Showing 105001 words to 108000 words out of 397328 words
ran ba kuma, ita fa a yanzu gwarama ta samu kanta a gidan aikatau in dai ba cin zarafi da ɗaga hankali da ta samu kanta a gidan sarki matsayin sarauniya, duniyar sam bata gabanta, abinda ya fi damunta kwanciyar hankalinta da abinda yake gabanta, ta yi waje ne ta ajiye Tasneem matsayin mahaukaciya, tana tausayawa Hajia ainun da Yaya JAFAR, tana fatan matarsa ta shiryu ko ya samu wacce ta fita hankali ta kwantar masa da hankali, daga wannan babu abinda ya haɗata da ita, kuma bata tunanin zata iya kulata har abada.
Da wannan saƙe saƙen kowace ta kwonta bayan sun gama abinda zasu yi, yau Hajia ko leƙo su kasa yi ta yi, ciwon zuciyarta na damunta, haka kuma yaran nan kamar ƴaƴan guna, sai addu'a kawai a hankali sa daidaita.
*BAYAN KWANA BIYU*
Ƙa'ida ce ta lauyoyi dama idan zasu zo wani abu da ya shafi wanda suka wakilta, bayan bin dogayen hanyoyi an basu izini a rubuce, su kaɗai suke shigowa wajen ganawa da su, kamar yadda sai dai suyi sammako su zo sannan su tafi. Tun ranar da Brs. *Mukhtar* ya haɗu da AA a PG dama ya ci alwashin gano asalin ɓoyayyen mutumin dake bayan rigar AA ta hanyar yin bincike, ba kuma tare da ya tsagaita ba dinga bincikar wa ye AA saboda a sirrance ya ɗauki hoton shi da wayar sa a lokacin da ake ƙoƙarin tura shi mota, ya sha mamaki ba kaɗan ba da ya gano wa ye shi, sai kuma ya yarda tabbas aiki ya kai shi canza kamannin shi, sannan aiki ya saka shi zuwa PG a wannan yanayin, haka kula har aka sada shi da babban prison. A kwana kin nan bai zauna ba bai kuma huta ba har sai da ya zo suka haɗu da Chef, bayan ya sanar da shi ya san waye AA sannan Chef ya faɗa masa abinda ya kai shi, dan hakane suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen bin dokokin da zasu fito da AA daga wannan gidan ba tare da kowa ya ji jiki ba.
Yanzu haka kallon kallo suke shi da AA dake fuskantar shi, kuma kowa da abinda yake rayawa a ran shi, Brs. Mukhtar tunani yake ina ma AA bai da girman kai kasancewar sa babba ɗan babba? Shi kam da ya yi abota da shi irin wacce kowane lokaci zai iya faɗawa gidan su ko hakan zai sake zama silar shiryuwar ƙannen shi marasa jin magana wanda tun ranar da ya firgita masa su suka kasa daina bin hanyar islamiyya da masallaci akan lokaci, da an musu magana ya haka? Da kan su suke cewa _"Makashin mahaukaci ya ce zai zo har gida ya zane mu idan bamu bar rashin jin ba."_ A yadda suka bayar da labarin mahaukacin soja, tabbas ba ƙaramin ɗan daba bane zai iya kwantar da shi, shiyasa yanzu haka yake nan dan yana so alaƙar su ta fara daga nan ɗin.
AA kuma mamakin wanda Chef ya turo masa a matsayin lauya yake, a ganin shi kamata ya yi ya turo wani wanda yake daf da yik ritaya a aikin shi, to wannan shine ya san makamar aiki, bayan haka ma shi ya ɗan yi fuskar sa kallon kamar ya taɓa ganin sa wani wuri, amma kuma da ya ji bai tuna ba sai kawai ya share zancen tunda abun dayawa wai inji mutuwa da ta leƙa kasuwa.
Kallon da yake masa ne ya bashi dariya har ya ɗan murmusa yana girgiza kan shi, sai kuma ya dube shi da kyau cikin nutsuwa yace "An sallame ka *mr. Chairman*, zamu iya tafiya gida yanzu dan ka samu kayi wanka."
