Showing 69001 words to 72000 words out of 397328 words
dan ya rabu da kai lafiya ne, amma akwai mafita ɗaya."
AA dai kallon shi ya ke a wani lalace, ɗorawa ya yi da" Alhaji Suraj Sidi Kofa, shine kaɗai idan ka tunkara za ka san komai da kake son sani har ma wanda baka san kana so ka sani ba, sai kuma shi yanzu..."
Shirun da ya yi ya sa AA yace" Uhummm?"
A tausashe ya ɗora da" Ba za ka iya ganin shi ba gaskiya."
"Saboda me?" Ya tambaya da gatsali, amsa ya bashi da "Alhaji Kofa ai yanzu kusan satin sa uku kenan yana babban prison ɓangaren sashen manyan miyagun laifuka, ba'a ganin shi, ba'a waya da shi, hatta ɗan sa ko mata babu mai ikon ganin shi a wannan sashin, a taƙaice dai yana cikin tsatsauran tsaron da mai kai masa abinci ma sai dai ya tura masa ta ƙasan kejinsa, ba connection tsakanin wani da Kofa a yanzu dai, kaga kenan ba zai ganu ba."
Shi ba tsaron bane ya bashi mamaki dan ya san da wannan tsaron, kuma ana yin sa ne ga mutumin da laifin kisa ko fasa ƙauri na miyagun makamai ko ƙwaya ya tabbata a kan sa, ko wani babban ta'addanci irin na fashi da makamo da sauran su, to wanne a ciki Uncle Kofa ya aikata? Mutumin nan na hannun daman mahaifin sa ne, sannan shi ma mai kuɗi ne tun asali haka ya san shi, to wane haramtaccen kasuwancin ya yi da ta kai shi ga babban prison a sashen manyan laifuka? Kallon Isoufu Hassan ɗin ya yi yace "Me ya aikata?"
Wata irin dariya ya yi tare sa girgiza kai yace "Kamar yadda na faɗa maka, lamarin nan da sarƙaƙiya yake sosai, ba zaka iya jin komai daga bakina ba."
Miƙewa AA ya yi da yanayin ɓacin rai yana kallon shi yace "Zan ji wani abu daga bakin ka ko ba yau ba ɗan Hassan, dan ina mai tabbatar maka nan kusa zan ga uncle Kofa."
Murmushi Isoufu ya yi yace "Fatan nasara." Dan ya san a dokance ma lauyan Kofa sai ya bi wasu dokoki da ƙa'idoji kafin yake iya magana ta minti biyu zuwa uku da shi, ba wani farar hula ko mai saka kaki da zai ga Kofa a inda yake saboda tsaro, sai dai idan gwamnati ce ta bayar da izinin a gan shin.
Tun a mota ya gama tunanin yadda zai ga Uncle Kofa, sai dai matsala ɗaya shine dole sai ya samu sahalewar wani babba na ganin shi idan ya je prison ɗin, kuma tabbas Chef ba ya da wannan ikon sai dai ya nema masa alfarma, gashi shi kuma aikin sa na sirri ne, idan suka nemi wannan izinin to fa shakka babu wasu daga sama za su san me zai je yi a gidan yarin, idan aka sani kuma za'a shiga tamtama saboda ya kula dai lamarin sarƙaƙiyar sa ba kaɗan bace, dan haka kawai tun yana a hanya ya kira Chef akan ko yana gida ya same shi yanzu? Sanin AA bai da shamaki da gidan sa ya sa ya ce e yana gida har ma yana shirin kwantawa saboda yau ya gaji sosai, da taƙaitacciyar amsa ya ce gashi nan zuwa sannan ya kashe wayar.
Yana isa gidan Chef 11:00 har ta ɗan wuce da kaɗan, kai tsaye babban falon su na nan ƙasa ya same shi, shi ma bai jima da saukowa ba ya umarci yara da su je su kwanta zai yi baƙo, Nabihat ce ma da ke kallon film ɗin da take so ta turo baki tace "Abba wane irin baƙo kuma yanzu cikin dare? Kallo fa muke."
