Showing 294001 words to 297000 words out of 397328 words
Intisar kuwa sai da ta bari ya tafi sannan ta bi bayansa, duk da ta so gyarawa Hajia ɗakin ta amma ta bari saboda mijin Hauwa dake falon, bata son wani abu ya kuma faruwa da zai ɗagawa Hajia ko yaya Mubarak hankali, a kullum fatanta Allah ya sanyaya zuciyar sarakuwarta, tana yiwa Hajia uzuri sosai a rayuwa dan halayanta daban suke, Hajia na fifita ƴaƴanta da soyayyar ƴaƴanta sama da ta kowa, duk abinda zaka yiwa Hajia kuwa bata taɓa daidaitaka da ƴaƴan da ta haifa, sai dai a tsakanin ƴaƴan nata kuwa tana matuƙar girmama wanda ya fi girmamata, ita ta san bata haɗa Mubarak da kowa shi yasa a kullum take ƙara nuna masa yiwa mahaifiyarsa biyayya shi zai sa ya tsira gobe ƙiyama.
Sai da suka tafi Hauwa ta samu bakin magana, dan tunda yaya Mubarak ya hayayyaƙo mata ta yi laƙwas cike da tsoro, yanzu kuwa ranta ɓace ta ƙaraso gaban Hajia ta zauna ta ce"...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:55 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*73*
Sai da suka tafi Hauwa ta samu bakin magana, dan tunda yaya Mubarak ya hayayyaƙo mata ta yi laƙwas cike da tsoron yanayinsa dan bai taɓa yi mata irin haka ba, yanzu kuwa ranta ɓace bayan sun tafi ta ƙaraso ta zauna gaban Hajia tana kwaɓe ɗan ta dake tambayarta wai wani suna ne Uwale da Yayanta ke kiranta da shi? A gaban Hajia bayan ta zauna ta ce" Hajia, kina kallo ta ja shi suka tafi? Wallahi Hajia an asirce maki ɗa kina ji kina gani? Caɗdijan wannan ai ta fi ki faɗa yaya ya ji Hajia, yanzu me yaya yake nufi? Mu fita daga nan mu je ina to? Kuma so yake ya ce zai komawarsa mu bai sama mana mafita da maganar sharrin nan da aka yiwa shubidy ba? Hajia wallahi kar ki yarda tashi ki je ki ɗaga musu hankali ya saki wancen ƴar iskar ko ki masa baki Hajia, wallahi in ya ƙi sakinta sai ki masa baki mu ga in zai yi albarka."
Hajia ta zuba mata ido, tunda take maganganu a kan lamuran ƴan uwanta bata taɓa yin wanda ta ji tsoron ta irin na yau ba, kai hatta sunnan da ta ci na mahaifiyarta sai da ta ji ina ma ba shi ta saka mata ba? Domin sunan nan suna ne na masu daraja sosai, duk masu ɗauke da sunan nan suna da dattako sosai da halin kirki amma ban da ƴar nan.
A hankali ta ce" Uwale, in yi masa baki kika ce?"
Hauwa ta dubeta jin ta kireta da sunan da ta ja warning ɗin kar a saki a kireta da shi, wai wani Uwale na iya shege sai kace a ƙauyen ƙayau, sai dai bata ce mata komai a kan maganar sunan ba ta dai yi abinda yake gabansu kafin ta sake tuna mata ita fa ta girmi sunan nan, dan ko Hauwar nan su kaɗai ke faɗin sa ta jima da canzawa kanta suna fa, da yanayin ta tanƙwasata ta ce" Eh Hajia, wallahi in dai ya ƙi bin umarninki ki tsine masa, kawai ya saki yarinyar can, kuma ya maida hankali ya gyara takardun mu mu koma, kuma ya bar maganar fiddamu daga nan, ta yiwu inda zai kai mu babu ac, ko akwai ai bamu da kuɗin biyan wutar, kawai ma yi zaman mu a nan ya biya in ba haka ba Hajia ki tsine masa."
Hajia ya gyaɗa kai tana kallonta ta ce" Amma ke akwai shaƙiyiyyar yarinya ban da sunanki! Ke Uwale baki da kunya ashe? In tsinewa yaron dake ɗawainiya da ni da wahalata da komai kuma ni kuwa in nufi ina? Ai kin san dai ba dai ke zaki riƙeni ba ko? To ke Uwale ki duba ki gani fa zaki ce ya saki matarsa matar rufin asiri? Ai kin san ko dukiyar ce sa zo ɗaya soyayya kawai ta sa suke zaune da juna, ke dai kawai ki yi abinda ya ce nima yanzun ai biyayya zan yi saboda ban taɓa ganin abinda na gani yau ba gaskiya, kawai ku je da mijinki da ƴaƴanki har ya huce na masa maganar takardun na tabbata in dai da abinda za'a yi zai yi ai Mubarak ne akwai biyayya, ku yi haƙuri kawai amma babu abinda zan iya yi gaskiya yaro kuwa Allah ya masa albarka ya ƙara ɗaukaka min shi ya tsare duniya da ƙiyama, matarsa kuwa in ma ta shanye shi ba wani abu tunda bata hana ya kula da ni ba Allah ya ƙara danƙon soyayya kawai."
