Showing 354001 words to 357000 words out of 397328 words

Chapter 119 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70026

fita saida ta shafa kumatun ta da kulawa tace "Baby, are u ok?"

A sanyaye ta kalle ta ta amsa da "Fine aunty, thank u."

Da rashin gasgatawa ta tambaye ta da "Sure?"

Da gasgatawa ita kuma ta gyaɗa kai tace "Na tabbata aunty."

Shafa kanta tayi sannan ta wuce suna mata a dawo lafiya, za ta miƙe kenan dan maida abincin ta koma ɗaki Anna dake fitowa daga falonta ta miƙo mata wayar ta tana faɗin "Ina kika aje wayar ki? Kawun su Sulaiman na ta kira ba kya ɗagawa?"

Kallon Anna ta yi, ita wallahi haushi yake bata yanzu, aure fa zai yi ashe shima? Hmmm! Ma ci amana kawai, turo baki tayi ta maƙale kafaɗa tace "Anna ki share shi kawai, ni ba kawuna bane daga yau, Yusrahn ma na daina yi mata kara."

Ɓoye murmushin ta ta yi tana ganin wauta da hauka ƙiri-ƙiri, abin duk da ya sa Sulaiman dake ɗaukar ta matsayin uwa ya kirata ya ce a bashi Manal ai kasan ba ƙarami bane, amma da ta tambaye shi lafiya dai ko? Sai ya ce wai zai tambaye ta ta duba masa wasu litattafan ta da ta masa alƙawarin bashi, sai kawai ta share ta zo ta kawo mata wayar, shine ita kuma take mata wannan haukan, sai kawai Anna ta juya kamar za ta shiga wajen Aba tana faɗin "Shikenan, sai a barshi ai ya mutu a can tunda bai da gata."

"Na'am Anna." Manal ta faɗa tana tsareta da idanu, juyowa Anna tayi ta kalle ta tace "Magana na miki?"

Girgiza kai ta yi alamar a'a, dan haka Anna ta ci gaba da tafiya za ta shige wajen Aba, wayar ce ta sake ƙara ya maido kira, da gudu Manal ta tarbe ta tace "Anna kawo to na ɗauka na ji, nasan dai ba zai wuce kayan sa zai karrrrɓ..."

Tuhumammen kallon da Anna ta mata ya sa bata iya ƙarasawa ba sai karɓan wayan tare da juyawa a guje tana haura matakala, da kallo ta bita kafin ta yi murmushi ta girgiza kai tana ayyana _'Allah ya shirya ku, yara yanzu wai ba sa son nuna abinda suke so.'_

Buɗa ɗakin Aba ta yi ta shiga da sallama Aba ya amsa yana tashi daga kishingiɗar da ya yi yana ta hailala da tasbihi. Dubanta ya yi a tsanake yace "Annar yara, ya kike?"

Murmushi ta sakar masa tace "Alhamdulillah, ya ƙarfin jiki kuma?"

Shi ma murmushin ya yi yace "Alhamdulillah, dama kuma babu abinda yake damuna, ubangiji ya shiga lamarina."

Jinjina kai tayi tace "Zuciyar ka mai kyau ce AA, shi kuma ubangiji yana duba zuciyar bayi ne sai ya musu hisabi da ita, Allah zai ci gaba da kiyaye ka in sha Allah."

Da jin daɗin maganar ta ya sake faɗaɗa mirmushi ya riƙe hannun ta yana mamatsawa, cikin fara'a yace "Tom, yanzu bani labari? Ya ɗan ki kuwa? Ya ci gaba da addabar ki wajen kira?"

Sunkuyar da kai tayi tana ƴar dariya tace "Ɗan Aliyu ba, ko da safen nan mun yi waya da shi."

Turɓune fuska Aba ya yi yace "Kashhhh! Ina tsoron yaron nan ya kasa aiwatar da komai fa, bayan kum..."

"Jika kake so ko?" Ta katse shi da wani kallon ita fa bata son haka, murmushi ya yi ya gyaɗa mata kai yace "E mana, ke ba kya so ne? Ɗa daga jikin AA ƙarami."

Murmushi kawai ta yi kafin tace "Ni ba wannan ba, ni kam shawara gare ni Aban twins."

Gyara zaman shi ya yi ya nutsu yana duban ta yace "Ina jin ki maman twins."

A nuts ta shiga faɗin "Akan Manal ne da uncle Sulaiman, na ga fa kamar suna ɓoye wani abu a tsakanin su wanda suma kamar ba su san da shi ba, suna yawan yin waya da sunan kawai ƙawance suke ko suna taimakawa juna ne ta ɓangaren karatu, amma jiya da yau na tabbatar da son junan su suke kawai dai suna waskewa ne suma, saboda..." Abinda ya faru jiya da yanzu ta sanar da shi kafin ta dora da" Shiyasa na ce bari na maka magana dan mu ankara tun wuri, shi Sulaiman n ga kunya ba zata bar shi ya faɗa ba, Manal kuma hauka ke damun ta."

