Showing 312001 words to 315000 words out of 397328 words

Chapter 105 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70004

Anna tace "Jikan Anza, matar ka ce fa."

Kamar yana gabanta ya shafa sumar kanshi yace "Sorry Anna, amma dai a faɗa mata, ban son abin nan da take wa yarona ko kaɗan."

Girgiza kai Anna ta yi tace "Na ji." Sannan ta kashe kiran, Yusrah d kunya ke hanata zama anan tare da su ta kira lambar ta madadin sai wani ya hau sama kiran ta, tana ɗaga kiran da ladabi Anna ta faɗa mata saƙon shi ta hanyar faɗin "Yusrah, wai akwai ecouteur ɗin Safwan ta tablet da ya bari anan?"

A sanyaye sosai Yusrah ta amsa da "E Anna, tun ranar da ya koma ya manta."

Anna tace "Yawwa, to ki sauko za ki bawa Dadyn sa ne ya kai mishi, yana falona yana jiran ki."

Saida Yusrah ta lumshe idanu kafin ta amsa da "To Anna, gani nan zuwa."

Yanke kiran Anna ta yi Yusrah kuma ta shiga inda indar inda zata saka kanta, tunda ya hauro mata ɗaki basu haɗu da shi ba, kuma ba ta daina hushi da shi ba, Nabihat ce ma dai ta fara gane takon ta take kuma so da fatan ta mata wani gangancin, amma shi ko? Ya Allah! Tashi tayi jiki duk a mace ta shiga canza kayan jikin ta daga riga da wando zuwa doguwar riga, saida ta shafa turare mai sanyin ƙamshi ta yana kallabin rigar sosai sannan ta saka takalmi flat kafin ta ɗauki earpeace ɗin ta shiga saukowa a nutse.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:55 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*78*




Duk da sun gaisa da aunty Fadima amma sai da ta sake yi musu sannu cike da kunya ta nufi falon na Anna, me Anna ta gani sai kawai ta kira sunan Yusrah, tana juyowa ta amsa da "Na'am."

Anna tace mata "Kinga zo, Manal tana nan madafa za ta ɗaukowa Akhin su abinci, ki karɓo sai ki tafi mishi da shi."

"Lahaula wala ƙuwwata illa billah!" Shine kaɗai abinda Yusrah ke faɗi a ran ta, da wannan matsananciyar kunyar ta sake kama hanyar madafa, tana shiga ta samu Nabihat tana rarrashin Manal akan ta bari zata zuba ta kai masa, ita kuma umarnin Anna ne basa yarda su kauce shi, shiyasa ma ta ƙi bata har Yusrah ta same su, Yusrah na isa gare su bata ko kalli Nabihat ba ta dubi Manal tace "Yawwa kin zuba ne?"

Kallonta Manal tayi tace "E, ko zaki karɓeni ne?"

"Haka Anna ta faɗa." Cewar Yusrah tana duban Manal ɗin ita ma, sai kawai Manal tayi murmushi tana aje robar ruwa da ta jus ɗin da ta san yana so tace "To Alhamdulillah, wataƙila ban da rabon shan faɗa ko duka ne, tunda mai guri ya zo ai sai mai tabarma ya naɗe."

Ita fa sam ba ta faɗi haka da wata manufa ba ko dan Nabihat, kawai ta yi ne a zuwan tunda ga Yusrah to ita me zai kaita wurin shi, amma sai Nabihat ta bita da wani mayataccen kallon tsana da jin haushi har Manal ɗin ta kusa ficewa daga madafar bata ko san tana yi ba.

Yusrah kuma a nutse ta ƙarasa wajen farantin mai kyau da kwalliya ta kai hannu ta riƙe mariƙi ɗaya Nabihat ma ta riƙe ɗaya hannun farantin, hakan yasa suka aikawa juna wani irin bahagumen kallo mai cike da tambayoyi, cike da tsiwa da zauncewa Nabihat tace "Me za ki yi to? Ke baki sameni anan bane? Ko kina nufin ke za ki kai masa abincin?"

Da fari da mamaki ta kalleta, sai kuma ta saki wani malalacin murmushi ta gyara tsayuwar ta tace "Da na fara tunanin amsar da zan baki, sai kuma kika amsawa kan ki da kan ki."

Wata muguwar harara ta bita da ita tace "Nufin ki ke zaki kai masa? Dan kawai an ce ke matar sa ce?"

Da wani ƙayataccen murmushi Yusrah ta amsa mata da "Kuma duniya ta shaida hakan ba, a yanzu ko ƙaramin yanzu zai bayar da shaidar ni nafi kowa lasisin ba wa *jikan Anza* abinci a yanzu, dalilin ma kenan da ya sa Anna tafi ganin cancantar ni na zo na kai masa, dan hurumina ne ba na kowa ba."