Maganar da yake masa, da yadda yake masa maganar sai kawai ya wa AA kama da wanda yake son ya tsonake sa haka ko ya saka shi dariya, sai kawai ya ɗan taɓe bakin sa yace "Ta ya ya? Wa ye kai?"
Da fara'a Brs. Mukhtar yace "Lauyan da ya kare ka, kuma Chef ne ya turo ni kamar yadda na faɗa maka da fari."
Kafin AA ya ce masa wani abu aka buɗo ƙofa aka shigo, babban jami'in wurin ne tare da wani suka shaida masa an sallame sa, kuma abun mamaki ɗaya jami'in ma har da sara masa ya yi, daga nan suka cike abinda zasu cike suka sallame shi dan dama ba wasu kaya gare shi ba, amma dai saida ya je ɗakin na shi bai ɗauko komai ba ya fito, wurin Arif ya tsaya ya bashi hannu yace "Ni zan tafi, amma na maka alƙawarin biyo bayana ba da jimawa ba, dan ina son zama da irin ku, sannan wani albishir..."
Saida ya sassauta murya sannan yace "An tabbatar min da ana shirin maida mahaifin ku gida saboda jikin sa ya yi tsanani sosai, nasan kuma gwamnati za ta masa afuwa a mayar da shi ɗin ko dan ya yi jinya acan."
Da farin ciki sosai Arif ya amsa mishi yana masa godiya, daga haka sukayi sallama ya fita ba komai tare da shi sai kayan jikin shi, cikin motar Brs. Mukhtar suka fita daga prison ɗin yana mai shirya yadda zai fito da uncle Kofa da kuma Arif.
Tunda suka fito a cikin motar ya zamo ya yi shiru ya ɗan kishingiɗa kaɗan idanuwansa lumshe sanyin motar na ratsa shi, da kuma ƙamshin cikin motar, har wani ajiyar zuciya yake saki a ɓoye idanuwansa kuwa har kamar zasu ɗauki nauyin barci, domin rabon sa da samun nutsuwar zuciya har ya manta, tunda ya faɗa kuwa cikin cel hancinsa ya tabbatar masa dole zai ringa wuni da juwa dan kuwa ba ƙaramar wahala wari ke bashi ba.
Jin tafiyar ta yi nisa dan a ƙalla sun ɗauki minti arba'in motar na tafiya, dan ma irin manyan motocin nan ne da ba zaka gane gudu ake sheƙawa da kai ba sai an je wajen da minti talatin ke zuwa a minti goma zaka fahimci haka da tuni ya gane cewar sun fa shigo cikin gari sun kuma kusa ƙarasawa MENTION ALIYU ANZA, sai da ya buɗe idanuwansa ya ɗago daga ringeshen da sauri ya bi hanyoyin da kallo sannan ya kalli Brs. Mukhtar da ɗan mamaki ya ce" Ina zaka kai ni?"
Brs. ya ɗago daga danna wayar da yake yi ya zuba masa ido shima ya ce" Gida zamu je mana."
Da ɗan mamaki AA ya ce" Gida? Wane gidan fa?"
"Gidan Aba mana, mention Anza." Brs. ya faɗa yana gyara zamansa da kyau dan ya ga reaction ɗin AA ɗin, ai kuwa Aswan ya tsare shi da wani kallo na tuhuma, sannan ya kalli dreban da kyau ya sake dubansa ya ce" Kai! Waye kai?"
Brs. Mukhtar ya ɗan yi baya kaɗan dan sai da Aswan ya raruko masa ido sosai kafin ya yi tambayar, a nutse ya ce" Ni ne lauyanka, sunana Barister Mukhtar."
"Na san wannan karatun, bayansa wani nake son sani, dalilin da yasa ka san gidanmu da kuma dalilin da yasa zaka ɗaukeni a haka ka kaini gaban Aba da Anna a haka?" Ya ƙarashe yana nuna jikinsa.