A nutse ya gama sauraron ta kafin ya numfasa yace" Ma sha Allah, idan abinda kike tunani hakane ai ina ga abun farin ciki ne, Sulaiman yaron kirki ne sannan ga shi ɗan uwa ne ga Yusrah, sai dai fa ki sani mune da ƴa mace, dan haka a ganina mu ɗan jinkirta mu ga ko zai bayyana da kan shi, idan bai yi hakan ba kuma muka tabbatar da suna son junan nasu, kinga sai mu fito da hanyar da zamu sa su bayyana kan su, ko ya kika gani?"

Jinjina kai ta yi tace" Hakan ma ya yi, Allah ya tabbatar mana da alkairi, Allah kuma ya daidaita tsakanin su."

"Ameen." Ya amsa da shi kafin yace "Tidin ma yanzu take min maganar yaron nan Mukhtar jiya ya zo ya gaishe ta, kuma ta gaya min ita dai ya mata dan ta gamsu da shi, na faɗa mata ta yi ƙoƙari yau ɗin nan ta samu dangin mahaifin Abrar ta sanar da su sai ya je ya gaishe su, idan sun amince da shi suma kinga ai abun farin ciki ne."

Da murna sosai Anna tace" Kai ma sha Allah, ai kam ma na san za su amince in sha Allah, tunda Mukhtar yaron kirki ne kuma ɗan babban gida sannan mai abun yi, in sha Allah za su amince tunda naga Abrar tana yin shi sosai."

Jinjina kai Aba ya yi da gamsuwa yace" Allah ya sa." Da fara'a Anna ta amsa da" Ameen."

Hirar su suka ci gaba da yi cikin nishaɗi da fahimtar juna, Anna ta ji daɗi sosai akan zancen Abrar, kuma tana fata su amince dan gaskiya ba ta ware Abrar da su Manal ba, dan wani lokacin ta kan faɗawa kan ta ba twins gare ta ba sai dai triple, dan haka idan har bikin Abrar ya tashi za ta yi abinda za ta yi ga bikin Nawal ko Manal ne, ko da hakan ba zai ma uwar ta daɗi ba ita dai za ta yi, dan bata ga ranar da zasu shirya da Tidin ba, tunda ba ta ga laifin da ta mata a rayuwa ba da za ta daina shi sannan ta bata haƙuri, kenan kuwa sai dai su yi ta yi.



*AA MENSION*


Tunda ta farka ba ta gan shi ba ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar shadda, duk da ba ta yi kwalliya ba amma ta fito sak a amaryar ta, sanyayyan yanayin ta ya kasa barin ta saboda har yanzu tana tuna kiran da yarinyar nan ta yi masa shi kuma ya ɗaga a gaban ta, yarinyar da zai aura nan da sati uku ko ma ƙasa da haka, ganin idan ta zauna a ɗakin za ta sake ɓarkewa da kuka sai kawai ta fito falo, anan ne ma da ta ga masu dafa abincin nan ta tuna da akwai wasu mutane a gidan.

Da wannan yanayin na ɗumm da zafi zafi ta ce su je kawai za ta neme su, take suka bi umarnin ta dan ta yi niyya ba wacce za ta yarda ta zauna gidan ta dan kawai ta dinga dafa mata abincin da daga ita sai shi za su ci kamar wata musaka, masu gyaran gida ma idan sun zo za ta ɗauki ɗaya dan ta dinga tayata gyaran gidan tunda yana da girma, idan ita kaɗai ce dole wata rana za ta gajiya ko kuma ta yi nan ba ta yi wani wurin ba.

A haka ta shiga madafa ta fara haɗa musu abincin rana, tana tsaka da aikin ta a saiɓance ta ji ya rumgume ta ta baya tare da cusa kan shi tsakanin wuyan ta da kanta yana shinshinar wuyan ta, lumshe idanu ta fara yi sai kuma ta ɗan nemi zamewa saboda haushin shi fa ta tashi da shi wallahi, akan me zai yarda ya auri yarinyar nan to? Saboda ya fi son ta ko? Wannan abu da ta tuna da rashin tabbacin wa ya fi so tsakanin jita da Nabihat ya sa ta jaye jikin ta gaba ɗaya ba tare da ta ko juya ta kalle shi ba ta ci gaba da aikin ta.

