce" Anna, wannan na Y. Turaki ne, dan Allah a yi kiranta ta ɗauka na tabbata bata ci komai ba."

Anna ta bi pizzar da kallo, sannan ta raka shi da ido bayan ya sake yi mata sai da safe, murmushi ta yi a ranta ta ayyana _'Tabbas idan ka ga ana cewa ba'a iya abu ba, ba'a samu wanda ya dace a yiwa ba, Aswan Allah ya sa ba kana ji kana gani zaka rasa abinda ke saka ka biyayya ko da ba ka shirya ba dan wauta ko tunanin ba haka bane.'_

Ta ɗauki pizzar ta shiga haurawa dan idan ta basu tana saukowa zata nufi ɓangaren Aba saboda tana so su tattauna ya ya su aka karɓe su da jaka hmnsin kuɗin sadaki? (dubu ɗari da ashirin da biyar).


*GOGGO HINDA*


Kamar yadda Aba ya umarci uncle Suleiman ya je ya sanar da Goggo Hinda maganar lefen Yusrah da za'a kawo, nunawa ya yi sam ba shi ba Hinda a dai yanzu, saida Aba ya yi zama sosai da shi ya nuna masa kar fa zumuncin da ya rage musu su lalata shi? Kar su yarda sheɗan ya yi galaba a kan su, dukansu suna buƙatar junan su, sannan kar abinda ya faru ya zama silar wargajewar zumunci, idan sukayi duba da ba iyaye a raye, sannan mahaifin su Yusrah shi ma ba ya raye. Da ƙyar dai ya aminta zai je da Aba ya ce masa su ba komai suke buƙata daga gare ta ba, kawai ta saka albarka sannan a bata darajar ta matsayin ta na Yayar mahaifin yarinya.

Da ya je kuwa ya samu ta fatattaki Khadija da bala'in cewa ita ta haɗa ta da uncle Suleiman ɗin, dan haka ko zama bai yi ba daga tsaye ya sanar da ita abinda ya kawo shi, sannan ya faɗa mata ranar da inda za'a yi komai da komai abisa amincewar sa, idan ta samu dama ta leƙa dan ta sa albarka, daga haka suka fito tare da Khadija yana rarrashin ta da faɗa mata suyi haƙuri da yadda mahaifiyar su take, nan sukayi musayar lamba da shi har ya bata lambar Yusrah ma sannan ta masa alƙawarin halartar taron kawo lefen in sha Allah.

A gida kuwa Goggo ta yi alƙawarin ba za ta je tarban kayan ba, za ta bari sai an ɗaura auren sai ta je taga makwancin ta da kuma bajintar da mutanen za su mata da har za'a dinga yi mata wannan iskancin, tana raye a ce za'a kai kayan Yusrah a wani gida na dangin dangiro ba nata ba? To babu inda za ta je.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
06/06/2024, 09:27 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*59*




Hankali tashe maman Joli ta haura kan gadon tare da tallabo uncle Hamat ɗin tana neman fashewa da kukan sangarta tana faɗin "Ideal, me ya same ka ne? Wai me yake faruwa da kai ne? Dubi za ka mutu bana tare da kai, wai me ya sa yanzu kake hanani kwana tare da kai ne? Oh Allah."

Sosai jikin uncle Hamat yake rawa na wata matsananciyar yunwa da ta sako shi gaba kusan sati ɗaya kenan saboda rashin cin abinci dan damuwa, hakan ya kwantar da shi a jigace sai zazzaɓi ya rufe shi da matsanancin ciwon kai da na ƙirji kamar yana ci da wuta, kuma a hakan yana kwance sigari kawai yake ta bankawa wuta yana zuƙa daga kwancen, hakan ya sake haddasa masa ciwon kamar na mutuwa.

Joli ta kalla da ita ma take kan gadon amma hankalin ta akan game ɗin da take bugawa a wayar mahaifiyar ta ta tace "Joli bani wayar nan na kira Dr. ya zo ya duba shi?"

Maƙale kafaɗa Joli ta yi tare da juya mata baya a sangarce ta furta "Um um! Um um!"

