Showing 363001 words to 366000 words out of 397328 words
na rawa da muryarta ta ce" Baba ƙarami ina yini, Khadija ce, Khadijan ka."
Uncle Sulaiman ya yi murmushi ya ce" Na gane ai, fatan kina lafiya?"
Gabanta ya sake faɗuwa, dan ba haka suka saba waya da shi ba, in suna waya ya kama musu ƴan waƙe da faɗin wanenshi wanenshi, amma yau ya daƙile ta, bata yi ƙasa a guiwa ba ta ce" Uncle, dama kira na yi in sanar maka abinda yake faruwa, wallahi baba ƙarami Mamar mu na cikin mugun hali, ka san gidan nan a million huɗu da za ta bayar ɗaya ta biya, shine mai gidan ya bata sati ko ta fitar masa daga gida, tunda aka yi haka ta yanke jiki ta faɗi ba'a kuma gane kanta ba, ka ga dama Babanmu ya saketa fa ya yi tafiyarsa shi da Goggonmu, wallahi baba ƙarami ta kai wajen da abinda za'a ci a gidan nan yanzu wahala yake yi, kuma kawai su auta ƙarami suka yi facali da ruwan zafi ya watsun masa sosai a ƙafa aka yi biris da abin, yanzu haka yanzu ni dai ƙafar tashi tsoro take bani, dan wasu ruwa take fitarwa ga kumburi sannan sai kaga kamar tsutsa ta faɗo a ƙafar, gashi ta sandare na yi na yi na lanƙwasata ta ƙiya, wallahi bamu san inda zamu saka ran mu, ba dan Allah ka taimaka mana baba ƙarami."
Uncle Sulaiman ya sauke numfashi yana sauraron ta, sosai zuciyarsa ta karye balle na yaron, sai dai wallahi ransa a ɓace yake a kan Hinda dan haka ya ce" Allah ya sawaƙa, Allah ya baku yadda zaku yi."
Ta ɗan yi jim da jan hancin da take yi, murya na rawa ta ce" Baba ƙarami shine na ce wai ko zaka taimaka ka biya mata kuɗin gidan, idan ya so sai in je in nemi na abincin da na asibitin nasa?"
Kai ya girgiza ya ce" Kina ji? Ni idan kika kashe kar ki kuma kirana, ita ta san yadda muka yi da ita ai, in mahaukaciya ce ita zan gani ne ai, dukiya dai dukiya, kuɗi dai kuɗi, da ita duk abin nan da take bata kama dahir ɗin ba? Ai mallakar gida shine dahir ga wanda yake tunanin duniyar matabbata ce, a lokacin da ɗan uwanta ya faɗi ya mutu da matarsa da ƴarsa babba aka bar ƙaramar da ƙarami ai cewa ta yi ba waje a gidanta, kuma kema ai baki yi kirana kin faɗa min ba kuka yi shiru yarinya take ta gararamba cikin gari, yanzu an taɓo naku files ɗin har kun fara bazawa duniya? Ki ji da kyau nima kuɗin gadona yafe mata na yi ai, da wanda ta cuci Yusrah duka ta haɗe ta cinye, to ina ta kai su? Ina taƙamar kuɗin siye da siyarwar? Duka kaf ta haɗa ta kashe damuwarta, ta isarwa kanta, mai kuɗi ce ai Hinda, ki gaya mata na tabbata ita zata ce ke ki yi kirana ko na ɗaga, ki faɗa mata na ji halin da take ciki kuma babu abinda zan iya yi mata, sai anjima."
Ƙitt ya kashe wayarsa yana miƙewa ya shiga harkokin gabansa, wayar ta mutu amma ta kasa sauketa daga kunnenta, har sai da wacce aka ce bata cikin hayyacin ta ta ɗago da ƙyar tana kallonta ta ce" Yaya kuka yi ne?"
Aunty Khadi ta ce" Wallahi ya ce ba ruwansa ki nemi yadda zaki yi."
Goggo Hinda ta fashe da kuka da ƙyar tana nishi saboda yunwar dake ƙwaƙularta ta ce" Inna lillahi! Ina zan shiga? Ina zan yi? Ya ya zan yi? Yanzu Sulaiman haka ya faɗa? Shi sai riƙo da muguwar zuciya? Yana ji za'a koreni daga gidana amma ya ce in yi yadda zan yi? Na shiga uku ga yara ga rashin lafiya ga rashin muhalli? wayo Allahna ni Hinda ina zan saka raina?"
