Showing 144001 words to 147000 words out of 397328 words
taɓa bari ki yi kuka ba, kin ji ko? Ni ce nan mamanki kuma ni ce babanki, in sha Allah zamu rayu cikin aminci kin ji Yusrahana."
Wani irin kallo Goggo Hinda ta mata tare da taɓe baki, wanda tsaf hakan a idanun Intisar da Fatila da su dai suke matuƙar mamakin matar. A hankali ta ɗora kanta saman cinyar aunty Fureira ta fashe da sanyayyan kuka tana faɗin" Ameen aunty, aunty kinga yadda rayuwa ta yi damu ko? Rana tsaka, mun rabu da Babanmu da Mamanmu, sun mana sai da safe, sannan sun saka mukayi alwala mukayi addu'ar bacci, har Babanmu yana cewa aunty Hannah ba ya son iskanci idan tana tsokanar masa auta Safwan, ashe aunty wannan dariyar ita ce ta ƙarshe da dukan mu zamuyi a rayuwar mu, kawai farkawa mukayi muka ganmu a gadon asibiti su Mamanmu kuma wai duk sun ras..."
Ƙara rumgume ta aunty Fureira tayi a jikin ta ita ma ta sake fashewa da kuka ta katse mata maganar ta da cewa" A'a Yusrah, in sha Allah, da izinin Allah bakuyi dariyar ƙarshe ba, ku da kuka rayu har yanzu kuna da sauran dariya nan gaba, ki kwantar da hankalin ki kin ji?"
Su Hajia da Intisar duk saida sukayi hawaye, da ƙyar Hajia da Maman su Yaya Mubarak suka yi ta rarrashin su kafin su yi shiru sai Yusrah dake ta ajiyar zuciya tana shasheƙa kamar za ta haɗiyi rai.
Saida aka nutsu sosai Hajia cikin dattako tana ƙara saɓa mayafin ta a kafaɗa tace "Abinda ya sa muka taru anan shine dan samawa yaran nan marayu mafita a rayuwar su da kuma garkuwa da zata hana su tozarta a ko ina, ammm... Hindatu."
Hajia ta faɗa tana kallon Goggo da fuskar ta ke matse taf, kallon Hajiar ta yi ta amsa da" Ummm!" Dan har yanzu tana jin haushin Hajia akan shirun nan da ta mata sanda suka je gidan ta da safe, da nutsuwa Hajia tace" Ke ce babbar uwa yanzu ga su Yusrah, sannan masu alhakin yanke hukunci akan rayuwar su saboda kune dangin uba, waɗandan mutanen da kuma ni muna so ku bar mana Yusrah a hannun mu, saboda ta samu nutsuwa da hutu da kuma sa'idar neman ƙanin ta da nan cikinmu babu wanda ya san ina yake, wannan shine dalilin zaman nan namu."
Saida Goggo ta saci kallon Yusrah da ta rage sautin shasheƙar ta ƙwarai sannan ta kalli Hajia tace" Hajia, abinda ban gane ba, za'a riƙeta ne na dindindin? Ko na wucen gadi ne?"
Yaya Mubarak ne ya bata amsa da" Za'a riƙe su dai, har da Safwan idan mun gani in sha Allah."
Kallon shi ta yi sannan ta ɗauke kai kawai ta yi shiru, kusan kowa kuma ita ya zuba ma idanu yana jira ya ji me za ta ce, amma cikin ikon Allah Goggo ta yi ɗif tana ta saƙe saƙe a ran ta, ganin ba shirun ya tara su ba aunty Fureira kuma idan so samun ta ne yau idan suka ga Safwan ta juya da su dukansu magriba ta musu a gida ya sa ta kallon Hajia da girmamawa tace "Hajia, ni kam ko ita za ta yarda ta bar su, gaskiya ba zan ɓoye muku ba ni na fi so na tafi da su a kusana ina ganin su, hakan shine kwanciyar hankalina."
Murmushi Hajia ta yi tace "Fureira, ki bari mu ji ta bakinta tukuna, da alama nazari take, tunda ba abu bane da kai tsaye za ta yanke, ai ina jin har yanzu akwai ƙanin mahaifin Yusrahn da shi baya nan saboda baya gari, ko ba haka ba?"