Ɗaya hannu tasa ta riƙe farantin da kyau sannan ta fizge shi a hannun Nabihat ɗin, a nutse ta raɓata ta wuce za ta bar mata madafar, Nabihat kuma da takaicin maganganun Yusrah ya rufe ta sai kawai ta dafa kafaɗar Yusrah ta baya tana faɗin" Har ke wacece da zaki gaya min haka? Auren haɗin? Auren je ka nayi ka? Auren da nake da tabbacin zai iya sauke shi a kowane lokaci? Har a kan shi ne zaki dinga cikawa mutane baki?"

A hankali Yusrah ta juyo tare da aje farantin saman desk ɗin babba mai kyau, sannan ta saka hannun ta na dama ta ɗauke hannun Nabihat daga kafaɗar ta sannan tace" Ya zama na ƙarshe da zaki sake kawo hannun ki a jikina, sannan aure da kike magana, ina ga da ya so tsinke igiyoyin ai bana jin ko Aba zai iya dakatar da shi, sannan daga ƙarshe...idan kin duba dukanmu ni da ke auren haɗin ne ai, dan ko ke da aka saka muku ranar ban ga alamar yasan da zaman ki a rayuwar sa ba."

A hassale sosai Nabihat tace" Ƙarya kike wallahi, Yaya AA ya san da zamana tunda har ya kai kuɗin auren sa gidan mu, ke kuma fa?"

*Yunwar* da ta addabe shi ce ta sa ya buɗo ƙofar madafar daga falon Anna dan tafi kowace hanya sauƙi da niyyar yana haɗa idanu da Manal ya ce _'Dan uban ki sai yunwa ta kasheni za ki bani abincin?'_

Amma yana sako kan shi sai ya ci karo da ƴan mata na shirin dambacewa a kan shi, da fari dariya ya yi yana girgiza kai har ya kalli fuskar shi ta madubin ƙofar falon, ya shafa gemun shi ya ɗagawa kan sa gira cike da shaƙiyanci yace "Ɗan Aliyu kenan, ashe matsayin ka har ya kai haka kaima? Yau dai na farko zan ga yadda Y. Turaki zata nuna haukanta ga wani ba ni ba nima nayi kallo."

Gyara tsayuwa ya yi, lokacin da Yusrah ke tabbatarwa da Nabihat ita ke da lasisin bashi abinci, sai kawai ya yi murmushi cikin raɗa yace "Gaskiya ne, ke kike da haƙƙin ciyar da ni yanzu."

Amma saboda iskanci da Nabihat ta jera mata tambayoyi akan auren haɗin za ta cika baki? Sai kuma ya taɓe baki ya yatsina fuska yace "Gaskiya kika faɗa, auren haɗi ne fa."

Har yanzu da Nabihat ta bata amsa da yasan da zamanta tunda ya kai kuɗin auren ta, cike da tabbaci shima ya ɗaga kai yace "Gaskiya ne, yo jaka ɗari biyar an banza Y. Turaki da zan manta ta alhalin ba aiki aka min ba, ina sane da kuɗina wallahi."

Wata irin dariya Yusrah ta yi da ta saka shi darawa shima yana ayyana _'Kai Y. Turaki duniya ce wallahi, wato ita kowa ma addabar sa take yi.'_

Yusrah kuma tana kallon Nabihat tace" Ban taɓa sanin cewa baki karanci zaman duniya ba ai sai yanzu, ashe dama abinda ya faru a kaina ba darasi bane gareku ƴan baya? Aure ma an ɗaura shi ba'a tare ba aka samu matsala, bare kuma maganar kai kuɗi, sannan kinsan da akwai wanda yake yadda kuɗi ninkin ba ninkin wanda aka kai gidan ku, sannan ya manta a kwanaki ƙalilan? Ƴan mata, ba kai kuɗi gidan ku ya nuna mahimmancin ki a rayuwar sa ba, da auren haɗi, da auren je ka nayi ka, da auren sai dai a kai gawata, ai duk ana kai musu kuɗi suma, ya kamata ki sake bibiyar lamarin da kyau, kin ji?"

Yana gefe ya saki murmushi yana shafa sumar shi yace" Gwara da kika faɗa mata gaskiya, dan wallahi ko ni na sha yada kuɗi musamman ma waya, amma haka nake haƙura bare wata ɗari biy."