A hassale yace "Ke za ki tashi ko sai na taka ki, AA ne zai zo ya same ku nan bai min kallon da ban fahimce shi ba."
Tunda ya ambaci sunan AA Nabihat ta dai hau saman ne amma tana laɓe inda za ta ga shigowar shi kai har ma da zaman shi, dan duk kujerar da zai zauna tsaf za ta ƙura masa idanu... Hakan ce kuwa ta faru, gaba ɗaya AA bai ɓoyewa ganin ta ba har ya zauna kan kujera irin baki bakin nan sannan ya tangale guiwoyin hannayen sa da na ƙafafun shi ya haɗe tafukan hannayen shi yana kallon Chef ɗin da ke sanye da doguwar farar rigar bacci yace "Aba, ka yi haƙuri da zuwana yanzu."
Murmushi ya masa yace "Ba wani abu, ina fata dai lafiya?"
Ba tare da ya daina kallon shi da mamamtsa hannayen shi ba yace "Lafiya amma ba ƙalau ba, Aba ka san da Uncle Kofa yana prison?"
Ƙura masa idanu ya yi sosai yace "Na ji labarin AA, sai dai ban samu tabbacin hakan daga bakin wani ba, gashi kuma babban prison yake ba damar ganin shi."
Iska ya feso daga bakin shi yace "Aba, akwai wasu abubuwa dake faruwa ba daidai ba, a ɗan binciken nan da na fara da bai fi sati ba, na gamu da abubuwan al'ajabi da ban mamaki iri-iri, mutum na ƙarshe da zamu samu makullen buɗe wasu sirrikan da nake nema, shine uncle Kofa, na gama tsara hanyar da zan gan shi, taimakon da za ka min Aba shine sama min hanyar da zan ga uncle Kofa idan na shiga prison."
Da mamakin lamarin ɗan nasa ya ɗago daga kujera yace" Amma AA ai ba'a zuwa ko da ziyara, idan ma kaje ba zasu bar ka ba haka za ka dawo, ta ya kenan za ka shiga har ka gan shi?"
Wani shaƙiyin murmushi ya yi yace" Laifin da ya saɓa doka zan aikata, kawai ka bani tabbacin za ka min hanyar da zan ganshi idan na shiga, ni kuma na maka alƙawarin zuwa daren gobe za ka ji labarin ta'asar da nayi ya karaɗe gari."
Girgiza kai Chef ya yi da yanayin tsoro yace" A'a fa AA, bana so ka aikata abinda za'a zo a buga ka a jarida, me za ka aikata?"
Zuba masa idanu ya yi kawai bai ce komai ba, dan haka Chef yace" Ba za'a rasa yadda za'ayi ba AA, sai dai ina tsoron abinda za ka aikata, AA kai fa yanzu babban mutum ne, sannan Alhaji yana shirin hawa wani matsayi da yanzu duka gidanku idanuwan mutane akan ku yake, sai kana kulawa fa."
Murmushi ya masa yace" Kar ka damu Aba, akan aikina nake, ko da an zageni a farko, daga ƙarshe dai za'a yaba min idan an gane wanene ni."
Jinjina kai Chef ya yi yace" Shikenan, fatan nasara son, in sha Allah ni kuma zuwa safe zan yi magana da mai alhakin kula da tsaron ƴan gidan yarin, za ka ga Kofa idan har ka shiga da sunan jami'in bincike na sirri."
Sahihin murmushi ya qaki yana miƙewa tsaye yace" Na gode Aba."
Shi ma miƙewa ya yi ya bishi da kallo bayan ya furta masa sai da safe, saida ya ga fitar shi daga falon sannan ya juya dan haurawa sama, sai lokacin Nabihat ta tashi da gudu ta shige ɗakin baccin ta tana dariyar jin daɗin ta ga AA dai, tana shiga ɗakin ta faɗa kan gado ta dafe ƙirjin ta tana rarraba idanu, sai kuma ta saki ƴar dariya tace "Allah ka nuna min na mallakin bawan nan naka, Allah ka sa shi ɗin mijina ne ni kuma matar sa ta har abada, Allah ka sa guy nan nawa ne ni kaɗai har a duniya."
