Showing 114001 words to 117000 words out of 397328 words

Chapter 39 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70063

murya ƙasa sosai Hajia ta ce" Tasneem, kin ga, Tasneem, jiya ba na maki magana ba? Me yasa bakya ji ne ke? Wuce ki tafi gidanki wuce kin ji?"

Tasneem ta kai dubanta kan Hajia, hakama Maryam wacce sai a lokacin ta ji hankalinta na neman tashi dan kuwa bata zo gidan nan dan ta ɗagawa aminiyarta hankali ba, wallahi kawai ta shiga abinda ba'a sakata bane dan ya zama dole, inna lillahi Hajia kamar zata faɗi haka idanuwan Maryam suka nuna mata, da sauri ta ƙarasa ta tallabi Hajiar dan kuwa har ta yi luuu...zata kifa
sai a lokacin Yusrah ta gani, hankalinta ya idasa barin gangar jikinta, da sauri ta tallabi Hajia Fatila kuwa da gudu ta nufi wayarta dan kiran Yayansu domin Hajia na da hawan jini mai ƙarfi ma kuwa, dan duk abinda ake yi na kai kawo ana kaffa-kaffa da lafiyarta sosai shi yasa suke kiyaye biyewa Tasneem dan ba wata riba sai dai a zazzagi juna gobema a kuma kawo rainin babu wanda ya taɓa taɓa lafiyar jikinta sai itama dake taɓa tasu dan a cikin su uku babu wace bata sha marinta ba.

Tasneem ta gyaɗa kai ta cije leɓe da sauri ta juya ta nufi galan ɗin nan, daidai shigowar mijinta tana faɗin" Bari ki ga, yau zan gwada maki ni mahaukaciya ce."

A rikice Fatila ta saki wayar ta rugo wajen Hajia ta kamawa Yusrah da Maryam muryarta na rawa ta ce" Ku kamata mu gudu ciki, Ku kamata kar ta ƙona mu ku kamata."

Jafar idanuwansa sun gama kaɗewa yana duban Tasneem ya ce" Tasneem , idan kika saki kika ƙarasa wajen su Hajia yau sai na tsinke igiyar aurena da ke, kuma ki ji sai na auri Yusrah na zauna da ita zaman aure, duk abinda zaki yi ki yi, ki fita ki bar gidan nan in ba haka ba yau sai na baki mamaki Tasneem, ki fita ki bar gidan nan."

Tuƙuƙin kalamansa ya saka Tasneem ƙarasawa inda suke tana buɗe galan ɗin ta ce" Ka sake nin in ka isa, ka sake nin idan har ka isa Jafar, wannan zaka aura ko? Idan tana raye ko? Bari ka gani."

Da sauri Maryam ta sakarwa su Yusrah Hajia ta tare galan ɗin da Tasneem ta buɗe suka shiga kokowa kan sai ta ƙwace ita kuma tana ƙoƙarin juye mata shi a jikinta tana faɗin" Bari in fara da ke dan wallahi baki isa ki mare ni ki ci banza ba."

Da sauri Jafar ya hayo carfet ɗin da takalmin sa zai ƙaraso dan ya ƙwace galan ɗin, sai dai yana daf da ƙarasowar Maryam ta samu ta ƙwace galan ɗin nan ta ɗaga shi a haukace ta juyewa Tasneem shi a jikinta gaba ɗayansa, ta saka wani ihu tamkar mai kamun aljannu ta juya da gudu ta nufi kicin tana faɗin" Ke dan ubanki bari ki gani, bari a maki aiki da ilimi, ni in ƙone kin in ƙone banza dan kuwa ke kika zo da shi zaki ƙona ni muna kokowa ya zubun maki kika ƙyarta ashana, ina ashana ke mai aiki bani ashana?"

Jikin mai aiki na masifar rawa ta raɓe jikin abin gas cike da tsoron Maryam dan ko kuɗi aka saka aka ce mata Maryam ba mahaukaciya bace ba zata yarda ba.

A falo kuwa Tasneem cike da matsanancin tsoro ta bi hanyar kicin ɗin da kallo, kunnen ta na jin abinda Maryam ta faɗa ko ta ƙaiƙayin da fetur ɗin ke yi mata a jiki bata bi ba, tana jin motsin fitowar Maryam daga kicin ta juya a guje ta zubar da takalmanta a nan ta fita a guje tana ihun za'a ƙonata ta faɗa mota a rikice ta tayar ta bar gidan jikinta na mugun rawa tana tuƙi cike da tsoron kar ta bi ta gefen da aka kunna wuta ta tashi da ita har ta isa gidan iyayenta tun a tsakiyar gidan ta je ƙarƙashin pampo ta sakarwa kanta ruwa tana ihun a bata sabulu ta shiga darzar jikinta sai a lokacin kunnayenta suka ringa amsa mata amon muryar Jafar yana faɗin " Tasneem na sake ki saki ɗaya!"

