Showing 153001 words to 156000 words out of 397328 words

Chapter 52 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70016

"

Anna na duban Intisar dake gaisheta fuska wani iri ta ce" Ban hana ki keɓewa da ita da yin ire iren maganganun nan ba?"

Intisar ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Anna tana ganin Yusrah ta so ta yi maganganun a gabanta shine na janyo ta nan ta yi a nan."

Anna ta girgiza kai ta ce" Shikenan, ki kula, in har kin ɗauki ƴar mutane ki zauna da ita da zuciya ɗaya , da yawa zasu kawo maki suka ko wani abin, ki ji tsoron Allah ki kiyaye ɗauka, yadda kika hana babarta tafiya da ita ki zame mata uwa, ita kuma da bata da hankali ta ci gaba da yi duniya ce, sai kace ita ɗin ba zaune nake da ita ba harda ƴarta, ba'a yi kiranta gandandan ba sai ita ce zata kira wani, ko ji take har yanzu shekararta biyar ko kuwa jikin ke ta tsufa hankalin a baya? Allah shi kyauta mu je in ga yar tawa."

Daga nan suka koma falo, aka haɗe fira ta kaure sosai, Anna ta ja Yusrah a jikinta sosai, domin ko da lokacin cin abinci ya yi Anna ta umarci su je su ɗauko har da Yusrah ta saka, dama kuma su yan biyu sun sakata dole sakin jiki da su ya zamo ko wajen cin abincin tare suka zuba a babban tire suka riƙe abin cin abincin ƴan Chaina suna ɗiba suna shan dariya domin kasa ɗiban abin kirki suke yi Anna kuwa na ta ƙoƙarin koyar da su, hakan ya sa ta saki jikinta sosai a cikinsu har sai da yamma ta yi sosai suka wuce, amma tsakaninta da Nabihat ko ci kanka basu cewa juna ba, Anna kuwa sai addu'ar fara aiki lafiya take yi mata da jaddada mata idan weekend ya yi ta tabbatar a nan wajenta zata ringa yi, sannan ta haɗa mata sha tara ta arziki, hakan ya sa Yusrah ganewa cewar kyauta a jinin ahalin Anna yake, bata haɗu da Aba ba, bata san yaya yake ba shi, amma tunda ta haɗu da Anna ta ji har cikin ranta matar ta kwonta mata.

Suna tafiya Anna ta tarda Goggo Tidin saman table tana cin abinci, ta yi tsaye face to face da ita ta ce" Tidin, yarinyar ai ƴar ɗan uwan naki ce ta ɗauketa zata riƙe, shi ma kuma mijin ya yarda, inaga ai ba laifi bane riƙe ɗan wani, dan kuwa haka ɗin taimako ne kawai, bayan shi ba lalle ba dole, taimakon ne dai kawai da son samun kusanci wajen Allah ba dan a birge wani ba."

Daga nan ta yi tafiyarta, ta bar Tidin baki buɗe cike da mamakin yau ita ce Anna ta yiwa magana haka? Amma wa take nufin tana riƙewa da taimako? Ita ko Abrar? Bata isa tace taimako take yi mata ba tunda gidan nan na Yayanta ne ba na uban wani ba, ok haka take so su yi ko? Zasu yi za'a ga waye marar mutumci cikin su biyu.

Su Intisar kuwa suna shiga gida wanka suka shige, cin abincin dare ma sai a ɗakinta ta yi dan gajiya, ta kuma kwanta da wuri bisa umarnin Intisar saboda ta samu shiga asibiti da wuri.


*Washe Gari*


Washe gari ƙarfe takwas a asibiti ta yiwa Intisar, ta yi shiga ne na atamfa doguwar riga wacce ta bi lafiyar jikinta ta kwanta das, atamfa ce mai tsadar gaske, sannan mai kala mai kyan gaske, haka kuma haɗin da ta yi mata na baby hijab da takalmi ƙafa ciki marar nauyi mai ɗan tudu kaɗan, da kuma jaka sai agogo mai kyan gaske ruwan baƙa ga tsararren turaran dake fita daga jikinta kana ganin ta zaka bata hanya bayan ka gaisheta da girmamawa.

Suna zaune Docter Siddik ya ƙaraso da gaggawa yana ba Yaya Mubarak haƙuri da Intisar sannan ya buɗe office ɗin sa suka shiga su duka yana amsa gaisuwar Yusrah.