Aminu ma da a babur ɗin sa ya zo bayan su Hajia ya amsa da" E hakane, Suleiman ba."
Har lokacin Goggo ba ta ce komai ba tana dai jin su, dan haka aunty Fureira ta sake cewa" To naga ta yi shiru ne, mu kuma ba shirun muka zauna ji ba, ina ga kawai Yusrah ta haɗo duk wani tarkace da ta san nata ne ta tashi mu wuce."
Kamar Intisar za ta yi kuka ta ɗan matso kusan aunty Fureira ta riƙe mayafin ta da rarrashi tace" A'a aunty, dan Allah kar ki ɗauke ta daga gareni, aunty ki bar min ita, kinga wallahi Yusrah a zata yi rayuwar kaɗaici ko maraici ba, na miki wannan alƙawarin aunty, dan Allah ki bar ta, ita ma tana son zama dani ƙawar ta."
Girgiza kai aunty Fureira ta yi a hankali tana murmushi tace" Na gode ƙwarai da kulawar ku akan ƴata, haƙiƙa duk wanda ya so wannan yaran ni ya so, amma ba zai yiwu na barsu a nan ba, gwara suna kusa da ni ya fi."
Da sauri ta juya ta kalli Yaya Mubarak dake nazartar Goggo da ita kanta aunty ɗin tace" Ba... Oga, dan Allah ka sa baki kar aunty ta tafi da ita, tana da damuwa fa, kuma anan take saka ran ganin ƙanin ta, ta bar ta ta zauna damu ko da na wani lokaci ne mana."
Kafin wani ya yi magana Goggo ta taɓe baki cike da takaicin lamarin na Fureira ta kalleta a wulaƙance tace" Hmmmm! Wallahi kina bani mamaki, ban da ɗan adam da kullum ba ya fatan sauƙi wa rayuwar sa, ta ya ana neman ɗauke miki nauyi na budurwa balagaggiya da kuma yaron da yanzu bayan cin kuɗi babu abinda zaman ki da shi zai anfane ki, amma har wani botsarewa kike? Bayan abinda za ki ci sai an fita ake nemo shi a kawo, shin wannan ba sauƙi bane ya zo miki?"
Duka ɗakin kallon ta sukayi da tsantsar mamakin kalaman ta, wanda basu san ta sai suka yarda da labarin ta da suka ji, wanda suka san ta kuma suka sake gasgata lallai bata da kirki, kenan yanzu a wajen ta su Yusrah nauyi ne? Kuma sauƙi ne idan suka bar su kalan dangi hannun wasu bare?
Da haushin wannan magana ta ta aunty Fureira tace "Tirrr da son zuciya irin naki, wallahi Hinda kinyi asarar rayuwa, tabbas ni talaka ce kuma kowa ma dake nan ya shaida ko da na tafi da Yusrah akwai safiyar da zamu iya tashi bamu da abin da zamu ci, amma ku sani wallahi tallahi dan marayun nan biyu su ci zan iya ɗaukar tiri na ɗora a kaina na tafi talla, abinda ke kika rasa kenan wadatar zuci."
Wata irin shewa Goggo ta yi tace" Wallahi ƙarya kike, ki sani idan kika ƙarawa kan ki nauyin nan to duka gidan ki yunwa ce za ta kashe ku, burgar? Burga ce kawai kike, amma ke da ba zaman kanki kike ba har kin isa ki yanke wannan hukuncin? Ke a wa?"
Murmushi aunty Fureira ta yi tace" Alhamdulillah, duk abinda zan yi saida shawara da kuma umarnin mijina, bamu da arziki, amma kuma muna girmama mazajenmu da sakawa abinda suka kawo mana albarka, ki sani mijina har ya fini damuwa akan na gaggauta tahowa da yaran nan, dan shi yana tuna ranar da zai buɗi idanuwan shi ya ganshi a makwancin da ba zai iya motsawa ba."
