Showing 177001 words to 180000 words out of 397328 words
da kafaɗun shi ya haɗata da jikin jirgin yadda sam duk jarabar ta ba kuma za ta iya motsawa ba idan ba shi ya ga dama ba.
Tunda ya zaunar da ita nan ta shiga salallami a zuciyar ta tana jinjina girman fajircin wannan bawan Allah, yanzu yana basamude haka da shi ita balagaggiya ya wani matse mata haƙarƙari haka har suna haɗa kwankwaso? Wai shi wannan dan Allah ta nawa yake sha ne a mashayar? Ta ma wace ƙasar yake sha? Shine har yake ikrarin Safwan ɗan sa ne? Idan ta bar Safwan hannun wannan me zai zama? Kai ba zai yiwu ba wallahi dole ta karɓa shi, amma dai yanzu za ta nutsu dan ta kula aljanun shi sun fi nata, ta yarda haukan dake kan shi ɗanye ne jagab da zai iya duk abinda ya ce mata zai aikata, dan haka Yusrah ta ɗan gyara zaman ta tare da juyawa dan ta kalli window.
Amma tsabar iskanci sai muryar shi ta ji cikin raɗa yace "Ke ki daina taɓani a gaban ɗana muke."
Kallon shi ya yi, sai kawai ta masa wata harara kamar za ta zazzago idanun ta waje tare da ɗauke kai tana leƙen Safwan sai kuma ta bi uban nashi da hararar ƙasan idanu.
Tunda ya yi mata haka ya samu lafiyarta, ita ɗin ma sai ta yi ta kama sunayen Allah kanta a ƙasa tana fatan ya sassauta matsewar nan ya kuma bata dama ta ga ƙanin ta, amma fir ya ƙi bata wannan damar har sai da kafaɗunta suka ringa amsawa.
A sauran awanni ukun nan barci ko ɗis bai ɗauketa ba, shi ma kuma haka, ya yi shiru yana son gane menene zai sa ta tafi ta bar yaro a irin wannan halin a yanzu kuma dan rashin kunya ta yi ta ihun ƙanin ta ne? Tana son shi dama? Tana nufin tana son shi? Yana son ganewa dan ya ga ko zai iya bata damar ganin ɗansa, ko zai iya sassauta mata ta ga ɗansa, sai dai duk sanda ya hanga ya rasa ganewar, irin halin da ya ga yaron nan da rigar dake jikinsa da wani wando shi ba pant ba shi ba gajeran wando ba sai ƙaiƙayi yake yi masa a jiki ya matuƙar ƙona zuciyarsa.
Shigowar hostes ta ɗan duƙa ƙasa ƙasa da turancinta wankakke ta sanar masa cewar zasu sauka nan da ƴan mintuna ta juya ya saka shi dubanta kaɗan, ya sake gane cewar idan bai yi mata gwari gwari ba wannan ba zata taɓa risunuwa dan ihunsa ba, dan haka ƙasa ƙasa sosai ya ce" Kina ji? Idan jirgin nan ya tsaya, ki bari a ɗauke shi a ɗora shi saman kujerarsa, motar asibitin da zata yi masa aikin bayansa na jiran mu, zaki fito a nutse mu je, idan an je ki yi dukkan abinda ya dace a aikinki, ki bari idan ya samu lafiya dukkan abinda zamu yi sai mu yi, but now bana son abinda zai ɗaga masa hankali, aiki ne za'a shiga da shi, ke likita ce, kin sani sarai idan hankalinsa ya tashi komai na iya faruwa, i love my son so much, idan dalilin ki wani abu ya samu yarona *Y. Turaki* (Yusrah Turaki) i swear sai na hana maki zaman lafiya har tsufan ki."
Yusrah da ta zubawa hannunsa mai ɗauke da agogo ido, a hankali niyyarta na ana tsayawa zata je da gudu ta ruƙunƙume ƙanin ta ta ringa gogewa a zuciyarta, a hankali ta sake kallon hannun nasa dake jimƙe ta kuma kalli fuskarsa
Idanuwanta ta ɗauke ta lumshe tana ji a ranta eh, ko menene ya dace ita ma ta yi haƙuri har ya fito lafiya ya warke sannan ta yi, kuma zata ɗauki wayarta ta yi kiran aunty Intisar ta gwada mata shi, ta yadda zata yi screen shot a ba Yaya Mubarak ya kai wajen jami'ai a shiga nemansa ko da ya masu wani mugun abun, sannan a amshe mata ƙanin ta da zarar sun dawo, in taƙamarsa ya taki wani abu ita ma ai ta taka, bai isa ya ƙwace mata ƙani ba ya zauna lafiya.
