Showing 96001 words to 99000 words out of 397328 words

Chapter 33 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70118

ga inda zai je, yaro ma da ya yi adopten yanzu haka a ƙarƙashin kulawar mu yake, so lamarin Aswan ya fara bani tsoro."

Da kulawa Chef yace" Kar ya baka tsoro Elhaj, ka dinga yi masa addu'a a duk inda yake ya zama mai yin nasara akan abinda ya sa gaban shi, AA ba yaro bane yanzu, kar ka manta da ya yi aure da wuri da zuwa yanzu kun saba da jin shirun shi, dan kwaramniyar iyali ma za ga ɓoye muku fitilar gidan ku."

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace" Hakane Chef, sai dai idan Aswan ya yi aure, zai ƙara nutsuwa ya daina yin abu irin haka, yanzu da ace yana da mata, da bamu tambaye ta ina yake ba? Kuma kana ganin za ta rasa sani ne? Sannan zai je ya kwana wani wuri ba gidan sa tare da matar sa ba?"

Sai kuma ya furzo iska daga bakin shi yace" Ina so ya yi aure Chef, shi kaɗai nake son ganin matar sa, ina so na ga zaman Aswan da matar sa ko dan na kasance mai lallashin ta a sanda ya mata halin sa na gaggawa, zan so na nasihanci matar sa da haƙurin zama da shi, sannan da ƙauracewa gayyato hushin sa da zai iya saka shi ɗaukar ƴar mutane ya buga ga ƙasa ba tare da ya yi la'akari da komai ba, daga bisani na zama uba gare ta dake faranta mata, dan ita ma ta ji ƙarfin guiwar zama da shi a duk yadda yake... Sai dai har yanzu bai fara tsara wannan jadawalin ba a rayuwar sa, ban sani ba ko sai na mutu haka zai faru?"

Da rarrashi Chef ya shiga tausar sa har yana faɗin" Idan ya dawo ka zaunar da shi ka ji me ye matsalar sa da aure? Ta nan za ka fahimci yana so ya yi auren shi ma ko a'a, idan ka gane kawai ba ya ra'ayin auren ne saboda wata aƙida da ta yi kama da ta yahudawa, to zaka iya yin fatali da hujjar sa sannan ka nema masa mata a gida ka ɗaura masa aure, idan kuma ya na so kawai lokaci ne bai yi ba, to ku barshi ya nutsu dan gaggawar ba ta da anfani."

Cike da gamsuwa Aba yace" Hakane Chef, kuma in sha Allah zan yi yadda ka faɗa min, na gode sosai."

Da haka suka rabu a wayar kowa da abinda yake tunani musamman ma Chef da ya shiga tunanin ta yadda zai yi magana da AA da gaggawa dan ya zama a ankare, dan ƙarara alamu suka nuna wasu sun gano shirinsu na gidan yarin nan, kasantuwar haka kuma zai jawo a hana shi ganin Sidi Kofa, idan haka ta faru kuma an samu gagarumar matsala, dan daga ƙarshe duniya za ta san Aswan Aliyu Anza na babban prison bisa tuhumar shi da ta'addanci, sannan mahaifin shi ma ba zai ƙyale shi ba idan ya ji da sa hannun sa AA yake wannan aikin.



*PRISON*


Ba wani saƙo ko inkiya da ya ƙara shigo masa har yanzu, hakan ya nuna masa da gaske an toshe masa duk wata hanya da zai gana da kawu Kofa, hankalin shi ya tashi, dan baya so hankalin Aba ya karkato ga neman shi bare har a zo ya gano inda yake, sannan kuma ba ya so ya nuna sarewa, yana so dole ya ga kawu Kofa dan ya nunawa wanda ba su so ya gan shi shima a shirye ya zo.

Amma sai abubuwa ke ta kwaɓewa suna rincaɓe masa, ba wata hanya ta ganawa da Kofa ɗin face wata ƴar ƙaramar damar da ita kan ta ba ya jin hanya ce mai ɓillewa. Haka ya ƙarasa wayar gari ya shiga sahun sauran mutanen dan wankin kayan su a can farfajiya, kuma hakan ma zagaye suke da masu tsaro da kamarori suma suna nasu aikin, har suka gama kowa ya koma ɗakin shi yana dube dube ne dan san ganin wata kafa komai ƙanƙantar ta.