Dakatar da cuɗa sabulun ta yi kamar ta suma, lokacin da mahaifiyarta ta ƙaraso cikin tashin hankali tana tambayar lafiya, a rikice ta kalli maman nata ta fashe da kuka tana ɗora hannayenta bibbiyu saman kanta ta ce" Mama Jafar ya sake ni, Jafar ya sake ni ko? Jafar ya sake ni!"

Ita da kanta uwar sai da ta ji kamar juwa zata kwasheta, saki? Eh lalle yau dubu ta cika, Jafar ya saketa? Eh lalle yau sun shiga uku, daga su har ita sun shiga uku domin ƙaryarsu a duniyar nan ai ta Jafar ce! To ko gidan da suke ciki Jafar ya gine masu shi, filin kawai babansu ya siya shi kuwa ya sa aka gine gidan ya fiddo su a anguwa har suka zama manya suma, me? Saki? Ina ai yau sai ta faɗa mata abinda ta aikata ma Jafar yaro mai haƙuri har ya saketa, yau sai ta faɗa mata wani rashin hankalin ta aikata masa har haka ta faru, saki? Subhanallah!


*Zagaye* suke da Hajia a ɗakinta su huɗu, maganinta suka bata ta haɗiya shine suka zagaye ta kowa na tofa mata addu'a, dan kuwa asibiti yace a tafi Hajiar ce ta nuna a'a ba sai an je ba, idanuwanta a lumshe cike da auna abinda ya faru a yau, wanda ya zamo cikin tarihin rayuwarta, dan kuwa ta tabbata har ta mutu ba zata manta wannan rana ba.

Tarin tausayin Yusrah ya cike zuciyar Hajia, matsanancin mamakin Maryam da girmama lamarinta da ajiye lamarinta a cikin zuciyarta da wani tunanin daban wanda take ganin bai dace ta yi shi ba bayan ta yi shi a kan Yusrahrta ba kuma ta yi shi a kan Maryam ba, da mamakin ashe za'a wayi gari Jafar ya saki Tasneem? Tasneem fa ta taɓa buɗar baki ta zagi Hajiya, ashe za'a zo ranar da zai saketa? Da kuma tunanin yanzu sai me kuma suka sakata kasa buɗe idanuwanta a kwance da take.

Maryam tsoro sai yanzu ya kamata, balle da Yusrah ta ƙi kallonta dan kuwa idanuwanta na kallon ƙasa ne ta ƙi ko da kallonta ne, tsoro take ji kar ta yi fushi da ita, yanzu ta gama ce mata bata ji daɗi ba da ta daki Arifa sai gashi ta yiwa uwar Arifa rashin mutunci. _"Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, ya Allah ka sanyaya fushin Yusrah a kaina dan na san duk haukana ta fi ni, Allah ka sa ta gane na yi haka ne dan na ga matar bata da mutumci idan ma aka tsaya tsaf zata cinna mana wuta, Allah ka sa ta gane na yi haka dan in tsorata matar ne ta bamu lafiya ya Allah."_ Shine abinda take ta ayyanawa a cikin zuciyarta.

Yusrah kuwa, kanta dake ƙasa da idanuwanta tausayin Hajia ya gama kashe mata zuciya ta yadda ta yarda cewa ƙwarai duk daɗin zaman da take ji da irin yadda Hajia ta nuna mata ita uwa ce a wajenta zata bar gidan nan a yau yau, domin ita ba mahaukaciya bace ta sani cewar duk daɗin zobe bai yi ya wuyan hannu ba, babu wani anfani da zamanta zai kawowa Hajia sai ɓacin rai da tashin hankali, yau gashi har Hajia ce kwance ba lafiya sanadiyar ta? Ta tabbata matar Jafar ba zata taɓa daina halayanta kamar a kuntaciyar mahaukaciya ba, kalaman da take faɗa kuwa tabbas wata rana sai ta aikata dan kuwa ba kullum zai zamo Hajia ta tare mata ba, shin idan aka cin mata yaya Safwan zai yi? Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, yanzu idan ta fita ina zata je? Ya ya zasu yi?