Hakan ya sa Brs. binsa da kallon shima kafin ya saki murmushi ya ce" Ina cike da mamaki, ina matuƙar mamakin yadda aka yi baka taɓa lafiyar samari uku marasa jin maganar anguwa da cikin gari ba, amma ya zamo a yanzu basu da magana sai ta makashin mahaukacin soja, ashe kaima kana tsoro? Ashe kana tsoron a ganka a haka kaima? Lallai ba zan so Samir ya san kaima da wanda kake tsoro ba."
Ɗan tsai Aswan ya yi yana kallonsa, a hankali ya tuna a inda ya ga fuskar, ƙwarai Yayan boys ɗin nan uku ne ko? Ƙwarai haka ya ji Chef ya faɗa a office ɗin sa a lokacin da yaron ɗaya ke cewa su tafi, sunayen yaran sun zauna masa daram a ƙwaƙwalwa, domin sun bashi nishaɗi sosai, bai san cewa zaratan samari irin haka zasu nuna tsoro haka ba sai yau, ga rashin ji ga tsoro, Dauda, Samir, nd Attahir.
"Uhum!" Ya ɗan fitar a hankali na murmushi a lokacin da ya maimaita sunayen a zuciyarsa, sai kuma ya sake kallon Brs. a tausashe ya ce" A kai ni gidana, Please."
Daga haka ya yi shiru, dan ya tabbata tunda ya san gidansu zai san nasa gidan, a ransa kuwa ƙara ayyanawa yake yi _" Ban ga dalilin da zai sa Aba ya ganni da wannan shigar ba ya yanke jiki ya faɗi, Anna kuwa ta tsine min kafin ta suma."_
Dan tsaf ranta zai bata ya zama dealer ɗin sholisho da su cocaine da ganja.
Shi kuwa barista ƙwarai ya yi mamaki da ya ce da shi please, nan take kuwa ya ba dreban damar a je ɗaya gidan, domin dama gida biyu aka basu kwatance, ya zata dai ko zai fi so a kai shi gidansu, ashe ba'a san aikin da ya aikata ba? Suna zaunen nan, nan da nan dreban ya bayyana gaban gidan, sai dai suna tsayawa tsaf aka nuna masu ba zasu shiga ba oga baya nan, sai da ya buɗe inda yake zaune ya fitar da ƙafarsa ya yi magana sannan aka buɗe masu suka shige.
Masu tsaron gidan suna ƙara cika da mamakin shigar nan ta ogansu domin nan da kwana bakwai da ya fita da su ya fita kuma ya dawo da su, gashi Oga na ta nemansa da sauran masu masa aiki saboda irin pression ɗin da oga ya saka masu a kan neman nasa ya zamo duk motsi sai wani ya bugo ya tambaya wai ko wulginsa babu?
Bayan ya sauka daga motar har ya juya ya fara takawa kuma sai ya ja ya tsaya, a nutse ya juyo ya dawo inda barista Mukhtar ke tsaye ya yi masa ɗan murmushi sannan ya miƙa hannu ya amshi katinsa da ya fitar tun a cikin motar yana niyyar bashi, a nutse ya ce" I'm sorry, sauri nake in je in ga my son da su mim, thank you Barista sai na kira."
Shi ma murmushin ya yi ya sara masa yana kallonsa har ya shige sannan ya koma motar ya zauna yana murmushi da girmama girman sojojin mu a zuciyarsa, ƙwarai yana ƙaunar soja, ya so ya saka kaki rashin lafiyarsa ta hana shi a lokacin da ya je gudu, ciwon hukar da ya gada ta hnna masa dogon zango a dole ya haƙura da mafarkinsa, a yanzu da yake kallon AA sai yake ganin burinsa ne ya tabbatar masa, soja mai hazaƙa, soja mai sunan soja, sojan da ya san me yake yi, sojan da baya tsoron mutuwa, sojan da zai yi yaƙi ko da dan gidan su ne dan ƙwatar haƙƙin ɗan ƙasa, dan haka dole zai girmama Aswan and dole zai zama abokinsa.
