Showing 288001 words to 291000 words out of 397328 words

Chapter 97 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70049

duk da kuwa ba ta ji tana buƙatar kyautar ta ba sannan ta ja Safwan a nutse suka kama hanyar barin falon.

Da ɗan sauri ya miƙe tsaye ya yi tako na farko da niyyar bin bayan Yusrah sannan ya tambaye ta me take nufi da sun dace shi da ƴar can? Amma kuma sai ya ji motsi da muryar aunty Intisar da aunty Fureira suna saukowa ƙasa, haka kuma sai ya kalli Nabihat da take binshi da wani ɗan banzan kallo kamar mai jiran ta ga me zai yi, a dolen dole ya dakata duk da kuwa ya so riƙo hannun Yusrah su yi ta ta ƙare, idan ma haushin sa take ji dan an musu auren dole, ai shi ya kamata ya ji wannan haushin ko? Shi da yake ta kula da kan shi shekara sama da talatin da biyar, kwatsam a wani yi masa auren je ka an ɗaura ga ɗakin ka can.

A nutse ya dakata yana zuba wayar sa aljihu ya kama wuyan hannun shi mai ɗauke da mundun azurfa mai sunan shi yana murza shi, kuma har lokacin idanun shi na kan su Yusrah da basu ɓacewa ganin shi ba, duk da ta yafa mayafin ta, amma dai bai hana shi tsare tsarin kyakyawar zubin halittar bayan ta da take takawa cikin nutsuwa bayyana ba, shi har ma mamaki yake yi yadda... Kai Astagfirullah, wannan lamari bai shafe shi ba, bai taɓa raka bayan mace da kallo da wata mummunar manufa ba, bai kuma taɓa dire idanun sa akan ƙugun mace haka ba ya yi ta kallo yana jin abun na neman birge shi ne ko kuma dai yadda ma ya birge shi ɗin ne ya sa shi gagara ɗauke idanuwan sa ba sai yau.

Saida y ga sun tsaya ita da su aunty suna magana sannan ya ɗan wani karkace kai cike da basarwa ɗin nan sannan ya juya da niyyar ƙarasawa wajen table ɗin da aka ƙawata da kayan ƙwalam dan ya ɗauki lemun da ya ga ya fi so wanda yake da tabbacin Anna ta aje shi anan saboda shi, dan ko Humed ba ya shan lemun nan, daga shi sai Aba, Aba ma ba sosai yake sha ba yanzu kamar yadda shi yake sha, ikon Allah sai ya samu yarinyar nan Nabihat har yanzu idanun ta akan shi, shi take kallo, kallo dai na gudun wuce sa'a, kallo dai gashi nan shi har ya ji ma y rasa me kallon nata ke nufi, abun ya yi yawa sosai, ka tsare mutum da idanu haka ba ko kunya ko aiki da abinda islama ya faɗa, fisabilillah me take nufi da wannan kallon na jaraba haka? Kan ta ɗaya kuwa? Ko kuma dai...ba ya son yin mummunan tunani a kan ta, ba ya son munanawa kowa zato a rayuwa, kamar yadda shi wasu suka dinga masa ana ganin ya ƙi aure ne saboda yana samun biyan buƙata a wajen mata duk lokacin da ya so, wasu ma gani suke yi ko wata shirkar yake yi da ta sa ya ƙi auren, yanzu kuma idan ya ambaci Safwan da ɗan sa a gaban mutane, sai ya ga an zuba masa idanu an kalle shi irin da mamakin ɗan ka kuma? Daga ina? Ta ya ya? Yaushe ka same shi? Hakan bai taɓa damun shi ba gaskiya dan ya san wa ye shi.

Amma yanzu da Nabihat ta cika masa wannan kallon masifa haka, sai kawai ya ji wallahi hankalin sa ya tashi sosai, yana tuno maganganun mutane barkatai da wasu abubuwan da yake gani a fina-finai, wato idan macen da ta saba da maza ta ga namijin da komai na shi ya mata, ta kan gagara ɗauke idanu daga gare shi, hasalima burin ta ta birge sh... Kai! To ko wannan ne dalilin yarinyar da ko magana za ta mishi sai ta yi ta abu kamar mai son tayar da aljanu? Kallon ta gare shi, maganar ta gare shi, tafiya a gaban shi, komai sai kaga dai ba yadda ya kamata a ce cikakkiyar budurwa na yi take yi ba.