Fincikota tayi da takaici ta figi wayar tana faɗin "Za ki bani nan ko sai na ci uban ki? Iskancin banza, kina gani mijina zai mutu?"

Duk ta yi maganar ne tana ƙoƙarin kiran wata lamba, amma dake a haka suka raini ƴar su, ta fashe da kuka amma kuma dan taurin kai sai da ta rarrafo akan gadon ta riƙe hannun uwar gam tana son ƙwatar wayar. Rintse idanu uncle Hamat ya yi dan kukan na yarinyar shigar masa kai yake yi sosai, ita kan ta uwar dan ba zai iya korar ta bane da ya ce ta tafi ta bashi wuri, amma shi kaɗai ya san irin damuwar da yake ciki ta rashin yarinyar nan Yusrah, tunda ya ji labarin za ta yi aure kuma ba wani da nisa ba hankalin sa ya jima da barin gangar jikin shi, tun ranar bai sake samun nutsuwa ba har yau da raunin jiki ya danne shi ya hana masa tashi.

Cikin jin zafin maman ta falle fuskar ta da mari tana daka mata tsawa kan ta bari ko ta sassaɓa mata, da hanzari ta kira lambar ɗaya daga cikin likitocin asibiti ta ce ya yi sauri ya zo ya duba Dr ɗin, ba musu aka amsa mata da yanzu kuwa sannan ta kashe wayar tana sake rumgume shi a jikin ta sai kuma ta fashe da kuka, tana fa son mijin ta, sosai take son mijin nan nata, dan kafin ta same shi ba ƙaramar wahala ta sha ba, dan haka ba za ta so rabuwa da shi yanzu ba, ba ta ma shirya rabuwar da shi ba a yanzu.

Har ƙuryar ɗakin likitan ya shigo ya shiga duba uncle Hamat da taka tsantsan dan kar ya masa ba daidai ba ya samu matsala da shi idan ya samu sauƙi, duk abinda ya kamata ya yi mishi da kuma faɗawa maman Joli ta samu ko madara mai ɗan sanyi ya sha dan cikin shi ya ɗauki wani abun, haka ta shiga lallaɓa shi tun yana baya so ba ya so har ya daure ya sha sannan likitan ya saka masa ƙarin ruwa da allurai a ciki kafin ya tafi da tabbacin zai dawo da dare ya sake duba shi ya kuma saka masa ƙarin ruwa.

*Cikin* magagin bacci ya fara sambatu na abinda ke ranka ɗin nan yana ɗan juya kan shi da ambaton "Yusrah na yarda, wallahi na yarda, ina son ki Yusrah, kar ki gujeni, e na yarda Yusrah..."

Mafarkin da yake yi a baccin sa ya saka maman Joli ganin murmushin da ya jima bai mata irin shi ba, ga kuma wani masifafen yanayi da ta tsinci kan ta a ciki, Ideal ɗin ta? Papan Joli nata? Hamat ɗin ta? Hamat dai nata da take alfahari da samun shi a cikin dangi da ƙawaye? Dr Hamat dai? Shine yake ambaton wani suna can daban a baccin shi ba nata ba kuma ba na ƴar su ba?

Bata san sanda kishi ya turnuƙe ta da wani irin hargagi irin na wacce bata shiga islamiya ba ta mishi wata jijjiga tana fasa ihu da iya ƙarfin ta a rikice tace "Hamat, kai Hamat tashi, Yusrah? Wacece kuma Yusrah? Wae tsinanniyar ce da bata neman albarka? Yanzu Hamat duk iskancin da kake yi a gari ina ji ina kuma hankale banza kawai nayi maka dan gwara ka mik kishiyar waje da ta gida, shine hakan bai ishe ka ba sai ka zo cikin gidana, akan gadonmu na kwana kana ambatar min wata ƴar iska da bata tsoron Allah?"

