Showing 3001 words to 6000 words out of 397328 words

Chapter 2 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69989

*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*2*




A kaɗan ya kusa awa ɗaya yana ta saita nutsuwar shi kafin ya zauna kan kujera ya na ƙara jawo kwanfutar shi ya buɗe ya fara duba wasu muhimman abubuwa, nan ma ya kwashe awa ɗaya da kusan rabi har ɓacin ran na shi ma ya sauka kawai kira ya shigo wayar tangarahon dake gefen shi wani matsakaicin telephone mai kyau, sai da tayi kuka sau uku kafin ya zura hannu ya ɗaga yana karawa a kunne ya yi shiru.

Muryar mace ce ya tsinkaya da girmamawa da kuma kiyaye ɓacin ran shi tace "Yallaɓai, in ji chef wai ka same shi bureau yanzu."

Shiru ya yi ka rantse ba da shi take ba, ita ma dake sauraren ya bata amsar yana zuwa ko ba zai je ba addu'ar rabuwa lafiya take da shi, duk soja mafaɗaci ne amma ban da Anza, faɗa da masifar AA ta fi ta sauran sojawan, a haka wai dan ya tashi gidan da akwai ne, bai san yunwa ko wahalar rayuwa ba, da a ce ma akwai talauci ne sai ka ce har da talauci ke rikita shi.

Ita dai ba ta sauke wayar ba dan bata so ya ce tayi laifi, sai da ta ji dan kan shi ya aje wayar yana jan siririn tsaki, duk da haka bai yi niyyar tashi ba sai da yayi enregistré ɗin abinda yayi mai mahimmanci kafin ya rufe na'urar ya miƙe ya bar office ɗin cike da wani takon shi kamar na sarkin dawa (zaki).

Kasancewar office ɗin chef ɗin cen ciki yake sai da ya yi tafiya mai yar nisa sannan ya ƙarasa, yana zuwa sakatariyarsa ta sheda masa yana ɗayan ɓarin wajen tattaunawa, dan haka ya ƙarasa ba faɗuwar gaba ko wani ɗar, duda ya san abinda ke jiransa.

A lokacin da ya shiga duk wani babba dake gabansa ya halarta a wannan ɗakin taron, suna tataunawa ne kan abinda ya dace da shi, waje ya samu ya zauna bayan ya sara masu sun bashi damar zaman.

Chef ne ya buɗa baki a nutse ya ce" Me ya haɗa ka da colonel Garba?"

Ba wani kwane kwane, ko ƙarya dan ya kuɓutar da kansa ya ce" Ya sameni a office ɗina ne kan maganar da na san ko ba yau ba ana iya yinta, ni kuma a lokacin ina cikin yanayin ɓacin zuciya, shi ne na roƙe shi ya je zan same shi office ɗinsa amma ya ƙi saurarona!"

Gaba ɗaya kallosa suke yi da mamakin ƙarfin halinsa, shin bai san me ke jiransa bane ko menene? Da dan ɓacin rai colonel Jadi ya ce" Shine dalilin da zaka dake shi?"

Ɗagowa ya yi ya ɗan zuba masa ido, sai kuma ya sadda a nutsensa ya ce "Ba dukansa na yi ba, shaƙarsa kawai na yi, da dukansa na yi ai ba zai iya kawo kansa ba."

Ya faɗa ne dan gaskiyar abinda yake tunani kennan, su kuma sun ɗauki hakan matsayin raini da taƙama da yake da ubansa da kuma ɗaurin gindin da yake da shi duba da yadda yayi maganar a gadarance, duk da sun san dama shi ɗin mutum ne da wani lokaci ko zo ya ce zaka ga kamar cikin gadara ya yi, amma sam rikicinsa su baya wani firgitasu, ko me ya zo da shi a shirye suke a fantsama.

A wannan lokacin sai da wajen ya zamo babu mai ba ɗan uwansa haƙuri, kuma gaba ɗaya laifinsa ya fito ƙarara da irin hukuncin da ya dace da shi, a kausashe ainun wanda suke da gala ɗaya da juna wato commandant Salisu ya ce" Kana matsayin babba ko da shekarunka basu kai namu na ya dace ka fara tanƙwasa zuciyarka, zuwa gaba idan da rai kai ne jagabar wannan waje, a irin yadda sam baka san tanƙwasa fushinka zaka iya tafka ɓarna mai girman gaske, a dole yau ka ɗauki punition, za'a kai ka cel sannan a dakatar da kai kamar yadda aka tanadar wa mai laifi irin naka, ko baka yarda ba?"