*AA* kuma da ya fita bai san da wata Nabihat ba ma, kai shi fa a jadawalin sa sam babu mace wallahi bayan ƙannan sa da Annar sa, shi kan shi zai zo ya samu lokacin fara kula su, amma idan ya tuna hayaniyar su da yadda suke gwara kan jama'a suke kuma alfahari da hakan, sai ya ji kawai ma wasu mazan ai ba da aikin da ya shagalar da su ne shiyasa.
Asibiti ya wuce, anan ya samu Aba ma ya zo duba Safwan, sai dai har lokacin bacci yake yi a nutse bawan Allah, dake akwai wanda zasu kula da Safwan sai kawai ya ga Dr. Siddik ya faɗa masa zuwa safe wasu rahoton lafiyar na Safwan zai fito sai su ga abun yi in sha Allah.
Haka su Anna suka tafi gida amma AA ya ce zai ɗan zauna kafin ya wuce gidan, sai dai suna tafiya ba jimawa ya bi bayan su zuwa gida, har wajen parking ya ajiye motar sannan ya shiga ciki...
Kayan shi ya fara cirewa ya shiga ban ɗaki, dake a buɗe ya bar ƙofar su Mim da Angel na tare da shi, man kai da ba ya anfani da shi ya ɗauka ya shafa a kan shi har zuwa gemu, asalin sa dama na gashi ne ya yi sulbi da santsi, sai da ya shafa ya bar shi na wasu mintuna, wanka ya yi gaba ɗaya ya tsane jikin shi, ai kuwa sai ga tsili tsilin gashin kan shi da ya fara fitowa ya yi wani irin mummurɗewa duk ya kwanta saboda sulɓi, haka ma gemun shi kamar dai zai kama shi ya masa kitso, haka ya kama gashin nashi na kai ya dinga ƙara mummurɗe shi yana yin kamar kitso daga gaban in da ya fi yawa.
Wata ƙaramar aska mai kaifi ya ɗauka dake cikin box ɗin kit na sol de janeiro, ƙara matsanta fuskar shi ya yi ga madubin kawai ya sa askar tsakiyar girar sa ya ɗan yi wata tsaga, ma'ana ya aske gashin wurin tamkar ya yi hanya. Fitowa ya yi daga ban ɗakin tare da su Mim dake ta ƙuriniyar su ya fara shiri cikin kayan da shi kan shi ya san idan ba aiki bane bai iya saka su.
Cikin ƙanƙanin lokaci AA ya fito sak wani ɗan daba, ɗan daban ma irin riƙaƙƙun nan wanda kana ganin su jikin kake shaida su wanene su, baƙin wando ne jikin shi na jeans irin kamammun nan masu matse mutum sosai, gashi da wani yaga yaga a cinya da guiwa, sai jar rigar t-chirt da ta matse shi ita ta fito masa da duk damatsan shi lafiyayyi, takalmin shi ma ƙafa ciki ne irin masu zane zanen nan. Fitowa ya yi daga gidan ya shiga motar sa wacce kusan kowa ya san shi da ita, saida ya yi nisa ya tsaya bakin titi wajen wani mai shago, kasancewar yana siyar da madarar raƙuma ya sa suka saba sosai dan yana yawan siya, makullin motar ya bashi ya ce akwai in da zai je.
Daga nan ƙasa ya ɗauki hanya ya nufi irin unguwannin nan da ya sa dole ake baza jami'ai idan dare ya yi saboda wajen akwai manya, yana karya kwanar doguwar hanyar nan tun daga nesa ya hangi wasu jami'ai biyu, murmushin shaƙiyanci ya yi tare da saka hannu aljihu ya ciro sigarin da mutumin nan ya siyo masa ranar bai sha ba sannan ya kunna ta yana tunkarar su...
