Showing 84001 words to 87000 words out of 397328 words

Chapter 29 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70085

sai yayi kashi a wandon sa ba tare da ya sani ba, sai kawai ya bada haɗin kai aka gama dukkan abinda ya dace aka miƙa shi ciki.



*YUSRAH*



Tuƙi yake yi hankalinsa a rabe, kunnayensa na sauraron mitar da matarsa ke yi dan kawai ya yiwa yarinyar da ake yiwa aure yau katifa da kuma kyauta wa mahaifiyar ta, yarinyar ƴar ƴar uwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya, amma Tasneem ke faɗan nan tamkar zata aro baki.

Huci Tasneem ta fitar ta ce" In ba kai ba Aban Momy, yaran nan girmamamu suke yi? Basa zuwa gidan mu, basa zuwa gaishe mu, sai dai ka ji labarin sun je gidan ƙaninka, amma ba dai su zo inda muke ba, a haka ka kashe dukiyar ka a kansu? Ai wallahi ni ko sisina ba zan ba mahaifiyar su ba, balle wai su, hum aikin banza sai da aure ya kusa take damuna da kira ko kunya bata ji!"

Wato idan TASNEEM na faɗa da zagin danginsa gaba ɗaya mantawa take yi cewar shi ɗin jininsa ne, takan manta cewa duk daɗin zobe bai yi ya wuyan hannu ba, bata san cewa ba maganar sabo ba kuma maganar ta zame masa uwa ko uba, sunanta matarsa, lalle da wahala a yi wanda zai kaita kusanci da shi a yanzu da rayuwa ta yi nisa har suka ɗauko shekarun da za'a masu kallon dattijai, ya zamo sun wuce misalin jeka ka dawo sai muguwar ƙaddara, hakan baya nufin zata taɓa maye masa gurbin ƴan uwansa ko mahaifiyarsa ba, ba ruwanta, bata masa kara, kanta kawai ta sani, a zamantakewar su idan zai ƙara danginta murna da farin ciki ba'a kaita, takan nuna masa taimako ya yi, ita ya yiwa ya gyara mata, amma idan nasa dangin ya shafa takan manta kanta ta manta komai, son kanta ya fito ƙarara.

Wani wawan tsaki ya ja tare da dukan sitiyari yana cewa "Kai! Kai Subhanallah! Tasneem da me zan ji? Tuƙi a wannan babban titi mai cunkoso? Ko da jarabar ki?"

Ai kamar ya ƙara bulbulawa wuta fetur sai kuwa ta sake gyara zama ta hayayyaƙo tana faɗin "Oh! *Jafar* ni ce ma ke maka jarabar? Saboda ba ka ɗaukeni bakin komai ba ko? To na yi magana Jafar ka yankani, gaskiya ce ba ka so na faɗa, amma ƴan uwan ka ba girmamani suke yi ba bayan kaf cikin su babu mai rufin asiri kamar ka, sannan kai ne ke share musu kukan su idan suka zo da shi, idan da mutumci ai kamata ya yi ina zuwa inda suke su dinga..."

A tsawace ya kalle ta yace" Tasneem ki min shiru, wallahi masifar ki ta isheni, da kike maganar ba sa girmamaki ke wane girman kike basu? Iye! Faɗa min wane girma kike basu da zai sa su san ke matata ce? Sai ke da kika fi kowa son girma da karramawa dan suna tsorrrrrr.... Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Shikenan, kin ja mana jafa'i hankalin ki ya kwanta."

Da mugun sauri bai ji amsar ma da take mayar masa ba cewa ita ba ruwan ta shi ne ai garin yi mata masifa ya kaɗe mutum... Kwance ya tarar da *Yusrah* wacce ke ta bulayin neman abun hawa tun fitowar ta daga PG, kuma tsabar kaɗuwa da ta yi da lamarin ya sa ta ƙi tsayawa tun a can ta samu abun hawa saida ta yo nisa da gurin, amma yunwar da ke ciciyar ta ga tarin damuwar da Allah ne kaɗai ya san adadin nauyin dake danƙare a ƙirjin ta ya sa idanuwanta suka yi ta ƙoƙarin liƙewa, da ƙyar da siɗin goshi ta kawo kanta bakin hanyar nan, amma tana zuwa za ta ƙetara ta ji jin ta ya sake yin nesa da ita, ganin ta kuma yana barin ta gaba ɗaya, bata ankara ba ta ji kamar an yi sama da ita haka kuma kamar an tunkuɗata da mugun ƙarfi, daga haka bata sake sanin me yake faruwa a duniyar mutane ba.