Wata zuciyar ta bata amsa kamar haka _"Zan je gida mana, kafin na je zan fara zuwa asibiti idan dreban ya dawo mu yi magana ya baki ƙanena sai mu je gidanmu, duk da babu wajen zama mai kyau, na gyara wani wajen mu zauna kafin na kai shi asibiti a masa aikinsa, in ya samu lafiya kuma sai in samu sana'ar yi dan ki riƙe shi, amma idan na zauna a gidan Hajiya ya zamo. Azama silar tashin hankalin ta kullum ƴaƴan ta ma tsanata zasu yi, wannan mata kuwa ta Jafar bata sani ba, ko a makance aka kai ni gidan su na laluba in gudu dan a yanzu bani da gatan da zan yi faɗa da kowa, wacece ni da zan rama dan an zage ni? Duk wanda yake haƙilon nan iyaye gare shi, ya san in dai ya taɓo a tare masa ne."_

Jafar kuwa ciwon mahaifiyarsa ya fi damunsa, bayan wannan jinsa yake yi wani sakayau, yau ya rabu da ƙaya, yau zai je gida ya kwonta ya tashi lafiya lafiya, kai? Ashe zai iya sakinta? Ashe tana tsoron mutuwa? Bai san tana tsoron mutuwa ba ai da ya gwada shaƙeta ko sau ɗaya ne ko ta ji tsoron sa, lallai! Alhamdulillah ya godewa Allah ya godewa Maryam, aure kuwa ba fashi yanzu ya ga lokacin aure kuma a kwana kusa in sha Allah zai yi shi.

Fatila kam, rashin lafiyar Hajia kaɗai ya hanata kunna kiɗan ƙwarya a filin gida ta rausaya ta kuma yi kiran ƴan uwanta su tayata rausayawa yau Allah ya nuna masu ƙarshen marar kunya, ashe itama akwai wanda ya dameta a balaki? Kai jama'a...

Da ƙyar Hajia ta iya buɗa bakinta a hankali ta " Ja'afar, yaran nan su tafi ɗakin su su huta, sannan kaima ka je k huta ni fa Alhamdulillah hutawa kawai nake son yi kaɗan."

Jafar ya ƙara risinawa a hankali ya ce" Hajia, ko Fatila ta zauna kaɗan ko?"

Hajia ta ɗaga kaɗan tana murmushi ta dubi su Yusrah ta ce" A'a su yi tafiyarsu su dukansu, ka ga tashi ma zan yi na tuna ban gama magana da malamar yaran nan ba."

Ta idasa tana cicciɓawa da kanta ta tashi da kanta dan sun zaburo dan su kamata ta nuna zata iya, a dole suka fita suka nufi ɗakin Fatila.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*31*




Da mamakin jin wai Aba ne ya zo masa gida da sassafe haka ya fito daga ɗakin motsa jikin wanda ya kwashe sama da awa ɗaya yana yi saboda ya kwana biyu bai yi ba, baƙaƙen kayan na jikin shi sun matuƙar karɓar jikin sa da yi masa kyau, haka takalmin na ƙafar sa suma baƙaƙe masu ratsin ja da fari kamar dai kayan na shi suka amshe shi, sai ƙaramin lallausan baƙin towel mai ɗauke da tambarin *A Anza* da ƙasan shi wanda ba kowa zai iya ganin rubutun ba yana share gumin fuskar shi har zuwa wuya da damatsen shi da kuma wani matsakaicin gurde yana buɗe shi ya ɗaga ya ɗan sha ruwan ciki da ba masu sanyi bane ko alama.

Zaune ya hangi Aba yana wasa da su Mim da sai daren jiya ya taho da su, shi kaɗai ya samu kan shi da yin murmushi, wato maganar da Aba ya ce zasu yi jiya idan ya same shi office ita ce ya zo su yi nan gida? Tunda ya je office ɗin ya samu ya yi baƙi ya ce ya je kawai zai neme shi, kuma ga dukkan alamu shi ma Aba motsa jikin sa ne ya fito da yake yawan yi musamman ma tattaki a cikin unguwar tare da rakiyar Sk da abokan aikin shi.

Da fara'a ya ƙaraso tsakiyar falon yana tsayawa kusa da Aba ya miƙe tsaye daga shafa su Mim da yake yi ya dube shi yana murmushi yace "Jikan Anza, ga ka magunan ka sun fara gane wa ye mahaifin ka, ina shigowa suka tarbe ni fa."

Murmushi AA ya yi da mamakin maganar ta Aba yace "Aba, waɗannan fa magunan fikira ne dama, ta yadda duk mutum ya so yake renon su, suna gane mutum ta ƙamshin jikin sa, yau da gobe kuma Abana ai ta wuce wasa ko?"

Shi ma Aban da mamaki dan bai fahimce me yake so ya faɗa ba yace "Kenan har sun fahimci nawa ƙamshin?"

Murmushi AA ya sake yi ya kama hannun Aban suka nufi kujerar zama irin na turkish ɗin nan masu laushi ba masu kwalliya ba yana faɗin "Babu ranar da ƙamshin ka ba ya gauraya a jikina Aba, hakan ma ai ya ishe su gane girma da kusancin mu."

Ƴar dariya Aba ya yi yace "Hakane kuma, to ya ka tashi?"