Bai ƙarasa maganar sa ba ya ga Yusrah ta nuno Nabihat da yatsa a kausashe sosai tace" Kinga, baki san wacece Yusrah ba, shiru shirun da nake miki dan mu zauna lafiya ne ba dan ina tsoron rigima da ke ba, amma idan tashin hankali kike so mu yi da ke, ki jira na lokaci kaɗan a ɗaura auren ki da shi ki sameni gidan, a wannan lokacin zan buɗe miki shafi-shafi na karatun sanin wacece ni, idan kuma hakan ya miki nisa, to ki tambayi shi *mijin nawa* ya faɗa miki wacece ni, sannan ya faɗa miki inda muka fara haɗuwa da yadda haɗuwar tamu ta kasance, amma kar ki sake min wannan ɗanyan kan a gidan surukaina, dan ba lallai na iya riƙe kaina daga gotaki ba."

Sai kuma ta nuna mata abincin da ta ajiye tace" Ga abincin, zan baki duk abinda na mallaka idan har kika kai masa ya kuma karɓa da farin ciki ya ci, akasin haka kuma za ki gane wacece ke a gurin shi."

Rai ɓace ta juya kai tsaye ta ƙofar da ma'aikata ke shigowa, tunanin ta yana falon Anna ba za ta bi ta can ba, haka ma ta babban falo tunda su Anna na nan za su tambaye ta abincin fa? Tana ficewa Nabihat da ta zaro idanu saboda wani shakkun lamarin Yusrah da ya ɗarsu a zuciyar ta na tunanin a ina suka fara haɗuwa? Sun san juna dama? Me ya haɗa su? Wacece ita? Me ye tsakanin su kafin yanzu? Me ya sa suke rainawa mutane hankali? Wannan tashin hankalin ya sa har AA da ya auno mata harara yana ayyana _'Jarababbiya, yanzu ta hassala ta tafi kenan? Ke ma dai Y. Turaki da neman magana wallahi, mtssssss! To yanzu ni ɗin wani cake ne da za'a dinga rabona ina tsaye kamar wani gidan gado? To naga mai ɗaukata a cikin ku.'_

Shigowa ya yi madafar kai tsaye ya nufi inda abincin yake, wato ba ma wanda ya damu da cikin shi? Sai faman faɗan su kawai suke yi. Wani kallo Nabihat ta shiga bin shi da shi da tarin tambayoyin fil, duk da ya gani sai ya ɗauke kai yana ayyana _' Aikin banza, ni kika iya tsarewa da idanu ko? Da ki musawa Y. Turaki mana kiga yadda za ta tayar da aljanun ta a gaban ki, ta bubbugaki a ƙasa a banza wallahi ba abinda ya dameni.'_

Ɗaukar farantin ya yi har ya fara takawa sai kuma ya dakata ya juyo ya kalli Nabihat da idanunta suka fara cika da hawaye, ba tare da ya damu da haka ba yace "Kina ji ko? Idan za ki jata rigima ki dinga bari sai ta ci abinci, yanzu haka ba ta ci komai ba, kuma haukanta zai sa ta ƙi ci saboda an ɓata mata rai, nima kuma yanzu dole na je gaban ta na ci dan ta tabbatar ba'a gaban ki na ci ba."

Ko da ya gama faɗa mata haka ya sake juyawa ya koma falon Anna sannan ya fita ta ɗaya ƙofar ya haura sama dan zuwa ya zauna gaban Y. Turaki ya ci abincin, shi wallahi wannan jaraba ma ya rasa da me ta yi kama? Yanzu kenan haka da zai yi dan kar a yi tashin hankali ne? Ko dan yana tsoron ran ta ya ɓace game da shi? Mtssssss! Allah yana gani wannan ne dalilin da ya sa ya jima bai shiga sabgar mata ba, ina zai iya da wannan kulafuci? Kawai namiji har namiji garƙaƙa da kai amma ka dinga abu kamar kana tsoron mace, macen ma ƙaramar yarinya kuma ba uwar ka ba.

A matuƙar nutse ya buɗa ƙofar ɗakin yana wani shan ƙamshi ya shiga sannan ya maida ƙofar ya rufe, kallon juna sukayi da ita tana ninke sallaya da ta bari, kallo ɗaya ta mishi ta ɗauke kan ta taci gaba da abinda take yi, shi ma kuma kallo ɗayan ya mata ya ja kujerar dake gaban madubi ya zauna tare da ajiye farantin a gaban madubin sannan ya ɗauki plate ɗin ya tallabe a tsakiyar tafin hannun shi ya ɗauki cokali ya fara ci da bismillah. Ita kuwa gaba ɗaya sai ta takure ta zauna can gefe kanta ƙasa bata ce da shi komai ba, shi ma haka har ya gama ya miƙe ya fita yana wani shan ƙamshi ya bar mata farantin a nan ya sauka ya nufi ɓangaren Anna ya mata sallama ya yi tafiyarsa.