*Aswan* kuma sauri yake yi yana duba lokaci wajen shirin sa, amma a haka bai hana ya yi wanka mai sunan wanka ba da ya ɗauke shi minti talatin a baho yana ninƙaya, ya saɓa sabulu da turaruka na ruwa na wanka kala kala saboda yana jin kamar akwai datti a jikin sa, splash da body lotion ba wanda bai yi anfani da shi ba. Ta ɓangare ɗaya kuma yana ji wa zai je ya fara ganowa ne? Yaron sa dake kwance? Ko su Anna da yake mararin gani? Dan su Angel ya san suna tare da su idan ya ga su Anna ya gansu.
Daga ƙarshe dai haka ya gama shiryawa cikin wani ɗanyen boyl fari sol da ya masa kyau da gani bayan ya yanke shawarar zai fara ziyartar iyayen sa ya gaishe su tunda safiya ce har yanzu.
Kasancewar safiya ce kuma Aba ya makara da fita yau ya sa har ya same shi yana shirin fitowa daga falon shi Anna na bayan shi dan yi masa rakiya. Daga shi har su kusan a tare wani irin farin ciki ya baibaye su na ganin junan su bayan kwanaki musamman ma su da basu san ina ya nufa ba, ba tare da wata kara ko alkunya ba Aba bai tsaya jin komai daga gare shi ba ya riƙo kunnen shi ya murɗe cike da wata raunatacciyar murya yace "Kai jikan Anza, daga ina kake? Ina ka tafi? Ina ka je baka neme mu ba?"
Kallon Aban nashi ya yi da farin ciki yana murmushi ya haɗe hannaye alamar roƙo yace "Ka gafarceni Abana, ba zan sake ba daga yau, naje wani guri ne."
Sakar masa kunne ya yi yana tsare shi da idanu yace "Wani guri bashi da suna?"
Murmushi ya yi yana ɗan murza kunnen shi da ya riƙe bai ce komai ba, sai kuma ya saci kallon Anna da ya san rigimar sa da ita zata fi ta Aban, ɗan leƙa fuskar ta ya yi ta hanyar kautar da ganin shi daga kan Aba cike da rarrashi yace" Pardon ma prefere."
Kawar da kan ta tayi cike da shagwaɓa ta kalli inda Aba yake tace" *Aban Humed & twins*, ni zan koma ciki, sai ka dawo, Allah ya tsare."
Juyawa ta yi za ta koma nata ɓangaren, AA ɓoye dariyar shi ya yi wato Aban su ba nashi ba ko? Da sauri ya bi bayanta yana faɗin" Haba Anna, please..."
Juyowa ta yi ta nuno shi da yatsa tace" Ka biyoni zan wanka maka mari Aswan, ai kasan ba girma ka yi da hakan ba ko?"
Marairaicewa ya yi a tausashe yace" Na sani, amma ki yi haƙuri Anna, kin san adadin kewar ki da nayi kuwa?"
Aba da ya bisu da kallo yana murmushi ne ya dubi AA yace" Ina da magana da kai guda biyu mai mahimmanci, ina za ka sameni? Gida ko office?"
Juyowa ya yi da ladabi bayan ya riƙo hannun Anna ya hanata tafiya yace" Aba zan zo office ɗin, hakan ya yi?"
Jinjina kai ya yi alamar e sannan ya fice daga falon, hakan ya sa Anna take tafiya da son ƙwatar hannun ta shi kuma yake biye da ita yana ci gaba da rarrashi har suka isa nata falon na alfarma, nan suka zauna tare kan kujera mai zaman mutum biyu suna kallon juna shi yana rirriƙe da hannayen ta kamar za ta suɓuce masa.
Kallon fuskar shi ta yi sosai kamar za ta fashe da kuka tace "Aswan ina ka je? Dan Allah ka faɗa min me kake aikatawa? Gaba ɗaya hankalina ya kasa kwanciyar da lamarin shige da ficen ka, Aswan me ka ke aikatawa?"
Cikin rarrashi yana tattausa mata hannayen ta yace "Annata, ki kwantar da hankalin ki a kaina, ba zan taɓa yarda na aikata abinda zai ɗaga muku hankali ba, ki tayani da addu'a na kammala abinda na fara, in sha Allah nan da lokaci ƙanƙani za ki san komai Annata, yanzu dai ki daina hushin nan da ni."
