Showing 21001 words to 24000 words out of 397328 words
da mamaki da kuma saƙe-saƙe a zuciya
"NURSE *YUSRAH*!" Aka faɗa da ɗan ƙarfi, hakan ya sa ta ɗaga da sauri , sai kuma ta cira ta nufi ɗakin haihuwar da yanzu yanzu aka shiga da wata mata dattijuwa, ga dukkan alamu ta kusa samun lafiya.
Tana shiga ɗakin ne tana saka safar hannu haɗi da gyara ɗan baby hijab ɗinta fari, haka kuma da ɗan gagawa ta ƙarasa inda docter ke tsaye a gaban matar dake zufa da wani irin ƙoƙari dan ta riƙe numfashinta, domin a kan kunnuwan Yusrah likitan ya sanarwa matar nan ta fa daina nishin nan, dan kuwa tsaf zata fasa cikinta ba zata iya haihuwa da kanta ba tiyata za'a shiga da ita.
Sama sama matar nan ke hailala, zufa na sake karyo mata tamkar zata rasa ranta, likitan kuwa yana neman sanƙamar da numfashin Yusrah sanadiyar abinda yake aikatawa ra'ayne da ayne yana mayar da kan yaron dake neman fitowa.
Jimirin kallon baƙon lamarin nan ya saka Yusrah neman shekarewa tana faman bambance yaren bahaushe a wajen da yake faɗin kalamai kamar haka ' *An kuma, mace ta haifi mace*' , domin ƙiri da muzu take sake fasarawa kanta cewa wannan lamari na gangan ne ba maganar wasa a ciki ko cewar eh lalle ciwo ya haddasa! abin nan zahiri ne ba wai ba ..
"Ke! wannan wani irin hauka ne? yaya zaki min tsaye a kai? ki bani allurar cen ki haɗa min ita yanzu yanzu!" Ya faɗa da muguwar tsawar da ta dawo da Yusrah hayacinta, kasantuwarta ƙaramar likita kuma wace ke bautar ƙasa a wannan asibiti ya saka wanda ba docter bama ke taka su son ransa bale docter.
Da sauri ta ƙarasa ta haɗa masa allurar da yake nufi, still zuciyarta cike da mamaki, domin allurar nan ba ta komai bace sai ta kwontar da naƙuda, lokaci ɗaya kuma ta sake zubawa hannayen likitan ido bayan ya yiwa matar nan allurar sai kawai ya idasa daidaita zaman yaro daidai yadda zai zamo wajibi yankawa a fitar ko a yi biyu babu ko a rasa ɗaya a cikin biyu, wato uwar ko d'an.
Sai da ya fice a ɗakin haihuwar dan ganawa da mijin matar sannan Yusrah ta iya ɗaga ƙafarta ta ƙarasa bakin gadon da matar ke wani irin nishi, ga jini ta zubar, ga ruwan haihuwa yana daf da ƙarewa, a irin wannan lokacin, da irin yanayin da ya sakata ga shekaru ga haihuwa ta zo gangarar nan, tabbas ƙarfin ikon Allah ne kawai zai tashi wannan baiwar Allah.
Wace ta yi mata rakiyar ne murya a sanyaye itama ta kalli Yusrah ta ce" Likita, ni na zata kai ya bado fa? Tunda muke bamu taɓa zuwa da Hindatu haihuwa muka wuce minti talatin bata haihu ba, ko da jajayen sawayenta sai naƙuda ta nuna muke zuwa asibiti bale yanzu da ita ɗin ma ta yi jika, ta so ta haihu a gida dan kunya ni na ƙiya na ɗagawa Elhaji hankali muka yo asibiti, ashe ashe wannan ɗin zata zo da gardama?"
A irin wannan lokacin da ya dace ace idan bakinta ya buɗe kalamai ne zata fitar masu iya zubar da gini dan ƙarfinsu, masu iya saka barci dan nishaɗin su da kwantar da hankalin su, sai ta buɗi bakin ta ji ta fara inda inda tamkar mai yaren bebaye a bakinta
da ƙyar ta iya sarrafa harshenta daidai zuwan likitoci uku dake shirya mutun a kai shi ɗakin tiyata ta ce" Kin san lamarin haihuwa babu yadda baya zuwa mama, gwara da kuka zo asibitin, in sha Allah za'a samu lafiya a yi mata addu'a Allah ya sa a fito da ita lafiya da abinda yake cikinta..."
