Showing 129001 words to 132000 words out of 397328 words
ma juna, irin wannan taren kuma bata da rana, tabbas bata da rana kuma ita dai bata fatan zama da irin wannan mutanen da ba zasu ƙare ka da komai ba.
A waje Maryam ta same ta kafin suka tattake har inda suka samu adaidaita sahu suka shiga, sun ɗan yi tafiya mai tsayi kafin suka isa gidan Hajia Zeinab, sai dai tun a ƙofar mai gadi ya sanar da su Hajia ta fita tun da safe tare da Fatila da kuma Alhaji Jafar, bai san ina suka je ba amma dai ya tabbata gaskiya muhimmin abu suka je yi, dan jiya sun kwana da zulumin neman wata yarinya da suka taimaka Yusrah, hankalin aunty Fureira sai ya tashi jin kuma wai an rasa Yusrah anan, da wannan zulumin ta tambaye shi "Dan Allah baka san zuwa yaushe zasu dawo ba kuma?"
Girgiza kai ya yi yace "Gaskiya ban sani ba Hajia, sai dai akwai yiwuar su jima tunda Alhaji Jafar da kanshi yake tuƙa su."
Shiru ta yi tana tunanin abun yi, kafin daga bisani ta dube shi tace "To ba damuwa zamu tafi, amma anjima ko da zuwa bayan sallah magriba ne zan dawo, dan Allah ka min alfarma idan na zo zan gan su, nima ita yarinyar nake nema, ƴata ce."
Cike da rashin damuwa yace "In sha Allah ba damuwa Hajia, idan suka zo ma zan sanar da su."
Da gamsuwa ta mishi godiya sannan suka kama hanya ita da Maryam, a hanya ne ma ta dubi Maryam ɗin tace "Maryam, anan kusa baki san inda ake gyaran waya ba? Wajen cajin wayata ne ya samu matsala kwana biyu, dan danan sai waya ta ɗauke min wani lokacin ma bana sani sai ayi ta kira ba'a samu na."
Da sauri kuwa Maryam tace "Haba, shiyasa ko jiya da naje wallahi Yusrah ta yi ta kiran wayar ku amma ba'a samu, kuma ta ce min tun da ta karɓo lambar wajen Goggo Hinda take kira."
Da kulawa aunty tace "Allah sarki, nasan tana san sanar da ni halin da take ciki ne."
Maryam ce tace "A'a aunty, tana so ne ta tambaye ku ko Safwan na wajen ku? Da niyyar ta shine sai ta je can Funtuwa kawai."
Girgiza kai aunty Fureira tayi tace "Safwan ba ya wajena, ban ma zo ba bare na gan shi, kuma tabbas da na zo na samu Safwan a wannan halin, to ba abinda zai hana na ɗauke shi na tafiyata."
Murmushi Maryam ta yi tana jinjina lallai Yusrah ta san aunty Fureira shiyasa kawai ta fi tunanin Safwan na wajen ta, a hankali ta bata amsa da" Wallahi aunty anan dai ban san inda ake gyara ba."
Da gamsuwa tace" Shikenan to, muje yanzu a saukeni bakik tasha wajen Aminu sai ya rakani gidan shi dan ba zan iya kai kaina ba."
Maryam ce tace" E to daga nan ma ana iya gyara muku wayar ai."
Da wannan suka shiga adaidaita sahu kuma aka fara aje aunty Fureira kafin aka wuce da Maryam gida duk tana jin kunya na lulluɓe ta na rashin kyautawa da suka ma Yusrah, kuma ita har ga Allah abun ne bai zo mata ba kawai. Haka ta koma gida ta samu Maman ta har da kuka ta yi dan sai lokacin ita ma ta fahimci kuskuren su ne duka ba na Yusrah kawai ba, ƙwarai ta yarda ba ta kyauta ba, kuma idan zama zatayi da Safwan bata da matsalar mai kula mata da gida ko abinci, kawai dai ita ma bata yi tunanin tafiya bane saboda tana ganin kamar matsalar yarinyar ce ita kaɗai, sannan a ƴan uwa ma ba'a samu mai tsaya mata ba bare ita?
*AA ANZA*
Zuwan sa na biyu kenan asibitin yana tambayar Mani dreba, amma da abokin aikin na Mani ke tabbatar masa bai dawo ba har yanzu, sai ya dube shi da tsananin mamaki yace "To wai ba tare da oga ya ce sun tafi ba?"
Mutumin ya amsa mishi da "E, tare da oga suka tafi."
Dan son ya tabbatar ya sake cewa "Ai idan kuka ce oga kuna nufin Dr. Hamat ko?"
"Hakane yallaɓai." Ya bashi amsa shi ma, da mamaki yace "To amma ya akayi ogan ya dawo shi bai dawo ba? Bayan kuma tare suka tafi, kana ganin lafiya kuwa?"
