Showing 261001 words to 264000 words out of 397328 words
faruwa, da waye za'a ɗaura auren kuma?
A ƙofar gidan kuwa su AA na zaune daf da su Aba, kansa a ƙasa domin sau uku yana ɗagowa idan suka haɗa ido da Aba sai Aban ya masa wani kallo da ya kasa gane na fushin ne ko na gargaɗi ne, a hankali sai ya soke kansa zuciyarsa cike da nadama da son bada haƙuri sai dai ba hali.
A tausashe kalaman ɗaurin auren suka fara gabatuwa, a hankali ya ɗago idanuwansa a lokacin da Aba ya buɗibaki ya nema masa auren *Yusrah Abdul-Hameed Turaki*, a yanzu ne gaba ɗaya tsigar jikinsa ta ringa tashi, ƙirjinsa ya ringa dokawa da ƙarfin da bai taɓa ji ba, domin ba faɗuwar gaba bane, kowane kalma ne ke doka ƙirjin nasa kamar ana ƙwanƙwasa ƙofa, idanuwansa kuwa suka zama shedar kuɗin sadakin da Aba ya zube, da tabbatuwar ɗaurin auren bayan Yaya Mubarak ya baje goro a gaban maɗaura auren aka shafa fatiha.
A hankali ya lumshe idanuwansa yana jin wani irin gumi na son jiƙa masa babbar rigarsa ta zuwa ɗaurin auren da ya sako da hularsa, lokaci ɗaya masu son taya shi murna suka nemi jagula masa lissafi ta hanyar damƙar hannayensa, Aba kuwa bai ce masa ci kan ka ba sai kafe shi da ya yi da kallon daidai nake da kai duk abinda ka zo da shi ni na gama shiryawa ni da kai yau ɗaya zai fi ɗaya iyawa.
Hannun Arif ya jimƙa da kyau ƙasa ƙasa yace" Arif, ashe nine aka yiwa auren dolen?"
Arif dake watsa haƙora na farin ciki ya dube shi ya ce" Haƙƙun, wannan yanzu aka gabatar ai."
Ya yi wani shirun ya kalli Muktar yace" Kuma fa ɗana bai san da maganar auren nan ba, bayan wannan su Meem ma basu sani ba, kuma gaba ɗaya ni kamar an min fin ƙarfi fa."
Muktar ya miƙe ya ɗauki hular AA da ya kifa a gabansa yace" Tashi mu je, ka san dai a nan daga Aba har Chef ba sa'anin yara bane, mu je gida sai mu tausheka mu rarrashe ka, tashi mu je."
Ai kam miƙewar ya yi ya sake duban Aba da Chef, irin yadda suka hautsine da farin ciki sai hotuna ake musu da mutane ƴan gayyata ya kalli Mubarak sai wani sake baza baki yake yi ya gyaɗa kai bayan ya taɓe baki ya juya ya bi bayan aminansa dan gaskiya Muktar ya faɗa, a nan dai bashi da ta cewa, shi ba ma abinda yake tsaye a ransa sai idan ya tuna ana nufin yanzu fa ita ce matarsa? To yaushe wai aka canza masa matar ne shi duk bai sani ba? Kai jama'a to wai ya ya ma zasu zauna da wancen abar ne fisabililahi? Wani irin zama zasu yi ne? Kai wanda ya ɗauki vidion nan idan ya riƙe shi wallahi sai ya jijiga rayuwarsa, sai ya rikita rayuwarsa, wanda ya ɗora kuwa ai yayi kuskure da ya ɗora a pajinsa, pajin da aka san hoton fuskar sa, yau kwanansa biyu baya gidan iyayensa, zai san ya yi da masu kwana a jeji, zai san idan ana dara fidda uwa ake yi, ko wani hauka ya shiga kansa ya saka shi aikata wannan aikin sai ya yi dana sani marar anfani.
A cikin gida kuwa tunda sanarwar sunan da wanda aka ɗaura aure ke tashi ƴan matan Anna suka miƙe tsaye a firgice suna kallon juna da sake saurarawa, dan kamar kunnayensu na jiye musu da Akhi ne aka ɗaura auren fa. A rikice Goggo ta miƙe tsaye tana sake saurarawa, Aswan Aliyu Anza ɗin ke yi mata yawo a ƙwaƙwalwa tana son gane wanene, sai kuma lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ke son hasko mata wanene ɗin, da ƙarfi ta juya tana kallon mutanen falon, sai kuwa ta yi cikin ɗakunan da bata shiga ba tunda ta zo tsabar bakin ciki ya hanata leƙa ɗakunan ta zauna daga nesa tana faɗin ai gidan nan ba zai taɓa birgeta ba ko me za'a maida shi, ba ma zata taɓa iya kwanciya a cikinsa ba hankali kwance shi yasa ko ɗaurin auren sai yau ta zo, su dai suna sauraron ta suka yi mata banza, to me zata zo da shi kuma sabo ya basu mamaki? Kafin a gyara gidan ai ita ta zauna zaman makoki a cikinsa tun da sauran jinin mamatan a ƙasa a zubde.
