Showing 324001 words to 327000 words out of 397328 words

Chapter 109 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70119

anan?"

Da mugun sauri ya girgiza kai yana takawa inda AA ɗin yake yace "Bbba..., ba komai yallaɓai."

Yadda ya ruɗe lokaci guda, da yadda daga tambaya ya ga duk hankalin shi ya tashi sai zufa yake ya sa AA zargin shi sosai, sai kawai ya jawo kwalin da hannu ɗaya, ganin a rufe yake da leda sai kawai ya saka makullayen dake hannun shi ya keta tsakiyar kwalin, a nutse ya shiga buɗe har ledojin da aka rufe saman kwalin da wasu manyan takardu farare sol, ko da ya kai ga abun ciki sai ga wasu kwalabe a jejjere masu murfi shima na kwalba, ƙurawa abun idanu ya yi yana kallo ganin kamar wata halitta mai ban tsoro, har da kamar yatsu yatsu kuma dai kamar abun zai numfasa, amma kuma wani kala-kala haka irin wani gurin ya yi kore wani guri ya yi duhu, alamar lalacewa ne ya yi har ta kai ga haka.

Shi kam bai san ko menene ba gaskiya dan bai taɓa gani ba, kuma ba ya tunanin ko ƴaƴan sa ashirin zai ma wannan abun farin sanin da yana ganin ta zai gane ta, dan haka yake ta kallo da al'ajabin abun ya ɗan kalli dr ɗin yace "Me ye wannan ab...?"

Amai da ya yi barazanar taho masa ya sa shi saurin rufe baki yana lalubar aljihun rigar shi har saida ya ciro hankc. mai tambarin sunan AA babba sannan ya sake kallon dr Issa da duk ya yi zuru zuru yace "Me ye wannan?"

Zazzare idanu kawai ya shiga yi har Aba ma ya taso yana so ya ga me ye, hakan ya sa AA saurin jawo kwalin tissue ɗin dake saman table ɗin dr Issa ya miƙawa Aba, karɓa ya yi yana rufe hancin sa shima yace "Wai me ye a ciki?"

Nan ma dai shiru ya yi ba amsa, dan haka ran AA ya ɓace ya buga table ɗin da ƙarfi yana daka masa tsawa da cewa "Ba ka ji ana magana ne? Wannan nace me ye? Me kuke da wannan abun a asibitin nan?"

Aba da ya kalli abun sosai yake kuma kan kallon shi ne ya ɗan dafa damtsen AA yana kallon dr Issa yace "Wannan abun, kamar...kamar mahaifa ko?"

A razane AA ya kalli Aba, haka ma Aba yake kallon dr Issa, dr Issa kuwa sai ya shiga nan nan yana haɗe hannayen shi yace "Yallaɓai, nima ban san menene ba, wannan ɗin saƙon Dr. Hamat ne, da yana rashin lafiyar nan ne aka kawo aka ce a ajiye masa, nima ban san ko men..."

A hassale sosai AA ya matso kusa da shi yace "Ƙarya kake ka san ko menene, idan ba haka ba ya za ka ta ajiyar abu haka wari na neman illata ka, za ka faɗa min gaskiya ko sai n..."

Hannun shi Aba ya riƙe gam gam yana kallon fuskar shi da yanayin son kwantar masa da hankali yace "Jikan Anza, kwantar da hankalin ka, ka nutsu ka ji, calm down."

Sai kuma ya kalli dr Issa yace "Dr, ka faɗa mana gaskiya wannan na me ye? Me kuka aikatawa da wannan abun? Daga ina ma take?"

Da in-ina dr Issa yace "Ka yi haƙuri yallaɓai, wallahi nima ban san komai a kai ba."

"Ba dai za ka faɗa ba kenan? Ka fi so mu saka ƙafar wando ɗayan da zan zame maka tashin hankalin da za ka gwammaci mutuwa?" AA ya faɗa yana wani murmushi na alamun zai aikata tsaf, kallon shi dr Issa ya yi, sai kawai yace "Ka yi haƙuri yallaɓai, dan Allah kar ka yi sanadiyar lalacewar takarduna, idan ka yi haka zan rasa aiki a duk faɗin duniyar nan, zan faɗa maka gaskiya, amma ka min alƙawarin sassauci yallaɓai? Dan Allah?"

Wani kallon ashe ƙaramin shege ne kai ya masa ya ɗauke kai yana taɓe baki, sai Aba ne ya dubi dr Issa yace" Ba komai dr, na maka alƙawarik ba wani mummunan abu da zai same ka."

Jinjina kai ya yi da gamsuwa da maganar Aban, a hankali yana gige wani sabon gumin ya zauna kan kujerar shi, hakan ya sa Aba da AA damar sake zama akan kujerun su suma suka zuba masa idanu suna saurare.