A zafafe Goggo tace" Me kike nufi? Ni bana tuna mutuwar ne aka ce miki? Abinda na sani ne kawai Hure ba zaki iya riƙe ƴaƴan nan ba, ni ma kuma ba zan ɗorawa kaina abinda zai zo ya dameni a gaba ba, dan haka ni ban ga laifi ba idan mun bar su anan."
Ita ma aunty Fureira da zafi har tana gyara zamanta sosai tace" Ke ce ba kya tuna mutuwa, da kina tunawa da baki zalinci ƴaƴan ɗan uwan ki ba, Hinda me kika ɗauki rayuwa? Me kike taƙama da shi? Wallahi talaucina bai isa ya sa in zauna kina gaya min magana ba."
Da mamaki Goggo tace" Zalinci? Ni ce ma na zalince su? Ke..." Ta daka ma Yusrah tsawa tace" Me na muku na zalinci? Me kika faɗa mata na muku da na zalince ku?"
A tsawace aunty Fureira tace" Har sai ta faɗa min, ga abu nan ƙiri-ƙiri, wasu anan sau ɗaya suka haɗu da ke amma an shaida baki da mutumci, ke har jira kike dama sai wani ya gaya miki ba azzaluma bace ke kuma mai fuska biyu."
Yunƙurin miƙewa Goggo ta fara yi dake tana da jiki sai hakan ya sa bata iya tashi farat ɗaya ba, amma aunty Fureira da ta ga abinda take shirin yi tuni ta miƙe tsaye tana kallon Goggon dake faɗin" Dama ba hucewa nayi akan takaicin asarar da kika ƙunsa min ba, yau zan amaye ki dan ki gane ba tsoron ki nake ji ba Hure."
Cike da jin haushi aunty Fureira tace" Ai har abada ba ke ba daina ganin asara wallahi tunda har kika wulaƙanta marayan Allah, wai ke ba kya sauraran wa'azi ne? Wanda ma baka san shi ba cewa ake ka ɗauko ka riƙe, bare ke gaki k..."
Sautin siririya kuma tattausan muryar Yusrah ne ya sa ɗakin yin shiru sanda ta fashe da kuka ta furta" Hasbunallah wani'imal wakil! Hasbunallah wani'imal wakil, aunty kar ki min haka dan girman Allah."
Jiki a sanyaye cike da tausayik Yusrah ɗakin ya yi shiru, sai Intisar da Fatila da suka sakata tsakiya suka daddaɓata alamar ban haƙuri, aunty kam tuni ta koma ta zauna tana faɗin" Kin ci albarkacin ƴata."
Amma sai Goggo ta shiga tafa hannaye tana faɗin" Ni kuma kinga idan na so shuka rashin mutumci ba wani mai girma ko daraja da zai dakatar da ni, in kwaɓe zigidir mu cire raini ƙaramin aiki ne a gurina."
Girgiza kai aunty Fureira da Hajia sukayi, sai Maman Mubarak da take jin ga abun magana amma kuma ta kasa cewa komai, wani irin takaici da baƙin cikin matar nan ya gama mamayeta, tabbas kafin yanzu ba ta ji a ranta tana son zaman ta gidan nan ba, saboda ita gaskiya tana tsoron duniyar nan da mutanen cikin ta, sannan a ganinta kamar Intisar ce ta takura Mubarak ɗin akan dole sai Yusrah ta zauna dan a ƙara ɗora masa wani nauyi, amma yanzu da ta ga Goggo da irin tijarar ta, sai yarinyar ta bata tausayi musamman da take rera wani irin kuka mai tsuma zuciya, dan haka ta ƙarewa Goggo kallo tace "Ba shakka, ai ko baki faɗa ba zubin yanayin ki ma ya nuna ba sauƙi a lamarin ki."
Kallon tsohuwar ta yi za ta yi magana Aminu da yake jin ina ma yana da iko da ita wallahi da ya koreta daga nan, da sauri ya taka mata birki da cewa "Hinda wai me ye haka? Ya zamu zauna dan tattauna abu muhimmi amma duk ki hargitsa mana wuri? Ke ba yarinya ba kuma ba mai taɓin hankali ba, shin wannan ya dace saboda Allah?"