Ido ya zubawa commandant na ɗan lokaci kafin ya ce" Na yarda."

Gaba ɗaya wajen shiru ya ɗauka na yan sakwanni, sai su da kansu suka shiga wasi wasin anya kuwa hakan zai yiwu? Ko jira yake yi a matso shi ya damƙi wuyan mutum? A wannan zamanin dai,a gidan maza babu gagararen da zai fito gaba da gaba da shi, sai dai su far masa ta hanyar karin maganar nan da ake cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, har ga Allah shi da kansa Chef sai da ya sake zubawa ɗan abokin nasa ido kafin ya sauke ajiyar zuciya, a yau dole a ɗora masa hukunci daidai da laifinsa, dan da ace cikin sirri ya aikata haka tabbas da maganar bata fita ba, sai gashi sai da aka amshi colonel a hannunsa.

Ba tare da ya kalle shi cikin ido ba saboda shaƙuwa dake tsakaninsu da haɗuwar jini ya ce" Aswan Aliyu Anza, ka aikata laifin dukan jami'in ƙasa ba tare da ƙwaƙwaran hujja ba, daga yanzu zaka shiga ɗakin gyaran hali na tsayin kwana biyu, zamu dakatar da kai daga aiki na tsayin wata biyar ba albashi ba bindiga, ko taka ta gida zamu karɓe har sai ka gama amsar horo sannan mu maida maka, muna so ka bamu haɗin kai cikin salama a yi komai a gama cikin salama, idan ba haka ba zaka ja faɗan rai da rai ka ƙarar da mu ko mu ƙarar da kai a wannan ɗakin."

Shi din da kansa sai da ya ji abu mai girma da rauni ya shiga zuciyarsa ba, dan komai ba sai da eh lalle wannan faɗan nasa na rashin gaskiya ne, kuma baban abinda ke ɗaga masa hankali ace ya farka ba zai ɗauki bindiga ba, shin ina suke so ya saka zuciyarsa ne?
Miƙewa ya yi tsaye lokaci guda kusan su dukansu suka miƙe da miƙewa irin ta shirin zaro bindigoginsu dan shirin kar ta kwana saboda sanin da suka wa AA ɗin.
Shatata ya tsaya yana kallonsu da yanayinsu, sai ya samu kansa da sakin murmushi yana ciro hular kansa da alamun girmamawa ya ajiye saman table ɗin dake gaban su, ko ba komai zasu masa askin da yake yiwa kansa, wato kolo, ranƙyal,dan bai cika son tara gashi ba, Allah kuma ya yi shi mai baiwar tara summa.

A hankali ya ce" Kar ku zarro bindiga, ubana fa kuka zaunar ya yanke min hukunci, ai an gama ko me yace daga nan bani da ja."

Daga nan ya miƙa hannunsa aka saka masa ankwa ana fita da shi ba wani ɗar ko jin kunya aka shige mota da shi aka nufi gidan gyaran hali na sojawa, suna ƙarasawa aka nufi ɗakin aski da shi, sai da aka yiwa kan nan tal sannan aka tuɓe shi aka bar shi daga shi sai gajeran wandon da ya bi lafiyar jikinsa ya kusan bayyana wanene shi, wanda hakan ma wata babbar dama ce ta tsoratar da mazaje, ɗakin da aka ware masa aka saka shi aka rufe aka tafi da ky ɗin, ɗakin ko hasken kirki babu, ɗinɗirim ne, a ciki akwai bokiti da buta waɗanda aka aje su dan buƙata, uwa uba ko abinci zaka ci a nan zaka ci ba inda zaka je, wanda hakan ya dace ya girgiza zuciyar mutum.

Amma shi ba wannan ya fi damunsa ba irin hukuncin wata biyar cif ba kaki, ya Allah....A hankali ya lumshe idannuwansa yana jin zafi da raɗaɗin hakan a ransa, bai wani kula da sauro dake masa busa a kunne ba, bai kuma kula da cizon da yake naɗa masa a tausasshiyar fatar shi da ta jima da sabawa da jin daɗi da hutu, dan duk yadda zaiyi nesa da gida dan aiki, indai yana gidan to tamkar ɗan sarki haka yake saboda fadar da yake ciki.