Saida mutumin ya jujjuya ya ga ba mai kallon su sannan yace "Ban sani ba wallahi yallaɓai, kuma ban da hurumin da zan tambayi oga hakan."
Iska AA ya feso daga bakin shi yace "Gashi lambar wayar sa ɗaya ce gareni da nake ta kira bana samu."
Shi ma mutumin cewa ya yi "Wannan lambar dai ita ce, dan nima na kira ban same shi ba."
Ɗan dantse leɓen shi ya yi sai kuma yace "Ko kasan garin su?"
Girgiza kai ya yi da saurin bala'i yace "A'a, a'a yallaɓai, sai dai ko idan mai gadi ya sani."
Yadda ya bashi amsar ya tabbatar ma da AA kawai ba dai zai faɗa masa bane, dake kuma cikin mutane suke ba zai so ya takura shi ba, sai kawai ya jinjina kai yace "Na gode."
Yana faɗan haka ya yi gaba ya bar shi, wajen mai gadi ya ƙarasa, dake sun gaisa ɗazu yanzu sai kawai yace masa "Mani dreba nake son gani, dan Allah ka san garin su?"
Dake bai da matsala ko tunanin ta sai kawai yace "Sosai ma yallaɓai, ai Mani dreba mutumin kaɗata ne."
Yana jin haka kawai ya yi murmushi yace "Na gode." Gaba ya yi zuwa cikin asibitin madadin ya nufi motar sa, yana shiga a wajen layin marasa lafiya ya ci karo da ustaz ya fito daga ofishin shi ya gama duba wani yaro, hannu ya miƙa masa suka gaisa kafin AA yace masa "Amm...dan Allah wata nake nema anan, wata fara haka ƴar doguwa, da alama dai sabuwar fara aiki ce a nan."
Kallonshi ustaz ya yi sosai yace "E to, sababin ɗauka a nan suna dayawa, dan nima sabuwar ɗauka ne anan, sannan kuma akwai wacce stage ne take yi."
Da matsanancin mamaki AA yace "Stage? Anan ɗin?"
Da girmamawa ustaz yace "E yallaɓai, to na fi tunanin ma ita ce ka ke nema dan kamanin ta kenan."
Sai kuma ya kalle shi sosai yace "Amma ita ya sunan ta?"
Ɗan shiru AA ya yi dan shi kam ba ma zai ce maka ga sunan ta ba wallahi, kawai dai *mahaukaciya* ya san ta, duk da kuwa yana tuna ranar da aka kama su tana kururuwar nan tana faɗin ta shiga uku ita... *Yasira* ne ko *Surayya*? Kai kawai bai iya tunawa, yanzu ma *haƙuri* ya zo ya bata akan abinda ya mata wanda ya san bata ji daɗi ba, yana so ya ce ta yafe masa, kawai aikin sa ne ya ga zai ƙara bada citta idan ya haɗa da ita, sai kuma... *maganar asibiti* da yake so ya ji daga bakin ta, maganar zalincin nan da ta yi akan asibitin su yana so ya san gaskiyar me take nufi, dan haka ma ya zo ɗin.
Wannan shirun da ustaz ya ji daga gare shi ya sa yace "Ina ga dai Yusrah ce ka ke nema yallaɓai? Yusrah kuma ta bar aiki anan asibiti yau sati kusan biyu kenan ko ma sama da haka, sai dai ko in zaka kirata a waya sai ka ji."
Daga haka ustaz ya yi shirin barin wurin, AA kuma da ya tabbatar e ita ce tunda ai haɗuwar su ta ƙarshe a asibiti tana shirin barin asibitin ne, cikin nutsuwa yace masa" Kana da lambar ta? Ko adreshi haka?"
Juyowa ustaz ya yi ya sake kallon AA daga ƙasa har sama, shiru ya ɗan yi kwarjinin AA ya hana sa ce masa ba zai iya wannan wautar ba, kuma ya kasa bashi saboda duniya yanzu abar tsoro ce, ko da yake... Ai suna ta kiran ta basa samu, ko asibiti da ta zauna ba ya tunanin da waya a jikin ta saboda iftila'in da ya faɗa musu, sai kawai ya ɗan muskuta yace "Bata da adreshi yanzu, sai dai lambar?"