Juyawa ta yi kan shi da tijara tace "Kai dakata malam, ni ce mai laifi kenan? Ita koɗaɗɗiyar ƴar uwar taka baka ga me ta min ba? To na yi magana da bakina ai ba za'a hanani ba, dan haka malam ka min shiru na yi da ita dan ita ce daidai dani."
Miƙewa tsaye Maman Mubarak ta yi da sababin da ya fi na Goggo tace"Ke Hinda kike ko? Ke dallah fice min daga falo, maza ɗauki abinda kika san naki ne ki bar min falo, wannan wace irin jaraba ce? Ke duk rashin tabbacin da bawa yake da akan shi mutumin kirki ne ko akasin haka ai yana ganin ki dole ya yarda cewa shi ɗin mutumin Allah da annabi ne, wannan wace irin masifa fa? Gaban ƴar ɗan uwan ki? Ba kya ko jin kunya? Dama haka kike musu da mahaifin su yana raye? Ko bayan ƙasa ta birne idanun shi ne kika fara musu haka? Ina tsiya ina abinda ƴar nan za ta ci? Duka guda nawa take daga ita har ƙanen nata? To dallah fice min daga ɗaki ko na sa mai gadi ya fitar min da ke, gaba ɗaya nema kike ki tayar min da hawan jinina ne."
Kallon ta Goggo ta yi tana tutturo baki tunda ko Maman Mubarak bata haifeta ba a ƙalla dai tasan ba tsaran ta bace a shekaru nesa ba kusa ba, dan haka tana wani kakkauda kai tace" Daga gidana fa aka ɗaukoni dan na tsoma albarkacin bakina, ta ya kuma za'a ce b an zan faɗa ba yanzu? Allah yana gani yadda rayuwa ta canza mutum ke fafutukar neman abinda zai ci ma, ta ya ka ciyar da waɗanda ka haifa? Bare ka ƙara lodawa kan ka wani lodin da baka san iyakar su kan ci ba ma, ita Fureira da take maganar za ta ɗauka in ta ji tana iyawa ga wurin nan, kamar yadda ban hana duk wani mai son ɗaukar su ba dan a ganina ai kowa yana son ya yi taimakon, idan ko kowa anan ya ji haushina wannan matsalar ku ce, ni abinda na san ba zan iya bane na fito kai tsaye na faɗa, kamar yadda nasan ita ma idan ta ɗauka to cikin biyu za'a yi ɗaya, imma ta saka yarinya neman yaki halak yaki haram, imma kuma yunwa ta tagayyara rayuwar su sannan ta ce za ta maido mana mu dangin uba ko? To ba fariya nayi ba..."
Ta faɗa tana kallon aunty Fureira da hawayen baƙin ciki ke silalo mata tace" Indai akan wannan ne, to nan gaba duk abinda ya shafe su a neme ki ke da sauran dangin ku, *ni na bar miki matsayina na Yayar uban ta*, dan haka yanzu ke ce me ruwa da tsaki a lamuran nasu, ina ce shikenan."
Wani irin hak hak hak! Da Yusrah ta ja kamar za ta daina numfashi ya sa Intisar saurin miƙewa tsaye ta kama hannun ta tana ma Goggo wani matsiyacin kallo tace" Yusrah mu bar nan, raina bai iya ɓaci ba, kamar yadda ba zan juri ganin ki a haka ba."
Ganin tana ta jan hannun Yusrah ta ƙi tashi ya sa ta daka mata tsawa da cewa" Ki tashi mu tafi nace."
Girgiza kai Yusrah tayi tana share hawaye idanun ta tsam akan Goggo tace" A'a aunty Intisar, babu inda zan je ina nan, naga fiye da haka, mahaifiyata ma ta yi kukan da ya fi wannan a dalilin ta, kamar yadda ba baƙin cikin ta bane ya kashe Mamanmu, nima na san ba shi zai kasheni ba da izinin Allah, zan shanye, zan iya shanyewa aunty Intisar."
