Showing 150001 words to 153000 words out of 397328 words

Chapter 51 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70045

asibitin gida ba? A ganina takardar ki da irin ƙwarewar aikin ki cen ya dace da ke, kin ga basa ɗaukan ƙannanu ma'aikata fa su?"

Yusrah ta yi tsuru, sai kuma ta sadda kai ta ƙasa cewa komai
" Yusrah?" Intisar ta ambaci sunan ta a karo na uku, bayan ta yi mata tambayar dalilin da yasa a lokacin da aka tambayeta tana son komawa asibitin su uncle hamat ta yi aiki a cen ta yi shirun nan ta afka a duniyar tunani tamkar ta fita a hayyacin ta, bayan kwana biyu kenan da aka gama yi mata duk wani gwaje gwajen da ya dace, bayan matsalar bayan nan da aka ɗora ta kan magani duk wani rauni na jikinta sama ne bai ratsa jikinta ta yadda zai yi mata mugun illa ba, bayan nan kuwa burbuɗin abin ginnin nan da ya zubo mata ne ya bar mata ciwon nan, gashi bata tsaya ta yi treatment yadda ya dace ba tana ta faman ƙanin ta baiwar Allah, kuma tunda ta fara shan magungunan nan da kanta tace a yanzu bata jin ciwon nan dake yawan motsa mata wanda ke sakata dafe ƙugu tamkar tsohuwa mai shekaru casa'in har sai ya saketa, takan ji kaɗan kaɗan amma ba kamar da ba, har ita da kanta ta nunawa Intisar a yanzu tana iya fara aikinta, in ma da wani abin duka kaf a yanzu yi take yi nata jiran komai, a kwana biyun nan balle fa ta ga sosai yanzu yawon neman Mani polisai ke yi bisa ƙarar da Mubarak ya shigar ya kuma saki kuɗi masu yawan gaske dan a nemo Mani ɗin sai ta ji sosai nutsuwa na ƙara ratsa ta har ta rage lokacin tunanin rayuwa ta zuba lokacin a yiwa iyayenta addu'a da ƴar uwarta.

A ɗan zabure ta kalli aunty Intisar, ta haɗiyi wani yawu mai wahalar gaske a wuyanta, zuciyarta cike da tunanin shin idan ta faɗa mata waye Hamat ba zata koreta su daina nemo mata Safwan ba kuwa? Tana tsoron ya zamo su kasa fahimtar ta, sai kawai ta yanke shawarar faɗin wani abin daban.

A sanyaye ta ce" Aunty Intisar abinda yasa duk idan na ji sunan asibitin ko na ga asibitin hankalina tashi yake yi sosai, sai idanuwana su ringa hasko min mutuwar Aba a cen..."

Ta yi shiru tana sadda idanuwanta dan son ta hanna kanta gano mutuwar, domin ƙwarai ta ga lokacin da ya ɗago da ƙarfi sai kuma ya koma a lokacin da aka sanar masa babu mamansu da Hannah, Intisar ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Shikenan, in sha Allah ba zaki je ba ma balle ki tuna, tashi ko je ki huta."

Miƙewa ta yi ta ƙara rage tsayinta sosai ta sake yin godiya sannan ta nufi ciki, Yaya Mubarak ya ce" Dama kin dai nace ne kan ta je cen, asibitin nan tana da girma sosai, ban san ko zata iya jin daɗin aikin cen ba, aiki ya musu yawa sosai, ba gashi ba Docter yace eh yana da buƙatar ta, sai ta je cen kawai ta yi aikinta balle kin ga asibitin sa shima akwai aiki, kuma akwai biya, sannan asibitin sa akwai tsaro da ake badawa sosai na harkar mu'amalar patient da kuma likitoci, gaskiya zata ji daɗin aiki da su sosai, believe me bab."

Intisar ta yi murmushi ta ce" Hakane bab, in sha Allah sai ta fara zuwa ɗin, Allah ya tabatar da alkairi ya sa ta fara a sa'a."

Daga nan suka rufe maganar, sai da safiya ta yi ranar kwana uku da yin maganar sannan ya je da kansa wajen abokinsa Docter Siddik suka sake zantawa, ya ga takardun Yusrah ɗin sosai, ya nuna masa ba laifi ga albashin da zai iya bata, amma kafin ta fara shiga wajen yara sai ta yi aikin consultation ɗin yara a gabansa ko da na sati ɗaya ne, in yaso sai ta je ciki ta ringa kula da mararsa lafiyar ta.

Sosai abin ya yiwa yaya Mubarak daɗi, ya yi godiya sosai ya miƙe ya fito zai tafi motar gidan su Anna ta zo ɗauke da su Abrar da tagwaye, dakatawa ya yi har suka sauko da kayan dubiya a hannayensu, dan haka ya ƙarasa da kula yana tambayarsu lafiya waye a nan ba lafiya?