G zafi ga duhu ga ƙarancin iskar shaƙa, hakan ya zamo tunanin abinda ya riga ya yi a rayuwarsa, domin shi dai soja yake, sojan ma wanda ya san wahalhalun yau da gobe na sojawa, ya je jeji ya kwana cikin rami, sun yi rayuwa a cikin rana, sun yi nutso a cikin tafki mai caɓo, sun yi sama da sati basu ci abin kirki ba sai ruwa da suke ɗiɗɗika marar kyau, horo dai na sojawa sai da ya je ya yi kala kala kafin ya yarda ya hau matakin da karatunsa ya bashi dama, a yanzu ya fi tuna horon da ya hau kansa da kuma iyayensa, ya san a yi ruwa a yi wuta Dad ba zai iya barci bai ji inda yake ba, idan ya jin kuwa bai san yaya zasu kaya ba, babban addu'arsa shine Allah ya sa a ɓoye masa, dan wallahi kwanakin da aka diɓar masa sai ya cinye su ko da zai waiwayi gida!



********************


Akan mai naƙudar nan suke ba tare da sun yi nesa da ita ba, musamman ma dai Yusrah dake da zuciyar tausayi fiye da dubannin likitoci, agogo ta sake kalla ta ga lokacin tafiya gida wucewa yake, amma da ta sake duba matar sai ta saki murmushin da ya saka Sakina kallon ta tace "Ya dai Yusrah?"

Ba tare da ta daina murmushin ba tace "In sha Allah ta kusa haihuwa, kan ɗan ta gashi nan ya fara leƙo duniya."

Ita ma ɗan murmushin ta yi amma ba ta ce komai ba, safar hannun ta ta cire tace "Kai! Kinga na manta ba'a faɗawa Doctor an kawo mai haihuwa ba."

Da ɗan jin haushi Yusrah ta kalle ta tace "Ya haka kuma? Kenan da sai wata matsala ta faru ne za'a sanar da shi?"

Dariya Sakina tayi ta juya tana fita tana faɗin "Mantawa na yi fa."

Ganin ta fice Yusrah ta sake duƙufa akan matar nan tana mata sannu da cewa ta ci gaba da nishi kar ta wahalar da kan ta da ɗan ta a samu matsala, iya ƙoƙari kam matar na yi, hakan ya sa kan yaro ya fara fitowa Yusrah kuma na tallabe tana lura a nutse tana son ya ƙarasa fitowa...

Ba zato ba tsammani ita ko shigowar Sakina ba ta ji ba kawai ta ji ta jawo hannun ta da ƙarfi zuwa gefe, a razane ta kalle ta sannan ta kalli matar da kan yaro gashi nan ya fito amma ba gaba ɗaya ba, cikin tashin hankali Yusrah tace "Sakina lafiya? Me yake damun ki? Kan ɗa ne fa k..."

Ɗora yatsa tayi a bakin ta alamar tayi shiru, sannan ta mata raɗa tace "Doctor ne ke shigowa, ke baki san shi bane, ba ya son hayaniya."

Da wani sabon mamakin ta kalli Sakina tace "Doctor? To idan ba ya son hayaniya sai me? Mun buƙace shi a nan ne? Me zai kaw..."

Jin kamar motsin shigowa ya sa Sakina faɗin "Ke, yi shiru dan Allah."

Cikin jin haushi Yusrah ta fizge hannun ta tare da niyyar komawa ga matar nan, amma wani sihirtaccen ƙamshin turare da ya daki hancin ta ya tilasta mata dole ta waiwaya ga ƙofar, kallon rabin sakan ta mishi ta kawar da kai, amma kuma ba ta sake ɗaga ƙafar ta daga gurin ba. Ta rasa dalilin da ya sa ta gagara ci gaba ko baya, takon Doctor ɗin kuma ya sa ta sake ɗaga idanun ta ta kalle shi... Ba ta ce wane irin mutum bane? Amma dai a taƙaitacciyar jumla kamilallen dattijon da ba zai gaza ɗaukar shekara hamsin zuwa da biyu ko da uku ba, suma shekarun za'a iya hango su a fuskar shi ne da kuma kan shi, dan duk inda gashi ke fitowa to akwai sili silin farin dake nuna ba irin furfuren nan bace da ake kira ta baiwa, sannan fuskar sa ma ta babban mutum ce, amma kuma jikin shi da kayan jikin shi, sam ba su nuna haka ba, ko dan yana likita ne yake kula da jikin shi? Ko kuma bayyanar tsantsar hutun da zai baka tabbacin matsala gare shi ba dai ta kuɗi ba a sutura da jikin nashi kan shi, dan kuwa ɗinkin wata irin rikitacciyar shadda ce aka ma ƙaramin ɗinki, ba wai a farashi ba, a'a irin ɗinkin samari da matasa mai gajeran riga da ba ta wuce guiwa da gajeran hannu shima...