*Na* farko da ya iya daurewa ya ƙure fuskar ta da kallo saboda yana so ya gano me take tunani take kuma nufi da shi ƴar nan, yana so ya san me ye tunanin ta idan ta gan shi? Me take nufi da irin wannan kallon da take masa? Ƙara matsawa ya yi kusa da ita yana ci gaba da kallon fuskar ta da tasha kwalliya kamar irin ta ƴan Senegal ɗin nan a labta eyeshadow sosai, sannan ya gangaro kan wuyan ta dake da rama da ƙashi amma ya sha sarƙa mai kyau da kuma alamar tsada, a nutse ya ɗan kalli inda baya so bai kuma taɓa yi musu kallon su na kansu ba, wato ƙirjin ta... Har saida ya ji murmushi zai ƙwace masa, saboda yana kallon ƙirjin sunan wata halitta ce ta zo masa a rai, daga nan ya tsaya, dan tun a sama ma bai ga abun birgewa anan ba da ɗaukar hankalin da zai sa har yarinyar nan ta dinga ƙoƙarin sai ta ɗauki hankalin shi. Murmushi ya sakar mata saboda yana so ya tabbatar da tunanin shi, sannan ya raɓa ta ya wuce zuwa ga table ɗin ya ɗauki gwangwanin lemun ya sake juyowa.

Nabihat kuma har ga Allah ita kallon da ta ga yana ma Yusrah ne ya dinga bata mamaki har take masa wannan kallo, har fa gani ta yi Yusrah ta ɗora masa kyautar da ta bata a cinya kuma bai ce komai ba, to saboda me? Me ke tsakanin su? Yaushe aka ɗaura auren su bare ta ce har sun yi wannan sabon? Yanzun ma da kallo ta bi bayan shi sanda ya ɗauki lemun ya fice daga falon da niyyar komawa ɓangaren shi na da wajen uncle Sulaiman da yau ya bashi mamaki ya kuma gane ba ya tsoron Allah, ƙiri-ƙiri ya ce ba zai shigo taron nan ba tunda wai ai na ahali ne, sannan shi fa Baban Y. Turaki ne, to bari ya je ya masa kashedi kar ya sake yi musu irin haka, idan ya ce ya zo su yi abu to kawai ya taho ɗin, yanzu ma ba zai koma gidan sa bane saboda wataƙila Arif na can shi da masu gadin shi sun baza zaman asarar nan suna ziga masa shayi a tsakar gida, shi kam wannan abota da Arif bai san ya zai yi da ita ba, a kwanaki kaɗan yaron nan ya addabe shi... Murmushi ne ya suɓuce masa yana ci gaba da nufa ɓangaren, a yanzu kam zai iya sadaukar da rayuwar sa dan waɗannan aminan nashi guda biyu, Arif, Mukhtar, bai ta;a tsammanin zai samu wanda kawai zai dinga shiga masa hanci da faɗa masa magana kai tsaye ba sai ukun nan. Waɗancen biyun da ya lissafa da kuma wacce ta fi su gawurta da shahara wajen iya rashin kunya da raina manya sai *Y. Turaki*.

Aunty Fureira kuma sallama ta ma Yusrah da Safwan anan saman matakalar sannan suka sauko da rakiyar aunty Intisar, har saida Yusrah ta jiyo ta biyo su da kallo kamar za ta yi kuka ta furta "Dan Allah aunty fa nace?"

Juyowa aunty Fureira ta yi ta riƙe haɓa sannan ta kalli Intisar tace "Hajia Intisar ki gafarce ni, amma kinga ba dan kunyar ki da nake ji ba, wallahi da babu abinda zai hana yanzun nan in ma ƴar riƙon nan taki dukan tsiya, ka ji wani iskanci dan Allah? A ɗaura auren ki jiya, daga cewa baƙi na ƙauye za su tafi gobe za ki wani ce wai kina so ki zo ki musu sallama?"

Ƙwafa ta yi tana ƙarasa sauka, hakan ya sa Yusrah turo baki irin bata ji daɗi ba ta shiga haurawa sai dai a hankali sosai saboda riƙe take da Safwan, aunty Intisar kuma dariya ta yi tana sauka ita ma tace" Aunty, dan Allah to ko bayan bana nan a ci gaba da jin kunyata irin haka, idan an so a dakar min *aunty* a tuna da maraicin ta a yafe mata, kuma fa izini ne ta ce ki nema mata a wajen Anna, ina laifin ta?"

Kallon aunty Intisar ɗin ta yi tace" Na nema mata izini a wajen Hajia ni a wa? Ko ita Hajiar ita ce mai bata umarni yanzu? Shegantaka ce irin ta Yusrah kawai kuma ta samu kuna biye mata."

