Showing 63001 words to 66000 words out of 397328 words
ya ɗan kalli Safwan sannan ya juyo yana faɗin "Yallaɓai, akwai abinda ya kawo ka ko?"
AA ya ɗaga dubansa ya ɗan tsare fuskarsa da ido, ya fitar da huci a nutse ya ce" Eh zan dawo kawai in sha Allah."
"To shikenan." Ya amsa da shi da kuma ɗorawa da "Amma yanzu aka sanar min zan tuƙa oga gobe, ban sani ba ko tafiyar a je a dawo ne, ko zamu jima, ban ma san wani gari bane, kenan da zarar na samu sarari zan yi kiran ka dan kar ya ga wani abun." Mani direba ya faɗa yana ɗan ja baya dan ya rufe masa ƙofar.
Juyowa ya yi yana kallonsa ya ce" Yaron can, baya buƙatar kula ta asibiti ne? Sannan a wajen nan ai sauro na iya ƙara masa wani ciwon ko?"
Mani ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Kasancewar ni aiki ne na haya ban zo da shirin kula da shi ba, da masu gadi ke maganar ne na je na ɗauki yaron, gashi an ce gobe zan yi tafiya, dole wajen mai gadi zan je in nemi alfarma ya kular min da shi har in dawo."
AA ya yi shiru yana kallonsa tamkar wanda ke son karantar wani abu a jikinsa, sai kuma ya juya a nutse cikin motar ya ja abin ajiya ya ciro kuɗi yana kallon kuɗin zuciyarsa na masa tunanin kuɗin ya dace ya bada ko sama da kuɗin ya dace ya yi? A lokacin sai kawai ya miƙawa Mani direba kuɗin ya ce" Mani, dan Allah ka taimaka ka saka shi a hannu mai kyau, sannan a tabbatar da an bi diddigin danginsa, yaro ne, idan ya shiga wani hali a yanzu ta yiwu shikenan tashi ta ƙare, Dan Allah a kula idan da buƙatar wani abin ko menene, ko nawa ne ka sanar min ko a wani irin lokaci ne."
Mani ya amshi kuɗin yana rusnawa ya ringa godiya sosai, dan kuwa tabbas AA ya taimaka sosai kuma in sha Allah yanzu zai samawa yaron katifa da gidan sauro da abinci mai rai da lafiya kafin gobe ya miƙawa mai gadi shi da kayan abinci da komai na buƙata har ya dawo sai ya ga yadda zai yi, in sha Allah ba zai bar yaron ya tagayyara ba, domin shi ma ya shiga ransa sosai, da wannan AA ya nufi gidansu, ya musu sai da safe kamar yadda ya saba sannan ya wuce nasa gidan.
Tunda ya shiga ya yi dukkan abinda ya zame masa sabo, harda su motsa jiki, da ciyar da magunansa da cin abinci da yin wanka da yin nafila sannan ya haye gadonsa ya lumshe idanuwansa yana ƙara tsara yadda zai idasa aikinsa cikin sauƙi, sannan ya kwantar da haƙarƙarinsa yana lumshe idanuwansa, sai dai hoton yaron nan ya faɗo idanuwansa tamkar an kankara a jikin fatar idansa.
"Bata da hankali, tabbas ta zauce da har ta iya tafiya ta bar ƙaninta a wannan yanayin, ta yiwu rasuwar iyayen ne ya haukata ta, tabbas ta zauce, ama yanzu ya ya zai yi da ransa ne? Yaro ƙarami ga karayar ƙafafu duka? Ya rab!" A fili ya faɗi wannan kalamai har ya miƙe ya zauna ya samu kansa da haɗe hannayensa biyu ya zubawa waje ɗaya ido.
Kamar da wasa kwanciya ta gagareshi, tunaninsa ya ƙi daidaituwa a waje guda, hankalinsa gaba ɗaya ya kasa tsayawa waje ɗaya sai tunanin yaron da makomarsa yake yi tamkar wanda ya haɗa jinni da shi, wasa wasa barcin kirki gagarar AA ya yi, dan haka kawai yake tunanin sam maganar a barwa mai gadi yaron bai kwanta masa ba, gani yake yi da mai gadin yayi niyar riƙe yaron ko taimakawa yaron ai ba zai ganshi ya barshi ba, da ya taimaka masa ne, maganar tafiyar Mani ta saka shi a tunani mai tsananin gaske har ya dawo daga sallar asubahi hankalinsa a wani wajen daban.