Aunty Khadi ta share hawaye a raunane ta ce" Mama, kin ga abinda nake son ki gane kullum kina ƙiyawa ko? Ita rayuwa ana kyautata ta ko dan gobe, ana yi ana daidaita rayuwa saboda gobe, Mama rayuwar gaba ɗayanta ya zamo ana sara da duba bakin gatari, Mama duk yadda na so ki tausasa sai in zama abar gaba ni da kika haifa ina wani bare? Ita duniya ko wa ye kai ta iya yi maka kwantan ɓauna ta ja ka sai kun lula sararinta ta sake ka, ko me kake taƙama da shi kuwa yana iya ɓacewa ɓatt, bari in je gidan in ga abinda zan samu saboda ƙafar nan tasa ta fi komai ɗaga min hankali, Allah ya rufa mana asiri kar ace ba zata kuma amfanuwa ba kuma, ki sha kokon kafin in dawo mu sake duƙufa faɗawa Allah da istigfari ko a dace ya ƙara mana lokaci, a yanzu kam kaina ya gama cinkushewa."
Ficewa ta yi ta nufi gidanta, Goggo Hinda kuwa ta sake ɗora hannu a kai daga kwance tana fitar da huci mai zafi na rashin madafa, balle idan ta waiga ta ga hatta Safiya gari na wayewa take yin tafiyarta tana yawon gidan ƙawaye tana cin abinci dan kuwa bata zama ta sha wahalar nan har ta sha wahalarta tsaf take gujewarta sai ta ji hankalinta ya ƙara tashi, anya kuwa ba biyu babu ba ta tafka a rayuwa? Babu nan ɗin babu can asara bibbiyu kenan? Inna lillahi Wa'inna ilaihi raju'un.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
06/07/2024, 18:11 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*92*
Ta gidan su Nabihat kam shiri ya kamkama ana ta yi ba ji ba gani, Maman ta shirye shirye take kamar za ta kashe kan ta, gayyata take yi ta har ta wuce hankali duk dan tana so a zo aga abinda ta shirya dan bikin Nabihat ɗin, ba ta da wata matsala saboda dama ta tanadi kuɗi dan wannan ranar, sannan Chef ya zube mata wasu dan duk a fita kunya, ga kuma nauyin kayan da Aba ya ɗauke wanda take nan har yanzu ta kasa zaɓar wanda take ganin sun dace da ƴar ta, diddigi take bi tana so ta gano kayan Yusrah wane kala ne, dan ranar da ta je dan ganin hakan da idanun ta sai ta ga Fauziyya a can ta tahowar ta, dan haka yanzu take ta son ganowa dan tana so ta zaɓar ma Nabihat wanda suka fi na Yusrah tunda har Aban ya basu damar zaɓa da kan su sai su faɗa masa kuɗin ya bayar.
Tana son tambayar Fauziyya amma har yanzu ba wani shiga sabgar ta take yi ba, duk da kuwa ta ji daɗin kakkauran gudummawar da ta bayar a auren na ƙanwar ta, da kuma ɗinki kala uku da ta gwangwaza mata duk dan ta birge ta, kuma ba ƙarya ta birge ta ɗin kawai dai faɗin rai ne ya hanata saukowa ta rumgumi ƴar ta ita ma, ga kuma yadda ta ga Nabihat tana jan ƴar uwar ta ta a jiki wajen yi mata shawara, kuma tana iya ƙoƙarin ta wajen basu shawarar da ta dace dan ganin komai ya tafi daidai.
Sai dai duk da haka bai hana Nabihat ci gaba da haɗuwa da Imran ba, maye ne, kuma idan yana son abun ya son hanyar da yake bi yana samun shi, dan haka ya gama kama Nabihat ɗin kamun da zuwa yanzu ita ke kiran shi ta ce ya kamata fa su haɗu, duk da haka kuma a tsorace take sannan tana komai da taka tsantsan saboda sanin wa ye wanda za ta aura kuma wa ye mahaifin ta, a haka fa har yanzun bikin ta da Aswan ya rage saura ƙasa da sati ɗaya, lokacin ne ta nuna masa ba zasu sake haɗuwa ba shikenan, amma shi ya san ba shikenan ba, ya san za ta sake neman sa dole ranar da buƙatar ta ta ciyo ta.
*Wajen su* Anna ma dai suna shirin, sai dai gaskiya ba wani armashi kamar yadda aka gudanar da na farko, hasalima idan ba lamarin ɗinkuna da ƴan biyu da Annan ke yi ba babu wani abu yanzun da ake yi tunda namiji ne da su, amarya kuma tana gaban iyayen ta, a ganin Anna dai ko za ta fara wani shagali to kuwa sai ko kwana biyu saura bikin in sha Allah.
Da wannan ne ma yau da Aswan ya zo gidan ta sake tambayar shi wai yana leƙawa wajen Nabihat? Amsa kawai ya bata da zai je in sha Allah, amma shi damuwar sa ba bikin nan bane, shi a ganin shi ma duk bikin ne ke rikita masa ta gidan, yanzu za su kasance lafiya lau anjima ka ga ta sauya fuska kawai ya kasa gane mata.
