Showing 315001 words to 318000 words out of 397328 words

Chapter 106 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69993

ido kaɗan idanuwansa na tara ƙwalla sosai, dama tafiya zai yi wajen yaya Mubarak saboda yaya Mubarak ɗin ne da kansa ya nemi haka bayan Hajia na yi masa kukan jikinsa ya ƙi sauƙi, sai ya ce idan ba damuwa ta tura masa shi ya ɗan huta ya kwantar da hankalinsa sai ya dawo, haka kawai ya ji bari ya zo ya yi musu sallama ya kuma tafi da ƙudirin in sha Allah zai cire matar wani a zuciyarsa na din-din-din shine ya sameta ta fito ta fitar da kayan aikinta.

A nutse yake nufo inda take har ya ƙaraso face to face da ita kaɗan, idanuwansa ya ɗauke daga kanta kamar yadda ta ɗauke, ya yi ɗan murmushi wanda har amonsa ya shiga kunnayenta, ya ƙara ɗagowa ya kalleta a karo na ba adadi, a hankali ya juyar da kansa yana jin lokacin da ta ce" Yaya Bilal, i...i...i...ina yini, au i...i...ina kwan...."

Ƙarshen harafin ne ya tsaya a saman leɓenta, girgijen tashin hankali na girgiza ƙirjinta tana neman katsata da ƙasa sakamakon hango hancin motar uban tafiya, ɗaya daga cikin motar da idan ka ganta ka ganshi ne.

Idanuwanta ta haɗe ta dantse da ƙarfi ta ɗan ja baya kaɗan saboda irin kusan da suka yi da Bilal dan ba zata so hakan ya sa ya mata wata fassarar ba, Manal da ta biyo Nawal da Abrar ne suka zaro ido da sauri suna kallon lokacin da ya tsayar da motar har kusa da ta Bilal sannan ya buɗe ɓangaren dreba wanda yake ɓarin da suke gaba ɗayan su ya fito daga motar a nutse ya saka hannunsa yana ɗan gyaran cravate ɗin dake wuyansa wacce ya saka saman baƙar riga da baƙin wando na yadi mai kyan gaske sai takalmi ƙafa ciki ruwan ash mai duhu sosai sai agogon hannunsa mai tsadar gaske wa'inda suka haɗu suka mahaukacin haska fatarsa da madaidaicin askin kansa wanda ya fito da tsarin girman ni'imar kyau da tsaruwar da Allah ya masa.

Ƙasa ƙasa Manal ta miƙa hannu dan ta taɓo Abrar dan ta faɗa mata wallahi su je su kirawo babarsa dan a tsayuwar nan da ya yi ya dubi inda su Yusrah suke sau ɗaya sannan ya juya ya dubi wajen mazaunin dreba ya zubawa wasu takardu ido, lokaci ɗaya jijiyoyin wuyansa na wani irin nuna kansu, sai kawai ta ji ta dafa iska, hakan ya sa da sauri ta juya, sai dai ikon Allah wayam ba Abrar ba labarinta.

Da sauri ta juya ta yi ciki ganin ya taho, tsai idanuwansa a kan fuskar Yusrah wacce ke kallonsa ita ma tana ɗan ƙiƙifta idanuwanta zuciyarta na ci gaba da harbawa, da sauri Bilal ya juya ganin ta kafe waje ɗaya da kallo.

Wallahi shi da kansa sai da ya ji faɗuwar gaban da ba zai so ya sake jin irin ta ba, tashin hankali sai kace an kama shi turmi da taɓarya da ita? Haka ya ji hankalinsa na neman tashi da sauri ya juya ya koma gefe yana ƙoƙarin yi wa Aswan barka da zuwa, domin ko a da ya san waye Aswan, ya san waye shi, sai dai ya faɗawa wanda bai san shi ba waye shi, kuma ko gidan suka zo suna girmama shi sosai, kuma suna gudun yin fitina da shi a matsayinsa na yayan Aunty Intisar.

Gaishe shin da ya yi ya sa ya ɗan sake kallonsa sau ɗaya jal, kafin ya sake dubanta bayan ya masa alamun amsawa da hannunsa na dama ya ɗan sakar masa fuska sannan yana maido hannun a hankali ya sakaya cikin nata da take ta jimƙewa tana buɗewa sannan ya juya da ita ya shiga nufar kicin ɗin dan ita kaɗai ce hanyar da yake iya shiga da ita mafi kusa da shi.

Suna shiga Nawal dake tsaye dan tun shigowar Manal ta ɗan faɗa mata sama sama ta yi ciki da gudu, ta zuba musu ido da sauri ta ɗauke idanuwanta a lokacin da Yusrah ta tirje tana kallonsa bayan ya shigo da ita ta ce"...