Cike da ɗar-ɗar yana sharar gumi da hannayen shi yace "Yallaɓai, gaskiya ne wannan ɗin mahaifa ce, kuma ta matan da muke karɓan haihuwar su ne anan asibiti, muna cirewa ne mu ɓoye ba tare da sanin matan ba sai mu killace ta, kamar yadda kuka gani ann mukan yi anfani da sinadarai da dama da suke iya sakawa ta jima bata lalace ba bare ta yi wari, yanzu ma jimawar ce ta wuce misali saboda tun kafin Dr ya kwanta rashin lafiyar nan suke ajiye anan, shiyasa har ta buga take warin nan, kuma dama a yau nayi niyyar fitar da ita daga asibiti cikin dare na kai can wani waje mai nisa sannan na ƙona."

Dafe kai Aba ya yi yana cire hular sa ya ajiye jikin sa na kyarma, AA da bai kula da hakan ba ya tsare dr Issa da idanuwa yace" Me kenan kuke yi da ita? Hakan ai zalinci ne? Kenan shiyasa da jimawa da na zo nan na samu wata tsohuwa na faɗa akan sai an basu mahaifar su?"

Jinjina kai ya yi yana sadda kanshi ƙasa yace" Hakane yallaɓai, dubbanin mata sun ma wannan asibitin Allah ya isa, wasu kuma Dr. Hamat suke ma saboda ga da ga yake cutar su kuma suna gani, mahaifar kuwa nima ba da sa hannuna bane, kawai ina taya shi ajiyewa ne har sanda yake turasu ƙasar waje."

A ɗan razane AA yace" Ƙasar waje? Mahaifar? Me ake da ita acan?"

Numfashi dr Issa ya yi yace" Ai ƙasashen nan suna anfani da ita sosai, musamman wajen sarrafa mayukan nan da mata ke shafe shafe da su, irin su jan baki da sauran su, sannan akwai ɗaiɗaikun mutanen da yake siyarwa masu zaman kan su ba irin kamfanunuwan nan dake sarrafa abun siyarwa ba, ba na ce ga abinda suke aikatawa ba, amma dai yana siyar musu suma."

"Subhanallah! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Aba y faɗa da ƙarfi jikin sa na ɗaukar rawa sosai, da sauri AA ya miƙe tsaye ya riƙe Aban dake faɗin "Kaini gida Aswan, ka kaini gida bana jin daɗi."

"Shiiitt!" AA ya faɗa yana kama Aban sosai ya miƙar da shi, kallon dr ɗin ya yi da wani irin mugun gargaɗi da saida cikin shi ya sake hautsinawa, dan wallahi a cikin kallon nan ya ga shi ɗin banza ya ce ma zai gudu ya bar ƙasar, ya je ina? Ina zai shiga ya ɓoye masa? Yana kallo ya ja Aba suka fita ya kai shi mota ya zaunar sannan ya dawo mazaunin shi, ruwa dake motar ya buɗe ya ba Aban yana ɓalle masa botir ɗin rigar sa ta ciki yana faɗin "Please Aba ka nutsu, ka nutsu dan Allah Aba kar ka ɗaga hankalin ka, sha ruwan nan a hankali, yawwa Abana, yawwa Aba."

Ruwan Aba ya sha da basu da sanyi sannan ya jinginar masa da kansa a kujerar ya lumshe idanuwa yana sauke numfashi sosai, da sauri ya ja motar shi kuma suka isa gida hankalin shi a tashe, da taimakon shi ya shigar da Aba har falon shi ya zaunar da shi, Anna na ta tambayar me ya faru? Amma bai bata amsa ba saboda miƙewa da Aba ya yi yace "Zan shiga ciki na yi alwala, jikan Anza, ka je gida ka huta kai ma."

Daga haka Aba ya shige ɗakin sa, AA ya jima zaune yana jiran fitowar Aba amma shiru, sai kawai ya ce Anna ta je ta zauna da shi dan Allah kar wani abu ya sa ta bar shi ko na sakan ne, hakan ta yi cike da jin ba lafiya ba, amma da ta same shi yana sallah kan sallaya sai kawai ta zauna kan kujerar ɗakin ta zuba masa idanu tana kallo.

Saida ya ga Safwan ya faɗa masa zai kwana anan kafin ya bar gidan, sanin ko ya je gidan ba zai samu nutsuwar da yake da buƙata ba saboda su twins da masu kitson da ya baro, sai kawai ya wuce wasu sabgogin dan dai kar ya zauna shima ya ce zai takura kan shi da tunanin da zai haddasa masa ɓacin rai. Daga ƙarshe office ɗin Humed ya je ya sake yi masa magana akan kayan da uncle yake bashi yana fitar masa da su, saida suka tattauna sosai har ya samu Mukhtar ma a gida sukayi magana akan case ɗin na Humed, anan ya yi sallah magriba da isha'i sannan ya mishi sallama ya kama hanyar gida.

