Showing 396001 words to 397328 words out of 397328 words
nuna da gaske yake dan haka suka tashi cikin kaza kaza suna kwaso kaya suna tarawa har suka gama sannan suka kama suka fitar da kujeru da kafet da labulaye ɗakin ya zama kamar kango, ya kuwa sa aka barbaɗa omo da javel suka saka tsintiya yana tsaye suna darzar falon har da jikin bango yana zuba ruwa da tiyo datti na gangarowa har suka gama wankewa sannan aka bar ƙofar a buɗe, ya yi kira aka zo aka kwashe kujerun da labulayen da kafet ɗin aka tafi da su, ya yi kiran kanfanin da yake siyan kayan ɗaki ya sa aka zo da wasu kujeru da labulayen da kafet aka shiga sakawa bayan an cire gidan tautau da komai falon ya ɗauki haske domin dama pentin na kirki ne kawai datti dai yayi dan ƙazanta ba'a gogewa sannan komai gogawa ake yi, kamar da wasa dai ya zauna da kujerarsa su kuwa suna ɗirkar wanki dan kayan Hajia tuni ya sa Mukhtar ya ɗauki nauyin kai wa wajen wanki da guga da na babansu, kayan ƴan matan ne kawai har yanzu a zubde ko'ina har ɗakin Hajiar shi yasa yau ya nemi waje ya zauna suna wanki kamar hannayensu zai cire gashi ba damar yin magana sai dai su harari junan su kamar su sukawa kan su laifin.
Suna cikin wankin Hajia ta zo, tun daga ƙofa da ta gansu suna wanki ta yi turus tana kallon ikon Allah, tana idasa shigowa ta ga AA zaune yana mata murmushi da sannu da zuwa ta tafa hannu ta ce" Ni na san kai sake ƴaƴan nan ba zasu aikata abin alkairin nan ba, ɗan nan ashe kai ne ɗan arziki irin albarka, ya ya jikokina ina ƴar tawa ina fata suna lafiya?"
Ya amshi jakar hannunta yana faɗin" Lafiya ƙalau Hajia, mu je ki huta."
Ai Hajia na shiga ɗakin sai ta gigice ta kalle shi ta ce" Yaro nan ɗin ina ne?"
Yayi ƴar dariya ya ce" Ɗakin ki ne Hajia, ai yaran nan yau sun sha aiki."
Hajia ta sake kallon ɗakin ta ce" To ɗan nan duk aikin da zasu sha ai ba zasu canza ɗakin nan haka ba, ka ga sabin kujeru da kafet da labule ɗaki kamar na amarya, Astagfirullah Allah na tuba, yau ko Elhaji ya dawo daga ƙauye ai sai ya gigice balleni."
AA ya ce" Zauna mana Hajia, ni abinda ya fi damuna ƴan marayun nan namu, dama ace ki bani su in kai su wajen Anna su kwana biyu, Hajia wannan in muka musu aure a haka ai zaginmu za'a yi ace bamu basu tarbiyya ba, ki duba ki ga ƙazantar ƴaƴan nan, abin na damuna sosai har barci yake hana min."
Hajia ta ƙarasa ta zauna ta fashe da kuka tana dafe haɓa ta ce" Allah sarki, ashe ba ni kaɗai ke kasa barcin nan ba? Alkur'an sai dare ya raba in tashi kiri-kiri ina zufa ina hawaye, shin ina zan kai wannan damuwa ne ni yaron nan? Abin na damuna sosai, dama ina cewa zan je gidan naku in kai magungunan baki da na cadi a ɗaurawa su Haidara da Hamidu sai gaka ka zo, yaron nan ai ƴaƴan nan da ace zaka kai sun wallahi da na ji daɗi, abun na damuna."
Samir da su Attahir da suka shigo tun shigar su Hajia suma mamakin ƴan matan Hajia ya kashe su suka ƙarasa dan su ga me yake faruwa ne suka tarda wannan zance, Samir bai san lokacin da ya saka dariya ƙasa ƙasa ba ya koma daf da Rihab ya ce" Za ki ci ubanki Rihabatullah, wallahi za ki ci ubanki, bari in bar anguwar tun kafin ya ji ra'ayin tafiya damu mu shiga uku, in sha Allah kun shiryu yara sai dai wani abin, amma ba dai ƙazantar nan ba."
Da sauri su Attahir suka bi shi suka bar gidan suka bar su Rihab cikin halin kaka-naka yi, ga gajiya ta rashin sabo da aiki ga zulumin an ce a tafi da su, a je da su ina? inna lillahi! Sun shiga uku.