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:55 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*79*



A lokacin da Yusrah ta tirje tana kallonsa bayan ya shigo da ita ta ce" Ka dakata mana, ka tsaya mana, ya ya zaka ringa min kallon nan kamar ka kama ni da wani bayan babu abinda idanuwanka suka gani? Idan ma akwai wanda ya dace a tuhuma ai kaine, ina ce kwanan baya kai ka kai Nabihat har gidan aunty Intisar, kuma a nan a gabanmu sau nawa kana tsare ta da kallo, har abincin hannunta kake amsa...."

Juyowar da ya yi ya janyo ta da ƙugun ta ya ɗan turata baya baya har bayanta ya haɗe da jikin garun wajen mai tsayi ɗan kwalinta ya faɗi ƙasa ya ɗan duƙo sosai daf da fuskarta ya zubawa fuskarta ido yana jin irin yadda ƙirjinsa ke harbawa da wani irin ƙarfi, gumi na tarun masa a gashin kansa, idanuwansa kuwa sun riga sun kaɗe jajir yana kallon yadda take zaro ido tana ƙoƙarin leƙawa inda Nawal ta fita da gudu ta haura sama.

Muryarsa a haɗe sosai da irin amon da bai saba yi mata magana ba ya ce" Menene? *Yyyyusrah*...ki barni haka..."

A hankali sosai ya ajiye maganar yana sake duban idanuwanta da suka cika da ƙwalla, a hankali ya sake buɗar bakinsa ya kai sau uku yana rufewa, da ƙyar ya iya sake buɗar bakin nasa ƙasa ƙasa sosai ya ce" Son sa kike yi ne har yanzu?"

Yusrah gabanta ya sake faɗuwa, tana kallonsa muryarta a cakule ta ce" Ya ya zaka min wannan tambayar bayan ni ban maka ita ba a kan Nabihat?"

"Nabihat...Nabihat...Nabahat..blablabla...tu peut ouvrir ta bouche me repondre a cette question bon sang?(zaki buɗe baki ki bani amsa ne?)" Ya ƙarashe yana dukan garun nan har ya zamo ta tsorata sosai har ta ƙanƙame jikinta.

Anna da sauri ta idasa shigowa ta ƙaraso ta riƙo hannunsa tana faɗin" Subhanallah! Jikan Anza, kaine a gida? Lafiya? Subhanallah! Sannu da zuwa, ina fatan lafiya!"

Riƙo hannunsa da Anna ta yi da muryarta ya saka a dole ya saki ɗayan hannun ya duƙar da kansa yana kallon hannun Anna dake ta ɗago fuskarsa tana kara faɗin" Jikan Anza, calm dawn, what hppn sweetheart?"

Idanuwansa ya sake buɗewa a kan Anna, a hankali ya ce" Anna, ita wannan yarinyar so take yi lalle lalle sai ta ga waye ni a kanta? Ya ya zan mata tambaya ta ƙi bani amsa? Tambayar da na maki nake son amsarta Y. Turaki."

Ya ƙarashe yana ɗaga murya, hakan ya sa da sauri ƴan matan Anna guduwa daga laɓen da suke yi, a rikice Yusrah dake kuka ta dubi Anna ta ce" Anna, wai dan kawai ya zo ya tarar da yaya Bilal ya zo ina gaishe shi shine fa, shine yake tunanin wani abu, bayan wallahi ba wani abu na fitar da fulawa ne na ganshi shine na gaishe shi sai kawai gaya nan ya iso."

"Ƙarya kike yi, ni ba tambayar da na maki ba kenan, tambayar ki na yi in har yanzu kina son sa? Kin ƙi bani amsa , kin ƙi ki bani amsa, dama kin isa kina aurena ki yi tunanin zan yi tunanin wani abu? Da ace wani abun da kike tunani na yi da ba a kan ƙafafuwanki Annarki zata same ki ba, ki kiyaye, ki kiyaye, bana son in...."

Sai kawai ya yi ɗif sakamakon irin yadda yake jin muryarsa shi da kansa sama sama, subhanallah, subhanallah, subhanallah! Idanuwansa ya rintse yana jin kansa kamar zai buga, a birkice ya saki hannun Anna da sauri ya damƙo nata ya jata ƙiiiiii ya fita daga kicin ɗin da ita.

A guje ƴan matan Anna suka shigo har da Nabihat da Annan suka mara masa baya, Anna zaro ido take tana faɗin" Jikan Anza bani ƴata, bani ita nan, kar ka saki ka daketa, bani ita nan..."

Sai dai bai tsaya ba sai da ya je wajen motarsa ya buɗe ya sakata gaba tana ihu da komai ya rufe ƙofar da ƙarfi sannan ya juyo inda Anna ta ƙaraso da gudu gudu tana ƙoƙarin cakumo shi ta ce" Idan ban wanka maka mari ba kace ba Aslama aka saka min a zanen sunana ba, dan gidanku ina zaka kai ƴar? Dukanta zaka yi?"

