Showing 30001 words to 33000 words out of 397328 words
daugther, ke ce a asibitin namu?"
Da fara'a sosai suka ƙarasa suka shiga gaishe gaishe, kafin take cewa" Ai aunty Zahra'u matar Yaya Marwan ce ta haihu nan ba jimawa, na ma haɗu da likitar da ta karɓi haihuwar, ita ta sanar da ni kuna ciki, shiyasa na zo na gaishe ku."
Da mamaki ya kalleta yace" Dan Allah, ki ce wacce ake faɗa min ta haihu yanzu matar Marwan ce?"
" E wallahi uncle." Ta faɗa da fara'a, jinjina kai ya yi ya ɗauki waya yana cewa" Ban sani ba, amma bari na kira nurse Yusrah na sanar da ita ta ci gaba da kulawa da su har zuwa safe da za'a sallame su."
Murmushi kawai ta yi bata hana shi ba har saida suka ji ya yi umarni da a turo masa nurse Yusrah yanzu, ci gaba sukayi da tattaunawa har saida Yusrah ta yi sallama ta shigo da tunanin ko me zai faru kuma yanzu?
Amma tun daga ganin fuskar shi yana ta dariya shi da su Intisar ya bayyana mata cewa ko dai ƴar sa ko ƴar uwa, duk da babu kama ta fuska akwai ta jini ga kuma suffa, gaishe su tayi da barka da hutawa tana kallon shi dan jin me zai ce mata?
Ba kunya, ba tsoron Allah ya kalleta yace "Nurse Yusrah, wannan da kike gani ƴata ce, wacce kika karɓi haihuwar ta kuma matar Yayan mijin ta ce, dan haka ki kula da su sosai da duk abinda suke so har zuwa safe, idan kika zo aiki gobe sai ki zo ki sanar da ni kafin mu sallame su, kin gane?"
Da sauri ta jinjina kai tace" To Docter."
Har ta juya ya sake cewa" Sannan..." Juyowa tayi tana duban shi yace" Kin yi ƙoƙari sosai wajen karɓan haihuwar nan, dama kuma abinda yasa kenan na ɗauke ki stage anan, ƙwazon ki da hazaƙar ki, ki je nima yanzu zan je na sake duba uwar da ƴar dan na ƙara tabbatar da lafiyar su."
Mamaki hana Yusrah magana ya yi, kawai ta juya jiki a saɓule tana magana da kanta da cewa _" To da ba waɗanda ya sani bane ba fa?"_
Saida ta fita Intisar ta kalle shi tace" Uncle stage na ji ka ce? Na ɗauka ai sabuwar ma'aikaciya ce."
Murmushi ya yi kawai yace" Tana da ƙwazo ne yarinyar, ai kema kin gani, ita ɗaya ta karɓi haihuwar."
Jinjina kai tayi tace" Gaskiya kam."
Daga haka suka ɗan taɓa hira sannan suka miƙe, tare suka fito ya je har ɗakin mai haihuwar ya gaisa da maman su Bilal sannan ya ƙara duba su, wasu sababbin magunguna ya rubuta ya ba Bilal ya ce sun fi waccen da Yusrah ta rubuta kyau da inganci sannan ya koma ofishin shi.
*AA ANZA*
Ya yi niyya ne mai sunan niyya, hakan ya janyo daga asibitin nan asibitin koyarwa ta Saddi Ja ya nufa, sai dai tun daga cikin mota ya saƙala bavet (facemask) dan tuni mai gadin ya yo kan shi yana so ya shaida wanene kafin ya buɗe masa ƙofar.
A hankali ya zuge glass ɗin motar zuwa ƙasa, mai gadin na leƙowa yace "Barka da rana yallaɓai?"
A tausashe tamkar wani ɗan sarki ya amsa da "Barka."
Mai gadin ne ya sake cewa "Yallaɓai ciki za ka shiga ne? Ko wani ake nema?"