Tunda ta yi kwaratsin nan da jijjiga shi ya farka a tsorace yana fiƙi-fiƙi da idanuwa, dan ba laifi ya jijjigu kasantuwar yunwa duk ta lashe wani tagomashi na jikin shi, saida ta sake shi kafin ya shiga tariyar kalaman ta har ya gano abinda ya faru, wato mafarkin da ya yi Yusrah ta amince za ta aure shi amma tana gindaya masa sharuɗai ne ya fito fili, a gaskiya ba ƙaramar cuta maman Joli ta masa ba, da ya san zai dinga samun irin haka a bacci bai abinda zai hana shi cika ɗakin shi da allurar bacci ta yadda zai yi ta sumar da kan shi dan ya dinga ganin Yusrah a bacci wataƙila har ya ga rayuwar auren su.

Wani kallo ya mata a shashance sannan ya ɗauke kai yana gyara kwanciyar shi da kallon ruwan da aka saka mishi saboda ganin har yanzu basu yi rabi ba, da takaici ya sa hannu ya ƙara gudun ruwan saboda yanzu burin shi shine su ƙare ya ji ƙarfin jikin shi yadda zai tarkata ya bar mata gidan, wallahi gidan shi zai koma yadda ba ita ba sake ganin shi har sai yadda ta yiwu kawai. Amma jaraba irin ta maman Joli sai ta ƙara gyara zaman ta a saman gadon, ba abinda ya dame ta da ƴar su dake ɗakin kuma wayon ta ya isa ta fahimci komai idan ta ji shi, da wani sabon hargagin tace "Hamat da kai nake magana, wace ƴar iska ce kake cewa kana son ta a cikin bacci? Wacece Yusrah? Ƴar gidan uban wac..."

A tsawace shi ma duk da a jigace yake yace mata "Ke dallah ya isheki haka, e ɗin na faɗa ina son ta, Yusrah ba, ina son ta, sai me? Kin isa ki hanani soyayya ne? To ina son Yusrah son da ban taɓa yi wa wani mahaluki ba, kuma kiji nan idan har na daidaita tsakanina da ita, to ba ke ba ko Elhaj *Muhammad Anza* ya dawo duniya bai isa ya hanani auren ta ba, dan Yusrah ita ce rayuwata a yanzu dai, daga ƙarshe..."

Da yatsa ya nuna mata ƙofa yace" Idan kina son kan ki da lafiya, maza tattara ƴarki ku fice min daga ɗakin, dan ba abinda zaman ku anan yake ƙara min sai baƙin ciki da takaici, maza tashi, ku fice min daga nan, shashashar banza kawai."

Hasbunallah wani'imal wakil! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! La'ilaha illalah! Wani tashin hankalin ma ba ya fassaruwa, kamar yadda akwai abinda zuciyar ka ke gagara ɗaukar shi, haka maman Joli ta yi ta rasa kataɓu, saida ta miƙe ta kama hannun Joli dake kallon uban dan ta ji duk abinda ya faɗa sannan tace "Ka yi auren mu gani Hamat, ka sani shi Anzan ba ya duniya bare ya hanaka, amma ni ina raye ta yadda cikin biyu za'a yi ɗaya, ko kai ka mutu, ko kuma ita karuwar taka ta mutu, amma sai na hana wannan aure."

Juyawa tayi a fusace ta fice daga ɗakin ya bita da harara yana sake jin wata tsanar ta na lulluɓe masa zuciya, shi ina ma a cikin sharuɗɗan Yusrah akwai na ya saki matar sa? Sannan a ce ya yi nasarar furta mata a haka a cikin baccin, to da wataƙila ya samu ƙarfin guiwar jadadda mata e hakane ya sake ta, amma yanzu a zahiri ba zai iya ba, ko kaɗan ba zai iya bane, ba wai dan ta masa wani halacci a rayuwa ba, ko dan so ko alkunyar magabatan ta, a'a kawai ko ta masa abinda yake jin ta cancanci saki ya yunƙura zai yi hakan sai ya ji ya kasa wallahi.