***Tunda Chef ya ƙara duba takardun da ya ce lokaci yayi AA ya kawo masa komai ya bar masa komai saboda abubuwa sun yi zafi sosai a kan Hamat kuma ana buƙatar komai na bincike ya ɗago yana dubansa ya ce" Son, ban ga bayanin wanda ya saka mana binciken mu a Tiktok ba, ka san babbar kotu ce za'a yi zaman, kuma kai ba zaka hallara ba sunanka dai zai je, ka kuma san duk wani abu da ya gama duniya idan bamu saka komai dalla dalla ba ana iya samun matsala, kuma a nan ban ga bayanin ba."
Ɗan jim ya yi kafin ya ce" In sha Allah nan da gobe zuwa jibi zan kawo bayanan."
Chef ya bashi hannu yana faɗin" Allah ya aminta yarona."
Miƙewa ya yi suka gaisa ya sara masa sannan ya tafi, yana tuƙi saman hanyar gidan Anna yana tunanin abinda ya sa ya sha'afa bai yi binciken nan ba? Ta yiwu har da rigimar da Yusrah ke yi masa a fakaice ne, kwanakin ƙarin auren nan suna ƙara matsowa tana ƙara rikice masa a birkice, jiya fa hatta gado sai da ya farka ya ga bata nan, da ya duba ya ganta ƙasa kwance ta duƙunƙune shi ma ya bita suka kwanta a ƙasan, ta yiwu gadon ne bata so, shi bai san yadda zai yi da rikicin ta ba, ya yi tambayar ya yi magiyar, ta nuna ba komai amma kuma a aikace yana ganin koman.
Ajiyar zuciya kawai ya fitar bayan ya shige gidan ya nufi ciki yana tunanin anya ba ɗansa zai kai mata kusa da ita ba? Ko ta sauko ta daina rikicin? Ko ya kai mata su Meem? gashi Anna ta ce sai ta yi watan ta cir kafin a kai mata su dan ta saba sosai a gidan ta, shi kam ya ya za'a yi ta gane cewar kaf duniya damuwar sa ita ce? Ta rufa masa asiri ta kwantar masa da hankali, ya ya za'a yi ne abin nan ya daina ɗaga mata hankali? Da ace za ta shiga zuciyarsa ta duba da ta ba kanta lafiya a kan maganar kowace mace a duniya ƙasa da Anna, duk macen da ba muharamarsa ba wallahi ba ta gabansa.
Bayan ya gaisa da Manal da ta soke wayarta da gaggawa ya ɗan bita da kallo da ta tashi dan ta kawo masa abin buƙata na tarbar baƙo, da ta dawo ɗauke da kayan sha ta ajiye masa ta miƙe zata tafi a nutse ya ce" Yaushe ake baku hutun karatun nahdar?"
Manal ta dawo ta duƙa ta ce" Nan da wata daya ne Akhi, kuma hutun sati ne ake yi tunda zango gajere muka zaɓa."
Ya yi ɗan jim kafin yace" Zuwa lokacin kawun Y. Turaki ya shiga na shi hutun ai ko?"
Manal ta ɗago tana ɗan buɗa ido ta ce" Na'am?'"
AA ya dubeta cikin ido yace" Ba na son raini."
Da sauri ta sadda kai tana faɗin" Eh, ina ga sun samu hutu suma."
AA ya ce" Ok, kawai in ya zo hutun sai a yi auren, tashi ki je."
Wani saƙalau ta yi ta rasa gane inda ya nufa, a dole ta tashi ta nufi ciki tana lalubar wayarta dan ta yi kiran matarsa, dan kuwa maganar nan tasa wallahi tana so a yi mata fashin baƙinta, shin abin ne ya zo ko maganar aurensa yake yi? Kai inna lillahi! Yayan su akwai bahagumen mutum.
Bai taɓa komai ba ya shiga wayarsa a nutse ya shiga Tiktok ya je wajen favoris ɗin da yake sakawa heart idan ya gani, ya ringa wuce ball ball da abinda ya shafi harbi da ƙyar ya je kan vidion, dama ya saka mata heart ɗin ne dan idan ya tashi buƙata ya samu, yana shiga ya shiga dubawa, ya kuwa taki sa'a ya ga wanda ya ɗora ɗin yana yawan ɗora mutane da sunan masu neman taimako, sai kawai ya shiga wajen cmnt section ya rubuta abu kamar haka _" Ka min dm, akwai taimako daga yaron gwamna dan in ji inda zaka amsa."_
Daga haka ya fita ya shiga kiran wayar Yusrah yana lumshe idanuwansa dan ya san yanzu bugun zuciyarsa zai cenza, yanzu zai afka duniyar bege, in ba dan yana son ganin Anna ba yau bai so fitowa ba, sai kuma chef ya yi kiransa, so yake yi ya yi ya koma dan ya samu daddaɗan girkinta, su ci tare su kwanta a makwanci ɗaya, ta sake bashi haja ya kwasa cike da ganima sassauƙa, ya na so yayi ya je gidan dan burinsa ya jita a ƙirjinsa tana zuba masa shagwaɓa, kai Y. Turaki duniya ce.
