Showing 321001 words to 324000 words out of 397328 words
wani hamshaƙin mai gidan kan sa.'_
Da wannan ta ci gaba da daddaɓata tsawon lokaci kafin ta kula da ɗinkin Maman dake kan kujera ta miƙe tana dubawa da yabawa Maman tana zuzuta akan dole gobe ita kaɗai za' a gani idan ta shiga taron nan tunda ai ba biki bane, Anna kuma duk ta gama shigar bikin ta tun a ranar da aka yi bikin. Sai dai rashin sani ya fi dare duhu, domin kuwa Anna ɗinkin da ta yi waccen karon ai na auren Bilal da Yusrah ne, manyan ɗinkuna ne ga manyan kaya suka kuma samu lafiyayyar fata, amma duk da haka Anna shirin ta da tanadin ta na gobe ne in sha Allah, gobe ne za ta yi shiga da za ta nuna ita ce uwar Aswan Aliyu Anza, sannan suna rana ne ta taron auren shi, dan haka ma duk wani mai ruɓaɓɓen tunani irin wannan mamaki ne zai haukata shi ko ya sumar da shi saboda ganin abinda bai yi tsammani ba.
*AA MENSION*
Jiki a mace ta gyara zamanta ta ɗaga kanta sama tana kallon clng ɗin falon da aka yi masa shima wani irin tsari irin na manya, ba ta san me yasa zuciyarta ke cike da tunani da damuwa na irin damuwar da ta gani a fuskarsa a kan maganar ba, so take yi in ma gidan kason zai mayar da su ya fito su je a yita ta ƙare kawai da wannan ƙumbiya ƙumbiyar, gaba ɗaya bata san dalili ba sai ta fi gane ace bala'i suka yi sosai da ya mata wannan tambayar da take ganin sam bata da wani matsuguni a duniyarta a yanzu, tunda ta yarda da maganar ba Bilal aka aura mata ba ai kuma dole zata yakice shi a duniyarta, ita da a yanzu idan ganin sa ta yi ya shigo takan rayawa ranta anya wannan zai so ta kamar yadda Bilal ya so ta? Anya zata samu haka kuwa? Ai kuwa tunda har take irin wannan tunanin bai dace ya yi mata irin haka ba, ko da yake shine fa, shine fa, babu abinda ya gagare shi sai addu'a kawai da haƙuri.
Yana shiga ɗakin da yake nasa ne kamar yadda aka tsara yanayin gini' gidan, suna da ɗakuna a falo kuma suna da a sama, sannan ɗakunan a buɗe saboda ko yau an zo an ƙara yin saukar Alƙur'ani sannan an yi gyara da komai da komai.
A hankali ya ƙarasa wajen gadonsa ya zauna ya ɗan lumshe idanuwansa yana sake sauke ajiyar zuciyar da ya ringa yi tun abinda ta faɗa yanzu yanzu a falo, _'Ya Allah, shekara da shekaru ban yi abin kunyar nan ba sai yanzu da na yarda na fa girma shikenan sai in zauna yarinya ƙarama na fitar da ni a hayyacina?'_ Ya ayyana a zuciyarsa yana rintse idanuwansa, yana jin wani irin nauyi da kunya na son luluɓe shi.
Ringin ɗin wayarsa ya saka shi buɗe idanuwansa ya shiga lalubawa a aljihun wandonsa yana tunanin ko wanene? Gannin sunan Aba sai da ya ji wata kunyar ta ƙara kama shi, shin yanzu me zai cewa wani gobe dan ya kare kansa? Ai bashi da abin faɗa wannan abin kunya ya aikata kuma babu inda zai kai shi ana kallonsa da shi ne ido da ido, sai dai baya jin ko yanzu idan ya ga wani jinsin da ya saɓa nata na yi mata magana ta bashi amsa in har zai iya cire kansa ya ƙyale, ya rab ka sanyaya min wannan lamari.
Ya ɗaga wayar a hankali ya yi sallama, Aba ya yi murmushi jin muryarsa ya amsa sallamar ya ce" Fatan kana lafiya jikan Anza?"
AA ya kasa amsawa dan ya tabbata zuwa yanzu ai Anna ta haɗa ɗa da ubansa ne, Aba ya sake cewa " Kai amsani mana, ina ƴata ne?"
AA ya buɗe idanuwansa ƙasa ƙasa ya ce"Tana falo Aba."
Aba ya yi murmushi ya ce" To haka ake yi ne jikan Anza? Ai ba a yin saurin yin fushi ko?"
AA ya ce" Aba, a yi haƙuri, bari in dawo da ita."