Yana hanya a hankali yake tafiya kiran Arif ya shigo wayar sa, da fari sharewa ya so yi saboda baya yanayin farin ciki, amma kuma da ya tuna inda zai je zai tarar da wata halittar da zama bai taɓa kama su tare ba a ɗaki ɗaya, sai kawai ya ɗaga yana share duk abin dake ran shi yace _"Me ye kuma na damuna ina kan hanyar gida?"_

Arif kam dama ba gajiya yake da surutu ko tsokana ba, sai kawai ya taɓe baki yace _" Yo kana hanyar gida sai ba za'a dame ka ba boss? Me za ka je ka yi gida yanzu daga sallah isha'i?"_

Da alamar shaƙiyanci AA yace _" Matata tana gida, dan haka zan je ne in ga mata ɗan nan."_

A ruɗe Arif yace _" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! La'ilaha illalah, Muhammad rasulillah! Kai sirikin Chef wallahi ka ji tsoron Allah, yaushe aunty Yussy ɗin tamu ta tare ban sani ba?"_

AA ya bashi amsa da _" Arif, kar ka sake kira min matata da aunty, auntyn ka daga ina? Garjejen ƙato da kai dan Allah? Kuma da kake cewa baka sani ba, hala kai ne Anza ko?"_

Arif ya yi dariya yace _" Ba ni bane Anza, amma ni ne Arif, amma dai ka siye abinda ake ba amare kafin su ma su yarda su ɗaga bujen su?"_

Murmushi AA ya yi yace _" Arif ban son iskanci fa, yanzu sunan Anza ka kama kai tsaye? Kuma da kake maganar ɗaga buje, ni na faɗa maka ina buƙatar abun cikin bujen ne? Ai da ni da Y. Turaki duk ba lalatattu bane ko? Ina ruwanmu da wannan iskancin naku."_

Cike da tijara Arif yace _" E na gani, na gani boss, to in ka isa kar in yi bacci yau, kaga dama nima aurena ake shirin maidawa, dan haka gani nan gidan naka zan taho maka da tsaraba ka kai wa auntynmu."_

Cikin hargagi AA yace _" Arif zan ci u...ban hanaka kira min Y. Turaki da auntyn ka ba?"_

Dariyar ƙeta Arif ya masa ya kashe kiran yana tabbatar masa kar fa ya shiga gida gashi nan, shi ma dariyar ya yi kawai yana girgiza kai da faɗin" Allah ya shirya ka Arif, ni me ma zai aikeni fara yi wa Y. Turaki wannan kallon? Ita ma ai da ganin ta saliha ce wallahi, ba ma za ta taƙaleni da fitina ba."

Haka kawai da ya zo ƙofar gidan sai ya kasa shiga ya tsaya, dan ya sani maganar Arif dutse tunda ya ce zai zo sai ya zo ɗin, kuma haka ɗin ne ya faru, dan bai fi minti sha biyar ba Arif ya zo ƙofar gidan, nan ma saida suka sake haurawa sama da ya dage kawai su je ya raka shi shi kuma ya ce in ya isa ya ga kwalliyar Y. Turaki da ko shi bai gani ba to ya zama kwaɗo a nan take, da ƙyar dai Arif ya tafi yana mitar "Allah ya shirye ka, wallahi in faɗa maka gaskiya ba ƙaramin jarababbe za'a yi ba, ka ga ni mai ƙaunar ka ne da gaskiya dole in faɗa maka, amma wannan ka ci gaba a haka auntynmu ta gudu da ƙafafun ta, kuma idan Allah ya taimakeni ka zama kwaɗo yanzun da ka yi fata, tsaf zai ɗauke ka in kai wa auntynmu in ce saƙo ne ka aiko mata ta aje ka a ruwa."

Duk wannan jaraba da Arif ke yi AA motar sa ya shige ya danna horn aka buɗe masa ya shige bayan ya masa dariyar ƙeta da cewa idan yana da zuciya kar ya kira gobe, da wannan suka rabu yana ɗan jin sakayau a ran shi ba kamar kafin su haɗu da Arif ɗin ba.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
29/06/2024, 15:19 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*82*



A gajiye yake tilis, ga damuwar da ya bari a can ƙasan zuciyarsa na yanayin da mahaifinsa ke iya shiga idan komai ya idasa buɗewa, tabbas a yau ya yi babban ƙoƙari da ya ga abubuwan nan ya kuma ji wa'inda ya ji sannan ya jure ya daure bai sumar masa ba, yana roƙon Allah a cikin zuciyar sa ko me zai gani ya sa ya iya jurewa, ƙwarai ya san irin soyayyar da mahaifinsa ke yiwa ƴan uwansa, shi yasa duk ire-iren abubuwan da ya gani ya yi iya yinsa ya daidaita abinda yake iya daidaitawa, sauran kuwa ya ringa faɗawa Allah ya bashi hanyar da Aba zai ji cikin sauƙi ya kuma bashi ikon jurewa, dan ma ya haɗu da Arif ya saka shi dariya da bai san ya ya zai shigo gidan nan a yau ba.