Kusan ƙarfe goma ya fito sanye da ɗinkin yadi ruwan ƙasa, hannunsa riƙe da makullin motarsa wacce bai cika fita da ita ba sai in zai yi fitar sirrin da baya so a san shine a ciki, domin ko lambar ta da take da ita ta Naija ce, sai a yi tunanin ɗan Naija ne ya shigo garin da motarsa.
A nutse yake taka motar, idanuwansa sun ɗan kumbura kaɗan na rashin samun wadataccen barci ya nufi asibitin yana dannawa Mani direba kira ransa cike da wasi wasin abinda zai kai shi, sai dai yana ɗagawa abinda Mani ɗin ya faɗa masa ya saka shi take motar ya ƙarasa asibitin a sukwane ya nufi can baya ɓangaren masu gadin da ma'aikatan asibitin.
Tunda ya zo Mani direba ya ƙaraso yana ɗauke da Safwan, AA ya buɗe bayan motar Mani direba ya shiga da shi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya na rikicin da suka sha da mutanen can a kan ya nemi alfarmar wani ya riƙe masa yaron amma ƙiri-ƙiri kowa ya nuna ta kansa yake yi, ya ajiye yaron a nan za'a ringa amso masa abinci har ya dawo, shine abin ya ɗaga masa hankali har ya fara tunanin irga awanni ya gani idan zasu bashi dama ya kai yaron garin su wajen iyalinsa ya dawo kafin su yi tafiyar nan da oga sai ga kiran AA.
AA na kallon fuskar Safwan dake ta zubar da hawaye ya kalli Mani, ya sake duban Safwan a hankali ya ce" Kukan me kake yi kai da baka da lafiya?"
Safwan ya sake duban mutumen, irin indiyawan nan da suke gani a tv a anguwa wajen mai shayi sak, ya sadda kansa ya fashe da kuka yace" Aunty Yussy nake so a kaini, wai ta gudu ta barni in ji likitar nan, wai bata so na, dan Allah a kai ni, ance su Mama sun rasu, su baba sun rasu, shikenan yanzu bani da kowa? Wa zai ringa bani abinci? A ina zan zauna? Wanene Babana da mamana yanzun?"
Ya ƙarashe yana fashewa da wani kukan da ya saka AA lumshe idannuwansa a hankali ya sauke dubansa a kan Mani direba wanda ya saka bayan hannu yana share hawaye ya furta" Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, in ba Allah ba, wa ya isa ya yi wannan kyauta? Alhamdulilah, ka ga mutanen can duk irin halin da yaron nan ke ciki na rasa wanda zai ɗaukar min in je in dawo, maganganun nan da yaron nan ke yi sun fi komai ɗaga min hankali, ina ma ace in na roƙi alfarmar a yi tafiyar nan da wani direban za'a yi ba tare da an min barazana da aikin da nake ciyar da iyalina ba? Wallahi da mun tafi na saka shi a hannu mai kyau sannan in dawo."
Idanuwansa ya sake saukewa a kan Safwan a hankali ya ce" To kai ba an faɗa maka rago ke kuka ba? ko dai rago ne kai?"
Safwan ya zuba masa ido, sai kuma ya ɗora kansa a jikin Mani direba yana ta sauke ajiyar zuciya, a tausashe AA ya ce" Idan ka yarda ka bani shi in tafi da shi, zan kula da dukkan abinda ya dace nasa, amma da sharaɗi."
Ya ɗan yi shiru sannan ya dube shi ya ce" Daga nan zan zame wajen masu kula da haƙƙin yara, zasu zama sheda sannan su bani takarda,zan kai kotu ta saka min hannu , koma waye ya tafi ya bar yaron nan ya rasa shi, idan yana so ɗin kenan, domin ko waye bashi da hankali kuma bashi da tunani, yaron nan zai zama *ɗana* zan riƙe zan ba shi dukkan kular da ta dace, ko wa ya zo neman sa daga baya ba zan bayar ba, ka amince?"