Ajiyar zuciya ta sauke ta sake duban farantin sannan ta miƙe ta ɗauka ta nufi ƙasa dan maidawa, a zuciyarta tana tafe tana tunanin shin me yasa take jin tsana mai girma irin wannan a cikin zuciyarta na Nabihat? Me ta tsare mata ne? Can kuma sai ta ɗan ɗage kafaɗu a cikin zuciyar nata ta ba kanta amsa kamar haka _' Meye ma zai hana in kasa jin haushinta bayan kullum cikin nemana da fitina take yi? Ina jin haushinta ne dan kawai ta zamo mai neman fitina, daga wannan ba wani abun.'_

*Nabihat* kuwa da ƙyar ta iya kai kanta ɗakin ta
hankalinta ya tashi matuƙa da abinda ya faru, a gaban idanuwanta ya yi haka dan kawai suna faɗa da Yusrah? kenan Yusrah ta san ba son ta yake yi ba? Kuka ta fashe da shi ta ɗora kanta a saman gadon ta tana dirzawa kamar ranta zai fita, wallahi bata san idan har aka bata wuƙa ko zata iya ƙin kashe Yusrah ba, ta tsaneta ta tsaneta ta tsaneta, gashi mamanta da ta yi kiranta shekaran jiya ta ce wai babanta ya ce maza ta dawo, kar ta saki ta dawo ta faɗawa Aba tana son zama babanta ya ce ta koma ta tabbatar shi zai ce masa shi ya ce ta zauna, shin ya ya zata yi ne? Cewa take yi ta yi yaƙi ta ƙwato AA, yaƙin yi take yi tun ƙarfin ta amma abin ya ci tura, inna lillahi! Ina zata saka ranta ne? Damuwar nan ta sa ta yi kiran mahaifiyarta, sai dai a yau ɗin ma maganar ɗaya ce dole ta yi haƙuri ta yaƙi AA, a yau ɗin ma ta ƙara kwaɗaita mata cewar idan bata yi yaƙi ba ba zata iya samunsa ba, ta nuna mata namiji mai tsada ai dole a sha wahala a kansa, ta faɗa mata tana cikin yaƙin nema musu hanyar da zai saki Yusrah cikin ruwan sanyi ba sai ta sha wahalar zama da ita ba, dan haka kar ta damu kanta, da wannan ta yi zamanta bayan ta ɗauko cornflask da madara da jus a ɗakin ta ya zamo ta yi niyyar zamanta ba zata je ko ina ba balle har su ɓata mata rai, kuma zata yi nesa da Yusrah dan wallahi tana ji a ranta tana iya sukar Yusrah da wuƙa ta kasheta ko ranta zai huta.


*WASHE GARI*


Yau ma Yusrah na kicin tana aikinta hankali kwance kasancewar bata zuwa aiki dole ta auri shiga kicin dan bata iya zaman nan na waje ɗaya ba, gashi yau asabar ce, kowa na gidan ban da Aba da ya fita da sassafe ya je asibiti, ita kuwa ta sauko ƙarfe tara ta shiga ƙoƙarin yin donut dan ta tabbata zasu so shi, balle idan ta masa haɗi kala kala na su madara da chacolate.

Sai da ta gama fitar da komai sannan ta shiga zuba fulawar bayan ta buɗe ta daga gidanta, irin fulawar nan ce ta cikin katan da leda a ciki wacce ke ɗauke da date na expear, bata da komai na datti, lufluf haka take a hannu da ido, shi yasa ana zuba ta ake yin anfani da ita hankali kwance, a nutse ta saka awon duka kayan buƙata ta yi mata kwaɓin daidai misali ta ɗauko leda fara ta rufe ga da ita ta ɗauka zata kai waje daidai shigowar Nawal tana hamma zata yi wata maganar ta fasa ta bi Yusrah da kallo ta ce" Ma sha Allah dear, kin ga yadda ɗinkin nan ya karɓeki kuwa? Wallahi sai na yi irin sa, iyeah, ɗaurin ne ma ya hau da ɗinkin ma sha Allah."


Yusrah ta yi murmushi tana faɗin" Kin ga, haɗa kayan jus ɗin nan ki markaɗa ki kai frij, sannan ki zo in baki aiki malama, ɗinkina kuwa na ƙi ba za'a yi irinsa ba."

Ita ma ta yi dariya tana faɗin" Wallahi zan ce maki aunty idan baki bani ba."

Yusrah ta fice tana girgiza kai tana murmushi ta ƙofar baya ta kicin ɗin ta fita can fili tana neman rana saboda ta ajiye fulawar ko ta taso da wuri dan su yi su gama kafin Anna ta sauko daga ɗakin ta, ajiyewa ta yi ta ɗago tana ɗan duban wajen rana da miƙa hannunta dan ta ji ko tana da zafi yau.

Dubowar da ta yi gabanta idanuwanta suka sauka a kan Bilal da ya fito daga motarsa ya ganta shi ma sai ya samu kansa da ɗan zuba mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login