Daga nan ta ƙarasa ta amshi abin aski da na wanke jiki wanda zata yiwa matar ta shiryata da kyau saboda ɗakin tiyatar sauran likitocin kuwa suka shiga aune aunensu dan su gama a wuce da ita, zuciyar Yusrah tamkar zata faso ta bakinta dan dokawa da ɗacin da take yi mata, zuwa yanzu kuwa, tabbaci take da shi na abinda take sassaƙawa.....tabbas a wannan asibiti ana aiki na neman kuɗi ko da kuwa za'a yi kisa, domin a yau ta gama yarda cewar docter da kansa ya yi sanadin wannan tiyata.
Sa'ilin da aka kammala tiyata lafiya, kamar kusan kullum yanzu ma Sakina ce ta fito da babyn zuwa ga ahalin matar, Yusrah na tafe a bayan ta jiki a matuƙar sanyaye, kamar daga sama ta ji muryar Docter cikin kakkausan lafazi da kuma gurɓatacciyar hausar sa ba tare da ya dube ta ba yace "Ki same ni office ɗina yanzu."
Dama kuma bai kalle ta ba, maganar ce kawai ya yi dan yana da tabbacin za ta fahimce shi, Sakina ma juyowa tayi ta kalli Yusrah da take da tabbacin da ita yake, rarako idanu tayi cikin raɗa tace "Yusrah, ina ga fa hanaki shiga tiyatar sa zai yi, dan ni kaina abinda kikayi jiya da yau ya ban haushi da mamaki, kamar jiya kika fara shiga ɗakin tiyata, ko dan Docter yana baƙo a wurin ki?"
Yusrah kallon Sakina kawai take, ba wai bata fahimtar ta bane, sai dai gaskiya abinda ta gani jiya da yau bata jin akwai wani abu da zai sa ta ji likitan nan ya birge ta har ma da asibitin gaba ɗaya.
Ba tare da tsoron komai ba ta bi bayan shi, zuciyar ta na raya mata idan ya hanata shiga tiyata ma ya kyauta mata, dan ba lallai ta iya jurar wannan lamari ba gaskiya.
Yau ce rana ta farko da ta shigo wannan office ɗin na babban docter ɗin da aka ce mata ƙane ne ga mai asibitin baki ɗaya, kuma shine mai kula da duka asibitin da abinda ya shafe ta, haƙiƙa ta so ƙarewa aljannar duniyar kallo, ofishi kawai, da mutum zai zo na lokaci ya yi aiki ya koma? Shine aka ma wannan ƙawar ta gidan duniya? Shine aka kashe ma irin wannan mahaukatan kuɗin? To ina yake rayuwa? Ya gidan sa yake? Uwa uba kuma shi kacokam ɗin mai asibitin?
Zaune da ya yi a wata rikitacciyar kujera zaman mutum uku tare da ɗora ƙafafunshi saman centre table ɗin dake tsakiya da ya dace da kujerun tare da zuba mata mayatattun matsakaitan idanun shi fuska a ɗaure ya sa dole ta gagara ƙarasa kallon abubuwan da ta fara ta nutsu wuri ɗaya, sadda kanta ƙasa ta yi dan yadda yake kallon ta duk sai take jin ta tsargu kuma ba daɗi.
Saɓanin muryar da tun jiya yake mata magana da ita, yanzu cikin lumana da tausasawa har saida ta ji kamar ta ce yadda ya yi maganar da daɗi saboda ba hausa bace gangariya a bakin shi yace "Me ye ma sunan ki?"
Ba tare da ta ɗaga kan ta ba cikin ladabi tana wasa da hannayen ta tace " *Yusrah Abdul-Hameed Turaki* yallaɓai."
Ƴar fuskar ta mai kama da ta yara ya sake tsarewa da idanu yace "Yusrah, kin kwana biyu a asibitin nan, kuma nasan kin yi aikin tiyata tare da wasu likitocin, to me ya sa naga har yanzu kamar kina jin tsoro?"