Mani direba ya zubawa AA ido, tabbas da sai ya fi kowa farin cikin haka! Kuma gaskiyar AA ne ko su waye suka bar yaron nan suka yi tafiyarsu suna nufin sun barwa duniya shi, kuma in har AA zai ɗauki yaron nan ya tabbata sai ya fi samun kulawar da yake masa kwaɗayi a wajensa fiye da wajen kowa, AA dai sananne ne, famillynsa sananniya ce, ko yaushe yake son ganin yaro zai ganshi ba za'a taɓa cutar da yaro ba.
Da kula ya dubi Safwan a tausashe ya ce" Safwan, yanzu ka gama tambaya wanene babanka? Kana so ka san wanene babanka?"
Safwan ya gyaɗa masa kai yana kallonsa,
ya yi ɗan murmushi ya ce" Wannan ne babanka, zaka je wajensa ka rayu? Zaka bi shi?"
Safwan ya kalli AA da fuskarsa ta nuna alamun sassauci da tausasawa sosai, ya kalli Mani direba ya ce" Baba ba kace kaine babana ba? Kuma wannan ai ba'indiye ne ko?"
Mani direba ya yi dariya yana girgiza kai ya ce" A'a, ba ka ji yana hausa ba kamar kai? Kuma ka ga shima babanka ne, in kana so shi zai kaika asibiti ya kaika school da islamiya ya siya maka kayan makaranta da su sweet, zaka je?"
Safwan ya sake zubawa AA ido, yanayinsa ya sake shiga zuciyar yaron, abinka da yaro da yarinta, balle shi da ya yarda nasa iyayen yanzu kuma babu su, ido rufe wasu iyayen da zasu riƙe hannayensa yake nema, sai ya yarda cewar zai bi AA din, ya zamo a nan Mani direba ya barwa AA Safwan domin hatta katifar da gidan sauron cewa ya yi ya barshi, dama kuma da suka fitar da shi ko takardunsa basu bashi ba, daga shi sai rigar jikinsa da gajeran wandon dake jikinsa, a hankali AA ya ja motar ya fice direct ya ɗauki hanyar office ɗin mahaifinsa, domin ba zai taɓa aikata aiki mai girma haka ba tare da yardar mahaifinsa ba, abu ɗaya ne ya sani mahaifinsa ya fi shi irin zuciyar taimakon nan, tabbas Safwan zai rayu da shi wannan garanti ne, hakan ya sa kawai ya tafi wajen aikin mahaifin nasa kansa tsaye.
A lokacin da Aba ya ga jikin Safwan da bayanin AA hankalinsa ya yi mugun tashi, shi da kansa ya ji cewar lalle ko wa ya tsayawa wa'inda suka bar yaron nan a wannan halin ba zai taɓa basu shi ba, nan ya tabbatar masa sun je ganin waɗanda wannan abu ya faru da su, kuma idan bai manta ba kamar ya ga yaron a lokacin nan shi da Anna, rai ɓace yace a bashi waya ya yi kiran asibitin ɗan uwansa dan a zo a ɗauki yaron, sai dai AA ya nuna sam, ba zai taɓa kai ɗan sa asibitin nan ba kuma.
Da mamaki Aba ya ce" Ɗan ka?"
AA ya lumshe ido ya gyara zamansa da kyau ya sake kallon Safwan dake kwance saman kujera inda ya shinfiɗa shi tunda suka shigo , a nutse ya ce" Aba, bari in kai shi clinik lafiya, a min ƙoƙarin takardun dan Allah."
Aban ya sake zuba masa ido yana kallo ya miƙe ya ranƙwafa ya ɗaukeshi ya rungume shi sosai a jikinsa ya kama hanyar fita, miƙewa ya yi da sauri ya bi bayansa har suka ƙarasa wajen motar ya buɗe masa ya saka shi yana kallon ledojin dake ajiye a gaban motar ya ce" Zan kira Humed ya masa siyayar kayan buƙata komai da komai, sannan a yi girki ya zo maka da shi, sai na zo, sannan zan yi kiran barista Isoufu dan ya kula da komai kafin in shigo..."