Ai kam a nutse ta ɗaga wayar can ƙasa ƙasa ta furta" *Rohi*."
Aswan ya lumshe idanuwansa a tausashe ya furta" *Ƙoramata*."
Ta shagwaɓe fuska ta ce" A'a fa, kai ko?"
Yayi dariya ƙasa ƙasa ya ce" Me kike yi?"
Yusrah ta langwaɓe kai ta ce" Ina zaune gaban hotonka, ina yi maka addu'ar ka dawo lafiya."
Wani tsadaddan murmushi yayi a hankali ya ce" I miss you more mine, zan shigo da wuri, me zan kawo maki?"
Yusrah ta ce" Kai kawai nake so ka zo lafiya."
A hankali ya ce" In sha Allah zan zo, i love you *Jaanu*."
Ta rufe ido tana ƴar dariya ta kashe kiran, shi kuwa ya yi wani saƙalau yana tunanin duniya, kai duk wanda baya soyayya ya shiga uku, ashe an jima ana cutar sa bai sani ba? Yo soyayya ai ta fi kuɗi gaskiya, shi da ya san haka abin yake tunda ya fara mafarkin manya da ya yi auren nan da yanzu ɗan Anza yana da jikoki ashirin a ƙalla, gaskiya ya jima yana shirme bai je ya rungumi mata ba, shi yanzu in ba ƙaniya ai ba zai iya rayuwa ba ko kaɗan, Allah dai ya ƙarawa Y. Turaki lafiya da nisan kwana dan kuwa ƙaniya sai inda ƙarfi ya ƙare, ci za'a yi a duk yadda hali ya bada.
*Yusrah* kuwa na ajiye wayar ta ga ɗaya daga cikin masu tayata guga na murmushi bayan ta ɗan zuba mata ido, murmushi ta yi ita ma ta soke kai kawai, domin matar ba yarinya bace, ta tabbata abinda ya bata dariya da ta ce tana gaban hotonsa bayan aiki suke sha a kicin da falo, to ya ya zata yi da ranta ita da ta shigo makarantar manya, ta shigo ne da ƙarfin ta, kamar yadda soyayyar AA ke son haukatata ita ma sai ta haukata nasa zuciyar, ba kishiya ba? Nabihat ta shigo, ta shirya tsaf zata amsheta yadda ya kamata.
Tana tuna maganar Nabihat da irin yadda ya zamo saura kwana huɗu yau a ɗaura mata aure da Aswan gaba ɗaya sai walwalar saman fuskarta ta ɓace ɓat, a hankali ta ringa jin zuciyarta na ƙuna sosai, a hankali ta ringa jin ɓacin rai na son rufe mata zuciya, tana daf da faɗawa a halin jin tsanarsa a ranta dan gani take yi ai laifinsa ne wayarta ta shiga ringin, tana ganin Manal ce ta ɗaga ta koma falo tana amsawa haɗi da ƙoƙarin cire tunanin nan a ranta, dan ta sani ba gudu ba ja da baya, Nabihat matar Aswan ce gwara ta saba rayuwa da haka a zuciyarta.
Da dare ya yi ya shigo bayan ya gama sallar isha'i ɗin sa ya sameta yadda yayi fata, bayan sun gama dukkan abinda suke yi kafin kwanciya suka garwaya a babban filin baje kolin soyayya suka farantawa juna har kamar su cinye juna, alƙawarurrukan soyayya babu irin wanda bai faɗa ba, zuciyarta kuwa ta karɓa ta gode suka yi barcin su a yau ɗin ma ba tare da ya je gidan su Nabihat ba kamar yadda Mamanta ta yiwa Anna ƙorafin ya ya za'a yi ace ƙafarsa bata taka inda matarsa take? Aure saura ƴan kwanaki amma basu zauna sun fahimci juna ba? Ya ce zai je kafin a ɗaura amma bai ga ranar ba, shi dai haka kawai yake jin ƙiwar zuwa zance wajen wata da ba Yusrah ba, Allah yake roƙo ya bashi ikon cinye jarabawar nan ya sa yayi adalci a tsakaninsu.
*Washe gari* kusan ƙarfe goma na safe ya shiga Tiktok ɗin sa bayan Yusrah ta tafi ɗakin ta da nufin zata je