Wani nauyayyan kallo ya bishi da shi yace "Ko kai na gani ma ba damuwa, ina so na san wani abu ne..."
Saida ya ɗauke kai daga kan mai gadin sannan yace "Za ka iya shigowa ciki muyi magana."
Shiru mai gadin ya yi yana kallon shi da tunanin ya zai raina masa hankali haka? A wannan zamanin? To amma kuma shi? Wannan tunanin da ya tsaya yi ya sa AA sake kallon shi a tausashe yace "Ba damuwa, za ka iya shigowa, ba abin da zan maka."
Dariyar da bai san da zuwanta bane ta kubce mishi, buɗe motar ya yi ya shiga yana riƙe dariyar shi, wacce ba komai ya sa ta zo mishi ba sai duba da yadda yake da yadda AA yake, ko riƙe shi AA ya yi fa tam ba zai iya kubcewa ba, in dai ba ko yana fama da ragonta na rashin ƙwarin jiki da hutu kan sa ƴaƴan masu abun suke tasowa ciki ba, amma jikin AA ma ai bai nuna haka ba.
A ɗarare ya zauna yana kallon AA ɗin da shi kuma yake kallon gefe guda, cikin sanyin murya yace "Wani abu nake so na sani, kai kaɗai nasan za ka iya bani amsar daidai, saboda na san duk wani abu da zai shiga ko ya fita ta ƙofar, to da sanin ka ne, hakane?"
Da gamsuwar bayanin AA ɗin yace "Hakane yallaɓai, dan ni kaɗai ne mai gadi a wannan makarantar, kuma anan nake rayuwata, iyalina ma suna ciki."
A daƙile AA yace "Da kyau, kwana huɗu da suka gabata motar ujila ta asibitin Anza clinik ta shigo nan cikin dare, zan iya sanin a wane ɗakin ajiya aka sauke kayan cikin ta?"
Da mamaki mai gadin ya kalle shi, yayin da AA ya yi murmushin mugunta, da gangan ai yake mishi tambaya kamar na yasan komai dan ya ji me zai ce, amma sai mai gadin yace" Clinik Anza? Yallaɓai kana nufin motar da ta zo nan kusan ƙarfe biyun dare?"
A yangance ya amsa mishi da" Ita nake nufi."
Sai kawai ya yi murmushi yace" Ayya, yallaɓai ai motar da ta zo a wajen ajiye motoci kawai Mani ya ajiye ta ya fito, ya bani makullin ya ce an ce za'a zo da safe a ɗauka idan an gama sauke kayan, to kuma yana bada baya bai fi minti talatin ba sai ga wani ya zo ya ɗauki motar."
Lokacin sosai AA ya kalle shi, duk da fuskar shi rufe take da fuske (facemask), amma daga yadda naman gaban goshin shi ya tattare ya nuna ya shiga mamaki ne yace" Aka ɗauke ta kuma? Tun a daren ka ke nufi?"
Gyaɗa kai ya yi yace" Tabbas yallaɓai wannan motar ba ta kwana nan ba, hasalima ba ta yi awa ɗaya cikakka ba aka fitar da ita."
Da ƙaguwa yace" To wa ya ɗauke ta? Kuma ina aka kai ta?"
Girgiza kai AA ya yi yace" Gaskiya yallaɓai ban sani ba, wanda ya zo ya ɗauke ta ban taɓa ganin shi ba ma, ya dai gaya min shine aka turo ɗauka ni kuma na bashi makullin."
Duka AA ya kaiwa sitiyari ya furta" Shiitttt!"
Tsaki yayi yana kawar da kai ya yi shiru, ranshi ya ɓace sosai, ta yadda ya ji kamar ba zai iya jurar wannan rainin wayon ba, to wai wa ma yake da hannu a cikin wannan abun ne? Ya akayi kuma suka iya ɓadda sawu haka kamar ana bibiyar su ko sun san za'a bibiye su? Da kaushin muryar dake nuna hassalar shi ya kalli mai gadin yace "Shikenan nagode, sai anjima."