Hannu ya ɗan ɗaga mishi yace" Ka kula da kanka Son."
Murmushi ya yi ya gyaɗa kansa ya koma gaba ya tayar da motar yana kallon Safwan a tausashe ya ce" Yaron Dady mu je asibiti ko? Ai zafin da sauƙi ko?"
Safwan ya gyaɗa kai yana sake rungume jus ɗin da ya sake buɗe masa mai sauƙin zaƙ yana kallonsa da tunanin ya faɗa masa idan sun je asibiti da lafiyarsa za'a kula ba zai tafi ya barshi ba, hakan ya sa ya kwantar da hankalinsa ya ringa shan jus ɗin nan har suka ƙarasa.
Sunna zuwa lamari ne aka yi na manya, sannan na sanayya, Docter Siddik abokinsa ne tun na yarinta, shi ya karɓe su da kansa yayi ja gabar sake gwaje gwajen lafiyar Safwan, aiki sabo da cin kuɗi da jira, sai dai ya sani komai sai an yi domin AA na tsaye a kan ƙafafuwansa komai yana talabbe da yaron da kiri-ƙiri ya cewa docter Siddik yaronsa ne, bayan shi dai bai taɓa jin aurensa ba bale har a kai ga haihuwa, amma kuma matsayin da AA ya taka ya saka bai yi masa musu ba ko jayayya ba, hasalima a saman file ɗin Safwan an saka *SAFWAN ASWAN ANZA* ne kamar yadda ya faɗa.
Wannan aikin ya ɗauke su lokaci kafin a basu ɗaki a jona masa ƙarin ruwa, ɗaki mai sunna ɗaki, nan da nan kuma sai ga Anna da Humed suka zauna tare da shi da yaron ba tare da ta titsiye shi ba duk kuwa da irin yadda ranta ke wassafa mata tambayoyi, tausayin yaron ya rinjayi komai sai ta adana tambayoyinta har su koma gida.
*YUSRAH*
Ranar ta yau ta fi jin ta fiye da kowace rana, dan kuwa a yau ne take ganin duk za ta haɗa kawunan kuɗin da take saka ran za'a ma Safwan aiki da su, wannan farin ciki ya sa ta karɓi aron wayar abokiyar tafiyar ta bayan sun zauna inuwa ta loda kati a wayar sannan ta fara kiran lambar kawun ta da Algerie, sai dai sam ba ta same shi ba a waya, dan haka ta maida kiran ga aunty Fureira ƙanwar Mahaifiyar ta.
Nan ma ta samu ƴar tangarɗa kafin daga bisaki ta samu wayar ta shiga, tun suna gaisawa matar mai dattako tace "Murya kamar ta Yusrah?"
Da ƴar dariya Yusrah ta amsa mata da "Ni ce da kaina aunty, kun gane ashe?"
Da zumuɗi auntyn tace" Allah sarki, Yusrah me ya samu wayar ki da ta Hannah? Haka ma Babanku ba'a samun shi, kuna lafiya?"
Jim! Yusrah ta yi tana jinjina abun kafin ta buɗa baki tace" Aunty, sai dai kuyi haƙuri, amma Baba, Mamanmu da aunty Hannah duk basa nan."
Da mamaki ta tambaye ta suna ina? Nan ta sanar da ita wannan tashin hankali, ta shiga kaɗuwa sosai kasancewar abu ne da ba ka yi tsammanin sa ba, kuka ta shiga rusuwa a wayar tana sallalami da salati da faɗin" Ashe dama zuwan da aunty Habiba ta yi ban kwana ta zo mana? Ace aunty Habiba ta rasu kwana har huɗu yau sai yanzu zamu sani? La'ilaha illalah! Shiyasa ashe kwana da kwanaki gabana ke ta yawan faɗuwa babu gaira, sai yawan mafarke mafarke da nake yi ina yawan tunaku, nayi ta kira kuma shiru na kasa samun kowa daga cikin ku."