Gaishe shi yan matan suke yi da girmamawa kafin Manal ta ce" Yaya Mubarak, yaron wajen Akhi a nan yake ai, amma gobe za'a bashi sallama in sha Allah."

Da ɗan mamaki Yaya Mubarak ya ce" Ayya, mu je in ga jikinsa nima, ranar da muka je gidan na tambayi babban Yayan jikin nasa ai yake ce min da sauƙi sosai, na zata ma an sallame shi yana gida ne fa."

Rankayawa suka yi gaba ɗayan su dakin, suna zuwa ya ga jikin Safwan ya masa Allah ya sawaƙa sannan ya tafi su kuwa suka yi zamansu kamar yadda suka saba kawo masa ziyara kullum.


Docter Siddik kuwa bayan tafiyar Yaya Mubarak cike da farin ciki ya sanar da AA in sha Allah an samu likitar da zata kula da Safwan a tafiyar nan, AA ɗin ma ya ji farin cikin hakan, har ya sanar masa idan ya gama wani aiki zai zo sai su yi maganar, dan yanzu yana da wani aiki ne da zarar ya gama zai shigo, da wannan suka yi sallama cike da farin cikin, cikin sauƙi Allah ya kawo likitar da ta dace da kula da Safwan, lallai yaron Allah na tare da shi.

_*SAJEERAH*_🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*40*



Yau tunda safe Bilal da ya farka yake da muradin ganin Yusrah, kwana huɗu kenan da ya san a gidan nan take rayuwa amma kuma kaɗaituwa da ita ya gagara, domin da ya gwada zai yi naci Yayansa ya dakatar da shi da nuna masa ba zai yiwu ba, bar Hajia na tsaki a lokacin domin a gabanta aka yi maganar tace in ma ba wani ɗorawa kai ba in an hana ka neman auren nata ka haƙura mana gari da yawa maye ai ba zai ci kansa ba, sai dai shi Yaya Mubarak da suka fito ya sake kwatanta masa ba yana ƙinsa da Yusrah bane, yana so a bata lokaci, a yanzu bata da wannan tunanin a ranta idan har ta kwana biyu zai fi in hankalinta ya dawo kan komai na rayuwa, a dole ya hakura, amma a yau yana so ya ganta ko da murmushin nan nata da ta taɓa yi masa a asibiti ne ta yi masa sau ɗaya ko da bata ce da shi komai ba.

Shiryawa ya yi cikin ƙananun kaya, ya yi kyau sosai, yana shirin fitowa kira ya same shi daga layin Goggo, da mamaki ya amsa kiran ya yi sallama sannan ya dakata yana sauraro.

Goggo ta ce" Bilal ne? Nice babar Yusrah, dama kira na yi dan in sanar maka an fa samu Yusrah ɗin an san inda take, sai dai gidan da nisa da ace ina da cenji nema sai in zo mu haɗu wajen danjar mai ruƙiya sai in kwatanta maka gidan ka je, dan ni da muka haɗu babu irin rashin kunyar da yarinyar nan bata min ba daga yi mata nasihar yawon nan bai dace ba ya dace ta kama ƙafarta, karshe dai yarinyar wajena wannan dai da ta gaisheka har kuka ta ringa yi tana bata haƙuri amma ta ƙi hakura da ƙyar na bata haƙuri ta hakura, ka ga ba zan so in koma inda ta zaɓi zaman ba gudun yaro kar ya zageka a gaban mutane, amma yarinyar nan sam bata kyauta min ba, kuma daga rasuwar iyaye ta zaɓi zama da masu kuɗi har ina cewa sai kace wacce ke jira?"

Jus ɗin dake hannunsa ya yi niyyar sha sai ya ji ya tsaye masa a harshe, tsabar kaɗuwa da mamakin matar suka taru suka yi masa yawa, da ace bai ji komai abinda ya faru ba yanzu da ta yiwa Yusrah wani sharrin ko? Subhanallah, mutane me suka ɗauki duniya ne? anya kuwa wannan ta haɗa jinin da Yusrah? Anya? Dan ya ga ƙarshen rashin imanin baiwar Allahn da irin ƙagenta sai kawai ya ce" Ayya, to shikenan yanzu yaya za'a yi kenan? Gashi ni kuma ina gidanmu ai da na bada na abin hawan."

Da gaggawa ta tare shi tana faɗin" Ai kana iya min Nita, ko ka min al'iza, tunda ga yara kusa sai su ɗauko kawai sai in shigo yanzu in taho."

Kai ya gyaɗa yana cije leɓe ya ce" Ba damuwa ki taho sai mu haɗe, in mun haɗe sai in ba mai adaidaitar ko in baki ki bashi."

Goggo ta ce" A yi haka ɗan nan?"