Da yamma kuma duka aka fito da su aka saka su wankin banɗakunan jami'ai da sharar duka farfajiyar gidan yarin, shima dai ƙarƙashin kulawar masu saka musu ido wanda ko numfashi ka yi da ƙarfin za'a kalle ka, kuma abun takaici a gidan yarin shine baka cika ganin mutum biyu ko uku ɗinke wuri ɗaya ba, kowa dai harkar sa yake yi yana so ya nuna shi ƙwallon shege ne ya ishi kan shi, amma kuma akwai waɗanda kana kallon su za ka ga basu da matsalar rayuwa, ma fi aksari sune za ka ga su biyu haka suna hira, wanda suma idan ba tun waje dama harkar su ɗaya bace, to ba masu laifi bane sai dai ace marasa gata ne aka ɗora musu laifin da ya fi ƙarfin su.

Da takaicin zasu koma ɗakunan su ya sake yin tsaye ya zubawa babban ɓangaren idanu yana tunanin shin su ba sa irin wannan fitowar ne wai? Ko da su sha iska ne ma haka ko wani abu? Ɗan siririn tsaki ya saki ya juya yana goge gumin da ya baibaye masa dogon karan hancin sa, kamar daga sama ya ji muryar raɗa daf da shi an ce "Kana mamakin su ko?"

Da sauri ya juyo ya kalli mutumin shima da irin kayan shi na prisonner, dariya mutumin ya yi irin bai da damuwa ɗin nan yace "Shekara uku anan gidan, ƙwaya aka kamani da ita da ta wuce misali, amma nake faɗa maka har yanzu da na ɗauki wannan shekarun ban ga alamar *mahaifina* ba bare na sanar da ƴan uwana cewa Abbanmu yana raye ko yana mace ba."

Da mamaki AA ya zuba masa idanu ya yi tsaye yace" Idan na fahimce ka daidai, ka shigo gidan nan ne dan kawai ka tabbatar mahaifin ku yana raye ko ya mutu ne?"

Jinjina masa kai ya ɗan fara takawa, hakan ya sa AA jerawa kafaɗa da kafaɗa da shi suna tafe yace" Ɗakin ka ne kusa da nawa, ban san manufar ka ta shigowa nan ba, amma dai nasan ba abinda ka aikata mai girman da ka cancanci wannan prison ɗin, sai dai ko ka zo duba wani ne ko yin binciken sirri, dan akan idanuna jiya aka fitar da kai zuwa asibitin manya."

Haɗe girar sama da ta ƙasa AA ya yi yace" Wai su babu lokacin da suke fitowa waje ne? Sannan ko sau ɗaya haka bayan wani lokaci ba'a haɗe duka ɓangarorin?"

Murmushi matashin mutumin ya yi yace" Ai duk kowane dare suna fitowa shan iska su yi hira kai har ma da wasanni, sai dai ba'a taɓa fito da su sai bayan mu an shigar damu ciki, kuma su kan su a tsakankanin su idan aka fito da su zaka ga duk an rarraba su nesa da juna, saboda gagarumin tsaro."

Kallon shi AA ya yi da son samun tabbaci yace" Kenan kana nufin ko yau ma za su fito?"

Da tabbaci shima yace masa" In sha Allah, daga ƙarfe 09:00 har zuwa 11:00 na dare suna nan."

Wani shaƙiyin murmushi AA ya yi ya jinjina kai, sarai mutumin nan ya gani dan haka yace" Ba dai wani abun kake tunanin aikatawa ba mai cike da ganganci?"

Da murmushi a fuskar AA yace" Ba zamu san ganganci bane har sai mun gwada."

Ƴar dariya mutumin ya yi ya miƙawa AA hannu sa'ilin da suke shigewa ɓangaren nasu ana biye da su kuma yace" Sunana *Arif Sani Galadima*."

Kallon shi AA y yi sosai a ranshi ya ayyana _" Sani Galadima? Ɗan sa ne kenan?"_

Sai kuma kawai ya miƙa mishi hannu shima yace" Ka kirani da Chairman kawai, na maka alƙawarin sanar da kai ko ni waye ranar da zan bar nan."

Wani irin tattausan murmushi Arif ya yi ba tare da ya saki hannun AA ba yace" AA, ca veut dire que Aswan Aliyu, AA Anza, zazzafan Canal ɗinmu na soja."

A ɗan firgice AA ya kalle shi dan gaskiya ya razana shi har gaban shi ya faɗi, dama ai shi tashin hankalin shi shine kar wani ya san wanene shi, hakan babban tazgaro ne a gare shi da ma aikin shi, sai kuma ya basar ya saki wani irin munafikin murmushi yace "Ya aka yi ka sanni?"

Murmushi ya yi yace "Tabbas fuskar ka ba sananniya bace, amma ga ire-irenmu da suke harkoki da dama, mu kan yi ƙoƙarin sanin ku saboda coinsidence."