Haka Yusrah ta amsa mata da ba laifin ta bane na Goggo ne, komai da yake faruwa ta sanar da ita, dake macece mai kawaici ga wanda ya mata, sannan wacce bata ɗaukar raini, ba ta da haƙuri da shariya kamar Mamansu Yusrah, sai dai tana da kirki fiye da tsammani, nan ta dinga faɗa tana tir da halin Goggo Hindatu, saga ƙarshe tabbaci ta ba Yusrah ko za ta yi dare a hanya sai ta shigo garin nan dan ganin halin da Safwan yake ciki, har Yusrah ta nuna mata a'a fa, tunda tafiya ce ba kaɗan ba kuma hanya sai a hankali, ta hakura da sassafe sai tayi asubanci, amma sai tace "A'a Yusrah barni na taho ke dai, so nake na zo na ga Hindatun, idan alaƙarku da ita ba ta min kuma sun ji ba zasu iya da ku ba, to ƙafar ku ƙafata wallahi sai kun dawo nan, dan ban son rainin wayo ko kaɗan."
Yusrah kam ta san ba abinda zai hanata zuwa sai dai uziri na rashin kuɗi ko lafiya, dan haka ta mata addu'ar zuwa lafiya dan tasan sai tayi dare kafin sukayi sallama.
*Sai da* ta bari magariba ta tunkaro ta sake komawa wajen gwagwonsu, a lokacin da ta dawo daga wajen aiki ta riƙo kuɗin aikinta cass, ko da ta je gwagwon nasu ta rufeta da masifar cewa bafa ta son takura ba zai yiwu ta fitar da kuɗi da hasken nan ido ya sauka kansu a biyo dare a ƙwace ta mutu ba, sai duhu ya shiga, hakan ya sa a dole ta fita ta samu wani guri ta ɗan zauna dan kar tayi tafiya biyu kuma baban burinta ta bata kuɗin nan ta yi shiga ɗaya, ta jewa Safwan ɗinta da albishir ɗin ta samo kuɗin da za'a yi masa aiki, sannan ta sallami Iya Abu sai kuma su yi zaman jinya ita da Safwan ɗin ta kafin komai ya lafa ta tsayar da matsayar inda zasu zauna, abu ɗaya ne ta sani ba zata taɓa zama a gidan gwagwonsu ba, domin a bayyane yake zasu ga rayuwar rashin gata iya ganinsu, a yanzu haka duk wannan hidimar da ake ta rashin lafiyarsa gwagwonsu bata taka ƙafata asibitin nan ba, tana gida tana neman kuɗin ta.
A lokacin da ta shigo Gwagwo na ɗaura alwallar sallar magariba bayan an jima da aka yi sallar, ta saki butar nan tana rafka salati ta nuno Yusrah da ƴar yatsarta ta ce" Wannan yarinya da kin shafi mayu idan kika kama mutum ya kaɗe dan wallahi sai kin kaishi ƙabari zaki bar shi, wannan bala'i da me ya yi kama? Mu je in baki ko kya daina min sanɗo a soron ƙofa a irin lokacin nan da sawaye ke ɗaukewa!"
Hankalin Yusrah sai da ya ƙara tashi, a birkice take kallon Gwagwo, ƙwarai a da ma Gwago akwai faɗa da tsatsauran ra'ayi, amma a lokacin da ƙasa bata rufe idanuwan iyayensu ba, abin bai kai haka ba, cin fuskar bata kai haka ba.
Jiki ba ƙarfi ta bi bayanta suka shiga har ƙuryar ɗakinta ta ciro wani ƙyale baƙi ɗaure da kuɗin ta wurgo mata tana faɗin" Jaka ɗari uku ne da aka kasafa, haka kason Babanku ya kama, gayanan sai ki yi sara da duban bakin gatari, idan kika kai kuɗin nan kaf kika zuba a ƙila wa ƙala ba lalle ki gane rayuwa ba, inai maki hannunka mai sanda, ki rage wani abin ki koyi sana'a saboda riƙe kai,