A hankali ta girgiza mishi kai tace "Ba tsoro nake ji ba yallaɓai, amma zan kiyaye."
Wani shaƙiyin murmushi ya yi tare da sauke ƙafafun shi ya tangala su a guiwoyin shi sannan yace "Da kyau, zan so haka, dan ni nafi jin daɗi aiki da mata a ko ma ina ne, idan kika kwantar da kai kamar dai irin su... Sakina, za ki ci moriyar aikin ki, wataƙila ma na ɗauke ki na dindindin."
Ta ji daɗi abinda ya faɗa na ɗaukar ta aiki, saboda tana matuƙar buƙatar aikin nan saboda ta dinga ɗauke wata hidimar a gidan su, to amma...! Abubuwan da take gani fa kuma a asibitin? Ko dai ita ce bata fahimtar su daidai? Sannan me ya sa sai da mace ya fi son yin aikin shi?
"Kin gane?" Wannan tambayar ta sa tayi saurin ɗaga kai ta amsa da "E yallaɓai, na gane."
Sake ɗora ƙafafun shi ya yi yana ɗaukar tamfatsetsiyar wayar shi ba tare da ya kalle ta ba yace "Za ki iya tafiya."
"Nagode yallaɓai." Ta faɗa tana juya, tsabar ƙwarewa ta sa ko kai bai ɗaga ba wajen bin bayanta da kallo, iya idaniyar shi ɗaya ce kawai ta gano mishi abinda yake son ganowa, har ta kama hannun ƙofar za ta fita ya ɗago kai yace "Yusrah."
Da ladabi ta juyo ta amsa da "Na'am yallaɓai."
Yatsa manuniya ya nuno mata da alamar gargaɗi yace "Ki kula, ka da ki sake min irin gangancin nan a karo na uku, ba zamu kwashe dake lafiya ba."
Saida ta kalli fuskar shi kafin ta gyaɗa kai tace "In sha Allah yallaɓai." Ƙarasa ficewa tayi ta rufo ƙofar shi kuma ya ci gaba da sabgogin shi a waya.
*PALACE ANZA*
Tun daren jiya bai rintsa ba, da fari farin cikin sake samun wata dama da zai iya kiran kanshi da jami'in soja ya hana shi, har ya kwanta dan yin baccin tare da magunan shi, kwatsam yana duba wayar shi sai ya ga shahararrun kuɗaɗen da shi ma aka turo masa a wannan wata...
Kallon adadin ya yi, ya ƙara kalla, ya tashi zaune yana ƙara zubawa adadin idanuwa, sai ya shiga maimaitawa kan shi tambayar da ya ma kan sa da safe, daga ina kuɗin ke fitowa? Shi bai taɓa damuwa da ya san haka ba sai yau.
Yana cikin tunanin wani abu ya zo masa a rai, shine da akan ce wai *'gida ba ta ƙoshi ba ai ba' a kaiwa dawa*', ma'ana ya fara samun kwokonto akan lamarin gidan su, ai ba buƙatar ya fara bincikar wasu na daban, dan haka bari ya fara sanin wa yake ɗaukar nauyin wannan albashin nasu, sannan motar asibitin da aka ce ta fita gari shaƙe da kuɗi madadin majinyata, kuma motar ma ta asibitin su, ita ma daga ina? Kuɗin cikin na wanene?
Take ya danna lambar Chef, dama shi ba mai tsala dare bare kafin ya yi bacci idan ba wani aiki ya riƙe shi, saboda yana tashin dare dan ganawa da wanda ya reneshi, yake kuma ciyar da shi daga ni'imomin shi, dan haka bai ji shayin kiran ba saboda tunanin dare ya tsala, dan ya san yanzu Chef ɗin bai isa kwanciya bacci ba.