Ƙwarai Arif ya birge shi, dan haka ma ya yi murmushi suka saki hannun juna yace "Mahaifin ka na sani sosai, amma ban san yana da ɗan takimar yaro irin ka ba."

Dariya duk sukayi suna kawowa ɗakunan su suka rabu suna dariya, a ƙalla dai kowanen su ya samu yin murmushi musamman ma AA da tunda ya zo ba wani abu da ya bashi dariya idan ba takaici ba.

Duk da abinda yake son aikatawa ya gama ɗaura niyya kuma ya shirya shi, amma bai fara haramar yi ba saboda yana so ya tafi da komai a hankali duk da yana son yin gaggawa dan ya bar nan, amma tsakiyar dare yana tsaka da sallar shi kamar yadda ya saba ya duƙa sujada ya ji ƙarar kamar an turo abu haka ya biyo tiles ɗin wurin suuuuuuu.

Wani ikon Allah duk da sunan nakiya ne ya fara zuwa masa a zuciya a lokacin, amma kuma sallan da yake yi sai ubangiji ya saka masa wata irin nutsuwa bai yi gaggawar ɗagowa ba har saida ya yi addu'o'in da ya saba yi a sujada, yana ɗagowa ne ya sauke idanun shi akan wata ƙaramar waya ƙirar Samsung ashcolor... Sallama ya yi bayan gama sallar shi.

Ƙofar ya kalla amma babu alamar wanda ya turo, ɗaukar wayar ya yi yana ɗan jujjuya ta, sai kawai kira ya shigo da ɓoyayyar lamba, a nutse ya miƙe ya nufi ban ɗaki sannan ya kunna ruwa suna ƙara kafin ya ɗaga kira ya kara a kunne, muryar Chef ya ji ya kira sunan shi, dan haka ya saki jikin shi suka gaisa da ya kake ya amsa da lafiyar sa ƙalau, nan ne ya sanar da shi labari fa ya je wa Aban shi cewa an gan shi a prison ɗin nan, amma ya tabbatar masa da kawai kama ce kamar yadda aka faɗa masa wai ko me kama da shi ne, dan haka idan har aikin nan ba zai yiwu ba su san yadda zasuyi a fito da shi kafin komai ya kwaɓe musu, ƙwarai hankalin shi ya tashi dan ya san halin Aba da saka abu a rai musamman idan ya shafi ƴaƴansa, dan haka ya roƙi alfarmar kwana biyu rak in sha Allah zai gama komai, idan kuma bai gama ba a kwana biyun dai su san yadda zai yi ya fita.

Har Chef zai kashe waya AA yace "Amma ta ina labarin ya fara fita? Wa ya sanar da Abana ina nan?"

Idan ya faɗa masa kawunsa Hamat ne ba lallai ya yarda kai tsaye ba, saboda ya san shaƙuwar dake tsakanin su, sai kawai yace masa "Ni ban ma tambaye sa ba saboda na kaɗu sosai, ka san fa halin shi da saka abu a rai?"

"Hakane, Aba dan Allah ka ci gaba da kulawa da Aba, sannan su kula min da my boy Safwan and my little Angel's."

Amsa mishi ya yi da zai yi haka kafin su yi sallama, dawowa ya yi ya zauna bakin gado yana tabbatarwa kan shi dole gobe ya gabatar da aikin nan sai dai komai zai faru ya faru, yana wannan tunanin wani jami'i ya wuce yana satar kallon shi da hannu ya masa alamar ya jefo masa wayar tare da wucewa dan shawagi ne suke, AA ma aje wayar ya yi ƙasa sannan ya turo ta zo bakin ƙofa, yana dawowa daga ɗaya kusurwar ya ga wayar da sauri ya duƙa ya ɗauka sannan ya ci gaba da sintirin sa.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*26*



Cikin wata kyakyawar roba ta saka ice cream guda biyu da su tuffa da inibi da ayaba sannan ta saka chocolat guda ɗaya babba har da su cup cake vanilla, tana rufe robar mahaifiyar ta ma ta zo wajen fridge ɗin za ta ɗauki Yaghourt, da wani irin kallo na sheƙeƙe ta bita ta nuna robar cike da izza tace "Ke kuma wannan menene? Ina ce a makarantar kuke cin abinci?"

Kallon ta tayi da fara'ar ta tace "Ba nawa bane wannan Mom, na ji su Nawal sun ce zasu biya ta asibiti ne ganin Safwan kafin su wuce islamiyya, shine zan tafi masa da wannan."