Turus ya tsaya yana kallon kyakyawa kuma farar fuskar da duk ta yamutse dan wahala da yanayin da ta samu kan ta a ciki, kayan jikin ta kan su ba wasu abun kallo ba, a dai yadda idanu suka nun ba wani mummunan ciwo da ta ji, dan haka ma da taimakon wasu daga cikin mutane suka bashi shawarar ya ɗauketa kawai zuwa asibiti, kallon Tasneem ya yi da gaggawa yana ranƙwafawa yace "Kama min ita mu kai mota?"

Wani irin yatsina fuska ta yi ta kalle shi sama da ƙasa tace "Ban gane in kama maka ita ba? Kai za ka taɓa ta da hannayen ka kuma?"

Wani kallo ya mata, amma sanin kaɗan ne a aikin Tasneem su tara jama'a anan bai dame ta ba sai kawai ya kalli wata mata cikin wanda suka tsaya yace "Dan Allah ƴar uwa kama min ita?"

Da sauri ta matso ta tallabi Yusrah wurin ƙirjin ta, har ya kama ƙafafun ta Tasneem ta tunkuɗe shi ba tare da tuna cewa shi ɗin mijin ta bane kawai ta kama ƙafafun Yusrah a wulaƙance har saida ɗaya matar ta kalle ta tace "Ke kuwa yar uwa tallabata da kyau, siket ɗin ta ya buɗe daga ƙasa."

Ba ta gyara ba sai ma harara da ta watsa mata, haka suka saka Yusrah a bayan motar da Jafar ya buɗe, godiya ya ma matar sannan suka shiga da sauri zuwa asibiti ma fi kusa.

Asibitin kuɗi suka kaita kuma aka karɓeta, dake ma anyi sa'a ba ta ji wani mummunan rauni ba, wajen guiwar ta ne ya bugu sosai inda motar ta dake ta har ya ɗan yi kamar ya lotsa, sai goshin ta da ta faɗi ba shiri akan kwalta shima ya kurje sosai haka ma kusa da guiwar hannun ta inda ta faɗi, bayan nan ba wani ciwo a jikin ta, nan aka kula da ita sannan aka saka mata ƙarin ruwa saboda bala'in sauron da ya cije ta a PG ɗin nan har ta fito tana susar jikin ta, duk da a lokacin ba zafi jikin ta amma a awon da suka mata ne suka ga zazzaɓin cizon sauron, dan haka suka mata rigakafi.

Ta yatsina fuska da taɓe baki ya fi a irga, har dai yanzu da nurse ɗin ta cirewa Yusrah hijabin ta, shafaffen cikin ta ya bayyana, faɗin kumkuminta ya fito ras kamar na wata yar rawa, ƙirjin ta ya tsaya wani cak da shi sai take jin hankalin ta na tashi sosai saboda gaba ɗaya Jafar ya kafe yarinyar da idanu sai kallon ta yake wai shi sarkin tausayi.

Gaskiya ba za ta iya jurar wannan ba, dan haka ta rangaɗa tsaki tace "To malam sai mu tafi ko? Allah ya bata lafiya, kasan ana jiran mu ai."

Kallon ta ya yi da ttsareta da idanu yace "Mu tafi ina? Mu bar ta a wannan halin da take ciki?"

Gyara tsayuwa ta yi ita ma tace "Ban gane a wannan halin ba? Me kenan za mu mata? Goyata da bata abinci a baki? Kaga malam dan Allah ka zo muje, iya haka ma da ka mata ai ƙoƙari ne, ka bada wasu ƴan canji kawai da za'a bata idan ta tashi ta ƙarasa jinyar kan ta."

Girgiza kai ya yi da mamakin hali irin na Tasneem yace" Amma dai wallahi ke baki da imani, yanzu idan ƙanwar ki ce a wannan halin za ki so a mata haka? Mu kaɗe yarinya bata farka ba muka bata ko da haƙuri, sai kawai mu sa kai mu tafi, mtsssss!"

Da hargagi ta matsa tana cewa" Jafar tsaki kake min saboda wannan *magen*? Yarinyar da baka sani ba za ka tsaya kana gaya min magana a kan ta, to ka wuce mu tafi ni na gaji da zama anan."




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*23*




Tunda aka shigar ɗakin sa da a dai ɓangaren kurkuku za ka iya kiran shi da ɗakin alfarma, saboda prison ne ba iya na masu manyan laifi ba, an yi shine ma dan killace manyan mutane da sunan an ɗaure su, ƙwaƙwaran tsaron da ake zubawa a gidan ne ya sa duk wani riƙaƙƙen mai laifi ake ajiye shi anan saboda ya kan yi wuya ya samu hanyar ci gaba da ta'addancin sa. A haka ma wai AA an ajiye shi a ɓangaren da ake ganin shi ɗin ba kowa bane sai mai laifin da ya daki jami'i, kuma a bayanan da ya bayar shine burin sa zai aikata wani ta'addanci ne da makamin jami'in, shiyasa ya ƙwata bayan ya sumar da shi, amma da za ka ga ɗaya ɓangaren da ake ajiye ƴan siyasa har su Kofa ma acan suke, da zaka yi mamaki a ce maka wai a cikin prison ne nan ɗin.