Sai da ta faɗa ɗakin ƴan matan ta tarda su suna ihu a rikice suna tambayar kansu wai tsaya Akhi ne fa? Yaushe hakan ta faru? Sai ta fito da ƙarfi ta auka ɗayan ɗakin ta samu aunty Furera a bakin gado rungume da Yusrah dake kuka kanta a saman ƙirjinta, harara ta sauke masu ta sama da ƙasan nan kafin ta idasa shiga da kyau tana kallon Aunty Furera ta ce" Fure, ban gane ba, da wa aka ɗaurawa yarinyar nan aure?"
Aunty Furera ta dubeta sama da ƙasa ta ɗauke kai ta ce" Da wanda kunnayenki suka jiyo, Aswan Aliyu Anza, ɗan gidan Elhaji Aliyu Anza babba."
Cikinta sai da ya sake juyawa tsabar kaɗawar da maganar ta yi mata, a firgice da kuma yanayin rikicewa ta ce" Wani irin Aswan? Au da aka fasa auren da Bilal ne kuka munafunceni kuka bata Aswan?"
Yusrah da ta rage sautin kukanta tun ɗazu idanuwanta rintse a ƙirjin aunty Furera ne aunty Furera ta ɗago a hankali tana kallonta ta shinfiɗata a saman gadon ƙasa ƙasa ta ce" Kwanta in gama da ƴar kutumar...,ke Hinda ya ya aka yi kika san an fasa auren da Bilal? Nace ya ya aka yi kika sani?"
Goggo Hinda ita ma ta shigo da kyau ta ɗaga murya ta ce"...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
10/06/2024, 10:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*65*
Goggo Hinda ita ma ta shigo da kyau ɗakin tana ɗaga murya hakan ya janyo hankalin iya Abu, Goggo Hinda ta ce" Zancen duniya yana ɓoyuwa ne? Ko an faɗa maki tsiya ta ƙare a kaina ne da ba'a kallon Tiktok a gidana? A Tiktok na gani jiya har maganar fasa auren, bari ki ji da kyau, ba zai yiwu ba, babu wanda zai zo ya canzawa yarinyar nan miji kai tsaye ina raye ko shawarata ba za'a nema ba balle a sanar da ni dan tsohon wulaƙanci."
Da mamaki aunty Furera ta kama haɓa ta ce" Lalle baki da kunya, tunda kuwa baki da kunya ni da wahala idan zan kuma biye maki, dan gaskiya doguwar magana da irin ku ma bata da wani anfani, Hinda da wuri haka? Nace da wuri haka? Ke a wa? Ina ce a gaban shedu kika kakkaɓe ƴaƴan kika yafe mana, ko har kin manta ne?"
Goggo Hinda tana neman janyo aunty Furera dan wallahi haushinta take ji kamar ta kasheta, irin yadda take yi mata katsalandan a lamuranta gaba ɗaya ya sa ta tsaneta, ta cika shiga abinda ba lalle sai ta shiga ba dan neman masifa, da sauri iya Abu dake ta salallami tana sanar musu ana jin maganarsu har tsakar gida fa ta ringa ƙoƙarin shiga tsakiyarsu tana faɗin" Haba haba haba! Ku kuwa haba, dan girman Allah ku yi haƙuri a rarrashi baiwar Allahn nan, jama'a fa suna jin ku, kar ku manta alkairi ya tara mu, a yau ya dace ne mu yi wunin farin ciki da kwanciyar hankali ba a wuni ana tozarta juna da shiga haƙƙin juna ba, haba jama'a."
Da sauri Goggo ta ce" Kin ga Iya Abu a lamarin nan babu uban da zan ji kunyarsa, babu, kina kallo wai ace mijin da zai auri yarinyar nan ya fasa har an bata wani ba'a sanar da ni ba? Akwai wani shaƙiƙinta sama da ni a nan ne? Ki barni da wannan marar mutuncin da ita waccen banzar yarinyar, yau a faɗa min abinda ake nufi da ni?"
"Da kuma ni ba, nace a bar ki da kuma ni ba, ke shaƙiƙiyar wa? Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un! Ke Hinda ashe abinda kike aikatawa dan rashin jin tsoron Allah kenan? Kai, Hinda ni zaki ɗauka a ɗan iska? Ni da ace an ji ta tawa ba zaki shigo gidan nan ba bare har ki halarci ɗaurin auren ƴata mai daraja, an fasa aurenta da Bilal Allah ya bata Aswan ya ya ranki? Nace ya ya ranki?" Uncle Sulaimane ya ratse mutane ya afko ransa ɓace ya tare Goggo Hinda dake sababi, dama sun shigo ne da kuɗin sadakin nan harda Aba dan su bata su kuma yi mata nasiha suka tarar da abinda ake aikatawa.