Sai kawai ya ciro wayar sa ya nemo lambar ya shiga faɗa masa lambobin, AA kuma yana dai ɗauka ne amma yana tambayar kanshi _"Kamar ya bata da adreshi?"_
Ko da ya gama ɗaukar lambobin sai kawai sukayi sallama kowa ya kama gaban shi, ba dan Safwan ba daga nan garin su Mani dreba ya so nufa, amma sai ya wuce wasu sabgogin kafin dare ya yi ya tafi asibiti su sha hira da ɗan sa har dare ya tsala sannan ya bar nan.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*35*
Tunda sasafe Intisar ke yaba lamarin Yusrah, dama mace bata baƙunta sai dai idan maƙiwaciya ce, tunda Yusrah ta yi sallah take tsaye kan ƙafafuwanta tare da masu aiki su biyu suna aikin kayan kari da gyaran gidan, duk kuwa da Intisar ta nuna mata ta je ta huta ta nuna ai bata gaji ba zata iya a dole ta barta ta zauna a falo tana faman yi mata sannu ita kuma tana yin murmushi da mamakin ina ma aikin yake aikin da bai kai ya kawo ba gashi an samu hannayen mutum uku a kansa? Nan da nan suka gama ta nufi ɗakin nata dan ta yi wanka domin da asuba watsawa jikinta ruwa ne kawai ta yi dan ta ji sanyi sanyi.
Tana fitowa daga wanka ta ga abaya baƙa ajiye saman gadon nata da turare da ɗan kwalin abayar mai faɗi haka sai pant sabo fil a cikin ledarsa, kayan ta ɗauka ta saka har da pant ɗin ta fesa turaran kenan Intisar ta shigo, saida suka kara gaisawa sosai Intisar na yi mata murmushi ta gyara mata ɗan kwalin a kanta ta ce" Ma sha Allah, mu je mun yi baƙi."
Ɗan turus ta yi tana kallon Intisar a tausashe ta ce" Aunty Intisar baƙi?"
Intisar ta gyaɗa mata kai tana murmushi ta ce" Su Hajia ne, mu je."
Jiki da nauyi ainun ta bi bayan Intisar tana duba agogon dake jikin bango na corridor ɗin ɗakin, bata yi mamakin jin Hajia ta zo ƙarfe goma na safe ba, domin Hajia mutum ce mai sauko ma sha Allah, sai dai zuciyarta cike take da tsoron abinda zai iya faruwa a falon, domin ko jiya tsoron nan da ƙyar ya barta ta rintsa dan ma ta kwashi gajiya ne ya sa ta yi barcin, da ace bata tare da gajiya ta tabbata da zama zata yi ta yi ta tunani.
Suna shigowa Intisar ta yi murmushi ta ƙarasa daf da Ummi ta zauna tana fadin" Shigo mana Yusrah."
Yusrah ta shigo jiki ba ƙarfi ta ƙaraso gaban Hajia idanuwanta cike da ƙwallah ta duƙa har ƙasa kanta a ƙasa ta ce" Hajia dan Allah ki yi haƙuri."
Hajia da idanuwanta suka cika da ƙwalar itama ta kama kunnenta ta ce" Wani tunani ne ya shiga ƙwaƙwalwar ki haka? Fitowar taki ya kusan buga min zuciyar ba wai zamanki tare da ni ba, an faɗa maki zata kuma dawowa ta yi in ƙyaleta ne? Baki san sauƙi kika zo min da shi ba wanda na jima ina nema? Baki san alkairi bace ke a tare da ni? Allah ya sa kece zaki zo min da sauƙin da nake ta addu'ar samu, ina ce a gida na yi maki faɗan mace ta killace kanta shine rufin asirinta, amma kika take maganata kika bi dare, yanzun da sun cimmaki wani abin ya samu a kan wanda kike ciki mu yi ya ya da rayuwarmu?"
A hankali Yusrah ta fashe da kuka kanta saman cinyar Hajia a hankali ta ce" Dan Allah ki yi haƙuri Hajia, dan Allah ki yafe min, ban yi haka dan na ɓata maki ba, tun lokacin da ta zo ta zazzagi Yaya na gane matsalarta nice in dai ba daina ganina ta yi ba ba zata taɓa iya baki lafiya ba na yanke wannan shawarar, Hajia kin san Allah, in dai ba daidai da ita ta samu ba sakin da Yaya ya yi mata ba zata taɓa bashi lafiya ba, gashi baki da lafiya Hajia, sai ta zo a gaban mu ta wulaƙanta mana ke, ko da kin jure kin daure kin shanye baki nuna mana ba ai gayanan yana aiki a zuciyarki, Hajia uwa ce ke a gareni zan nema maki sauƙi ko wani iri ne, shi yasa na ɗauki matakin nan ba dan na raina ko wani nufin ba, ki yi haƙuri Hajiya."
Ummu ta yi murmushi tana kallon Hajia ta ce" ki yi haƙuri Hajiya ƴarki ta yi laifi."
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Shikenan, daina kukan haka, daina kukan haka, yanzu sai ki wuce mu je ko?"