Kayan jikin sa ya fara cirewa yana sauke wani daddaɗan numfashi saboda samuk sukuni da duk wata fata ta jikin sa ta yi, a cikin kowa ɗaki akwai ban ɗaki, dan haka ya shiga ya samu ya yi wanka mai sunan wanka duk da yana jin shi kamar ba daidai ba saboda bai yi anfani da sabulun da ya saba ma kan shi ba, amma dai ya ji shi shaƙat haka ya fito ya saka kayan da ake aje masa na yadi, iya wandon ma ya saka ya kwanta ya tallabe kan shi yana kallon fankar dake juyawa da ƙarfi sannan ya shiga tunanin yaushe ne zai haɗu da Uncle Kofa? Kafin ya samu wannan mafitar nauyayyan bacci ya ɗauke shi saboda gida ne dake cike da manya, ko ɗan ta'adda ne to ka kai maƙura a harkar ka da wata hayaniya ma ba taka bace, aikin ka ne kawai yake shaida waye kai, dan haka a lokacin gidan yake shiru.

*Kiran* sallah azahar da aka yi a matsakaicin masallacin dake gidan ya tashe shi, nauyin da jikin shi ya yi yasa ya ƙara watsa ruwa sannan ya ɗauro alwala da gaggawa ya fita...

Saida ya yi dube dube kafin ya doshi inda masallacin yake, haka kuma duk wani da ya gani sai ya kalle shi da kyau amma ko mai kama da uncle Kofa bai gani ba, hasalima duk manyan attajirai da ma'ikwantan da ke wurin bai ga kowa ba, ɗaiɗakun dake nan duk kusan waɗanda bai sani bane, bai yi mamakin haka ba saboda manyan nan fa dama killace su dai ne ake kawai ba su da ƴanci na yawo a gari, amma ba ƙaramin tsaro ake basu ba gudun wanda zasu iya farmakar su ba'a sani ba, dan haka wasu daga ciki ma lokacin da ake kai musu nasu abincin daban yake, waɗanda kuma suka ji suna iyawa su suke girkawa a kuka gas ɗin su cikin nishaɗi.

A taƙaice dai haka ya take wannan rana babu wani abu da zai iya cewa ya fara cimma wa a wannan gidan, dare na yi aka kawo masa abinci mai rai da lafiya ya ci ya sake yin kwance, tunanin yaron yake yi da maganar shi da Dr. Siddik ta ƙarshe, musamman da yake bashi tabbacin Safwan zai samu lafiya, a yi ƙoƙarin fitar da shi waje kawai, dan inda da wuri ne aka kawo shi da an shawo kan matsalar, yanzu wannan aikin nan ne yake so ya ga ya cimma, ko bai gama ba zai gaggauta kai ɗan shi wajen magani, idan ya samu lafiya sai ya ci gaba da aikin nashi... Sai kuma ƴan matan sa biyu wato Meem da Angel. Murmushi ya yi sanda ya tuna su sannan ya gyara kwanciyar sa da tunanin dare ya ƙara yi ya yi nafilfilin da ya saba yi sannan ya kwanta.



*YUSRAH*


A rikice ta ce" Jafar, ka san na rantse maka da Allah ba zan bar ka a nan ba? Yau na ga masifa kai kawai idan ka ga mace baka da kunya sai ka yaba? Wannan ɗin ma haramun ɗin ka ce jafar, ka fice mu tafi."

Ganin haukan nata na hauhawa sai kawai ya bata baya ya ƙarasa bakin kujerar dake daf da gadon ya gyara rigarsa da nufin zama, bata ga girman shekaru irin nasa ba da matsayinsa na mijinta ta saka hannunta ta janye kujerar da ya zo da nufin zama, hakan ya sa ya yi faɗuwa irin ta wuntsilawar nan har ƙafafuwansa suka yi sama.

A rikice ya dafe ƙugu ya ɗaga idanuwansa yana kallon matar jaraba, matar bala'i, ƙadararriyar matarsa, wacce bata tsaya nan ba ta ɗauki takalminsa da suka zube ta kuma riƙe rigarsa tana ɗaga murya fiye da kima tana masifa ta ce" Ko ni ko kai, da in bar ka a gaban wannan gwara in raunataka in yi jinyar ka."