Ajiyar zuciya ya sauke har saida ta ji sautin haka, a hankali ya kamo kafaɗun ta ya juyo da ita suna fuskantar juna, sosai yake karantar yanayin ta da kuma kallon fuskar ta da take ta ƙin yarda su haɗa idanu, saida ya kai hannun shi ya tallabi haɓar ta ya ɗan ɗaga sama yana ci gaba da duban fuskar ta ta, amma duk da haka ta ƙi ɗaga idanun ta dake da yalwar gashi ta kalle shi, hakan ya sa cikin sanyin murya yace "Kalleni nan? Me ye?"

Ƙara lumshe idanu ta yi cike da takaicin tambayar da ya jefo mata wai me ye? Bai ma san me ye ba? Shiru ta yi bata amsa shi ba kuma bata da niyyar amsawa, a hankali ya sake tausasa muryar sa yace "Yanzu ma kukan za ki yi? Wai me ake miki ne na kuka?"

Janye fuskar ta tayi daga riƙon da ya mata tana shirin sake bashi baya ta ci gaba da aikin ta, fizgota ya yi ya sake tsayar da ita gaban shi da ɗan ɗaga murya yace "Wai me ye? Ki kalleni ki yi magana mana, shirun nan da hawayen nan azabartar da ni yake, me ya sa kika kasa gane hakane wai? Me ya sa kika fi son hukuntani ta haka?"

Cike da ƙarfin hali ta buɗa idanuwan ta wasu hawaye masu zafi na gangaro mata wanda ba ta so hakan ba, cikin ɗan ɗaga muryar ita ma tace" Ba komai, me ya sa kai ma ka fi so ka azabtar dani ta wannan sigar? Me ya sa ba za ka tausaya min ba?"

Girgiza kai ya yi a tausashe yana tallabo fuskar ta cikin hannayen shi yace" Come on *mom Haidar*, da me nake azabtar da ke? Na miki alƙawarin zan daina, faɗa min please?"

Share hawayen fuskar ta tayi ta girgiza mishi kai tace" Ba komai, ka barni zan yi aiki, yunwa nake ji."

Tsura mata idanu ya yi yana jin kamar ya ƙwalla ihu saboda rashin sanin me ma yake damun shi, sai kawai ya sauke numfashi a hankali yace" Ina so zan je na ga ɗana, sannan zan ga Mukhtar akan wani case da za'a qhiga kotu gobe, kin yarje min na je?"

Ba tare da ta kalle shi ba tace" Na isa na hanaka fita ne dama? Allah ya kiyaye."

Kallonta ya sake yi kafin ya ranƙwafo ya sumbaci kumcin ta sannan yace" Saura ni."

Kallon shi ta yi tace" Me fa?" Amsa ya bata da" Sumbata ta?"

Jim ta yi kamar ba za ta aikata ba, sai kawai ta juyo irin tana ɗaɗɗaure fuska bata kalli idanun shi ta ɗan ɗaga ƙafafun ta dan ta kai daidai tsayin fuskar sa, da sauri ya ja baya yana girgiza kai yace" In dai a haka za ki min ki bar shi na gode, sai na dawo."

Juyawa ya yi zai fita duk sai ta ji ba daɗi kuma yana neman ƙara dagula mata lissafi, har ya yi tako na uku ta ɗan yi baya kaɗan ta yi nasarar riƙo wuyan hannun shi, dakatawa ya yi ya juyo yana kallon ta har ta gyara tsayuwar ta tana fuskantar shi, amma kuma ta tsaya ƙiƙam ba ta ce komai ba kuma ba ta yi komai ba.

Murmushi ya saki tare da girgiza kan shi kaɗan, na shi ajin ya sauko ta hanyar saƙala hanayen shi ya zagaya su ta bayan ƙugun ta sannan ya cirata cimak ya ɗora ƙafafun ta saman nashi ƙafafun dake sanye da takalmi ƙafa ciki hakan ya ƙara mata tsayi sannan ya ɗan duƙo da fuskar sa kusan bakin ta sannan yace "Oya, gani to."

Sannu sannu ta ɗaga kan ta ta kai bakin ta saman kumcin shi ta sumbata, hakan ya sa ya sake juyo ɗaya ɓarin nan ma ta sumbata, sannan ya taro bakin shi yana cewa "Saura nan, amma bana son sumbatar kan titin nan gaskiya."

Kallon bakin nashi take yi da yake magana har ya rufe bakin, a hankali ta lumshe idanun ta sannan ta tallabo fuskar tashi cikin hannayen ta, ba tare da ta buɗa idanun ta ya saka leɓen shi na ƙasa cikin bakin ta tsumdum, a hankali ta ɗan tsotsi leɓen kamar ta kama leɓen jariri sannan ta dinga janye bakin ta daga cikin nashi a hankali har ta cire tare da sauka a ƙafafun shi tana sunkuyar da kai, juyawa ta yi za ta tafi dan ci gaba da aikin ta, cikin nutsuwa ta ji muryar shi yace "Take care my lady."