Gyara kwanciyar shi ya yi ya afka tunani, wai shi Dr Hamat Anza ne aka wayi gari saboda tunanin Yusrah har tension ɗin shi na hawa yadda ba'a so, shi mai bada shawara idan haka ta faru sai gashi yau shine da kan shi, shi kam idan ya zurfafa tunani ma sai ya ji kamar kamashi ne ubangiji ke son yi da laifukan sa shiyasa aka jarabce shi da son ƙaramar yarinyar da bata jin wuyar faɗa masa magana... Ƙarar da wayar sa ta yi ne ya katse masa tunani, jawo wayar ya yi ya duba yana cije leɓen shi, ganin wani jami'in police ne wanda gare shi ya samu labarin kamar fa AA ne suka kama suka kai shi PG ya kira, saida ya fara lumshe idanu ya sauke ajiyar zuciya, ba zai gaza ɗaukar kiran sa ba saboda baya kiran shi ma ko da da gaisuwa ne sai akan abu muhimmi, dan haka yanzu ma ya ɗaga yana faɗin _"Oui, je t'ecoute."_

Daga ɗaya ɓangaren jami'in yace _"Yallaɓai na ce ko kana gida ne? Ina kan hanya ne ta zuwa zan sanar da kai wani abu."_

Shiru uncle Hamat ya yi na sakanni kafin yace _"Ina gida, idan ka zo ka ce mai gadi ya rakako zuwa ɓangarena."_

Amsawa ya yi da _" To yallaɓai, sai na iso."_

Aje wayar ya yi ya sake kallon ruwan har sun wuce rabi yanzu, sai kawai ya cire ƙarin ruwan tare da sauka akan gadon ya fita falo ya zauna zaman jiran shi da fatan jin labari mai daɗi daga jami'in nan.

Da jagorancin mai gadi har ya tsinci kansa a falon na uncle Hamat, ba su wani gaisa ba ya zauna yana fuskantar shi a tsanake yace "Yallaɓai, maganar Sani fa abun ƙara ta'azzara yake, dan yanzu haka a dai labarin da naji, idan aka kwatanta shi da yadda aka sanar da ni komai, to gaskiya a nawa ganin kamar fa Sani dreba *yana hannun* chairman ne, dan akwai wani saurayi da ya tabbatar min da yana dawowa daga gona can wajen fita gari ya ga motar chairman ɗin ajiye a ƙarƙashin wasu bishiyu kusa da wasu gonannakin, sannan akwai wanda ya tabbatar da ya ga gilmar ƴaƴan Mani dreba ta hanyar wajen gari, sai kuma Sani dreba da shi ma aka tabbatar min ya yi wannan hanyar can bayan sallah magriba haka, to amma basu sake ganin shi ba daga nan, dan babue ɗin sa ma anan inda suke zama ya bar shi bai ɗauka."

Dafe goshi uncle Hamat ya yi, kawai ya yarda da abinda ya faɗa, kuma wannan shine dalilin canzawar Aswan gare shi, kawai Sani na hannun shi ya kuma san komai, amma me ya sa bai bayyana ba sannan bai masa komai ba? Wannan ne kuma bai sani ba, amma dai ya san ba ƙyale shi ya yi ba, Aswan ne fa, canal Aswan da ya sani, tabbas akwai tanadin da yake masa, ko kuma tarko ya ɗana masa da yake so ya rufta ciki... Ko ma dai menene yanzu shi ba wannan ne gaban shi ba, Yusrah ce yanzu, dan haka ya kalli jami'in yace "Shikenan?"

Girgiza kai ya yi ya ciro wayar shi yana ɗan danne danne kafin ya miƙe ya bawa uncle Hamat wayar yana cewa "Ka duba ka gani Yallaɓai, da na ce maka kamar chairman ne muka kama, sai aka raina maka wayo da cewa wai mai kama da shi ne, amma ni nasan ko akwai mai kama da chairman a duniyar nan to ba anan kusa ba yake, amma gashi nan an tabbatar da shine, wannan videon a lokacin da ake kama su ne shi da yarinyar da ya yi ikrarin matar sa ce, gashi nan ɗaukar ta fito fili kuma fuskar shi ko nace fuskokin su duka sun bayyana."

Wannan video ma bai saka shi jin daɗi ba da ya ga AA, dan shi yanzu ko Yayan nashi ba wani abu da yake haɗa shi da su,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login