Ƙoƙarin kwatantanta tsaruwar dattijon ya sa Yusrah har bata san ya isa ga matar nan ba, ba ta san me ya mata ba dan duk da ta shagala da kallon dattijantar ka sa da kamala dake mata kama da na mahaifin ta, dan hatta shekaru ma a ganin ta wannan mutumin zai fi mahaifin ta, sai kawai sautin wata narkakkiyar muryar shi ta ji da sai yanzu ta tabbatar da wane yare ne shi ɗin (buzu) a harshen da sam ba ya fita sosai yace "Wane irin sakaci ne wannan? Matar nan aiki za'a mata yanzu."

A rikice, a ruɗe Yusrah ta kalli ƙeya da kafaɗun Doctor ɗin, sai kuma ta zabura da sauri ta koma kusa da matar tana kallon shi tace "Amma fa Doctor matar nan za ta iya haihuwa da kan ta, dubi ma kan yaro ya f..."

Tana maganar ne tana duƙawa dan son tabbatar masa yaron ya fara fito da kan shi, amma sarautar Allah wayam kan yaron nan ya koma, sa'ilin da likitan ya mayar da kan ta ba ta gani ba sai Sakina kawai da ta gama gane abinda yake shirin yi, da mamaki ta kalli ƙasan matar sai kuma ta sake kallon Doctor ɗin tace "Doctor, ka ba..."

A wani wulaƙance ya kalli Yusrah ya ɗauke kan shi ya mayar kan Sakina yace "A haɗa kayan aiki, zaku kasance tare da ni yayin tiyatar."

Sororo tayi tana kallon Doctor ɗin da ya juya Sakina ta bi bayan shi da sauri, kamar a mafarki ko dai haka abu mai kama da bacci ta ji muryar Sakina na ƙusƙus ɗin faɗin "Amma Doctor kuɗin ambulance ɗin da zata kai ta ɓangaren tiyata nawa ne wannan karan ko?"

Irin dai sumar tsayen nan Yusrah ta yi musamman da ta ji yace "E." Kawai ya faɗa ya fita daga ɗakin.




*_SAJEERAH_*🖊️


*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*3*





Bai yi mamaki ba da basu haɗu da shi gidan ba da rana, dan ya san yana da hanyoyi dayawa da zai iya cin abinda ran shi ke so, amma da dare ya yi haka lokacin da yake zuwa gidan ya yi bai zo ba, sai ya ji yana so ya san inda yake ɗin, dan in yana garin nan to bai da wurin kwana da ya wuce gidan shi, kuma kafin ya shiga gidan shi sai ya zo na su gidan, dan duk wasu halaye na Aswan ɗin da suke fatan ya canza, sun san baya neman mata, dan haka dare ba ya tsalawa ba tare da ya shiga ɗakin shi ya yi ta bincike da karance karance ba. Kiran farko aka shaida masa wayar sa a kashe take, bai haƙura ba sai da ya sake kira har sau uku, hakan ne ma ya saka shi miƙewa tsaye yana ɗan sake gwada kiran lambar, dan ya fi kowa sanin cewa AA ba ya kashe wayar sa duk uzurin da zai taso masa har ya hana shi zuwa gida duk da kasancewar sa soja, gashi yana kyautata zaton ba dai aikin da zai bar gari bane ya taso masa, ko da yake, kaɗan ne a aikin AA ɗin ya tafiyar shi ba tare da ya sanar da su ba, tunda ya san yau ya hassala shi.

Yana daf da sake kira uwar gida kuma amaryar sa ta shigo ɗakin ta ƙofar da ita kaɗai ce a gidan ke shigowa ta wannan ƙofa, kallo ɗayan da ya mata ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login