Sun sauka lafiya, likitoci huɗu na jiran su a mota biyu, ɗaya ta ambulance ɗaya ta docter ɗin ce, suna saukowa kuwa likitocin nan suka karɓi Safwan, tun a nan suka amshi maganin da za'a yi masa suka yi masa sannan suka ɗora shi kan gadon nan na turawa suka ɗora shi bayan ambulance ɗin, Yusrah ta shiga bayan ta zauna daf da hannayensa, Aswan ya shiga ya zauna kusa da kansa, sai Doctern da zai yi masa aiki shi ma ya shiga ya zauna ya amshi file ɗin dake hannun Yusrah sannan ya umarce ta ta bashi dukkan bayanan da ya kamata ace ya sani, irin reaction ɗin yaro a tafiyar nan da komai da komai, ya tabbatar masu suna zuwa za'a shige da shi an gama shirya komai, aikin awa biyar zuwa shida zai ɗauka, aiki ne da ake jimawa a kai, za'a yi masa allurar ɗauke hankali gaba ɗaya, idan an gama za'a kai shi ɗakin hutu za'a kula da shi, daga nan sai a kai shi ɗakin da zai yi kwana goma a ciki, suna fatan samun nasara a aikin.
Yusrah likita ce, ta san likita na iya ƙoƙarin ne dan a samu sauƙi amma babu abinda yake hannunsa bai isa ya saka ko ya hana ba, balle irin wannan aikin, aiki ne mai risk sosai, hakan ya sa idanuwanta cika da ƙwalla bayan ta gama yin bayanin, ta kalli AA dake ta jan carbi ya dafe kan Safwan yana ta tofa masa, gaba ɗaya jikinsa ya yi ja nunin cewa yana cikin halin matsewar zuciya da damuwa.
A hankali hawayenta suka gangaro, ta kama hannun Safwan na dama ta sadda kanta a hankali ta ɗora leɓenta saman hannun hawayenta ya ɓalle, bai san cewa shi ma nasa leɓen na saman goshin Safwan ɗin ba sai da Docter ya ce" Ku kwantar da hankalinku fa, komai zai je daidai."
A lokacin ne kuma motar ta shigo asibitin, kusan a tare suka ɗago kawunansu suka haɗa ido, idanuwansa ya yi jajajir, nata kuwa hawaye share share, kai ya cire daga fuskarta ya kai saman ta Safwan, ƙasa ƙasa sosai ya ce" Son, ka tuna me muka faɗa maka? Ko me ka gani kar ka tsorata ko?"
Safwan ya gyaɗa kai yana kallon baban nasa
ya ce" To, in sha Allah aiki za'a maka dan ka dawo tafiya daidai ka ji? Saboda ka je school, ka yi ball, ka yi wasa da kanka ko?"
Nan ma ya gyaɗa kai, Aswan ya yi murmushi a hankali ya ce" Fine boy, ina nan har a fiddo min kai lafiya in sha Allah ka ji?"
Safwan ya yi murmushin shi ma ƙasa ƙasa ya ce" Har da aunty Yussy tana nan ita ma?"
Da sauri Yusrah dake danne kukanta ta matso ta ce" Eh babbanmu, eh, ina nan ko?"
Ta ƙarashe da kallon Aswan alamar shi take so ya tabbatar masa, Aswan kuma ya kalleta a shashance, shine wai take tambaya? Sai ya ji kamar tausayinta haka dai ya ɗan daki zuciyar sa, shi dai ya ɗauke dubansa ya kalli Safwan ya ce" Eh ita ma tana nan."
Daga nan aka sauko shi , suna biye da shi har aka shige ɗakin tiyatar da shi sannan aka nuna masu wajen zama, sun zauna ne kowane cikin zulumi, addu'a ce suke yi ba ji ba gani, kowane yana jan abinda Allah ya bashi iko, a hankali a hankali har awanni huɗu suka cike ana ɗakin tiyatar nan ana yi, ban da sallah babu abinda ke tashin su, suna anfani da lokacin wayar su ne, shi sai ya fice, ita kuma sai ta tayar da sallar ta yi saman dardumarta, babu wanda ya dubi abincin da aka kawo masu daga hotel ɗin da suka kama ɗakuna, Yusrah takan fashe da kuka ne ta ɗora kanta saman cinyarta, shi kuwa sai ya kalleta ya ɗan jima yana kallonta sai ya taɓe baki ya sauke ajiyar zuciya, har docter ya fito ya ƙaraso inda suke lokaci ɗaya suna miƙewa da tarbar sa ganin a jikinsa babu kayan tiyatar har ya cire, ya dube su yana dariya ya ce" An yi nasara, yana ɗakin hutu tun minti arba'in da suka wuce, suna so su ga yanayin aikin ne kafin su saka baki gaba, yanzu sai jiran farfaɗowarsa sannan su shiga su ganshi da kuma fatan warkewarsa sumul."