A gidan ya wuni sai goshin magriba suka nufi gidan Anna yana tuƙa motar yaran na kukan zuci suka nufi gidan Anna, da ya kaiwa Anna su ya sanar mata buƙatarsa kawai kallonsa take yi da mamakin rigimarsa, sai da ta yi kiran Hajiar Mukhtar ta tabbatar mata da yawunta aka ɗauko ƴan matan sai ta samu nutsuwa, cikin hikima ta kwantar musu da hankali sannan ta ja su ɗakunan ƴan matanta da yanzu basa gidan ta sauke su nan ta nuna musu kar su wani damu gida suka zo babu abinda za'a musu, cikin hikimar nan ta zauna tana hirantarsu ta sa suka yi wanka, tana nan ta sa suka fesa turare sosai suka saka kayan barci sannan ta musu sallama ta ce su kwanta da wuri saboda a tashi da wuri a yi abincin kari, ta nuna musu tare zasu yi girkinsu ko? Yaran kuwa sun amsata sannan suka kwanta bayan an kunna musu ac suna ta murnar acn suka kwanta cike da jin daɗin jin hutu aka kawo su ba wani abu za'a musu ba.
Da Anna ta je ɓangaren Aba ta same shi yana waya, ta zauna a gefensa har ya gama a tausashe ta faɗa masa magana kamar haka" Aban Aswan, ina ga ka faɗa masa yaran nan a kawo su in riƙe, mahaifiyarsu fa na da wata kama, kuma ka ga ita ma yarinyar ce baiwar Allah ga rigimar mijin nan nata kar ta zo ta yi ta ramewa."
Da mamaki yace" Ciki wai? Yaushe aka yi?"
Anna ta yi tsuru tana kallonsa ta ce" Yaushe aka yi cikin?"
Aba ya kama baki yana kallonta ya ce" Aslama ki ji tsoron Allah, mace da mijinta nace yaushe aka yi ciki? Ina nufin yaushe ki ka san tana da ciki ni ba'a faɗa min ba?"
Kunya ta sa Anna dafe haɓa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Nima ba faɗa min aka yi ba, ganewa na yi da muka je ganin Manal ni da ita."
Aba yayi murmushi yana wani gyara zama yace" Jikan Anza dai ya gado babansa, ma sha Allah wannan kayan arziki haka."
Anna ta miƙe ta yi ciki tana faɗin " Allah ya kyauta."
Yayi dariya ya miƙe ya bi bayanta yana amsawa da amen amen.
*AA* bai isa gidan ba sai da yayi sallar isha'i sannan ya shiga da tsarabarsa jili jili, samunta yayi tana ƙara sakawa ɗakin turaran wuta, da murmushi ta tarbeshi tana buɗe hannayenta bayan ya ajiye kayan a hankali ta furta" Oyoyo my life."
A hankali ya saka hancinsa a wajen gashinta da ta ɗaure yana sinsinawa sannan ya saka hannunsa yana cire abayar dake saman shigarta, hannunta ya kama ya juyata a gabanta yana ƙare mata kallo kafin ya janyo ta gaba ɗaya ya ɗauketa irin ɗaukan masoya ya janyo ta jikinsa sosai ya furta" Kin yi kyau zuciyata."
A hankali ta shige jikinsa sosai yana nufa ɗaki da ita ƙasa ƙasa tace" Sai ka ci ƙaniyar zamu ci abinci kenan?"
Yayi murmushi yana sake riƙe ta a jikinsa ya ce" Ina ƴaƴana?"
Bayan ya direta saman gadon ta ɗago kaɗan ta ce" Suna ɓangaren aunty sun yi barci tun ɗazu."
Ya shiga balle rigarsa yana yi mata wani irin kallo dake daf da siɗeta ya janyo hannayenta ya cirata ya nufi bayi da ita yana faɗin" Ai kin san da wannan tsumin kika korani, dan haka da shi na dawo gidan, zan ci ƙaniya, zan cinye sumul Y. Turaki..."
Gam suka rufo ƙofar har sai da kaina ya gwaru tsabar basa so in ga abinda zai faru a bayin, a dole muka fito ni da kwate muna gurza ruwan byro ɗin mu domin ya cinye tassss ya ƙare.
*Tamat😍😍😍😍😍 jama'a wanda muka ba daidai ba dan Allah ya yafe mana, masoya da kuke bimu sau da ƙafa muna godiya sosai, Allah ya sakawa kowa da alkairi, in sha Allah sai kun ji Kwate a sabuwar tafiyar ta...*
*Luv u all guy's*😍🥰🥰
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*