Da sauri mai gadi ya buɗe motar shima yana godiya ya rufo masa ƙofar sa, tayar da motar ya yi ya juya akalar ta zuwa gida yana jan tsaki kala kala da mita a ran shi, ko abinci bai ci ba ya fito wannan aikin sa kai ɗin, gashi ana ta wani yawo da shi kamar ƙwallo, kuma ba zai yarda ya fara aikata abinda zai karya doka ba, dan a yarjejeniyar su da Chef akwai kiyaye hakan a gare shi da ya zama wajibi, ba dan haka ba da Sani da yake ganin kamar ya san abubuwa dayawa zai ɗauko ya yi ta jibga har sai ya faɗa masa komai... Amma kuma ƙwarewar sa yake so ya nuna ta wannan ɓangaren, dan haka zai je gida ya huta ya samu nutsuwa, zai sake komawa wajen Mani dreba ya tambaya ko an dawo da motar? Idan an dawo da ita wa ya kawota to? Ya san ai ba zai rasa samun wata makamar ba anan ma.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*10*
Haka Yusrah ta ci gaba da kulawa da mutanen nan da bata san komai akan su ba har sanda ƙarfe 06:00 ta yi sannan ta fara shirin tafiya gida, bayan ta gama kimtsawa saida ta zagayen duk waɗanda ya kamata ta duba kafin ta tafi, daga ƙarshe ɗakin da Zahra'u take ta nufa dake su suna vip, da sallama ta shiga ɗakin kuma duk suka amsa mata da fara'a har Aunty Bilkisu na faɗin "Sis Yusrah, ya ɗawainiya?"
Da fara'a ta amsa da "Alhamdulillah aunty Bilkisu, ya baby da maman ta?"
Amsa aunty Bilkisu ta bata da suna lafiya yayin da take nufa wajen gadon tana ɗaukar katin Zahra'u tana dubawa, da sauri kuma ta kalle su tace "Aunty Zahra'u, wai har yanzu ba'a bayar da sunan da za'a rubuta ba?"
Ƴar dariya Zahra'u tayi tace "Mama ki ji wai likita sai ta dinga kirana aunty? Bayan kuma ta girmeni fa."
Yusrah ma dariya tayi tace "Na sani tunda na gani rubuce a katin nan, amma ai yanzu ke uwa ce, Allah ya baki girman."
Dariya dai mutanen ɗakin suke yi, sai dattijuwar da tace ma Yusrah "Sunan ne wai har yanzu suke ta tunani, shi uban ne bai gama yankewa ba, a dole sai ya fara sanin ma'anar suna kafin ya saka."
Murmushi Yusrah ta yi da girmamawa tace "Ai hakan ma yana da kyau Mama, idan ba'a san ma'anar ba sai ayi kwaɓa."
Aje musu katin tayi tana cewa "To, nasan sai zuwa safe ko kuma idan Sakina ta hau aiki sai ta saka, ni yanzu gida zan wuce sai kuma gobe idan Allah ya kaimu."
Aunty Bilkisu ce ta miƙe ta nufi wajen kwanukan abinci da kayan ƙwalam tace "Gida zaki je Yusrah? Ina zuwa dan Allah."
Tana tsaye ta ga tana ta haɗa kayan arziƙi irin wanda ake ta kawo musu suma a asibitin wasu a leda wani a kwano mai kyau, saida ta gama ta miƙo mata tace "Yawwa Yusrah ga wannan ko, kema kya ɗan huta gajiya idan kin je gida..."
Girgiza kai Yusrah tayi tana cewa "A'a wallahi aunty Bilkisu, ki barshi ma nagode."
Nan fa kowa dake zaune ya sa baki kan sai ta karɓa tana a'a, har Intisar da ke nan har lokacin tace "Idan baki karɓa ba fa ba zan ƙara zuwa asibitin nan ba, haka ke ma dai?"