A hankali ya riƙe hannun Anna, idanuwansa da suka rikiɗe suka yi ja ya sauke a nutsatsiyar fuskarta, sannan ya haɗe hannun nata cikin nasa biyu a hankali ya kai kusan fuskarsa ya ɗan shafa fuskar nasa a hankali ya ce *" Anna, ba zan iya dukanta ba, ta riga ta gama dani, kawai na gaji ne da in na zo in samu ta fita, sai kawai in hangota da wata shiga ita da ƴan matanki, Anna wallahi ina ji a jikina da zuciyata sosai, kuma ba ruwanta tana fitowa har nan ba hijab babba, har ta tsaya tana kallonsa? Anna kallonsa take yi ido cikin ido..., please ki rufa min asiri kar ta ja in je in aikata wani abin da zaku yi kuka ku duka, zan kaita gidanta ne Anna, ranar da kika saka zaki mata rakiyar sai in kawo maki ita tunda safe sai ku rakata da yamma, but yau idan har na barta a nan ban san me zan iya aikatawa ba, trust me ba zan yi mata komai ba, ko da na so kakkaryata a yau ban isa ba Anna..."*

Ya ajiye maganar a hankali, ya sake riƙe hannunta a hankali ya ce" Wallahi na san ban isa ba Anna..." Sai kawai ya saki hannayen nata a hankali ya juya ya buɗe motar ya shiga sannan ya yi baya-baya kafin ya saita hancin motar zuwa gate ɗin gidan sannan ya harba motar zuwa waje da gudu.

Duk da ta ji tsayar su da odar da ya yi, da gaisuwar da ta ji wani ya mishi shi kuma bai amsa ba a dai jin ta, bata iya ɗagowa dan ganin ina ya kawo ta ba, kawai ta gama yarda cewa PG ya dawo da su, in ma a rufe ta ita ɗaya ko su zauna tare, amma kam ta san nan zai ɗaure ta, har ta ji sun sake ɗaukar *wata tafiyar* can ta ji an sake dakatawa dai bata ɗago ba, saida ta ji ya buɗe mazaunin shi ya fita ya kuma rufo ƙofar irin da ƙarfin nan har ya sakata zabura ta ɗago bata shirya ba.

Shi ta fara bi da kallo da hanyar da ya bi ɗin har ya ɓacewa ganin ta, hakan ya sa tana shasheƙa ta shiga kallon makekiyar rumfar ajiye motocin da motar ke ƙasan ta, sannan ta hangi iya abinda za ta iya hanga na daga gidan daga nan zaune, bata san gidan shi ba wanda suke zaune da Safwan, dan haka ba za ta iya sanin nan ɗin wane gida bane kuma. Mayar da kanta tayi jikin kujerar mota tare da shafa kwantaccen gashin ta da a tsarin su fa yau ne za'a mata ƙunshi da kitso, amma gashi ya ratso da ita wani wajen ba ko ɗan kwali a kai... Maganar ɗan kwali da ta yi ya sa ta gaggauta duba ƙafafun ta, suma dukansu babu ɗaya mai takalmi alhalin tasan da takalmin ta a ƙafa kafin faruwar wannan abu.

A hankali ta buɗe motar ta fita tana ci gaba da kallon gidan, wani irin haɗaɗɗen tsari ne aka zubawa gidan na musamman gwanin birgewa, da yadda aikin ginin ya kasance sak irin gidajen da kake gani daga waje, sai ya ɗauki hankalin ta sosai ta shiga juyawa tana kallo da mamakin waɗannan mutanen wai wace irin dukiya ce da su ta ban mamaki haka? Duk yadda take ganin ba kamar gidan su Anna, sai ta ga wannan ɗin ya fi shi kyau nesa ba kusa ba da tsaruwa sosai, kawai girma gidan su Anna zai nunawa wannan ɗin...

Wani gagarumin ɗawisu da ta gani ya fito daga wata kusurwar cikin wata irin hamshaƙiyar tafiya mai kyau da gani ya sa ta zabura da sauri ta kama hanyar da ta ga ya nufa shi ma, tun bata ƙarasa kaiwa ba ta ji kukan wasu tsintsayen daga wani wurin daban da bata san daga ina yake fitowa ba, hakan yasa ta matso wasu ƙwallan tana ayyana _'Dama ka kawoni nan ne tsintsaye su cinye banza kuma ba yadda za'a yi da su ko?'_

Ta inda ta ga ya bi nan ta bi, wata ƙanƙareriyar ƙofa ta tarar, ba madubi bane, amma kuma dai a wurin ta ba zata kira shi katako ba, dan alƙur'an kamar irin itacen nan na China da suke sassaƙewa suna sarrafa su ta hanyoyi da dama, a kuma jikin ƙofar ta ga wurin empreint da kuma jerin madannai da lambobi, ba ta yi mamakin ganin wannan ba dan ko wajen shiga falon Aba ta ƙofar baya akwai irin wannan digital ɗin, sannan ta ji daga wajen su Manal a gidan shi ma akwai sanda ya sa aka saka har da na Safwan cikin masu buɗewa.