Kafin ya isa gare su ɗaya daga cikin jami'an ya hau moto har da saka hular kwano sannan ya nufo inda AA yake da alama gida zai tafi ya sauka daga aiki, da gangan AA ya dinga tare mutumin nan har saida ya tilasta masa tsayawa a zafafe yana faɗin "Yau ga buru'ubar banza, kai wace shegiyar ce ka shayo yau?"
Ya faɗi haka yana taka birki, sai kuwa AA ya ƙara tsaya masa a gaba yana cire makullin babur ɗin shi cikin wata irin muryar layi kamar wanda ya sha wani abu sosai ya maku yace "Ƙaramin ɗan iska, ku ba karyar iskanci kuke yi ba, abunda kaina yake ɗauka idan ka ce ka jaraba ɗauka a kan ka a sakan ɗaya kan ka zai fashe."
Makulin da yake shirin cirewa jami'in ya rike, hakan ya sa AA shima riƙe makulin da kan babur ɗin tamau, jami'in nan ya jinjina da niyyar ƙwata da ƙarfi amma ya ji ba wannan alamar, sai ya tangale moton ya sauko ba tare da ya saki hannun AA ɗin ba yana faɗin "Oh! Haka ka ce? To yau ko za ka gane kai ƙaramin ɗan iska ne, yau ka sakarcin banza, kai jami'in za ka ma haka? Na ga uban...sai na ga ubann, za ka saki ko sai n..."
Duk yana rarrabe maganar ne saboda da ƙarfi yake son ƙwatar makulin amma AA da fari sai ya mayar da shi shashasha dan bushin leda kasuwa, saida ya ga ya ƙara jan ɗamara ne ta ƙwatar zai yi kaɗai AA ya masa wata irin hankaɗa ta hanyar murɗa hannun mutumin, sai kuma ya bishi da wani zazzafan marin da ya fi kama da bugu irin na sosai ɗin nan da ya saka jami'in yin wata ƙara ƙara ihu ihu ya durƙushe, amma fa dan jaraba bai saki hannun AA ba, hakan ya sa AA jawo hular kwanon dake kan shi ya ɗaga da niyyar maka masa yana faɗin "Dan kutumar ubanka ba zaka saki ba, ku uban ku ne ya haifemu da kuke mana fin ƙarfi, ku kuma ku ce ba zaku bamu aron taku..."
Saida ya maka mishi hukar kwanon sannan ya ƙarasa faɗin "Kadarar ba, shege kai." Kalaman shi dai na ƙarshe wannan jami'i bai ji su dan bai san inda kan shi yake ba saboda jinin da ya gabce masa a gefen kan shi kusa da kunne, wuya ce tasa ya saki makullin ya dafe kan shi yana wani irin birkiɗawa a ƙasa, sunkuyawa AA ya yi ya ɓalle ƙaramar bindigar jami'in dake rataye a kafaɗar shi kasancewar babba ake basu saboda tsaron da suke yi sannan ya laluba aljihu ya ɗauki ID card ɗin shi ya haye babur ɗin ya bar shi nan kwance.
Ta inda ya hangi ɗaya jami'in ya nufa, saida ya kai kusa da shi yana tsaye yana ta sintiri riƙe da bindigar shi irin ta waccen kawai AA ya harbo masa ƙafa duk da bai same shi ba yana ɓaɓaka wata dariya yace "Shakaran banza, je ka kwashi gawar ɗan uwan ka."
Ya faɗa yana wucewa ya bar jami'in da kallon bayan shi yana so ya gane wai babur ɗin abokin aikin shi ne ko kuma ya ya... Ai kam dai ya gane moton ne, da sauri ya nufi hanyar da yake ganin kamar dai mutum a kwance haka amma bai tabbatar ba saida ya ƙaraso.
AA kuma a hanya ya jefar da moton amma bai yar da ID ɗin ba saboda buƙatar shi ita ce hankalin hukuma ya gaggauta dawowa kan shi. A ƙafa ya koma inda ya bar motar shi, sam mai shagon bai yi mamakin ganin shi da bindiga ba saboda sanin aikin shi na soja, amma dai shigar da ya ganshi da ita yau da ta nuna ɗan daba ne ta fi tsorata shi, dan har da wani baƙi baƙi ya shafa a bakin shi kamar wanda ya sigari ta kassara.