Kusan kowa sai da ya girgiza kai da rashin jin daɗin wannan lamari har mazan kansu suna ɗan magana ƙasa ƙasa da zunɗen Goggon, dan haka ita ma da takaici ta kaɓe hijabinta ta juya fuuuuu tana faɗin" Banzan zama kawai, da nasan abinda zan tarar kenan da ban zo ba, har ni za'a nunawa gida ana kora ta, to wallahi ba zan ɗauki abinda ya fi ƙarfina ba, da sana'ata naji ko da kula da musaki?"
Duk da Goggo ta bar wurin, amma wannan zulumi da alhini ya kasa barin zuƙatan mutanen dake wurin, saida dai suka ga wannan ba za ta gyara su ba sannan suka bi Goggo da addu'ar shiriya sannan Yaya Mubarak ya dubi aunty Fureira yace" Auntynmu, Allah ya saka miki da alkairi akan riƙo da kikayi da zumunci, Allah ya dubi naki bayan."
Aunty ba ta iya amsawa ba sai mutanen ɗakin ne suka amsa da Ameen, kafin ya ɗora da" Sai dai aunty, dalilinmu mai ƙarfi ne na son Yusrah ta zauna da mu, na farko, anan aka haifi Yusrah, nan ta tashi kuma nan ta saba, rayuwa acan yanzu ko yane sai ta bata wahala, na biyu kuma aunty wanda shine dalili mai ƙarfi, Yusrah anan ta yi karatun ta, takardun ta duk na nan ne gaba ɗaya, Yusrah tana son yin anfani da kwalayen ta dan ta anfani kan ta, kuma ta faɗa mana burin mahaifin ta kenan, a yanzu kuma takardun ta ba zai bata aiki a inda kuke ba, cewa kuma ta sake maimaita karatu idan ana so ta ci moriyar sa ai kunga wani aiki ne, idan kuma aka ce ta haƙura ta zauna, to fa yanzu ana duniyar da zama babu wanda yake gyarawa ne, dalili na uku kuma aunty Safwan, Safwan har yanzu babu wanda zai iya cewa ba ya garin nan, anan aka rasa shi kuma dukanmu anan muke sa ran ganin shi, ko da ma baya nan mutumin da ya bayar da Safwan anan yake, dan haka ko shari'a ta kama muja da shi anan ne zamu shigar da ƙarar, da wannan nake roƙon ki da kiyi haƙuri aunty ki bar Yusrah a wurinmu na wani lokaci har komai ya daidaita, ita kanta na san ba za ta so yin nesa da garin da take tunanin Safwan yana nan ba."
Murmushi aunty Fureira ta yi tace "Gaskiya ne, duka dalilan nan masu ƙarfi ne, sai dai ka sani rashin sabo ba zai cutar da Yusrah da komai ba, me ye zai bata wahala a can ɗin? Karatu kuma ko aiki ina ga ai idan ta kama zan iya ce maka ba dole sai ta karatu Yusrah za ta ci abinci ba, akwai sana'o'i kala kala da za ta iya dogara da kan ta, dubannin mutane sun haɓaka a duniya ba tare da karatu ba, dan haka magana ta gaskiya da zan faɗa maka shine ba zai yiwu na tafi ba tare da Yusrah ba, na ji na gani zan zamar mata uwa da uba da duk wani abun da ta rasa."
Aminu ne ya dubi ƴar uwar tasa yace" Aunty Fureira, da dai kin ƙara duba lamarin, ni a ganina wanda ya nuna yana son naka ya gama maka komai, dubi kiga fa waɗanda su Yusrah suka zama dolen su ma sun yakice su a ƙafa, amma waɗannan bayin Allah sun nuna za su iya ba dan komai ba sai san su taimaka mana dukan mu, idan kika tafi da ita yanzu Safwan fa? Amma idan kika tafi ko saboda iyalin ki da kika baro ita sai ta zauna nan da ci gaba da cigata ɗan uwan ta, wannan karan ƙarfi da ƙarfe ne za'a haɗa wajen neman sa, kuma mutanen nan dukansu a shirye suke da su taimaka wajen neman nasa, ina ga kamar da kin barta ɗin."
Da sauri Intisar ta jinjina kai alamar gamsuwa tace" Hakane Yaya, dan Allah ka mata magana ta bar Yusrah