Aba ya ce" A'a, babu inda zaka dawo da ita, matarka ta yi zamanta Allah ya baku haƙurin zama da juna, dama ni na jima da yiwa Annarku maganar ya kamata ta ba namiji matarsa a zauna lafiya, ta ce sai ta sake yin wani taron, ita dai tana son yawon yin taro ta yiwu haihuwa bata isheta ba ina ga, yawwa kana ji ko? Allah ya baku zaman lafiya, a sassauta fushi a yi haƙuri kuma kar a saki a fara rayuwa da zargi, na tabbata mai hankali na baka, dan haka kar ka wani damu ka ji jikan Anza? Sai maganar takardun asibitin ka gama haɗa su?"
AA ya ce" Eh Aba, na gama haɗawa, saka hannunka ne kawai ake jira."
Aba ya ce" To shikenan, idan ka samu fitowa mu haɗu a asibitin yau in sake zagayen nan tare da kai in gani in har decision ɗin nan mai kyau ce cewar asibiti zai dawo hannunka har mu ga yadda hali ya bada, jikin nan na Hamat na bani tsoro, balle irin yadda baya magana ɗin nan, gani nake yi nima kamar wanda yake ganin mutanen ɓoye."
AA ya yi murmushi a nutse yace" Baya ganin komai Aba ciwo ne, Allah ya bashi lafiya, zan shigo in sha Allah."
"To ita matar jikan Anza ina zaka bar ta? Ko da yake na ga Annarku na waya da ko mai kitso da ƙunshi ta na cewa bari ta yi kiran ka su Abrar da tagwayen ta su je su wunin mata a yi mata ƙunshi da kitso ko me? Za ta yi kiran ka dai, ka ga in ka ga zata ringa tara maka ƴaƴan ta a gida ka ƙiya ka ji? Ka kore su kawai, dan babu wanda aka je aka hana rawar gaban hantsi balle wanda ya jima yana fama."
Kiskirim kawai AA ya yi ya rasa me ma zai cewa Aba sai da ya ga dama dan kansa ya kashe kiran, kuma yana kashewa kiran Anna na shigowa hakan ya sa ya dafe kai yana faɗin" Na shiga uku, yau bala'in ka ya janyo maka ka ɗauko masu ƴa zasu kasheka da ranka."
Ya ɗaga yana yin sallama, Anna ta ce" Kai ma amincin Allah ya tabbata a gare, ka bani ƴata."
A ɗan shagwaɓen da yake yi mata magana wasu lokutan yace" Anna, please fushi nake son yi mata kaɗan dan kar ta kuma yi masa magana a duk inda ta ganshi fa."
Anna ta ji tausayinsa ya kamata, dama wasu lokutan takan masa dariya idan ta ga yana faɗin Yaushe ma zai tsaya ya lalace ga abubuwa masu mahimmanci wai ya bautawa so? Ai gaskiya bai ce ba so ba amma shi ko soyayya zai yi ba zai yi ta bautawa mace ba gaskiya, sai gashi ko'ina ba'a kai ba halayansa da yake danne wa na son fitowa, ko da yake tunda ta san Yusrah bata taɓa ganin ranar da ya danne abinda ke ransa a kanta ba, duk wasu motsinsa idan tana waje tana hankalce da shi, sai ta yi murmushi kawai ta yi shiru, dan ba zata taɓa nuna masa ba domin zata so ko wa ya aura a rayuwa ya zamo ya riƙe abinsa da kyau ba tare da yana nuna haɗa su aka yi ba ko wani iya shegen dan ta san waye jikan Anza.
A tausashe ta ce" Haba mana jikan Anza, ai ba zaka iya raba tsakanin da ta haɗa ba, ita ma da ta ga haka gobe ai ba zata maimaita abinda ya faru ba, amma kuma abin ai duk bai kai na fushi ba ka ji? Ka yi haƙuri ko karyawa bata yi ba fa, ka ji?"
A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" To Anna."
Anna ta ce" Madalla da kai, kuma ka ga mai kitso zasu zo da yaran nan, dan su tayata shirya kayanta da kuma kitson sannan su mata girki, kuma nace kuna da buƙatar mai girkin da zata muku sati tana yi kafin masu aikinku su zo?"
A hankali ya girgiza kai ya ce" A'a Anna."
Anna ta yi ɗan shiru, sai kuma ta ce" To shikenan, sai sun zo ɗin."
Ya amsa da " To Anna sai na shigo, zan kawo son kamar yadda kika ce ɗin."
Anna ta ce" To shikenan, Allah ya yi albarka."