Tun daga bakin ƙofar falon da ya ga hasken fitila ya ɗan dakata yana tunanin haka ne fa, yanzu idan ya shigo yana iya tardo mace a falo na jiransa, kamar yadda suka rayu suke ganin Anna na kiyaye lokutan shigowar Aba tana tarbarsa da fara'a tana masa sannu da komai, idan har ya dace shima kamar yadda Anna ke faɗa lokuta da dama in ya ce yana so ya samu macen da zata kula da shi, to tabbas yana iya samun haka?
_'Anya kuwa zan samu haka daga wajenta? Anya zata iya bani kulawar nan?'_ Ya tambayi kansa a lokacin da ya yi tunanin to ai da wahala shi ya samu haka ɗin, sai dai ya jure ya kama ya shiga yana yin sallama saman leɓensa haɗi da wara ƙofofin hancinsa yana shaƙar daddaɗan ƙamshin turaran wutar da aka saka a lungu huɗu na falon suna tashi a hankali suna gama ɗakin da sansanyan ƙamshi.

Ajiyar zuciya ce ta ƙwace masa wacce ta nemi sauka da damuwar dake cikin zuciyarsa, Allah yana gani mutum ne shi mai tsafta da son ƙamshi, yana girmama ƙamshi a duniya wasu lokutan yana son zuwa ya zauna a falon Aba ya jima yana jin ƙamshin turaran wutar da Anna ke sakawa lokaci zuwa lokaci in dai Aba na gidan, domin shi yana samun tsaftar muhalli sosai, sai dai bashi da lokacin saka turaran wuta a wancen gidan, shi yasa wani lokacin sai ya ringa jin dakin na warin ajiya, wani lokacin har abinci ke yin wari sai an fitar an gyara haka haka dai na damunsa gaskiya.

AC ba a kunne ba, amma ɗakin da ɗan sanyi madaidaici da kuma ƙanshin turaran wutar nan, sai wajen ke fitar da wani sansanyan yanayi mai ni'imar gaske, idanuwansa ya kai can wajen table, ya hangi an jera wasu mayun kwanoni masu girma da kyan gaske.

Murmushi ne ya suɓuce masa a lokacin da ya shigo da takalmansa daf da cafet ɗin ya shiga ƙoƙarin cire su daga tsayan da yake, ɗakinta ta buɗe ta fito a karo na uku dan ta ga in har mai gidan ya dawo? Domin a yau bayan su Manal sun zo suka kirayo Maryam karatun ta nutsu babu irin wanda basu sauke mata ba, uwa uba aunty Intisar, faɗi take tana ƙarawa ta kula ta yi ƙoƙarin saka shaƙuwa a tsakaninsu ko me? Wai kar ta manta bayan Nabihat akwai ƴan duniya kurayen gari, ya zamo duk tsiya in dai ya fita tana zuciyarsa duk abinda zai gano zai yi mararin dawowa ya tardo ta gidansa ne.

Wasu abubuwan ma ita ba zata iya tunawa ba dan sun girmi ƙwaƙwalwar ta da auntyn ke so sai ta yi. Daga ita har shi turus suka yi suna kallon juna kafin ta sadda kanta tana jin ina ma ace an bar mata ko da ɗaya ce a cikin tagwayen Anna? Shikenan yanzu daga ita sai wannan rigimamen zasu zauna a wannan gansamemen gidan? Jiki a sanyaye ta nufo shi tana ƙoƙarin ɗago kanta dan ta aiwatar da ɗaya daga cikin tarin huɗubar uwar ɗakin ta, wato marabtar sa fuska ɗauke da ni'imar murmushi da yanayi da farin cikin ganin mutum.

A nutse ta miƙa hannayenta dan amsar kayan dake hannunsa a hankali ta furta" Barka da shigowa Aban Safwan."

Innalilahi, kai jama'a, sai kawai ya ji wani cika na ƙara cika shi, haka kuma idan kowa zai kira Safwan Aswan da sunan ɗan sa baya jin amon na ratsa zuciyarsa tashi guda ya shige shi ɗin nan kamar in ita ce ta faɗa, a ɗazu bai yi niyyar saukowa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login