Da iya gaskiyar ta tace "Wallahi idan na karɓa Mamanmu faɗa take min, sai ta ce akan aikina duk abinda aka bani na karɓa kamar cin hanci ne, dan Allah ku bar shi."
Mama da taji tarbiyyar ta ta birgeta ne ta kalleta tace "Ƴata, ki karɓa, wannan abinci ne, baki san da shi ba aka ɗauka aka baki, idan kin je ki faɗawa Maman ki ni ɗaya mamar taki na ce ki karɓa ba komai."
Sam ba dan ta so ba ta sa hannu ta karɓa fuskar ta duk a kyaɓe kamar za ta yi kuka, juyawar da za ta yi kenan sai ga Bilal ya shigo hannun shi da wasu ledojin, Yusrah dai bata kalle shi ba ma dan ta jima da tsarguwa da yawon kallon da yake mata, musamman da ta fahimci mutanen masu kuɗi ne sosai, tana shirin raɓashi ta wuce sanda yake aje kayan hannun shi Intisar tace "Yawwa Bilal, me zai hana ka aje Yusrah gida? Dan garin akwai hadari sosai fa."
Da sauri Yusrah ta juyo kamar a tsorace tana cewa "A'a aunty Intisar, ba sai ya kaini ba, zan je da kaina, nagode sosai."
Nan ma dai takura ta suka so suyi, amma sai Mama ta ce su bar ta kar takurar ta yi yawa, haka ta musu sallama ta fita tana mai rasa yadda zatayi da kayan nan, dan ko ledar dake hannun ta nauyi ne da ita saboda jibga jibgan lemukan kwalaye da aunty Bilkisu ta saka mata a ciki.
Bilal da bai ji daɗin haka bane ya zauna yana turo baki, kallo ɗaya Mama ta mishi tace "Me ye kai kuma?"
Dariya Intisar tayi tace "Mama, autan ki fa shi daga ganin jar yarinyar nan kawai yake jin ya yi mata, sai wani rawar kai yake mana."
Murmushi Mama tayi tace "In kuwa hakane ai sai nace ba ka yi zaɓen tumun dare ba, dan da alama yarinyar ta samu tarbiyya."
Aunty Bilkisu ce ta amsa da "Gaskiya ne Mama, alamu ma sun nuna haka, ba kamar sauran likitoci ba da zaka ga suna da hawa kai."
Intisar ma cewa tayi "Gaskiya kam, tana da shiga rai, ga kuma nutsuwa da hankali, komai nata a sanyaye ba hayaniya."
Wani daɗi ne yake kashe Bilal daga zaune, mutum biyu ne dama a duniyar nan yake fatan samun amincewar su, Mama da aunty Bilkisu, saboda su kaɗai ne mata da ba ya iya bijirewa umarnin su, ya ɗauka ba lallai su kula da tarbiyyar ta ba idan ba yar gidan masu kuɗi bace, dan shi tunda ya ga wayar hannun ta ɗazu tana waya da ƙawar ta *Maryam*, wata ƙaramar Oppo ce kuma ba sabuwa ba, a kuma wannan zamanin ganin budurwa kamar Yusrah, iya jar fatar ta kaɗai ma ta isa sama mata babbar waya, uwa uba kuma kyau da ta haɗa da shi mai ɗaukar hankalin mai kallo, to amma Alhamdulillah tunda suka yarda da tarbiyyar ta, iya haka ma da suka mishi ya ishe shi.
*Yusrah* na fita kai tsaye hanyar fita ta nufa har ta isa bakin titi, ai kuwa kamar jiran ta ake abun ka ga yanayin marka, saukar ruwa kawai ta ji a jikin ta kuma ba wai yayyafi ba, ruwa ne da ɗan ƙarfin su suka sauka da ya saka mutane neman mafaka wasu kuma na ƙara gudun ababen hawa, cikin sa'a ta samu adaidaita sahu ba kowa ta tsayar da shi, tana faɗa masa inda ta nufa ya ruɓanya mata kuɗi saɓanin yadda take bayarwa, sanin dole dama za ta sha tsada saboda ruwan nan ya sa ta rage kaɗan, ba gardama ya ce ta shiga suka ɗauki hanya.