Daga haka suka kashe kiran, Anna na ayyana _' aAi zan ringa kiranta in ta ce min ayyuka ka haɗata da su zan hana ne gaskiya, dan ba zaka kaita ka jibga mata lalurorin da zasu sa ta zo tana tsanar auren ba gaskiya.'_
Abinci ya fara yi mata oder, saboda tunda Anna ta ce masa ba ta ci komai ba abun ya tsaya masa a rai, da ya tabbatar nan da minti arba'in da biyar zuwa ƙasa da haka abincin zai iso gidan kamar yadda ya buƙata sai ya fito daga ɗakin riƙe da wayar sa a hannu.
Kujerar da ya tashi ya gan ta zaune a ciki ta rafka tagumi, gashin kan ta ya fara kallo dake kwance a gadon bayan ta dunƙule, a hankali ya ci gaba da takowa har ya zo kujerar dake fuskantar ta ta ya zauna ya ɗan miƙe ƙafafun shi, hakan ya sa ta kalli ƙafafun dake sanye da safa kalar sararin samaniya kamar best ɗin shi sannan ta ɗan cira idanuwan ta ta kalli fuskar sa.
Fuskar dai a sake take ba wani alamar damuwa, amma da suka haɗa idanuwa sai ta ga ya wani yatsina baki tare da ɗauke kan shi ya mayar kan waya, duk sai ta sake takurewa ta tsura masa idanu na wasu sakanni da tunanin ko ya sake kallon ta ta tsokane shi ma su yi faɗa, amma Allah da ikon sa dake ya yi niyya kamar yadda ya faɗawa Anna zai mata hushi sai kuwa ya ƙi kallon ta saboda sosai ya ji jikinshi ya nuna masa tana kallon shi.
Su Manal ne suka fara ƙarasowa gidan, dake yana nan a ladabce suka gaishe shi har da Yusrah dake murmushin rainin hankalin su, masu lallen ma gaishe shi sukayi kawunan su ƙasa saboda kwarjinin sa da tunanin ko yana ma jin hausar saboda shigar shi da fatar sa bata sa sun yarda zai ji yaren su ba. Bai fi minti biyu ba kuma sai ga nocking ɗin mai kawo oder, a nutse ya je ya buɗe masa ya karɓa ya saka hannu ya biya shi sannan ya dawo falon, har gaban Yusrah ya zo ya tsaya ya dinga buɗe mata bayan ya kalli Abrar ya umarce ta da ta kawo masa plate da ruwa, ba musu ta miƙe ta je ta kawo, dukansu falon kallon shi suke har Yusrah da bata fahimci me yake shirin yi ba, saida ya gama sannan ya jawo center table ɗin nan sannan ya ranƙwafa kamar zai sumbaci kumatun ta dan daf da kunnen ta ne ya raɗa mata "Oya, maza ki cinye ki aje plate ɗin, idan kika raga wani abu kuma Y. Turaki ke da Allah."
Ɗan zaro idanun ta ta yi, sai dai ina tuni ya bar ta da kallon ƙeyar sa dan ya juya ya tafi ba tare da ya bari ta ga yanayin fuskar sa ba, numfashi ta sauke ta kalli su Nawal da suke kallon ta fuskokin su sai gumtse dariya suke yi, ai ko suna ganin ɓacewar shi suka bushe da dariya suna zolayar ta ashe soyayya ma suke sha da Akhi shine Anna ta ƙi ba su damar shiryawa a tsanake, bata kula su ba kawai ta gyara zaman ta ta fara cin abincin tana wa dukansu bismillah.
Shawarma Abrar ta ɗauka ta cika baki da loma tana faɗin "Yasin ba na ƙi ci ba saboda ko kari fa Anna bata bari mun yi ba."
Nawal kam da ta ɗauki cinyar kaza irin kcf ɗin nan ta kai baki ita ma tana cewa "To dama ai da gani ba dan ita kaɗai ya siyo ba, kai bism..."
Ganin shi tsudum a falon ya sa ta ɗauke maganar ta, kallon da ya jefe su da shi yasa Nawal ɓoye ƙafar kazar dake hannun ta bayan ta tare da yin gum da bakin ta kamar ba ta cin komai, Abrar kuma sarkin tsoron AA tuni ta wurgawa Manal shawarmar a saman rigar ta tare da saka kallabin abayar ta ta rufe bakinta idanun ta a ƙasa, dan ita ma sai ta ga kallon kamar na me ya sa suke ci mata abinci ne? Karon farko a duniya da tsoron Abrar ya so saka shi dariya irin ta ƙyalƙyalawa ɗin nan, dan haka ya yi gaggawar kama hanyar barin falon yana faɗin "Y. Turaki na fita, a mun addu'a?"