Da kai kawai ta amsa mishi da to tare da ƙarasawa ta ci gaba da aikin ta, shi ma daga haka ya fice duk da dai yana farin ciki amma kuma ta wani ɓangaren ba ya jin daɗin wannan yanayin nata sam.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
05/07/2024, 10:45 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*90*




Gidan Anna ya wuce kai tsaye, da shigar motar shi gidan ya tabbatar da an cika umarnin da ya bayar na a kawo masa yaran sa wajen Anna za ta fi kulawa da su, saboda motar sa na yin oda suka fito a guje suna riga-riga na murnar jin wanda suka kwana biyu basu saka a idanun su ba, shi kanshi da wannan murnar ya fito daga mota ya ɗan rusuna ya buɗe musu hannayen shi duk suka shige jikin shi.

Da farin ciki yake kallon kowacen su yana kula da yanayik tsaftar su da kuma nauyin cikunan su, dan tsaftar dai ba laifi, amma ba sa ƙamshi na turaren da shi yake saka musu, sai kawai ya ɗan yi tsaki ya shigo da su a hannayen shi yana musu hira su kuma da kinibibi suna bashi amsa da yaren da suke magana shi da su.

Su Nawal ne kaɗai a falon suna ta shirmen su da shewa, da suka gan shi ne suka gaishe shi cikin nutsuwa dukan su ya amsa musu da barka, kallo ɗaya ya ma Manal ya ɗauke kai yana ayyana _'An dai ji haushi kawun Y. Turaki, ka rasa wa kake tsoro sai waccen ƴar.'_

Sai kuma ya ɗan dubi Abrar ita ma, sai kawai ya sake raya _' Hasbunallah wani'imal wakil! Dubi dai girman Mukhtar, amma wacce ya ma abu kamar yana ma Hajia.'_

Sai kawai ya taɓe baki tare da nufa falon Aba yana faɗin "Allah ya shirya ku."

Su kam da suke ta ƙus ƙus suna son tambayar Yusrah amma sun kasa, saida ya buɗa ƙofar falon zai shiga Nawal ta fuske sosai tace "Akhi ina auntyn mu Yusrah?"

Juyowa ya yi ya kalle ta, sai kuma ya kalli fuskokin su gaba ɗaya, wato ƴaƴan Anna akwai gulmar masifa da sa idon jaraba, ina ruwan su da sabgar shi to? Auntyn su? Share su kawai ya yi ya shige tare da rufo ƙofar, hakan ya sa Manal faɗin" Allah ya ƙara, ba na gaya miki kar ki fara ba, ai ga irin ta nan."

Harara Nawal ta cilla mata tace" To zagina ya yi ko duka? Amsa dai ce bai bani ba kuma shi ya sani, ai zamu kira ta a waya mu gaishe ta."

Taɓe baki Manal ta sake yi tace" Ni sai naga yana ta mata kallon ƴan iska ma wallahi, ko me mukayi?"

Murmushi Abrar ta yi tace" Ko dai me auntyn mu ta aikata masa a gidan ba, shine zai huce akan mu mu marayu?" Tintsirewa sukayi da dariya suka ci gaba da tattauna maganar Akhi ɗin na su da Yusrah, irin dramomin da suka gani da abubuwa dai kala kala.

*Yana* shiga falon Anna ce kaɗai dan Aba ya fita sai turaren wuta da take yi wa ɗakin tana zagayawa da shi, takalmin shi ya cire a matuƙar nutse ya ƙarasa saman carfet ɗin, ɗaya daga cikin filow saman kujerar ya ɗauko bayan ya aje Meem ya aje ƙasa sannan ya zauna yana tanƙwashe ƙafafun shi, takowa Anna ta yi a nutse bayan ta aje kaskon wutar ta nufo shi tana ƙare masa kallo irin na babba sannan ɗa da uwa, tuni Anna ta fahimci canjin dake tare da ɗan nata da wata ɓoyayyar sahihiyar nutsuwa dake bayyana kanta a fuskar kowane ango, wani ƙyalli ƙyallin goshin da ya sake fito masa da dogon hancin sa uwa biro sak gwanin sha'awa.

Zaune ta yi daf da inda ya zauna akan kujera tana faɗin "Ɗan AA babba, ka tashi lafiya?"

Wallahi yadda Anna ta masa magana sai kawai ya ji wata kunya ta rufe shi kawai ya ji kamar yana neman tsarguwa, to ko dai ana rubutawa a goshin mutum ne cewa ya aikato wannan lamari daga gidan shi?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login