Yana shiga motar ya aje bindigar gefen shi sannan ya sake nufa asibiti wajen Safwan dan ba zai je gidan shi ba a wannan lokacin, can ma yanzu jami'ai na can na gadi saboda akwai manya a wurin. Yana komawa asibiti basu hana shi ba, sai dai likitar dake kan aiki a lokacin ta yi ta kallon shi ganin ɗazu ba haka ya fita ba amma ya dawo a wani kangare haka dai, dan ita wallahi tsoro ma ya bata har ta nuna kasa yi masa ko sannu.
Ɗakin ya shiga Safwan na bacci sai juyi da ya gyara, ko takalmin ƙafar shi bai cire ba ya kwanta kusa da Safwan yana rumguma sa a jikin shi ya rufe idanun shi ya yi shiru, daga haka nauyin da ka shi ya yi na zafin aiki ya ya fara raguwa har bacci ya ride shi a wajen shi ma.
*YUSRAH*
Kowane lokaci dama ana samun motocin dake zuwa garin su Iya Abu, sai dai da dare akwai matsala irin na tara da, ake wasu lokutan idan babu jami'ai a wurin, haka ta shiga motar sam ita tunanin ta bai zo ga wani haɗari ba na hanya, musamman da ta ga mota ta cika sun ɗauki hanya, tunanin ta kawai shine sam Iya Abu bata kyauta mata ba, kuma za ta je ta ji wa ta bar wa ƙanin ta? Sannan yana ina yanzu ta je ta ga ƙanin ta, idanun ta akan hanya suke ta matsu ta ga ta isa gaban Iya Abu... Amma birkin da ta ji dreba ya taka da mugun ƙarfi yana faɗin "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! La'ilaha illalah, subhanallah!"
Shi ya saka ta firgigit tana jujjuyawa kamar dai yadda ta ga sauran mutanen nayi suna kuma salallami, ana cikin wannan kayaniya dreba ya juyo cikin muryar raɗa yace "Masu hanyar ne, amma waɗannan basu kai waɗancen manyan haɗari ba, masu neman na shaye shaye ne da abinci, kar wanda ya musu gardama dan Allah, kawai kowa ya basu abinda yake da mu wuce lafiya."
Da sauri kowa ya shiga lalubar jaka da aljihu kowa na son fito da abinda zai bayar sauran kuma ana ɓoyewa, haka ita ma Yusrah ta yi musamman da kuɗin dake jikin ta masu yawan gaske ne.
Saida kowa ya fito daga motar kafin aka shiga miƙawa matasan samarin kuɗin, haka suke ta bi layi layi suna karɓa har suka zo kan Yusrah, har ga Allah babu tsoron su a ranta a wannan lokacin, tunanin ta ɗaya shine, ina ma ace tana da tabbacin ba za ta samu cikakken bayanin inda Iya Abu ta bar Safwan ba, to da za ta ma waɗannan gardama da rainin wayon da ko za ta dace ɗaya daga cikin su ya ɗaga kokarar hannun shi ya gaura mata a tsakiyar kan ta wanda hakan zai jawo silar ɗaukewar numfashin ta da dakatar da bugawar zuciyar ta na farat ɗaya, kaga shikenan ba ta raye bare ta dinga tunanin Safwan.
Ba wannan alamar tsoron ta miƙa musu kuɗin, sai akayi sa'a a duk tafiyar kuɗin da ta bayar sun fi na kowa yawa, wannan ne dalilin da ya sa saurayin ya kalle ta yana ƙara duba kuɗin yace "Ta tabbata ƴan mata ce ke, to yane? Ina kika nufa?"
Kawar da kai ta yi daga barin kallon shi amma ba ta ce komai ba, hakan ya sa shi ƙara matsowa kusan ta ya ɗan riƙe hijabin ta yana tausasa