Ita dake ɗauke da hawaye share share sai ga dariya a saman fuskarta wacce ta jima rabonta da irinta tana furta" Alhamdulilah, Alhamdulilah Alla."
Ta juya ta ƙarasa wajen abincin nan ta ɗauka ta zauna ta ciro wayarta ta sauke jirgin nan da ta ɗora ta buɗe abincin ta shiga kaɗa kafa ɗaya kan ɗaya, daidai ya dawo da waya a kunnensa, ga dukkan alamu kira yake yi, ko wa yake kira? Ya dai shigo yana wayar ya yi turus ganin ta buɗe abinci tana daddana waya tana kaɗa ƙafa.
A ƙwaƙwalwarsa ya tuna irin kukan da take ɓarkewa da shi ɗazu ɗazun nan, yanzu kuma haƙora a fili sai kaɗa ƙafa take kamar kuma wacce ke sakar masa harara ko idanuwansa ne? _"Ta tabbata, wannan ta yiwu aljanu ne da ita masu ƙarfin gaske, domin mai lafiya ba zai taɓa iya yin irin kukan nan yanzu yanzu kuma a ganshi yana dariya ba, baiwar Allah, a haka take tunanin in bata ɗana? Uhum lalle."_
Ya ƙarasa ya zauna da carbinsa yana dannawa yana kuma ɗan satar kallon abincin dake gabanta, su mata basa iya haƙura dai da abinci? Ko da yake sun jure gaskiya shi ɗin ma yana jin yunwar sai dai ba zai iya cin abincin nan ba ya huce ai.
Kira ta dannawa aunty Intisar sannan ta saka camerar baya a ranta tana ayyana _"Tana ɗagawa zata ganka ɗan ballaja'u, sai ka san ka taɓo ƙanwar aunty Intisar dan idan ta fara wujijjigaka sai ka raina kanka."_
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
28/05/2024, 23:09 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*46*
Anna na tare da duka ƴan matan a madafa da kuma masu aiki kowa da abin da yake yi, cikin nutsuwa Anna ta dubi Abrar tace "Abrar."
Da sauri ta juya tana amsawa da "Na'am aunty."
Inda tanganran ɗin Aba suke ta nuna mata tace "Bani kofi biyu anan."
Amsawa ta yi da to tare da nufa wajen, sai dai Nabihat ce tsaye anan tana yanka fruit tana ta zubawa a cikin kyakyawan mazubi, ganin ita mq aiki take ya sa ba ta ce ta miƙo mata ba, Anna ma abinda ya sa kenan ba ta ce ta bata ba, hannu ta kai za ta ɗauko har tana ɗan ɗaga ƙafar ta... Amma dake Nabihat cike take da haushin Abrar tun daren jiya da suka dawo ya sa ta kallon Abrar ɗin da yanayin hassala sosai tace "Dallah malama me ye haka? Ba zaki ce na matsa miki bane? Haba!"
Ta ƙarashe da jan dogon tsaki tana matsawa nesa da Abrar da ta saki baki tana kallon ta da mamakin yadda ta hantare ta, Anna da su Manal duk juyawa sukayi suna kallon su, Nawal ce dama mai zafin a cikin ƴan biyun, dan haka ta buɗa baki tace" Nabihat ya zak..."
Da dubara Anna ta mata alamar ta ƙyale ta, hakan ya sa ta yi shiru ta ci gaba da abinda take yi tana kumburo baki saboda tun jiya ta ga Nabihat ɗin nata yi wa Abrar wasu abubuwa da tuni da ita ce ta sassaɓa mata kamanni kuma ita bata ga abinda ta mata ba.
Anna dake kula da Abrar ta san tana da sanyi ba lallai ta yi magana ba, amma dai yadda ta ga ta tsare Nabihat da idanu alamar za ta iya tanka mata sai kawai ta yi gaggawar dakatar da fitinar da bata san ƙarshen ta ba ta hanyar faɗin "Abrar bani kofin Aban ku yana jirana."
Hakan ne ya ɗauki hankalin Abrar ta ɗauko kofunan biyu ta ɗauraye su ta saka tissue ta goge yadda ta san Annar nayi sannan ta kawo mata, ɗauka Anna ta yi ta fice a madafar tana cewa "Ku gaggauta shirya wajen cin abincin nan kafin na zo."
Manal da Nawal ne suka amsa da "To Anna."
Saida ta fice tsaf amma sai ta dawo bakin ƙofar ta tsaya dan saurarawa ko Abrar ta mata magana saboda ta ga yadda har lokacin take kallon Nabihat, ai kam Abrar na ganin Anna ta fita ta kalli Nabihat tace "Kar ki sake min tsawa irin haka, ni ba ƴar ki bace kin gane, tun jiya kike hawa kaina amma na share ki, bana so gaskiya."