Hankali tashe Hauwa ke kallonta, murya na rawa ta ce" Hajia yanzu ni zaki yiwa haka? Hajia dan kin ga bani da komai ne zaki min haka?"
Hajia ta kawar da kai ta ce" Kayya, kayya Uwale, kayya, ba zaki gane ba, yanzu ni dai je ki suturta mijinki in samu in wuce ciki, so nake in je in yi nafilar dare gashi ba halin yi a falo, jeki in wuce wuff in baku wurin."
A dole Hauwa ta miƙe kamar ta ɗora hannu a kai ta yi ta rufa kuka, hankalinta duk baya jikinta ta nufi ciki sai ɗurawa ƴaƴanta zagi take yi dan sun isheta da mita da neman masifa bayan ga wani tashin hankalin ya nufo su, ita yanzu idan suka je wani gidan ta yi ya ya da ranta? Ƴaƴanta babu abinda suka iya a rayuwa, yau ko da an zube musu abinci da komai da komai in dai ba mai aiki aka ɗauko musu ba sai sun kusa haukatata, wallahi basu da tsari ko kaɗan na rayuwa, ban da su ɓata su lalata basu iya komai ba, dama masu aikin su Anna ƙarama ne, tunda uncle ɗin su ya ɗauke su ta nemi mai aiki dan a kwana biyu kacal sai da suka mayar da gidan kamar na mahaukata, hatta babansu sai da ya fara wari dan har wankin da yaran ke yi, da nata da komai, a yanzu idan aka kai su wani wajen ba lalle su samu arzikin kunna fanka bama balle ta ac, abincin ko akwai girka shi zai zama bala'i, uwa uba dattin dake tare da su ya fi komai ɗaga mata hankali, ita kam ta shiga uku, ko fitar da ya yi yau yawonsa na neman abin shansa ya je ya haɗu da su AA shi da Arif suna zagaye suka zane shi tass suka koro shi har gida sannan suka juya, ita kam yanzu ta fara gane sakarai take aure ba ɗan gayu ba, shin ya zata yi da wannan bala'in kuma?.......( lokaci)
*Su* Intisar tana shiga falo ta ƙarasa da sauri ta zauna a saman cinyar yaya Mubarak da ya ɗaga kai sama yana kallon clng, a nutse ta shiga kissing ɗin sa tana ɗan sinsinar wuyansa ta ce" Bara na ji wuyan nan da gishiri gishiri ko babu?"
Hannayenta ya riƙe yana ɗan ɗage gira ya ce" Bab na yi wanka fa."
Ita ma ta ɗage girar ta ce" Yaushe? Bari dai in ji mana."
Ƙiyawa ya yi ya janyo ta jikinsa ya rungume sosai ya yi shiru, ita ma shirun ta yi tana jin irin yadda ƙirjinsa ke bugawa, a hankali ya ce" Ina tsoron wata rana ki kasa haƙuri da rikicin gidan nan ki yi nesa da ni, ki duba ki ga har an fara rabani da ke na tsayin kwana biyar, idan wata rana kika je da kanki kika faɗi halin da kike ciki ya ya zan yi da raina ne?"
Idanuwanta ta lumshe sosai tana jinsa, a hankali ta ce" Shikenan dan mamana ta min faɗa sai in je ina yamaɗiɗi da ita bab? Ko wancen da aka yi shi yaje ya gani, kuma ka san babban Yaya da rikici bani da yadda zan yi ne na yi biyayya dan idan ban yi biyayyar ba wallahi sai ya ɗaga hankalin kowa, ai ka sani bab."
Yaya Mubarak ya ɗagota yana kallonta ya ce" Na sani, shine nake tsoron wata rana ya gani, har ya rabani da zuciyata."
Ƴar dariya ta yi tana kallon cikin idanuwansa tsai ta ce" Ba zai rabani da gagar jikina ba dan ba ruhi idan har babu gangar jiki, hey ka kwantar da hankalinka komai na rayuwa mai wucewa ne, yau da ace kai ne ke yin wasu abubuwan hankalina zai tashi sosai, amma ba kai bane, ka ga kuma Hajia fa da kanta ta ce muna iya tafiya, ka ga kuwa haƙurinmu ya mana rana ko?...nd ka sani kamar yadda zan iya duƙawa Anna haka zan duƙawa Hajia, bab ta isa da ni fa, wallahi ta gama min komai tunda ta haifo min Dadyn Anna ƙarama."