Ƙofa aunty Fureira ta nufa aunty Intisar kuma ta nufi wajen kayan ciye ciyen nan, a wasu mazubai da aka tanada irin na roba da basa bari abinci ya lalace dan har cikin fridge ana sakawa ta shiga zubawa aunty Fureira kayan ƙwalam ɗin nan tunda ta san can gidan ma da jama'a, to ya kamata su shaida an yi taron ba wa ƴar su kyaututtuka a wannan ahalin yau, saida ta gama zuzzubawa sannan ta ɗauka da ƙyar da kulawa dan kar su ɓare har ta samu aunty Fureira na shirin shiga mota dreba zai mayar da ita, nan ta zuba kayan aunty Fureira na faɗin har da wahala kuma haka? Ita kam da an bari wallahi, ba ta saurare ta ba ta ja ƙofar motar ta rufe mata tana mata fatan sauka lafiya.

*Yusrah* na shiga ciki kawai ita kyautar nan ta Nabihat bata kwanta mata a rai ba, sai kawai ta zaunar da Safwan bakin gado ta ƙarasa wajen wata drower ta buɗa ta aje kyautar sannan ta dawo ta zauna kusa da shi suna shiga fita tana masa tambayoyin da suka shafi lafiyar sa, shi kuwa ya zage yana bata amsa tare da saka mata sunan Dadyn shi a kowace kalma ta shi da zai furta, har saida ta kai ta taɓe baki ta ayyana _Kai dake yaro ne ai ka yarda ya zama Baban ka, ni kuwa da ban samu su Yaya Mubarak da Aba ba da sai dai na tabbata a marainiya, dan ba zan kira wanda ya jefani magarƙama a Babana ba, sam.'_



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:54 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨??👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*72*




Rakiya aunty Intisar ta yiwa aunty Furera har wajen motar da zata maidata sannan ta koma da ƙudirin faɗawa Anna maganar bankwana da ƴan garinsu Yusrah kamar yadda ta buƙata, tana shigowa ta samu Nabihat durƙushe a falon Anna ta haɗe kanta da guiwarta jikinta na rawa sosai, da sauri ta ƙarasa inda take tana kiran sunanta haɗi da kai hannunta ta nemi ɗagota still tana kiran sunanta.

Ɗagowar ta yi idanuwanta gaba ɗaya a caɓe da ƙwalla, fuskarta ta gama haɗewa da abin hodar nan da aka yi mata kwalliya da shi jikinta duk ta rikita shi, tana kallon aunty Intisar sai ta saka kuka, kuka mai ƙarfin nan mai ratsa zuciya sannan ta dafe ƙirjinta a bayyane ta ce" Na shiga uku, ya ya zanyi da raina? Wallahi na fita son sa, aurena fa aka yi shirin yi da shi, shine aka aura masa ita? Kina kallo abinda yake faruwa? Kina gani suke min abubuwan nan a gaban ki?"

Aunty Intisar na kallonta a duƙe kusa da ita, a tausashe ta ce" Nabihat, ki yi haƙuri ki sasauta kukan nan mu yi magana kin ji?"

Nabihat ta kasa sassauta kukan, sai da ƙyar ta iya sassauta shi dan ji ta yi zuciyarta zata buga, a lokacin nan da bata yi kukan ba da bata san ya ya zata ƙare da ciwon zuciya ba, a tausashe sosai aunty Intisar ta ce " Nabihat, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri kin ji? Tabbas zan baki haƙuri sosai domin ke mutum ce kuma ke mai rai ce, sannan kina da zuciya a ƙirjinki, haka kuma ban san girman soyayyar da kike ji a zuciyarki ta Akhi ba, abu ɗaya na sani shine dole a baki haƙuri dole a yi maki magana a tausashe, sannan zan baki shawara idan har ba zan takuraki ba."

Ta ajiye maganar a tausashe ainun tana kallon ta, Nabihat ta ringa gyaɗa kai tana kallon Intisar, duk da ta ciki na ciki dan ta ƙullaci ƴan uwansa da mahaifiyarsa sosai da sosai, dan wallahi ta yi alƙawarin duk ranar da zama ya zaunu ita da mijinta sai ta gasa masu aya a hannu saboda irin baƙin cikin da suka ƙunsa mata sanadiyar wannan auren, sai dai kulawar da aunty Intisar ta bata a yanzu ta birgeta sosai dan haka ta fuskance ta duk da babu babbar maƙiyiyar zuciyarta irin ta domin ita ce ta kawo Yusrah ahalin nan, da bata kawota ba da babu wannan maganar wallahi, sai gashi haka ta faru, babu damuwa dai a juri zuwa rafi tabbas sai ta raba a kan duk wani mai laifi a gidan nan.

Aunty Intisar ta yi murmushi a tausashe ta ce" Taso mu koma saman kujera mu tattauna."