Wayar ba ta jima tana ƙara ba Chef ya ɗaga yana sallama, saida AA ya sauko da ƙafafun shi daga kan ƙayataccen gadon ya sauke su kan wasu haɗaɗɗun belaru masu laushi ya saka amma bai miƙe tsaye ba, inda yake hango kanshi ta cikin makeken madubin dake zagaye da golden colors yana zagaya girar shi da yatsar sa ta tsakiya a tausashe yace _"Barka da dare Aba?"_
Amsawa Chef ya yi da _"Barka my son, ya kake?"_
A taƙaice yana wani ɗaɗɗaga gira yace _" Um! Ina lafiya, Aba dama ina so na san wani abu ne daga gurin ku?"_
Cikin sigar raha Chef yace _" Ohh God! Aswan, binciken kuma ta kai na zai fara?"_
Ba tare da yanayin fuskar sa ya canza ba ya ɗan dakata daga zagaya girar sa da yake yi yace _" No, dama akan albashin da ake mana ne duka gidanmu, Aba wai daga ina kuɗin nan suke fitowa ne? Saboda bana tunanin daga masana'antun Dad ne, duba da yana min tayin ja masa ragamar komai amma ina kaucewa, idan daga nan kuwa da zai dakatar, amma bai yi haka ba, dan Allah Aba ka sanar dani?"_
Da tsananin mamaki Chef yace _" Aswan, mahaifin ka za ka fara bincika? Dama ka karɓi matsayin nan ne dan ka fara ta kan shi? Amma kuwa idan ka yi haka ni kai na baka min adalci ba."_
Babbar yatsar sa da manuniya ya sa ya riƙe karan hancin shi yana rintse idanu, shi amsar tambayar sa kawai yake so ba wani ciwon kai na daban ba, ba tare da ya buɗa idanu ba cikin sake ƙasa da murya yace _" Aba, ba haka bane, kuɗin ne naga sun ƙaru, shine nake so naji, please Aba ka sani ko a'a?"_
Ajiyar zuciya Chef ya sauke har hucin hakan na sauka a kunnen AA kafin yace masa _" Ban sani ba nima Aswan."_
_" Ok."_ Ya faɗa kawai ya datse kiran tare da wurgar da wayar kan gado yana jan ɗan ƙaramin tsaki, wannan abu ya hana shi bacci da wuri kamar yadda ya saba, ya jima zaune yana shafa kan Meem da ta fi kusa da shi har saida ya ji ya tuna da mutane uku da zasu iya sanar da shi abinda yake so ya sani, na ɗaya sakaratan mahaifin shi wato *Bala Zakari*, na biyu kuma shine lauyansa *Br. Issufou Hassan*, sai kuma na uku wanda shine mai kula da duka harkokin Dad ɗin na ƙasar nan wato *Suraj Sidi Kofa*.
Haka ya kwanta da niyyar tashi tsakiyar dare ya yi abinda ya saba yi idan yana cikin aminci da sarari da tunanin gari ya waye ya tuntuɓi mutanen nan uku, ya san ba zai rasa ji daga ɗaya daga ciki ba, Chef shine aminin Dad kuma ya ƙi faɗa masa bayan yana da tabbacin ya sani, amma ba damuwa.
*WASHE GARI*
Dan haka gari na wayewa jiki kaɗai ya motsa ko wanka bai shiga ba saboda yadda ya riƙi wannan lamari ya zauna kan sofa ya fara kiran Br. Isufou, wayar ta ɗan jima tana kururuwa kafin daga wajen shi ya ɗaga yana faɗin _"Salama alaikum, barka da safiya yallaɓai."_
Yana cikin tsane gumin jikin shi da ƙaramin towel ya amsa da _" Barka, kana wani uzirin ne na kira ka anjima?"_
Da girmamawa Br. Ɗin yace _" A'a yallaɓai, ba wata damuwa, Allah ya sa dai lafiya?"_
A tsanake yace _" Dama albashin da ake bawa duk ahalinmu ne nake so naji, daga wane asusu kuɗin ke fita?"_
Saida gaban Isufou ya faɗi ƙwarai da gaske, dan shi gaskiya ba ya son rigimar Aswan ko kaɗan, ba ma zai iya da shi bane wallahi, da sanyin safiya haka ya kira shi kawai dan ya haɗa masa lissafi guri ɗaya, duk da ya sani shima, to ai ba shi kaɗai ba ma, wannan abu ne da ko mutan gari akwai wanda suka san shi duk da kuwa ana ɓoyewa, amma dan su wanye lafiya sai yace _"E to yallaɓai, da na sani ni kam da na faɗa maka, amma kasan iya harkokin mahaifin ka kawai nake kula da su, ban da abinda bai shafe ni ba."_