Bayan sun zazzauna da ɗan gaggawa ya sake nuna masu komai, sannan ya nuna mata rigar aikinta fara da ya tanadar mata tun ranar juma'a, ya kuma sanar masu lokutan hawanta da saukarta ya ɗora da faɗin" Ba lalle ne ta sauka kullum a kan lokacin nan ba, idan aiki ya yi yawa tana iya haura lokacin, ko yau zata wuni a tsaye saboda yau monday sosai asibitin na cika da mararsa lafiya, gashi Docter ɗin yaran biyu basa nan, sai ni kawai sai ita, gashi yanzu lokacin zazzaɓin yara da manya duka, akwai aiki sosai a gaban mu, ina fata ƙanwar tawa ta horu da aiki?"

Yusrah ta yi murmushi tana sadda kai, Yaya Mubarak da Intisar suka amsa da in sha Allah, sannan suka miƙe suka yi masa sallama tare da sake gode masa, a nan Intisar ke tambayar yaron wajen yayansu, Docter ya tabbatar mata ai jiya da dare a gida ya kwana da Abansa dan haka suka tafi tana ƙara jadadawa Yusrah kar fa ta yi wasa da abincinta, idan lokacin ci ya yi ta tabbatar da ta ci.

Yusrah kuwa na murmushi bayan ta saka rigar aikinta a karo na biyu ta ji farin cikin hakan a cikin ranta sannan ta rako su har wajen mota ta masu rakiya kafin ta koma ciki ta tarda tuni an fara shiga wajen Docter sai kawai ta je ta shiga aikinta, shi kuwa yana kallon dukkan ayyukan da take yi cike da gamsuwa da ƙwarewarta a aikin.

Can kusan ƙarfe goma sha ɗaya likitar dake kula da ɗakin wata yarinya mai suna Aisha ta shigo ta sanar da Docter yau ne za'a kai yarinyar clinik Alheri saboda aikin da za'a yi mata wanda yau ne Docter ya basu ranar da zasu kai yarinyar a yi mata aikin na ɗan lokaci ƙanƙani su dawo da ita nan a saka mata ƙarin ruwa.

Kai ya dafe cike da wani yanayi ya ce" Ya salam! Sister kin san da abin nan ya shige min gaba ɗaya? Gashi lokacin da ya dace ace an kaita ya yi, please a shiryata in ga yadda zan yi, a waje da mutane sosai ne?"

Likitar ta ce" Docter a waje a ƙalla mutanen sun kai talatin da wani abu kuma ƙaruwa suke yi, yanzun ma sai da nace da sister ya dace a dakatar da cirar takardar nan haka kai ɗaya ne fa yau."

Docter da ya miƙe yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa ya kai dubansa kan Yusrah dake ɗigawa wani jariri magani a bakinsa ya ce" Sister Yusrah, bani aikin nan, zo ki yi evacuation."

Yusrah ta miƙe tana miƙa masa maganin ta ce" Ok Docter."

Ya laluba ya ciro file ɗin yarinyar ya buɗe yana nuna mata komai da komai ya dora da faɗin" Docter Hamat Anza ne zai yi mata aikin, hanzarta kar ya shiga wani aikin ya tsayar da mu, mun gama saka masa kuɗin aikinsa komai da komai, daga an yi mata sai ambulance ta dawo da ku mu ci gaba da kula ta a nan in sha Allah, wannan kayan aikin dai sai na je na kawo mana su, dan tafiya wata clinik ɗin nan bata gyara mu."

Yusrah tunda ya ambaci sunan Docter Hamat jikinta ya mutu murus, har ta ji tamkar ƙafafuwanta ba zasu iya ɗaukanta ba, sai dai abu ɗaya ne ta sani dole ne dama irin haka na faruwa, daga wata clinik ɗin ana iya kaika wata dan yi maka wani aiki ko wani gwajin da babu kayan aikinsa ko likitan da zai yi shi a clinik ɗin da ake dubaka, sai dai bata taɓa tunanin zata kuma haɗuwa da wannan azzalumin a kwana kusa ba! Amma kashhhh! Ƙaddara ta rigayi fata, sai da ta samu kanta zaune cikin ambulance gefen mahaifiyar yarinyar da bata da lafiya riƙe da takardunta sun shigo asibitin lafiya ta gane cewar bata da damar yin baya sai dai ta ci gaba da tafiya kanta tsaye.

Saman abin turawan nan aka ɗauketa aka turata direct aka yi ɓangaren tiyatar da ita, ya zamo da wuri Yusrah ta bada takardunta wa chirurgien ɗin da zai yi mata allurar kashe jiki dan a yi mata tiyatar sannan ta yi masa bayanin duka da ya dace ace ya sani kama daga kan in yarinyar na shan su lipton da sauransu, ta sake tabbatar masa da komai sannan ta ja baya ta tsaya tare da mahaifiyar yarinyar suka shiga jira kafin mahaifin yarinyar ya iso shi ma daga wajen aikinsa suka zauna jira.