Bilal ya ce" Eh Goggo ya fi, mu haɗe ɗin a cen."

Daga nan ya kashe kiran yana girgiza kansa, a ransa ya ayyana _" Zaki je ki yi ta jira, yau ko kaɗan ne kema sai kin ɗan sha wahala saboda zagar min abar ƙauna da kika yi, in banda ma kin shafi jininta da sai na hauda maki hawan jini, aikin banza!_"

Daga nan ya nufi cikin gidan, sai dai da ya je ya samu mai aiki na ta aiki ta sanar masa sun je saloon, saboda Hajia ta ce gobe Hajia ƙarama zata fara fita aiki, a dole ya tafi shima ɓangaren Hajiarsa daga nan zai wuce wajen aiki cike da cin burin idan suka dawo sai ya biya kuɗin saloon ɗin nan yau.


__________________


Kusan rabin wuni suka yi a saloon, domin gashin Yusrah sai da ya sha gyara na mamaki, sannan aka yi mata su wankin ƙafa ne, da ɗan simple ƙunshi a hannayenta, sai hannun ya sake yin kyau ma sha Allah, haka ma Intisar ta sha ƙunshi sai da ya kama aka wanke masu suka fito Intisar ta ja su suka je wani boutique ta ringa yiwa Yusrah tsince tsincen kayan tafiya asibiti, kaya na gayu, takalma masu kyau da tsari, da yan baby hijab da agogo dai su Aple wach ɗin nan, ta kashe mata kuɗaɗe tamkar ba shekaran jiya ta yi mata siyaya ba, har sai da ta ce" Aunty Intisar, siyayyar nan ta yi yawa, kuɗin nan sun yi yawa sosai wallahi dan Allah ki rage."

Intisar ta yi murmushi bayan sun kama hanyar tafiya gidansu kamar yadda tace zata kaita ta gaishe da Anna yau da Abanta ta dubeta da kula ta ce" Yusrah, duk abinda kika ga na kashe maki kar ya wani ɗaga maki hankali, kin ga dai ni bana aikin gwamnati, amma ina kasuwanci sosai da sosai, bayan kasuwanci kin ga ƴaƴana da na haifa a US na haife su, duk ƙarshen shekara duk ɗaya ana bani million goma tasa, kuma babansu baya taɓa min ko sisi, sannan kin ga Aba yana bani kuɗin buƙata, dan ma Yayanmu ya ce min kar ya kuma ganin mun amshi albashin da ake mana ƴan gidanmu du ƙarshen wata tunda ba aikin da muke yi, da nace maki harda albashi gare ni nima kamar mai aikin gwamnati."

Yusrah ta ɗan zaro ido ta ce" Ma sha Allah, kai aunty Intisar babbar Hajia ce ke ashe, to kuma aunty Intisar dama ana yi maka albashi bayan baka aiki?"

Intisar dake ƙara jan Yusrah da fira dan ta ƙara warwarewa ta saku sosai da ita ta ce" Kin san yawanci waɗanda ke cikin gwamnatin nan haka ne, yanzu ne Yayanmu yace wai a dakatar, yace bai ga dalili ba, wai kuɗin talakawa ne a dakatar, ke dai gaba ɗaya gidanmu yanzu Goggonmu kaɗai ke amsa, mu duka yace kar a sake kuma ba ma zuwa amsa ina gama ya je ya dakatar da amsar ne."

Yusrah ta gyaɗa kai a ranta ta ayyana _" Ai kam gwara da ya hana tunda wannan ai kana ji ka san ba kyau, kuɗin da baka yi aikin komai ba aka baka ai ba ma zaka ci shi da daɗin rai ba, shi kam Yayan nan ya taimaka sosai dan kuwa ya raba danginsa da cin haramun"_

A bayyane kuwa ta ce" Allah ya sa hakan ya fi zama alkairi aunty, Allah ya ƙara buɗi."

Daidai suna shiga cikin babban get ɗin MENTION ALIYU ANZA Yusrah ta ɗaga kai tana kallon ikon Allah har suka tsaya wajen ajiyar motoci suka fito, Yusrah na riƙe da jakar aunty Intisar ɗin ita kuma ta bi motocin dake gidan a jere a nan ta ce" Ga dukkan alamu Aba baya nan, sannan Nabihat ta zo, kuma ƴan matan Anna suna nan da Anna, mu je."

Ita ma ta ji daɗi jin yan matan nan na Anna na nan, dan kullum sai aunty Intisar ta mata zancen su, zata so ta gansu ita ma, da wannan suka rankaya cikin babban falon wanda tun kafin su idasa shiga ƙamshin turaren wuta da na turaran jiki irin na anfanin mutane ya garwaye ɗakin sai firar yan mata sama sama haka kamar waɗanda suke gardama ne ko menene? Ita dai tana biye da aunty Intisar har suka shiga, suna ƙarasa shiga ƙauyancinta ya so bayyana, amma ta kame kanta ta sadda kanta tana hangen yadda ƴan matan ke ta ihun ganin Yayarsu suna yi mata oyoyo da rungume ta.