Zuba masa idanu ta yi tana kallo ta sauke numfashi tace" Aswan, na yarda da maganar Safwan, sannan na yarda zai zama jikana tunda haka kake so, amma sau ɗaya kai ma ka yi abinda nake so mana."
Yana kallon cikin idanun ta yace" Me kike so nayi miki Anna? Ki faɗa ko menene zan yi in sha Allah."
Ba wata kwana kwana tace" Ka yi aure Aswan."
Ɗan kawar da kan sa ya yi yana yin murmushi irin na tofa! Hakan ya sa Anna sake zuba masa idanu tace" Aswan aure ne kaɗai abinda za ka yi ya baka nutsuwa ni kaina na ji na nutsu, ta ya hankalina zai kwanta bayan nasan baka kwana gidan ka ba kuma ba ka gabana, sannan baka da mata? Ka duba maganata mana."
Shiru ya yi kamar mai nazari, daga bisani kuma ya kalle ta yace" Anna, zan yi in sha Allah."
Haɗe fuska Anna ta yi tace" Hey! *Ɗan Aliyu*, kullum haka kake faɗa, ina binka ta lalama ne saboda bana so ka kaini magaryar tuƙewa da raina zai sosu akan maganar auren ka, idan haka ta faru cikin biyu za'ayi ɗaya ne, in ma ka yi aure, ko kuma ka canza uwa, na san kuma za ka iya samo uwar tunda har kana iya haifar ɗa ba tare da mata ba."
Miƙewa ta so yi tana son ya sakar mata hannaye, amma dake hankalin shi na neman tashi sai ya yi gaggawar riƙe hannayen nata yace" Please Anna, kar ce min haka, Anna, yanzu asibiti nake so na je na ga my boy, daga nan zan yi magana da likitan shi, Anna da zaran ɗorin da aka masa ya yi kyau zan fitar da shi kan maganar tiyatar sa, na miki alƙawari Anna da na dawo zan yi aure ba daɗe, amma kar kuyi hushi dani dan Allah, ni ne fa."
Yadda ya ƙarashe maganar da rarrashi sosai har da sumbatar hannunta na dama da ɗora kan shi a cinyar ta yasa ta yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ta saɓule hannun ta daga cikin nashi ta shiga shafa kan shi da gashi ke ta cika shi, a taƙaice kawai ta iya furta "Allah ya sa."
Sun ɗan jima haka tana shafa kan shi yana jin nutsuwa na sake saukar masa kafin ya mata sallama ya tafi asibiti.
Saida ya fara shiga wajen Dr. Siddik, bayan sun gaisa yake tambayar sa "Siddik ya ɗana yake? Jikin sa yana yin kyau?"
Da fara'a Dr. Siddik yace "Jikin ɗan ka yana kyau sosai, in sha ma zuwa yamma zamu sake ɗaukar hoto dan mu tabbatar da ɗori da muka masa yana warkewa, nan da kwana biyu zamu iya warware masa shi ma in sha Allah."
Murmushi ya yi shima yace "Akwai yiwuwar na fitar da shi kuma a lokacin?"
A tsanake Dr. Siddik yace "No gaskiya, dan bayan haka akwai wasu gwaje gwajen da zamu sake yi masa, sannan sai mun ɗauki a ƙalla wasu kwanakin muna duba ɗorin, kasan ɗorin cinya da wuya da ƙashin baya su suka fi komai wahala."
Tsare shi ya yi da ido yace "A ƙalla sati nawa zan ci gaba da jira?"
Saida ya ɗan yi tunani kafin yace "Ummm! A ƙalla sati biyu zuwa kwana ashirin haka."
Da rashin jin daɗi ya kawar da kan shi yace "Shittt! Har lokacin kuma ɗana zai ci gaba da zama cikin raɗaɗi? Sannan ba ya taka ƙafafun sa?"
Da kulawa Dr. Siddik yace masa "Haƙuri za ka yi, in sha Allah kamar gobe ne, dole sai mun bi wannan