Basu wani jima ba suka isa, wajen ciro kuɗin ta bashi sai da ta shiga tunanin ya za ta yi gobe wajen zuwa asibiti? Dan su kenan gare ta kuɗin ta bashi, Baba ko Mama kuma bata da tabbacin ta samu wajen su, ko zata samu ma kunyar tambaya take ji, shiyasa take Allah Allah a mata albashin ta na farko ta kawo musu su yi buƙatun gida ko za ta ji daɗi a ranta ita ma cewa ta taimakawa iyayen ta.
Ana ta kiraye kirayen sallah ta shiga cikin gidan da sallama, da gudu kuma Safwan ya tarbeta yana ihun "Aunty Yussy ta sha kashin ruwa, mu muna gida zaune abun mu."
Kwanon hannun ta ya fara karɓa, ita kuma tana ta ƙoƙarin ɓoye jakar ta ko dan wayar ta dake ciki, dungure masa kai tayi tana dariya suka shiga ɗaki da gudu gudu dukan su, Hannah na tsaye bakin ƙofa tana kallon ruwa, Mama kuma na zaune kan kujerar katako da roba a gaban ta ta nan alwala a ciki dan kar ta jiƙa ledar ɗakin duk da kuwa ba sabuwa ɓace, Hannah ce ta fara ɗan musu suka wuce tana faɗin "Yussy me kika taho mana da shi haka har da kwanuka yau daga asibitin?"
Yusrah dai kayan jikin ta ta fara ragewa tana ma Mama sannu da gida, ita ma da fara'a ta amsa mata da "Yawwa Yusrah, ruwa sun dake ki ko?"
Tana cire baby hijab ɗin ta tace "Wallahi kuwa Mama, kamar a kasa na taho."
Alwala Mama ta ci gaba da yi ba ta ko kalli kayan nan da ta shigo da su ba, ita ma Yusrah ba ta kula ba sai ma shigewa ɗaki dan ta canza kayan jikin ta, kafin ta fito Hannah ta buɗa kwanon dan ganin ko menene? Ba wai dan kwaɗayi ko ɗaukar hankali ba, dan Safwan bai isa ya yi haka ba musamman a gaban Mamansu, dan haka shima ledar yana ajiyewa ya fara shirin alwala.
Mama na ganin abinda ke cikin kwanon ta kawar da kai, saida ta gama alwalar ta tsaf ta miƙe tsaye ta yi addu'ar ta bayan kammala alwala _"Ashhadu an la'ilaha illalah, wahadahu la sharikallah, wa ashhadu anna Muhammadan abduhu wa Rasulillahu, Allahuma-j'alni minattawabina, waj-alni minal-mutaɗɗahirin."_
Tana saka hijabi Yusrah ta fito, lokacin ne ta jefeta da wani kallo mai tattare da harara cike da tuhuma ta nuna mata kayan dake gefe a taƙaice tace "Daga ina wannan?"
Yusrah ba ta tsammaci wannan tambayar Maman za ta mata ba, dan haka ta ɗan sosa kan ta cike da alamun rashin gaskiya tace "Mamanmu, wallahi wasu mutanen ƙwarai ne a asibiti da ƴar su ta haihu, zan taho gida shine suka ban wannan."
Kausasa kallonta ta sake yi gare ta tace "A matsayin me kenan?"
Da dariya Hannah da ba'a tambaye ta ba tace "A matsayin kyauta ko?"
Kallon ta duk sukayi sai Maman da ta haɗe fuska ta nunata da yatsa tace "Kar na kuma jin bakin ki."
A sanyaye Hannah tace "Kuyi haƙuri."
Saida gaban Yusrah ya faɗi da Maman ta