Ganin rashin kunyarta tamkar na bayyananniyar mai cinye ɗa a bayan uwarsa ne ya saka shi miƙewa ya ja tunga, domin ko ba komai ita ce macen, shine namijin, duk tsiya yana tirzawa, dan ma an girma ne yanzun bai cika biye mata a gaban ƴaƴansu ba.

Da ƙarfi ya turata yana faɗin" Tunda halin zamu raba a asibiti bismillah, ni da ke shege ka fasa."

Kamar da wasa kokawa ta kaure tsakanin wannan mata da miji, kokowar da ta saka Yusrah farkawa a firgice sannan ta zuba idanuwanta tana kallon ikon Allah, domin bilhaƙƙi take ganin mace da namiji na kokowa har ya zamo ya kaita ƙasa ya kama ƙafafuwanta ya ja ƙiiii ya tura ƙofar da nufin hankaɗata waje.

Ido ta rufe da sauri, dan a tunaninta wannan abin da take ganin ɗaya daga cikin firgitacen mafarkinta ne, waɗanda ta tabbata idan har ta farka ba zata taɓa komawa barci ba, sai dai rufowar ɗakin da ya yi da ƙarfi ya danna ya sakata ta sake ta buɗe idanuwan a tsorace ta zuba masa ido.

"Jafar, ni ka daka a kan wannan wacce ana gani an san ta bijirewa iyaye ta fito yawon kwalta ne ko? Zan je in samu Babarka in sanar mata dan wallahi wallahi baka isa ba, in kwana ina masifa baya ce min komai, ke kuwa tsohuwar yar kwalta ki farka ki kama kanki ki nemi wani abin bin ba dai mijina ba, dan wallahi a kan mijina raina fansa ne, iskancin banza da wofi!"

Alamu na ana umartarta ta bar asibitin ne ya tabbatar masa cewar eh zata nufi wajen Hajia da maganar nan dan an koreta ne, dan haka sai ya rintse ido ya sauke ajiyar zuciya fiye da kima kafin ya juyo yana share zufa sai idanuwansu suka haɗe da na Yusrah dake kallonsa tamkar ta samu baƙuwar halitta.

Ɗan turus ya yi, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya ƙaraso yana ƙoƙarin zama, da sauri ta so janye ƙafafuwanta, sai dai kumburin da suka ɗan yi ya saka ta bar su tana rintse ido haɗi da neman ɗauki a wajen Allah a can ƙasan zuciyarta.

"No, ki yi haƙuri, ki yi a hankali ƙanwata, babu abinda zan yi maki, nine na buge ki da mota kuma na kawo ki asibiti ne, please calm dawn." Ya faɗa a sanyaye har muryarsa na shaƙewa yana kallonta.

Ido ta sake zuba masa, murya a can ƙurya ta ce" Ina son tafiya, babu abinda na ji, ina so na tafi yanzu."

Da mamaki yana kallonta ya ce" Tafiya? Ki je ina?Idan gida zaki je ki bani adireshin ki in je in sanar da iyayenki, amma a haka ai ba zan bari ki kama hanya ba, bayan kin ji rauni."

Idanuwanta ta kai ƙasa ta sadda, sanadiyar faɗar cewa yana so ya je ya sanar da iyayenta, a hankali ta yi ƙoƙarin sauko da ƙafafuwanta tana kallonsa, ƙasa ƙasa sosai ta ce" Iyayena basa raye, ka yi haƙuri, tsautsayi ya sa ka bige ni, bayan shi ba komai, zan tafi, inada da *WATA TAFIYA* a gabana wacce mahimmancin ta ya fi zaman nawa anan."

"Ya salam! Innalilahi wa inna ilaihi raju'un, i'm sorry, Allah ya masu rahama" Ya faɗa a sanyaye ainun,
sai kuma a sanyaye yana kallonta ya ce" Amma wace irin tafiya ce wannan da ta fi lafiyar ki?"

Yusrah da ta miƙe tsaye tana lumshe ido, a hankali ta ɗauki hijabin ta da har yake wani ƙarni ƙarnin rana ta kaɗe ta saka muryarta a disashe ta ce" Ba zaka gane ba, tafiyar ita na fi buƙata."

Magana take yi tana juwa, haka kuma tun daga kanta har ƙafarta kana kallo zaka fahimci abinda ta fi buƙata a yanzu shine ta yi wanka, ta ci abinci, ta huta, haka kawai yake bin ta da kallo yana ji a can cikin zuciyarsa ko wace irin tafiya take magana a kai tabbas mai mahimmanci ce kuma mai hargitsi ce, tausayinta ya ji ya kama shi fiye da ɗazu bayan babu abinda suka haɗa da juna.

A tausashe yana kallonta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login