Kasantuwar akwai hanyar da yake bi ya je ɗakin tiyata basu ga shigarsa ba, har aka yi aka gama aka saka yarinyar ɗakin observation aka fito aka ba iyayenta damar shiga su ganta sannan aka ba Yusrah file ɗin ta aka sanar mata ta je office ɗin oga yana son ganin ta.

In ba dan ta san cewa tabbas kan lamarin aikin da ya yi ne da babu abinda zai kaita office ɗin sa, sai dai ta san dole ta je, ta yiwu akwai abu mai mahimmanci sosai a kan aikin yarinyar, a dole ta juya ta nufi office ɗin nasa ta ɗan buga sannan ta dakata ta yi jiran a bata izinin shiga.

Sai da ya bata damar shiga sannan ta murɗa ta shiga, ya ɗago ne da niyyar fara nuna mata hali irin wanda wasu doctocin ke yiwa duk wani wanda ba Docter ba, balle waɗanda suke daf da su, domin tsayin shekarun karatunsa shekara ɗaya ce tak ta bambamta, ya zamo sukan yi masu isa da nuna su ɗin manyansu ne dole su masu biyayya, balle Hamat yana da wannan hali, duk wani wanda bai kai takardar shi ba in dai aiki ya haɗo su sai ya tuna masa biyayya zaya yi masa shi a gaba yake da shi, shine ya so yi a yanzu da ya ɗago da yanayi na raini raini dan ya faɗa mata idan ta je ta faɗawa mai kwalin Docter irin nasa kar a kuma kawo masa yara da datti a jikinsu, idan za'a kawo a tabbatar da an kula da tsaftar yara sosai in ba haka ba su ringa biyan kuɗin gyaran yaran a nan, sai kawai idanuwansa suka sauka a fuskar Yusrah, wacce hatta lips ɗin da Intisar ta goga mata bai fita ba, yana nan ɗas a fuskarta.

Gabansa sai da ya faɗi, ya ƙara zuba mata ido yana cire glass ɗin idanuwansa a hankali ya ce" Yusrah?"

Yusrah ta ɗan sake zuba masa ido, abubuwan dake cizota na sake sakata jin kamar ta tashi ta kashe tsinaniyar fuskarsa da mari, sai dai tuna cewa a yanzu haka maganar ƙanin ta na wajen hukuma sai ta danne kanta a nutse ta furta " Yes? An ce kace likitar da ta kawo Aisha ta zo?"

Ya Salam! Gaba ɗaya zuciyarsa sai ta ringa dokawa, ko a da yanayin yarinyar na matuƙar birge shi, yana jin sha'awar yarinyar fiye da komai, a hankali ya ringa jin bayan sha'awarta fa har da so, sai dai shi ba zai iya duƙa mata ba, shi yasa ya so ace ta yarda da shi, da a hankali abinda ya so nuna mata na tarayya zai girmama dan yana kyautata zaton wannan sai ta jera da Maman joli, sai dai ta yi taurin kai ta ƙiya, amma a yanzu ƙwarai ta daki zuciyarsa har ya ji kamar numfashinsa zai tsaya.

A hankali ya furta" Wow! Yusrah, ke ce? Amma ta ya kika zama ma'aikaciya a wajen Docter Siddik? Kuma ina ƙanin ki?"

Yusrah ta so arar ɗabi'ar da ba ta ta ba, ta hanyar watsa masa hannaye tace da shi yana gidan uwaka! Sai ta hani kanta, ta danne kanta sosai tana dubansa ta miƙe ta ce" Ba wani bayani da ya shafi marar lafiyar da na kawo?"

Docter Hamat ya tafa hannunsa ya ce" Oh yes, this is my Yusrah, izza a jininki take baby, baza izzar ki daidai da ke ne, amma ya dace ni a min a hankali ko ba komai mai son ka ai mai son ka ne, kuma in sha Allah sai na aureki yarinya."

Yusrah ta haɗiye yawu tamkar maɗaci a wuyanta tana dubansa a hankali ta ce" Ni kuma in sha Allah sai na ga bayan ka, idan kuwa hanyata ta haɗu da kai Hamat, ka sani dan in sabunta maka duk wata hallitar jikinka ne da reza, bunsuru!" Daga nan ta ɗauki file ɗin ta juya ta fice ta bugo masa ƙofar da ƙarfin da ya saka shi rintse ido.