Saida ya fara zaunar da Aban kafin ya ɗauko ɗaya daga cikin filon kujerar ya aje ƙasa kusa da ƙafafun Aba sannan ya zauna akan filon, hakan ya sa Aba ne a saman kujera shi a ƙasa saboda girmamawa, da ladabi ya amsa mishi da" Ina lafiya Abana, fatan kuma haka?"

Hannu ya kai ya shafa kan AA ɗin sannan yace" Alhamdulillah Allah kulli hal."

Sadda kan shi ya yi ƙasa ya furta" Alhamdulillah."

Sannan ɗakin ya ɗan yi shiru na sakanni, Aba ne ya fara da cewa" Jiya ka sameni office da baƙi nace ka je zan neme ka, shiyasa na zo da kaina gidan saboda girman maganar da zamuyi da kuma yadda nake so muyi maganar a sirrance ba tare da kowa ya ji ba."

Da kulawa sosai AA ya ɗan kalli fuskar Aban yace" To Aba, Allah ya sa dai lafiya ko?"

Numfashi ya sauke da ƙarfi yace" Lafiya ƙalau Aswan." Sai kuma ya gyara zaman shi sosai yana fuskantar AA ɗin cike da dattako yace" Magana nake so muyi da kai irin ta ɗa da uba, ina so kuma duk abinda zai fito daga bakin ka ya zama gaskiya za ka faɗa min, ka ji Aswan?"

Jinjina kai ya yi jikin shi na neman ɗaukar sanyi na taraddadin rashin sanin abinda za su tattauna ɗin, numfasawa Aba ya yi ya fara da" Aswan, ina ka je kwana kusan shida ba ka gidan ka kuma baka faɗa mana zakayi tafiya ba?"

Saida ya lumshe idanu saboda bai yi tsammanin wannan tambayar Aba zai masa ba, kai shi wallahi ya ɗauka ai an wuce wannan maganar kuma, ɗaga kai ya yi ya kalli Aban cikin tausasa murya yace" Aba, ku daina ɗaga hankalin ku a kaina, ba inda naje fa ina nan, kawai ina buƙatar kaɗaici sai na kaɗaice kaina, kuskurena shine ban sanar da ku ba, kuma na yi tunanin ganin bana aiki yanzu ba zaku ci gaba da ɗaga hankalin ku idan baku ganni ba."

Sai kuma ya sadda kanshi yana wasa da gourde ɗin hannun shi yace" Amma ku gafarceni, in sha Allah ba zan sake aikata haka ba tare da sanin ku ba."

Sam Aba bai gamsu da maganar tashi ba, to ai har jardin ɗin shi ya sa an duba masa, kuma a sanin shi da AA ba ya da wurin shaƙawata idan ba jardin ɗin tashi ba saboda ni'imar dake cikin lambun, wanda yanzu haka yana can ana ta cin moriyar kayan dake fitowa daga cikin shi wanda kusan zai iya cewa babu ce kawai babu, hatta attarugu wannan yana fitowa a gurin kuma ana ɗibar sa dan anfani. Sannan gona ma ya kira su can ko ya je ziyarar gonar ne duk da ba lokacin da yake zuwa bane? Amma aka ce da shi bai zo ba, to kenan ina yaje dan kaɗaicewa? Shi kam tsoro yake ji da rashin auren nan na sa wallahi.

Gudun kar ya ce sai ya takura sa kuma shi ba ƙaramin yaro ba ya sa yace "Shikenan na ji, magana ta gaba Aswan, har yanzu ba ka zaɓi ɗaya daga cikin zaɓin da na baka ba?"

Ɗan sosa ƙeya ya yi yace "In sha Allah Aba zan zaɓa, nan da wasu kwanaki."

Girgiza kai Aba ya yi da rashin jin daɗin amsoshin da yake samu kafin yace "Na ji shima, sai maganar aure, Aswan me ye matsalar ka da aure ne? Ko kuma kana da matsala ne da mata? Ko kana jin haka kamar baka son zama da mace, ko ka ji ka tsani mata gaba ɗaya, ko aure ma haka? Please son ka sanar da ni mahaifin ka kaji?"


Da yanayin tashin hankali AA ya kalli Aba yana gano girman damuwar su akan rashin auren sa, jiya sun yi maganar nan da Anna yau kuma da Aba, su kam me ya sa ba zasu fahimce shi ba? Bai da matsala da mace ko ta sisin kwabo, hasalima ya san abokiyar rayuwa ce *amma fa ta wasu* ba shi ba, sannan mace abar jin daɗin rayuwa ce ga wanda suka ɗauki hakan da girma, tunda shi yana rayuwar sa kuma hakan na masa daɗi bai da matsala, kuma tabbas shi ma wasu lokuta sha'awar ƴa macen takan bijiro masa, amma da ƴan ƙwayoyin shi da lipton yake kawar da ita, musamman ma yanzu da ake yawan saukar da lema gari sanyi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login