Ta ƙarashe maganar tana ɗaukar robar ta riƙe gam a hannayen ta, har za ta juya kawai Goggo Tidin ta fizgo hannun ta ta juyo da ita ta ƙarfi, hakan ya haddasa faɗuwar robar kayan ciki suka zube, ba ta damu da abinda ya faru ba ta kalle ta a haukace tace" Mahaukaciyar ina ce ke? Shi yaron ƙanen uwar ki ne ko na uban ki? Abrar ashe baki da hankali kema kamar sauran mutanen gidan nan? To bari kiji yarinya, idan haukan da zaki dinga yi min kenan wallahi zan tattara ki zuwa gidan dangin uban ki, kiga acan idan za ki samu jin daɗin da kike samu anan, yau ga haukan banza, yaron da baku san asalin sa ba, wani matsiyaci da shi an gudu an barshi shine ku zaku ɗaukowa kan ku? Aljani ne, maye ne duk bai dame ku dan baku da lissafi."

Wawan tsaki ta saki ta juya a fusace ta buɗa fridge ta ɗauki madarar sannan ta rufe, saida ta sake kallon Abrar dake kwasar kayan ta tace" Me kike yi haka? Ba zaki wuce ki tafi inda za ki je ba?"

Ɗaga kai Abrar tayi ta kalle ta idanun ta taf da ruwa tace" Momma, ni Safwan ba wai ina masa makauniyar ƙauna bane, a'a kawai ina tausaya masa ne saboda halin da ya tsinci kan sa, idan mu da muke da hali bamu taimaka ma wanda basu da hali ba, to su waye *matsiyata* a cikin mu da su?"

Wata irin kumbura Goggo Tidin ta dinga yi kamar za ta fashe tace" Dan Aswan kike haka? Kina hakane dan Aswan ya dube ki?"

Wani irin murmushi Abrar ta yi tace" Ban san takamaimai abinda nake ji akan Yaya AA ba, amma kuma ko sau ɗaya a cikin sakan ɗaya ban yi tunanin yi wa Safwan abu ba dan Yaya AA ya dubi hakan ba."

Girgiza kai Goggo Tidin ta yi tace" Dole ki bar gidan nan Abrar, dan ba zan bari haka ya miki nisa ba, dan da numfashina ba zan zuba ido ina kallo kina wahala akan wanda bai san mutumcin kowa ba har da uwar ki ma."

A fusace ta juya ta bar madafar, Abrar kuma ta ƙarasa tattara kayan nan sannan ta fice. *Anna* na tsaye ta ji komai da ya faru, dan ita ta falon ta ta shigo madafar, lallai ta yarda Tidin bata ƙaunar ta kuma bata ƙaunar ahalinta, to amma me ta mata? Me ta aikata mata haka da ba zata so Aswan ya auri Abrar ba? Shin wannan ba farin ciki da murna marar misaltuwa ya kamata su yi ba, sannan su shirya ma yaran su biki na ban mamaki.

Abu ɗaya shine ta ji Abrar ta shiga ran ta sosai kula ta birge ta, dan a maganganun yarinyar wacce su Manal ma sun girme ta hankali ne tattare da su da kuma nutsuwa, sannan ga dukkan alama AA kawai take so ba dan yana ɗan Aliyu Anza ba, ba dan yana ɗan uwan ta ba, ba kula dan yana kyakyawa ko wani abu kama da haka ba, soyayyar ta da alama dan Allah ne, tana fata Allahn da ta so Aswan dan shi ya so ta sannan idan akwai alkairi a tarayyar su, to AA ma hankalin shi ya karkata kan yarinyar ita kam bata da matsala da haka.



*YUSRAH*


Zama da mutanen dake baka kulawa ya kan saka duk wasu mugwayen tunani barin ƙwaƙwalwar ka, ka fi mayar da hankali kan ibadarka cikin nutsuwa, sannan lafiyar jikinka takan ninku, a zaman Yusrah tare da wannan ahali na Elhaji Jafar bata da bakin godiya sai dai ta yi addu'a, kula take samu ta musamman daga Hajia da autarta uwa uba shi wanda ya kaɗeta safiya bata yi dare ya yi bai zo gidan da tsaraba ta musamman ba sannan ya sakata a gaba da fira da son lalle sai ta saki jikinta da shi.

Sai dai a ɓangaren Yusrah sam ta kasa sakin jikin nata da shi, takan bashi girma da gaisar da shi da sakin fuskar da take warta da ƙarfin gaske daga yanayinta, amma idan ya zauna yace zai ja magana fiye da yadda ya dace sai ta sadda kai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login