Da sauri ya miƙe tsaye yana kallon ƙofar da ta bugo, tunda yake ba'a taɓa ci masa mutumci irin na yau ba, wai me take taƙama da shi ne?
Ya ya aka yi ta wanku haka? Suturar jikinta, agogon hannunta, yanayin maganarta kanta ta cenza, me yake faruwa da shi a yanzu da ya dace ya ji ya tsaneta fiye da komai sai wata zuciyarsa ke son ayyana masa _"Ina ina ma? Ace zata fuskance shi, ina ma ace zata gane a yanzu killaceta yake son yi ba lalata da ita ba? Ina ma ace zata yarda su gina *WATA TAFIYA* mai tsari ita da shi? Har cikin ransa wani irin sonta yake ji ya mamaye zuciyarsa._"

A hankali ya ɗora jimƙaƙƙun hannayensa saman table ɗin gabansa yana sadda kansa ya rintse ido ya ce" Na ji, ni ne bunsurun ko? Ba laifi ki zage ni, amma ki sani kanki kika zaga tunda mijinki nake, Yusrah sai na aure ki!"




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 09:47 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨??👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*41*




Tunda Allah ya halicce shi, bai taɓa shiga firgici irin na yau ba,
A saninsa a ƙasar nan ba'a hukuncin kisa ga wanda ya kashe ma balle shi da baki ne kawai bai buɗe ya yi magana ba, hukuncin ma irin na saudiya, idanuwansa na ganin tashin hankalin nan yau kwanansa uku cir da aka ajiye shi a wajen nan, bai rasa ci, sha, ko wajen kwanciya ba, abu ɗaya ya yi dana sani da ya gwada guduwa suka kamo shi suka ringa tankaɗeta mareta da shi kamar sun samu birin wasa sai da suka ga dama suka mayar da shi ɗakin sa, wato sojawan dake gadinsa, a ranar ya gane sojawanmu basa barci kuma suna kan aikinsu basa wasa, sai gashi yau kwana na uku da aka rufe shi a ɗakin AA ya zo sanye da sutura irin ta larabawa, wato jallabiya da hirami, sai wani baƙin abu dake wuyansa wanda ga dukkan alamu idanuwansa zai rufe da shi, haka kuma hannunsa riƙe da sharɓeɓiyar adda , irin doguwar wuƙar nan sai ɗaukan ido take yi,

Tunda ya zo ya sa aka kai Sani ciki aka saka masa jallabiyar shi ma sannan aka fito masa da shi filin nan ya zamo su huɗu ne a wajen ya dube shi ido cikin ido ya ce" Ka daina ihun nan, da kukan nan ka gyara, in ka so ka yi kalmar shahada in ka ƙi ka yi ihu, ina da wajen zuwa ba a nan kawai zan ƙare ba."

Wani ihun kukan Sani dreba ya fashe da shi yana haɗe hannayensa ya ce" Sir, dan Allah ka min rai, ka rufa min asiri, dukkan abinda kake so zan sanar maka, ko menene zan sanar maka dan Allah kar ka sare min kaina dan Allah yallaɓai."

Aswan ya ta;e baki ya dubi sojawan nan ya masu alamun su riƙe shi, ai kam suka riƙe shin, shi kuwa ya saka baƙar hular ya fitar da wuƙar ya wani jata a ƙasa, wanda ya saka Sani direba saka wani ihu sai kawai ya zube a jikin sojawan nan ya sume.

Turus AA ya yi yana kallonsa, sai kuma ya dafe goshi ya dubi sojawan da dariya ta kubce masu dole, suna sake yarda a kusa kusan nan da wahala a samu mai strategi irin sir Aswan, shi kuwa ya ce" Ji sakarai, ka san ba zaka juri wahala ba ka siyawa kanka, ku tashe shi ya bani information ɗin da nake so kar a yi sallah muna nan."

Bayan mintina kaɗan bayan ya dawo hayyacin sa sun sake tabbatar masa kansa a jikin wuyansa ya duƙa gaban Aswan dake zaune saman kujera yana sauraron Aswan ɗin, AA ya ce " Idan ka gama sanar min abinda nake da buƙata, zaka je ka ɓuya kamar yadda kuka umarci Mani, Sani ka sani ni bana faɗa in ƙi aikatawa, idan ka yarda na ganka ba tare da na gama abinda ke gabana ba Sani sai na sare maka kai, a nan zan sare kanka mu birneka sai dai a yi shari'ar a lahira, ka ji?"

Sani ya ce" Na rantse da Allah in na yi maka ƙarya ka sare min kai, kuma daga nan in na je inda aka taɓa sanina shi ma ka sare min kan, ni wiwi ma zan fara sha dan in haukace, ba sai da hankalina ba zan faɗi koma meye? Ni dai a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login