Waiwaya ta yi ta ga ɗawisun nan kamar gidan ne yake kewaya, sai ta sake kallon ƙofar ta kai yatsar ta babba ta ɗora wajen emp ɗin, ai ko a ɗan ƙaramin screen ɗin ya nuna yatsun nata sun shiga kuma ƙwaƙwalwar na'urar ta ɗauka, take ta ji kamar an zare sakata a nutse a jikin ƙofar, hakan ya sa kawai ta tura ƙofar daga ciki ta hanyar riƙe dogon ƙarfen riƙewa da aka yi, taɓe baki ta yi tana rayawa a ran ta _'Wannan ƙofa kamar ana ciyar da ita, ai da ba sai an yi wahalar saka wannan tsaron ba, tunda sai wanda ya ci ya ƙoshi zai iya buɗe ta.'_

Aka cewa duk kyan waje bai kai ga ciki ba, Yusrah dai kam da ta zauce ba da ta gaggauta hangen shi a salon zaune ba ya ɗora ƙafafun shi saman centre table ɗin dake falon da takalmin da suka haska ƙafafun nashi, ya cire rigar shi ta sama ya aje gefen shi saman kujerar sannan ya ɗaga kan shi sama tare da ɗora hannun shi saman goshin shi idanun shi a rufe gam, sai ɗaya hannun dake saman kujera ya jimƙe shi ƙwarai kamar wanda zai naushi wani.

Kamar marar gaskiya ta shiga takowa saɗam saɗam har ta je kusa da shi ta tsaya tana ƙare masa kallo tana kuma wasa da yatsun ƙafar ta dake cikin wani irin basaraken carfet da ta rasa gane laushi ne yake ko taushi, ka rantse da Allah a kan wani lafiyayyen bredi take ɗora ƙafafun ta.

Ko dan tana likita ce? Ko kuma dan tasan waye shi idan yana cikin damuwa? Ko kuma dai sanin cewa bata kyauta bane? Ɗaya daga cikin ukun nan dai ya saka ta ƙare mishi kallo har ta iya hango yadda jijiyar kan shi ke harbawa alamar kan shi na azababben ciwo kenan, a sanin da ta mishi kuma bata tamtama idan aka taɓa jikin shi ba'a ji zafi ba zazaaɓi ya rufe shi, take ta yi wani takwaf takwaf da fuska ita ma kamar za ta fashe da kuka, tunda ta san idan yana halin rashin lafiya ita ma hakan yakan dame ta sosai da sosai.

A hankali ta tsoma ƙugun ta kan hannun kujerar da yake zaune, hakan ya sa ta fi nashi zaman tsayi tana kallon shi, cikin wata irin kasalalliyar muryar da ta sha kuka da kuma shagwaɓa da son kwantar masa da nashi hankali ta furta "Aban Safwan."

Shiru babu amsa kuma babu alamar zai saurare ta, saida ta haɗe wasu yawu masu nauyi a hankali cike da tsoron yanayin irin cakumar da zai mata a gidan nan daga ita sai shi ta ɗora akan nashi hannun dake jimƙe sannan ita ma ta rintse nata hannun, murya kuma na ɓari sosai saboda bata yarda ba zai iya tattaka ta a gidan nan ba ta shiga faɗin " *Abanmu*, na rantse maka da Allah ba abinda ka ke tunani bane ya faru, wallahi tallahi ban san da zuwan Yaya Bilal ba, na fito ne kawai na gan shi kuma ina kwanan da nace masa ma ko amsawa bai yi ba sai ka shigo, please Aban Safwan kar ka saka damuwar nan a ran ka, ka san za ka yi rashin lafiya sosai, ni ma kuma...nnnnni kuma....*ni ma kuma hakan sai ya taɓani*."

A hankali ya ɗago kan shi ya sauke idanun shi a kan ta, bai ce mata komai ya dai zuba mata idanu yana kallon ta da idanun shi da suka zama abun tsoro, cike da ƙunar abinda ke ranshi kawai ya wani taɓe baki yace" Hmmmm!"

Sai kuma ya ɗauke kallon shi daga gare ta ya sake rufe idanun shi, duk da hmmmm ɗin nan ta mata zafi, amma sai ta sake marairaicewa tace" Wallahi gaskiya nake faɗa maka, dan Allah ka yi haƙuri Yayan Intisar,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login