Da sauri Intisar ta kalli Yaya Mubarak, sai kuma ta kalli su Hajia, muryarta har tana rawa ta ce" Am, Hajiya, am, ku je? Hajia dan Allah ku bar min ita, ko karyawa bata yi ba ma ko bab.....au ko Yaya? Dan Allah ka saka baki, Hajia dan Allah ku bar min ita, ƙawata ce kuma ina da burin taimako mai girman gaske a gareta, ko Yusrah?"
Yusrah ta dubi Hajia, ta sadda kanta, kanta a jikin cinyar Hajiar dai bata iya cewa komai ba,
Hajia ta dubi Intisar da kyau tana ɗan murmushi ta ce" Har da kuka ƴata? To ya ya zan yi in bar maki ita ni kuwa? Ni ma ai ina so ko ƴata? "
Kamar da wasa sai ga Intisar ta duƙa gaban Hajia tana kallonta ta ce" Hajia na sani sarai kina so kema, kuma mu dukan mu ƴaƴanki ne, sannan ko da yaushe kike so ta je ta gaishe ki zata zo, haka kuma ko da yaushe kika buƙaci ta zo ta maki weekend za ta zo, amma Hajia yanzun ki bar min ita na ɗan lokaci, ina son sosai in bi tsari na lafiyarta, ina so in yi mana create ɗin abubuwan da zasu saka ta saku ta dawo normal, ban ce zan sa ta manta damuwarta gaba ɗaya ba, amma in sha Allah zan yi duk iya yina in ga ta manta manya manyan damuwarta, Hajia dan Allah ki min alfarmar nan?"
Hajia ta rasa ya ya zata yi, Fatila ta yi saurin turo baki tana kallon wannan Intisar ɗin, Ummu kuwa murmushi take yi, Yayansu kansa murmushin yake yi amma idanuwansa ba a kansu ba, haka Yaya Mubarak sai da ya bari ta dire magiyar ta ta a tausashe ya ce" Kin ga koma zauna wajenki."
Intisar ta kalle shi a marairaice sai kuma ta zauna daf da ƙafar Hajiar ita ma ta ɗora kanta, hakan ya sa Hajia yin dariyar da bata shirya ba kamar yadda sauran suka yi.
Kai yaya Mubarack ya girgiza a tausashe ya ce" Hajia ki yi haƙuri da rigimar wannan, yawwa dama nace ina so in tambaya, zaman da ta yi a wajen ki ko akwai wani nata da kika haɗu da shi?"
Hajia ta gyaɗa kai tana duban Yaya Mubarak, a tausashe ta ce" Ƙwarai, akwai Goggonta da muka je muka gaisar, sai dai ko da wasa ba zan so yarinyar nan ta koma wajen matar nan ba, ko da wasa."
Da mamaki Yaya Mubarak ya ce" Me yasa fa Hajia?"
Hajia ta fitar da hucin takaicin abinda ta kwasa a ranar wanda bata bari sun yi maganar da kowa ba tana dubansa ta ce" Ɗana, ka san akwai ƙiyayya irin wacce ke gyaruwa akwai kuma ƙiyayyar da bata da gyara, irin abinda a gani a ranar nan ya ɗaga min hankali fiye da tunaninka, dalilin abin nan tunda na dawo idan na kalli wannan yarinyar da ita ce ta rage min a gabana sai in kalli wannan da Allah ya kawota rayuwata ko da na second ɗaya ne sai in ji hankalina ya tashi da tunanin idan ta Allah ta kasance a kaina kai tsaye ya ya ƴan uwansu zasu kula da su? A ranar da muka je kasa barci na yi har garin Allah ya waye, na yi kuka na yi kuka fiye da tunaninka, na yiwa kaina tambayar shin mutane basa zuwa islamiyya ne? Ba sa sauraron wa'azi ne? Ko duk a wai suke tunanin maganganun tsayuwar gobe ƙiyama? To ƙiyama gaskiya ce, kuma kowa sai ya tsaya gaban Allah, irin yadda ake wasa da zumunci kowa sai ya yi bayani, wai shaƙiƙiyar yarinyar nan, da ta san me yarinyar nan ke ciki gaba da baya, ta ga gawar iyayen yarinyar nan kuma ta zama shedar ciwon ƙaninta da ɓatansa har take iya wulaƙanta yarinyar nan? A ranar da muka je yarinyar nan tana shiga ta yi tuntuɓe da tasar masa ta jata sai cikin kwanonin wanke wanke, ina ga matar tana siyar da abinci ne...kai dai..."
Nan ta kwashe komai ta faɗa, ɗaya bayan ɗaya wanda hakan ya saka kowa yin shiru na tashin hankali da mamaki kai har da kokonton in har ƴar uwar mahaifin na Yusrah ce da gaske? Domin