Ƙwarai yanzu ya fahimci wasa ake so a masa da hankali, kuma hakan da suke yi sai ya ji hankalin sa na neman ya fara tashi, da fari so ne yake ya sani dan baya so ya saka kanshi binciken wasu manyan mutanen, daga ƙarshe *allura ta tono garma*, shiyasa yake so ya tabbatar ba wani abun ɗaga hankali daga gidan su, ahalin shi da ma shi kan shi, to amma yanzu sai yake jin kenan kamar ana aikata ba daidai bane, shiyasa ba'a so ya sani? Dan haka cike da gargaɗi mai razanarwa cikin muryar da ta saka Br. Isufou yin shiru yana shafa goshin shi da ya ji yana masa danshi danshi na zufa yace _"Shikenan, na san ka sani ba zaka faɗa min ne ba, hakan na nuni da cewa laifi ne kenan, zan bincika, idan kuma na gano gaskiyar da bata min ba, ka sani zan dawo kan ka."_
Yanke kiran ya yi tare da aikawa sakatare kiran dan ya ji daga gare shi shima. Inda Br. Isufou kuma ya wartsake gaba ɗaya daga baccin da yake yi yana tunanin ko ya kira Alhaji Aliyun ne ya faɗa masa dan ya masa tsakani da Aswan? To ya taka manya ma bare shi, ga labarin duniya da baya ɓoyuwa ya ji cewa ya damƙi Col. Garba sai da aka yi tattara aka ƙwace shi, to gaskiya ko ba yanzu ba shi kam zai kira mahaifin shi ya shata masa layi tsakanin sa da shi, dan ba zai yarda ya faɗa ma Aswan abinda Alhaji Aliyu zai zarge shi a kai ba, kamar yadda rashin faɗar ma ba zai bari ya saka rayuwar sa a haɗari ba.
*Aswan* kuma ko da ya ji sakataran ya ɗauka bai wani yarda an jata da nisa ba wajen gaishe gaishe kasancewar mutumin shi ne sosai da suke gane ma juna saboda yana da shekaru kuma sun jima da mahaifin shi tare, da yanayin gaggawa AA yace _"Alhaji, tambayar ka zan yi kuma tabbaci gare ni ba zaka ce min baka sani ba, albashin da ake biyan ƴan gidanmu nake so nasan daga aljihun wa suke fita?"_
Dariya sakataren ya yi, sanin da ya ma AA yasa har yake iya hango fuskar shi sanda yake maganar nan, irin a haɗen nan yana karkaɗa yatsa alamar a fa gaya masa ɗin nan sannan a huta, da kulawa da kuma raha Bala sakatare yace _" Chairman nawa, ban da abinka ranka ya daɗe, yadda gwamnatin nan take taku idan bata cire muku naku kasafin ba, ai tsinanniya za ta zama a bakunanmu."_
Jin abinda baya so ya ji ya sa shi saurin lumshe idanu cike da rashin jin daɗi yana ɗan dunƙule hannun shi na hagu, Bala sakatare da ya ji bai da niyyar yi masa magana ya sake cewa _"Chairman, ba ƙaramar gudummuwa Alhaji yake bayarwa a cikin tafiyar gwamnatin nan ba, tun ma lokacin yaƙin neman zaɓe Alhaji ke riƙe da wannan jam'iyya baki ɗayanta, dan haka fa kun cancanci fiye da haka ma."_
A matuƙar sanyaye kamar mai raɗa cikin jin zafin lamarin yace _" Me muka cancanta? Kuɗin talakawan? Ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi?"_
Takaici ya sa shi sakin siririn tsaki tare da yanke kiran ko sallama bai mishi ba ya aje wayar yana dunƙule hannayen shi wuri ɗaya, a cikin kuɗin al'umma ake basu wanda basu ma san ya zasuyi da su ba? Shi wallahi anfanin kuɗin nan gare shi shine ya siyi mota mai tsada da sutura, su ba siyan abinci ba, ba biyan kuɗin wuta ba, ba biyan na ruwa ba, tunda Dad ya saka kanshi siyasa duk aka ɗauke