A gaskiya samun mace mai son ka duniya ne, duk irin yadda hankalinsa ke tashe da tunanin a yanayin da zata shigo masa sai ya samu kwanciyar hankali a ɗan ƙanƙanin lokaci, hannayenta ya kama suka shige ɗaki suka shiga shirin yin wanka, dan so yake su kwanta ya rungume abinsa a ƙirjinsa ko zai samu nutsuwa ta sosai da sosai, tabbas tunda safe in sha Allah zai yi sammakon ya je harkar tikitinsu, zai gama komai a gobe in sha Allah domin komai na hannunsa kawai tikitin zai cira sannan su fara shiri, ƙwarai zasu tafi kuma idan sun dawo in sha Allah zai yi ƙoƙarin kai iyalinsa wani wajen, a yau ya ƙara yarda cewar Intisar ita ce duniyarsa, rayuwarsa, nutsuwarsa, zai yi ƙoƙarin faranta mata kamar yadda take yi ba ji ba gani in sha Allah, zai sakata dariya ta hanyar faranta mata da sanyaya mata zuciya, zai nisantata da duk wani wanda zai ci zarafin ta, Hajia kuwa zai ci gaba da yi mata biyayya har ƙarshen numfashinsa.
*WASHE GARI*
Washe gari tunda safe Yusrah ta farka da nufin zuwa kicin dan kwanciyar da hutun sun isheta hakanan, kuma tana son yiwa tagwayen Anna surprise sai sun sauko su ga ta gama komai, shi yasa tunda ta gama sallar asubahi ta ƙi komawa ta yi dukkan abinda zata yi dan kula da jikinta sannan ta sauko sai baza ƙamshi take yi ta kulle ɗakin ta da ky ɗin ta ta sauka a nutse dan ta je ta yi girkin breakfast.
Kulle ɗakin da ta yi ya saka Nabihat dake nata ɗakin tasowa da sauri ta buɗe ɗan ƙaramin abin leƙawa ta leƙa dan ta ga ko waye ya fito da sassafe? Ganin Yusrah ya sakata taɓe baki ta juya, har zata koma ta kwanta ta yi tsaye tana tunanin sai ta shige bayi da sauri dan ta yi wankan ita ma dan tana so ta je ta ga me zata yi da sassafe haka? Ta yiwu haka ta ringa yi ta siye mutanen gidan da kissa ta barta baki buɗe.
Yusrah na sauka ta gama nazarin abinda zata yi, hankali kwance ta shiga feraye doya dan tana so ta soya ta da ƙwai hakan na nufin sai ta silalata sannan ta yi suyar dan haka ta shiga aikinta cikin gaggawa gefe guda kuwa ta ɗora tea ta haɗa masa kayan haɗi masu daɗi ta bari ya tafasa ta tace ta juye cikin babban abin zubawa ta ajiye gefe dan sai ta gama zata jera komai ta kai falon, sai dai bata san me za'a girkawa Aba da Anna ba yau, dan Anna bata fito ba har yanzu.
A nutse ta ɗora silalan doyar sannan ta shiga kashe ƙwai tana zubawa a wani kyakkyawan bwl ta gama kashewa kenan ta shiga yanka su albasa da sauran kayan haɗi dan ta haɗawa ƙwan saboda tana juye doyar ta fara soyawa Goggo Tidin ta shigo sanye cikin kayan barci sakakku sosai da hular da ta dunƙule gashinta a ciki ta shigo da nufin zuwa ta ɗauki tea ta sha dan haka take yi tunda sassafe take shan tea mai zafi kafin ta ɗan yawata a filin gidan sannan ta zo ta karyawa.
Da girmamawa Yusrah ta gaisheta, sai dai ɗan turus ta yi ta ƙare mata kallo kafin ta ɗauke kanta a ranta tana ayyana _' Tofa, za'a fara nuna mana an zama masu ƴanci matan babban ɗan gidan kenan?'_
Ita kuwa Yusrah tunda ta gaisheta kamar yadda ta saba bata yi jiran amsa ba dan bata taɓa gaisheta ta amsa ba, sai ta ci gaba da daka kayan ƙamshin nan, abin nan mai ɗauke da kwai a kusan ƙafarta dan da zarar ya daku zata juye ta shiga suya ne, a lokacin da Goggo Tidin ke jira ruwan da ta ɗora ya tafasa ta haɗa tea ɗin ta Nabihat ta shigo kicin ɗin, ta ɗauki wanka sosai sai ƙamshin take bazawa ita ma.