Neman wartota yake yi dan walahi yana iya buga Hinda da ƙasa ya sumar da ita saboda abinda take aikata masa, Aba da aka ba hanya ya shigo sannan cikin halin dattako ya sallami jama'ar wajen ya nuna musu ba komai kowa yana iya shiga harkar bikinsa za'a wuni ana biki ba fashi, ƴan walima tuni suka cika ƙofar gidan yanzu za'a ɗora daga inda aka tsaya ya ƙaraso da ɗan sauri ya tare Uncle Sulaimane yana dubansa da kula ya ce" Kar ka ɗauki wannan ɗabi'ar, bata da wani anfani ka ji? Ka yi haƙuri hakanan."
Sannan ya kalli Goggo Hinda da ta fashe da kuka tana faɗin ita Sulaimane ke neman duka a kan gaskiyarta? Ita Sulaimane yake son duka yau dan kawai ta nuna damuwarta a kan ƴar ƙanin ta? Ko ya manta da shi da Abdul-Hameed duk ƙannan ta ne?
Da kula sosai ya ce" Ki yi haƙuri ki daina kukan ba'a kyauta maki ba da ba'a sanar da ke ba, abin ne ya zo mana kai tsaye mu kuwa muka yanke hukuncin da ya dace, lokaci ne ya ƙure ya sa baki ji ba, abinda yake faruwa na san ai kin ga vidion, to wanda ke cikin vidion Aswan ɗin ne, kuma tunda ya yi sanadiyar lalacewar auren ta a yanzu shi zai gyara abinsa da kansa, ina fatan kin fahimta kuma zaki yafe mana?"
Goggo Hinda ta gaza cewa um ko umum, gaba ɗaya firgicin abin da tsoron Sulaimane suka hanata yiwa wannan mutumin kallon banza ta ce da shi ita zai rainawa wayo? Waye Aswan ɗin? Aswan ɗin da ita ba zata iya nuna shi ba? Mutumin da sunansa suke ji basu san shi a fili ba, shine ɗansa na farko, duk wata dukiya sai ka ji ance na ɗan Aliyu Anza ne, a rediyo kullum sai an gaishe shi, a talabijin ƙarya ne a yi tallah ɗaya ta biyun bata zama tasa ba, sunansa ya gama garin ne za'a ce wannan kacarin ɗan daban shine, fuuuuuu ta fice daga ɗakin ta nufi ƴar ta dake tsaye tana zizziga da zage zagen su za'a rainawa wayo ta kaɗa ƙeyarta tana faɗin" Wuce mu tafi ke, ba gidan nan bane yau dan na shigo Sulaimane ke zagina? Yau har yarinyar can ta yi arzikin da Sulaimane zai zageni saboda shi? Ba laifi duniya ce tunda ka goge ni a iyayenta ba damuwa."
Rai ɓace suka fita suka tare ɗan sahu suka shiga, yana fara tafiya da su Goggo ta ɗora hannu a kai ta fashe da wani irin kuka mai cin rai na tarin baƙin ciki, abin nan kamar zai fasa mata ƙirji dan baƙin ciki, mai adaidaitar sai da ya ji tsoro ya juyo ya kalleta ya juya sai da Safiya ta nuna masa mutuwa aka yi mata sannan ya tuƙa su yana addu'ar Allah ya jiƙan musulmi a ransa yana mamakin da shekarunta take irin wannan ihun dan an yi mutuwa? Shin ba'a taɓa yi mata mutuwa ta makusanci sosai bane ko kuwa dai tana cikin mutanen da basu ɗaukan abinda ake ta faɗa a wa'azi da islamiyya? Ai irin kukan nan wa mamata bashi da kyau ko kaɗan.