Tashi ta yi ta bi bayanta suka zauna ɗin, aunty Intisar ta buɗi baki a tausashe ta ci gaba da faɗin" Nabihat, ki yi haƙuri, ba rayuwa zan koya maki ba, shawara nake son baki a matsayina na mace ƴar uwarki, Nabihat kin ga namiji ba'a yi masa haka balle irin mazan mu, ba'a ce kar ki nunawa namiji kulawa ba, ana so ki nuna masa amma saisa saisa, babbar kulawar da zaki iya yiwa namiji a rayuwa daga bakin lokacin da kika shiga ɗakinsa ne, wannan kuwa zaki yi kulawar ne bisa koyarwar addinin musulunci, wacce babu abinda ta bari, a nan zaki ci ribar kulawa da namiji ba a yanzu ba."

Kallon me kike nufi da take yi mata ya sa ta ci gaba da faɗin" Ki gane, auren nan da aka ɗaura da Yusrah ita da kanta bata sani ba sai da aka ɗaura ta ji da wa aka ɗaura mata aure, kenan kuwa a cikin tafiyar nan ina ga babu wanda ya tsammaci abinda ke jiransa sai da ya same shi, Nabihat ya ya zaki yi kwalliya da tufafin amare ki zo a irin wannan lokacin ki zauna ki yi tsammanin samun daɗin rai? Kin san idan har ke matar Akhi ce zata tabbata ko ana ruwan duwatsu ne, idan ta tabbata kuwa kina da naki lokacin wanda za'a daraja ki, za'a girmama ki sosai, amma a yanzu haka ɗin nan da kike yi in faɗa maki gaskiya kina ƙoƙarin zubar da kimarki daga idanuwansa ne da mu baki ɗaya, Nabihat ke da ya kamata ace kina can gida kin ɓoyewarki har sai mun je mun rarrashe ki? Ke da ya kamata ace a irin wannan lokacin kin zama tamkar gold kina ɓoye ki ja zarenki sai kin huce sannan ko da ido zai ganki ya ganki, amma shikenan sai ki taso ki zo, bayan kin zo kuma ki ringa abubuwan nan da na tabbata a wajen Akhi bayan ɓata masa rai babu abinda zasu yi, dan bai cika san ire-irin abubuwan nan na, Akhi yana da halayya daban da wasu mazan, abinda zaki yi dan ki birge shi ba lalle ne ya birge shin ba fa, ina mai tabbatar maki sai dai ya ɓata masa rai dan bai cika gane wasu abubuwan ba in dai ba shine ya sa kansa ba."

Aunty Intisar ta ajiye maganar tana kallon yanayin Nabihat dan kamar wacce ke harararta fa, kamar wacce bata gane abinda take faɗa mata, a tausashe ta ce" Idan na ɓata maki Nabihat ki yi haƙuri, na ga a yanzu ko Anna baki ba girmanta yadda ya kamata, tsakaninki da ƴan matan Anna kuwa ba kwa jituwa, tun kafin sanin idon ya gani cibi ya zama ƙari ai gwara ki yi haƙuri ki daidaita kin ji ƙanwata? Bari in je in haɗa kayana in ƙarasa gida dare na ƙara yi."

Daga haka ta miƙe ta haura sama, Nabihat kuwa ta rakata da kallo kafin ta taɓe baki ƙasa ƙasa ta ce" Ke ma zan rabo ki da ɗakin auren naki soon, tunda na kula sarakuwarki mahaukaciya ce zan samu abinda zai sa ta ce in mijinki bai sake ki ba Allah tsine masa, sai in ga ta iskanci da wani iya yi, aikin banza aikin wofi an ƙi a mutumta Anna ɗin, duk ba ita ce umal'aba'isin haɗa wannan ƙadararan auren ba, ƴan matan gidanku kuwa ai ni ba sa'arsu bace balle in yi abota da su, kaf ɗin ku zan saka ku a hannuna ne soon, mu je zuwa dai."

Intisar na haurawa tana ɗaga kira daga Akhi, a tausashe ta yi sallama tana buɗe ɗakin Yusrah ta shiga, bayan ya amsa ya ɗan yi jim kafin ya ce" Kin tafi gidanki ne?"

Aunty Intisar ta amsa a tausashe da girmamawa cewar bata tafi ba, ya ɗan ƙara yin jim kafin yace " Ok, mijin ƙanwar mijinki ya yi wata ƴar rashin jin magana, to shine dai an zane shi, to kuma dai ya ga fuskata shine matsalar, ta yiwu ki tarda wani abun da ba daɗi a gidan, idan kin san zasu iya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login