Ƙwafa ta yi tana ɗora ƙananun plate a babban faranti za ta kai kan dinning, Nabihat kamar jira take ta kalle ta ita ma ta ce "An miki tsawar Abrar me za ki yi? Na ce me za ki yi?"
Jinjina kai Abrar ta yi tace "Na dai faɗa miki, idan ma haushina kike ji to ai ba ni zaki nunawa hushin ki ba, sai ki je ki gwada ɓacin ran ki ga wanda ya ɓata miki."
Da zafi zafi Nabihat ta juyo gaba ɗayanta tace "Wallahi Yaya AA ba sa'an yina bace sai dai ke, ke in banda ma shishigi da jaraba, gaba ɗaya kin bi kin naniƙewa yaro kamar wani ke kika haife shi, har kina wani jin daɗi saboda wai kina samun duba daga gare shi ko?"
Duka idanu suka zuba mata dan ɓacin rai ya sa ta fallasa abinda ke ranta bata ankara ba, dan kuwa a maganar ai ba wanda ya yi maganar AA, hakan yasa duk suka gane shine matsalar ta kenan? Abrar kuma wani sanyayyan murmushi ta yi tace" Allah sarki, ashe abinda yake damun ki kenan tun jiya? To sannu kin ji, amma ki sani Safwan ko akan titi na gan shi zan masa abinda nake masa yanzu, bare kuma yana matsayin ɗan Akhi."
Tsaki Nabihat ta ja tace" Aikin banza, ba dai Safwan ba? To za ki gani, idan shine lagon AA da sannu zan jashi a jiki ta yadda ke baki sa ko tsayawa kikayi gaban sa ya kalle ki ba, sann..."
Manal da ta ga abun na Nabihat na neman wuce gona da iri ne ta yi gaggawar faɗin" A'a, wai me ye haka dan Allah? Ku rabu damu da maganar Akhi mana da baya ko ƙasar nan mana mu samu abinda muka saka a bakunan salatin mu."
Taɓe baki Nawal ta yi tace" Hmmm! Idan ma faɗan ki akan AA ne to zai fi kyau ki sassautawa kan ki, Abrar kuma da son shi take ko tana son ya kulata, ai ba yau take gidan nan ba ina ga da tuni ta samu kan shi."
Duk da Nawal ta yi maganar ne bata kallon inda Nabihat take, amma saida Nabihat ta harare ta tace" Ke ce baki fahimta ba, amma shishigewa Safwan da take ba'a banza take yi ba."
Juyowa Nawal ta yi tace" To me ye laifin ta idan ma hakane? A duniyar nan akwai wanda ya isa ya saka Akhi yin abinda bai yi niyya bane bare abinda ya mata jiya? Sannan fa hausawa sun ce ma so uwa ya so ɗan ta, ai ko ni kika nuna kina son jinina zan so ki iya iya ƙarfina zai ƙare."
Kallon ta Manal ta yi sigar gargaɗi tace" Nawaaaal."
Kallon ta Nawal ta yi, dan haka ta kalli Abrar tace musu" Please, ku je ku shirya table kafin Anna ta same mu anan."
Abrar ce ta fara ɗaukan farantin nan ta fice sannan Nawal dake ma Manal ɗin kallon ba fa na son haka my half, sakannin da kika bani ba fa shekara bane. Tun kafin su fice Anna tayi gaggawar bin hanyar da za ta sadata da falon ta sannan ta fita ta can zuwa ɗakin Aba tana jinjina lamarin Nabihat da hango sanyi da raunin Abrar har ta ji tana mai ƙara yi wa Aswan ɗin sha'awar Abrar fiye da Nabihat da ba dan Abrar na da sanyin halin ba da sun kaure da faɗan da kowa sai ya san me suke ciki akan wanda bai ma san suna yi ba.
Manal na ganin fitar su ta kalli Nabihat da ta ci gaba da yanka fruit ɗin tana huci tace "Take it easy sis, ki bi komai a hankali mana, matsalar shawo kan Akhi ita tafi wannan cacar bakin naku girma, dan Allah ku kiyaye irin haka ba daɗi."
Tana gama faɗa ita ma ta fito suka ci gaba da shirya table ɗin, suna aikin nan ne kamar daga sama Intisar ta zo gidan har Anna na ƙorafin daga ina take yanzu cikin dare? Ba ta shaida ma Annar komai ba, ita da ta so zuwa ma tunda safe, jikin ta ne da babu daɗi ya sa ta wuce gida sai yanzu ta ji tana so ta zo tayi dinner da ƴan uwan ta, nan ta kama musu aikin suna