Ita ma cike da farin ciki suka ƙarasa wajen kujeru tana faɗin" Ke cikani mana kin shaƙe ni."

Goggo Tidin ta fito daga kicin tana amsa waya, a lokacin da Nawal ta ce" Aunty, wannan ce Yusrah?"

Aunty Intisar ta sakarwa Nawal ɗin murmushi tana duban Yusrah ta ce" Ita ce Yusrahana, Yusrah ga yan uwanki, ga Nawal..." Ta fara nuna mata sannan ta nuna ɗayar tace" Ga kuma Manal, sai Abrar cousine ɗinmu ce."

Ta nuna Abrar dake murmushi sai kuma Nabihat dake ta gatsine fuska tace" Wannan kuma ƴar aminin Aba ce, amma an zama ƴan uwa yanzu, sunan ta Nabihat."

Irin yadda suka yiwa aunty gaisuwar runguma haka su ukun nan suka yiwa Yusrah, wacce ta ji wani banbaraƙwai, amma banda Nabihat da ta koma saman kujera ta zauna tana ɗan ɗora ƙafafuwanta saman table ɗin dake falon ta ɗan yiwa Yusrah kallon ƙasa ƙasa ta ɗauke kai ranta na neman cinkushewa, ba dan komai ba sai dan ganin irin tsarin nutsatsen kyan Yusrah, hijab ne a jikinta amma ya wani irin haskata, ƙunshi hannayenta ya wani bugo cewar macece mai classe, ɗan murmushin da take saki ta ɗan lumshe kwartayen idanuwanta kuwa ko ke mace ce sai kin kalleta kin yi murmushi domin abin vry cute, gaba ɗaya lullumin kyan baiwar Allahn suka cinkushe mata ƙirji har ta ji ranta na neman ɓaci, dan haka ta ɗauke kanta ta maida kan Goggo Tidin da ta bi Yusrah da kallo ita ma ta ɗauke kanta ta shiga amsa gaisuwar Intisar da kula sosai sannan ta ɗan ɗago tana duban Intisar ta nuna Yusrah dake zaune ta ce" Wannan fa?"

Intisar ta yi murmushi dan yanayin da ta yi tambayar da wani iri kamar ta ga kashin nan, sai ta kasa bata amsa a nan ta miƙe tana faɗin Mah mu je, ina Anna ne?Ko tana kicin ɗin?"

Tidin ta sake bin Yusrah da kallo ta taɓe baki ta bi bayan Intisar ɗin, Yusrah kuwa kanta a ƙasa, takan ɗan ɗago ta kalli tagwayen Anna dake mata fira da Abrar da ta sa aka kawo mata su ruwa da jus har take tambayarta me zata ci a dafa mata ne? Ta yi murmushi ta ce" Ba komai Abrar a ƙoshe nake, thank you."

Nabihat ta taɓe baki a ranta ta ayyana _" Abrar ɗin nan akwai banza uwar shishigi."_

Suna zuwa cen wajen cin abinci Intisar ta juyo da yanayin bata ji daɗin irin yadda aunty Tidin ke wasu abubuwanta ba ta ce" Mah, wannan fa yar gidana ce, a wajena take, ni nake riƙonta."

Goggo Tidin ta juya da mamaki ta kalli inda Yusrah take ta juyo tana kallonta ta ce" Ke kike riƙon ta ? Wannan gandamemiyar budurwar ce Mubarak ɗin ya baki riƙo? Yar waye ma? Allah dai ya sa ba muharamarsa bace, wannan ai sai dai ku riƙe juna, da me kika fita ne? Mtsssss, maza sam basu da hankali shi yasa ni ba zan ɗauki wannan ba, ni fa ko ƙanwarka ba zaka kawo min riƙo ba gaskiya dan ba zan ɗauki rashin mutumcin ƴar kowa ba."

Intisar zata yi magana Anna ta ƙaraso ɗauke da wani littafi wanda suka yi odernsa daga Chaina ita da yan matanta dan haka kawai suka ce kuma sai sun leƙa Chaina a harkar girki, shine yau suka fitar da kayan girkin suka yi, shine Anna ta zo dubawa, Anna ta yi murmushi bayan ta ja ta tsaya tana harɗe hannayenta tana kallon ikon Allah abinda Tidin ke faɗa.

Tidin kuwa na ganin ta fito ta wani haɗe fuska haɗi da jan tsaki ciki ciki ta yi gaba ƙasa ƙasa tana faɗin" Duk abin mutum dai bai isa ya rabani da ƴar ɗan uwana ba.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login