Juyawa ta yi ta kalle shi, wallahi sai ta ji ya sakata a kunya sosai, amma bata yi nauyin baki ba ta furta "A dawo lafiya mr. men."
Kamar an dakatar da shi sai kuma ya juyo da irin ya tuno wani abu ya nunota da yatsa yace "Amm..ɗazu kin kirani da Aban Haidar? Wane Haidar?"
Murmushi Yusrah ta yi ta saci kallon ƴan matan Anna da suka zuba mata idanu, saida ta dube shi sosai ta shiga buɗe bakin ta irin da raɗa raɗa tace "In ji twins wai burin ka ne ka yi wa Aba takwara, shine na tayaka fatan nima."
Murmushi ya suɓuce masa sosai saboda bai yi tsammanin haka ba shi ma, jinjina kai ya yi yace "Ok, ina fatan nan da wata bakwai ɗan Anza ya riƙe takwaran shi a hannu."
Nawal da ita ce mai jarumtar a ciki daɗi da ya kashe ta da fara'a sosai tace "I hope so Akhi..."
Duk da ta faɗa sai kuma ta rufe bakinta kanta ƙasa, saida ya ƙare mata kallo sannan ya juya ya fita bai sake bi ta kan su ba, ai kam falon kamar zai fashe dan ihu suka saka suna tsokanar Yusrah da ta kasa ce musu komai tana tunanin to nan da wata bakwai wa zai haifa masa takwaran na Aba? Ita ko Nabihat?
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
29/06/2024, 15:19 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*81*
A ƙofar gida da su Nawal suka bar Aba ya same shi yana ta ziga shayi, sannan ne Aba ya shiga tare da Safwan ya ƙara kimtsawa kafin ya fito suka nufi asibiti. Ko da suka je kamar yadda suka dan fara binciken abubuwan dake faruwa yanzu ma hakane suka ci gaba da yi, suna bin kowane office ne su haɗu da mai kula da shi su zanta sanna ya basu komai a rubuce, idan suka gamsuwa da aikin ka ne sai su fice suna maka fatan alkairi, idan suka ga wani abu da bai kwanta musu ba kuma sai su ɗauki komai su ajiye da zuwan zasuyi bincike sosai akan haka, suna so ne su gama da manyan ma'aikatan kafin su je ga ƙananan su.
Garin haka suka iso office ɗin Dr. Issa, tunda ya san da zuwan su hankalin shi ke tashe, dama tun ranar da ya ga AA ya fara zarya a asibitin sai yake ma asibitin zuwan asha ruwan tsintsaye, har mai gadi yake kira ya tambaye shi AA ya zo? Idan ya ce e sannan zai shigo bayan ya tafi, to kwana biyu bai zo ba sai Aba dake zuwa duba Dr. Hamat, shine yau suka kutso tare bayan ranar ma an ce masa sun zo kuma suna bin ofishin mutane.
Tunda suka shigo yake ta zufa yana sharewa yana yaƙar baki, amma abu ɗaya da yake da tabbacin shi shine ba zasu rabu lafiya ba gaskiya, haka dai suka zauna suna ta masa tambayoyin da suke ma kowa idan sun je, amma babban tashin hankalin shine yadda ya ga AA na ta wani haɗe fuska yana yatsina hanci irin kamar kana jin wani wari haka da bai maka ba, kuma sai ya ga ya kalli inda ba zai so idanun shi su kai ba bare ya zargi da wani abu.
Sai dai ina ya makaro, dan kuwa tsaf ya ga AA ya miƙe ya nufi inda gadon da dr ɗin ke duba majinyaci a tashin farko, ko da ya ja labulen dr Issa ya miƙe yana ƙara share gumin goshin shi da rashij gaskiya tsababa yace "Aaaa.mmm, yallaɓai! Ai da ka zauna ko? Ko wani abu kake da buƙata na sa a kawo maka?"
Wurin AA ya ƙarewa kallo, tabbas wari ne marar daɗin shaƙa a hanci kamar na gawa, a hankali ya ɗan sunkuya kamar zai yi ruku'i, wani shirgegen kwali ya gani, wanda kwalaye ne irin wanda ake tura saƙo daga wani gari zuwa wani ko ƙasa zuwa wata ƙasa, ɗagowa ya yi ya kalli dr Issa da ya shiga kalmar shahada a bayyane har Aba ya tsare shi da idanu sosai yace "Me ye