A can gida kuwa Aba ne da kansa ya sa Yusrah ta tashi ya zauna a saman kujera ita kuwa ta sauka ƙasa kanta a saman cinyarta tana ta kukan nan tamkar ranta zai fita, dama tunda safiya ta yi yau ta tashi da kukan nan, tana cikin kukan tuna iyayenta, a yau za'a ɗaura mata aure babu Mamansu da Babansu babu ƴar uwarta, a yau za'a kaita ɗakin ta babu su a gefenta, duk da an canza sanfarin ginin gidan nan da komai ama duk idan ta wulga sai ijiyarta su yi mata kamar tana iya ganin wulgawar mamanta, shi yasa tunda Aunty Furera ta yi mata gyaran jikin asubahi ta sa ta yi wanka ta ɗauro alwala ta sata ta yi turaren wuta aka shafeta da na ruwa aka sa ta saka wata doguwar riga mai kyau aka bata ƙaton hijab aunty Furera ta nuna ta yi zamanta da su zuwa yamma an shiryata dan ita bata son ta ga amarya an gwangwaza mata kwaliyar nan abin yana yin yawa sosai, shi ne ta yi kwanciyarta saman gado tana kallon ƴan uwanta da ƙawayenta sai ɗaukan wanka suke mai mak'up na cencana masu ita kuwa tana kwance tana hawayenta tana kallon su har aka zo aka shiga gabatar da ɗaurin auren zuciyarta cike da mamakin ace Bilal ko Manal ba zai kira ba ta haɗa su yau kwana biyu cirrr? Shine aunty Furera ta zo ta fita da ita suka je ɗakin nan take sanar mata wannan abu da ya rikita ta ya saka jikinta kwasar rawar tsoro da tashin hankali, tashin farko maganar da ta faɗa shine ita kam ƙaddararta ta fi ƙarfin ta, ita kam ta shiga uku ina zata saka ranta ne? Babu abinda zai miƙe a duniyarta na farin ciki ne? Duk abinda ya tunkarota sai ya zo da gardama ne? Ina ita ina auren oga? Ina ita ina wannan maganar? Oga fa? Gaba ɗaya babu wannan maganar a tsakanin su, tunda suke haɗuwa soyayya bata taɓa haɗa su ba sai faɗa, basu taɓa shirin minti ɗaya ba, bayan wannan mutumin da yake da fiancee lokaci kawai ake jira? Kai ita ba ma ta son auren soja bata da ra'ayin haka.
A tausashe sosai Aba ya ce" Ki daina kukan hakanan mana ƴata, yi haƙuri daina kukan hakanan."
Yusrah ta ɗago kanta tana gyaɗa kai, sai kuma ta ɗan kalli Aba kawai sai ta fashe da kuka ta duƙar da kai ta ce" Aba, wayo Allahna zuciyata zafi, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un."
Aba ya rintse idanuwansa zuciyarsa cike da tausayin yarinyar, ya buɗe ya kalli uncle Sulaimane ya ce" Sulaimane idan ba zata jure hayaniyar nan ba please a kawo min ita in kai ta gida ta huta a ɓangarena ba hayaniya, sannan ta ga likita, kana ganin yanayinta hankalinta a tashe sosai, ni kuwa ban so a ci gaba da yi mata ihun nan a kai."
Uncle Sulaimane shi ma ya share idanuwansa ya ce" To Aba idan can za'a je ɗin sai a je, amma in sha Allah babu wani da zai kuma yi mata hayaniyar, da na so mu je can ɗin mu wuni amma na fasa a nan zan wuni inda take in dai Hinda ce bata isa ta kuma ɗaga mata hankali ba."
Aba ya gyaɗa kai yana sauke ajiyar zuciya ya sake dubanta kanta a saman Aunty Furera dake kukan ita ma a tausashe ya ce" Ku daina kukan haka, bashi da wani anfani kun ji? Daughter kin san kowani bawa da irin ƙaddarar rayuwarsa, ban san irin son da kike yiwa Bilal ba, amma na san ba zaki taɓa samun kwanciyar hankali tare da Bilal ba, domin mahaifiyarsa bata son lamarin, a shekaran jiya na je da kaina na tabbatar da haka, kuma na yi mata magiyar ta duba lamarin amma ta ƙiya, shi yasa na haƙura, abinda ban yi ba dai ɗaya ne ban tambaye ra'ayinki a kan auren Yayanku ba, na biyewa shawarar Babanku ne chef dan ya nuna tunda har shi yana da bakin kiran ki matarsa bayan ba haka bane a tabbatar masa, shine zai gyara abinda ya ɓata, sai kawai muka aikata hakan, amma a yanzu idan har ba kya so dube ni nan, a yanzu yanzu zan sauke maki shi dan kuwa nan da kika ganni zan kasance mai yaƙi da duk wani mai son ɓata maki rai ne, ba zan taɓa yi maki dole ba, babu abinda zai faru dan an rabaki da auren nan yanzu, in dai auren nan ne damuwarki yanzu yanzu zan miki maganinsa kin ji daughter?"
Aunty Furera, da Iya Abu da uncle Sulaimane har haɗa baki suke wajen faɗin" Haba dai Elhaji."
Wasu na faɗin" Allah ya kiyaye, ina Allah ya kiyaye."
Aunty Furera ta ce" Elhaji ina ga kukan nan nata da ya tsananta ba na auren nan kaɗai bane ba fa, har da na wulaƙancin Goggonta, ai aure kuma in sha Allah mutu ka raba Elhaji."
Aba ya sake fuskantar ta bayan ya nuna musu su yi haƙuri ba zai iya barinta cikin wannan kukan ba ya tafi, idan har auren nan ne wallahi a yanzu ba sai an jima ba