Tana shigowa ta gaishe da Goggo Tidin sama sama, sai dai ga mamakinta yau ta amsata har da ɗan sakin fuska, ita ma sai ta samu kanta da sakar mata fuska sosai ta ɗan yi tsai tana bin kicin ɗin da kallo kafin ta nufi wajen tukunyar dake saman gaz mai ɗauke da doyar nan ta buɗe tana dubawa ta ajiye marfin gefe tana yatsine fuskarta sannan ta juyo ba tare da ta rufe ba da gangan ta nufi inda Yusrah take tana faɗin" Aunty Tidin wa ke cin doya da sasafe a gidan nan? Ba kwa tsoron ta sakar muku teba ta lalata muku kira?"
Goggo Tidin ta ɗan girgiza kai tana juya tea ɗin ta ta ce" No no no, gaskiya ba dai ni ba dan ina ba jikina mahimmanci sosai, bana haɗa kula da jikina da komai gaskiya, shi yasa nake sabuwa dal a kullum, wannan sai aikin waɗanda basu san darajar kula da jiki ba ai?"
Nabihat ta yi ƴar dariya tana saka ƙafa da gangan ta shure ruwan ƙwan nan gaba ɗaya ya wanku a ƙafafuwan Yusrah harda gefen rigarta, sai kuma ta haɗe rai tana faɗin" Ya Salam, me ye wannan kika zubar na saka ƙafa? Ke wani irin aiki kike yi mana a kicin cike da ƙazanta haka? Me ye wannan kika zubar har na saka ƙafata?"
Yusrah ta tsayar da dakan da take yi ta zubawa ƙwon da ya kai goma sha biyar ama Nabihat ta kife shi a jikinsu bayan tukunyar da ta bude ta bari a buɗe kuma ta ci gaba da zaginta a fakaice dan wani neman fitina ta ɗago idanuwanta da suka fara canza yanayi zata yi mata magana Anna ta sanyo kai kicin ɗin tana yin sallama dan ta ga yanayin da mutane a ciki.
Yusrah ta amsa salamar tana mayar da kanta ƙasa bayan ta gaishe da Anna, Goggo Tidin kuwa ta ce" Zubar da ƙwan kika yi dan ta taka ya jata ta karye? Yarinya ko da wani abu a tsakaninki da ita marar daɗi ai kya kiyaye mugun wasa, kuma in dan maganar auren da aka baki daga sama ne ai kin san ta rigayeki sai ki kiyaye, mtsssss ni na tafi kar a ɓata min rai da sassafe."
Nabihat ta ringa ɗage rigarta tana ƙaƙalo abin kuka ta ce" Yanzu Yusrah daga cewa kawo in taya ki dakan ne zaki watsa min ƙwan a jiki? Allah ya baki haƙuri bari in tafi dama gani na yi aikin kamar zai maki yawa shine na zo in kama maki."
Nabihat ta gama faɗa ta zagaye ita ma tana gaisar da Anna ta tafi, Yusrah gaba ɗaya hankalinta ya nemi tashi, kanta a ƙasa tana jin kamar zata fashe da kuka ta ɗago ta dubi Anna dake tsaye tana kallonta, muryarta na rawa ta ce" Anna, dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ba haka ya faru ba, ba nice na zubar da ƙwon nan ba, kuma ba nice na na...." Sai kawai hawaye ya ɓalle mata, dan wallahi da ta rasa madafa, sam bata iya irin wannan rayuwar ta munafurci ba, ta fi ganewa a yi fito na fito a rayuwa, bata iya zagaye zagaye munafurci ba, ga dai ƙwai a ƙasa ga kuma kalaman Tidin da Nabihat, waye zai ƙi yarda cewar bata aikata ba?
Anna ta yi murmushi a tausashe ta ce" Tashi ki je ki wanke jikinki, ƙwai akwai ƙarni sosai, ya ya aka yi kika fito tunda safe haka ne?"
Yusrah ta sake sadda kai hawayenta na zuba ta miƙe tsaye tana faɗin" Dama so na yi in yi girkin kafin su Manal su sauko, shine, shine haka ta faru, Anna wallahi ban yi abinda suka c..."
"Yusrah." Anna ta faɗa a tausashe tana katseta, Yusrah ta yi tsitt ƙirjinta na bugawa tana kallon Anna, a tausashe Anna ta ce" Kar ki yi haka mana, ke fa mace ce, kuma kin ga irin mijin da kike aure, idan har baki iya takunki ba kowace shara zata ce ta taka ki ne fa, wannan hawayen ki daina shi, sam ki iya riƙe shi, idan ranki ya ɓace ki cije ki haɗiye kukan kin fahimta? Gwara idan kika shige ɗaki ki yi ke