Showing 198001 words to 201000 words out of 397328 words

Chapter 67 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70092

dan haka ta je ta buɗe plate ɗin ta ita ma ta zauna daf da su tana ɗan jan su da fira kaɗan kaɗan suna amsata har suka gama sannan ta umarce su kan su ɗauro alwalla su yi sallar azahar, Anna ƙarama kam sai da ta kasa ɓoye damuwarta ta ce" Aunty kin ga a can mama ƙarama idan zamu yi sallah sai tace munafukai ne mu mu fake da sallah dan kar mu yi aiki, kuma sai Uka ta hana mu faɗawa mom wai kar mu ɗaga mata hankali, kullum sai in mun zo barci muke yin sallar."

Yusrah ta zubawa Anna ƙarama ido, wani abu ya tsirga mata zuciya, a hankali ta ce " Mama ƙaramar nan, ƙanwar Dadynku ce?"

Kai ta gyaɗa ta nufi bayin, domin a lokacin uka ta fito, ta ɗauki jaton hijabin Yusrah na sallah ta saka ta kabarta sallah ta shiga yi, Yusrah na kallonta tana irgawa hatta sallar asubahi a lokacin ta yi, ta yi azahar ɗin ta sallame ta yi addu'o'i sannan ta ba Anna ƙarama ita ma ta kabarta sallar.

A nutse Yusrah ta ce" Zo mu yi kiran aunty."

Ta faɗa tana dannawa Aunty Intisar vidio call, sace ke cen cikin kuka, ta rasa ya ya zata yi, tana jin tsoron kiran Akhi, kuma tunda suka zo yaya Mubarak mama ta yi kiransa sai faɗa take yi, bata san dai me yake faruwa ba har yanzu bai dawo ba, ɗaga kiran ta yi da sauri har jikinta na rawa.

Fuskar wacce ta gani a kusa sosai da Yusrah ya sakata sakin murmushi tana langwaɓar da kanta a hankali ta furta" Ukahhh, ke ce?"

Mabruka ta sauke kanta hawaye ya ɓalle mata, yarinya ƙarama haka ta iya cinye ɓacin rai da tashin hankali, ta ɗago kanta leɓenta yayi jajir hawaye na ta gudu kamar tana raɗa ta ce" Momy, ni ce, ga Anna tana sallah, mumy muna tare da dady2, muna wajensa Momy."

Intisar na sharar hawayenta ita ma a hankali ta ce" Me ya faru? wani abu aka yi? Dady2 ya yi faɗa ne?"

Yanzu kam Mabruka sai ta fashe da kuka, ta ɗora kanta a ƙirjin Yusrah dake kallonsu idanuwanta cike da hawaye, sai da ƙyar ta iya ɗagowa tana kallon Intisar muryarta na rawa sosai ta ce" Mumy dukan mu suke yi, mumy har school suke hana mu zuwa, ko sallah basa yarda mu yi a kan lokaci sai su ce wai dan kar mu yi aiki ne, mumy kullum cikin duka muke, prince ma kullum sai yana dukan mu bamu isa mu rama ba, idan aka bamu waya dan mu yi magana da ku sai mun yi wanka mun saka kaya masu kyau ana zaune a gaban mu muke yin wayar, mumy...." Sai kawai ta idasa fashewa da kuka.

Intisar da ƙirjinta yake ta tafasa ta ɗago idanuwanta suka sauka a kan Hajia da ta shigo ranta ɓace, Bilal da yaya Mubarak suna dakatar da ita ta ƙiya ta zo ta ce" Intisar, kin tura yayanki ya je ya daki mijin yarinyata ko? Ba damuwa duk irin halaccin da ta maki ta riƙe maki ƴan mata shekara nawa a hannunta ya riƙe maki yaya bai ƙi riƙewa ba shine za'a yiwa sakayya da duka dan kawai ya je ya samu yara na wanke kayan makarantar su? Ai ba laifi an gode Allah ya saka da alkhairi, amma ni ba ruwana duk irin hukuncin da zasu ɗauka su ɗauka, duk wanda ya ja ruwa ruwa ya dake shi, kai kuwa Mubarak ta maka kyau, ba dai ba yau har ɗaurewa matarka kake yi bayan baka san abinda ya faru ba ka nuna bata da laifi kuma ka tabbata Yayanta ba zai yi abu cikin rashin ilimi ba ko? Na ji, mune mararsa ilimin na gode!"

Daga nan Hajia ta juya ta yi tafiyarta ranta ɓace ya rage Bilal kawai dan yaya Mubarak ya bi bayanta dan ya rarrasheta domin ba zai taɓa iya bari ta je ranta a ɓacen nan har haka ba, tana iya yin kuka dan ɓacin rai, abinda ba zai taɓa yarda da shi ba kenan, ko menene halayyar mahaifiyarsa zai bita sau da ƙafa da fatan Allah ya sa su rabu lafiya ko shi ko ita, dan kuwa ya san duniyar ai ba matabata bace.

Zama Bilal ya yi yana dafe kai ya ce _" Anya kuwa wannan jahilar bata fita a musulunci ba? Kin ga yadda take magana? Kin ga suturar jikinta? Amma Hajia duk bata gani ba ta ɗauki abubuwan da suka faɗa, ni mijin nata kansa kamar a make yake kin ga goshinsa kuwa yadda ya zunɗume?"_

Intisar ta ja numfashi ta yi murmushi mai ciwo sosai sannan ta miƙe ta nufi ɗakin ta tana masa alamun tana zuwa, da ta shiga a hankali ta ce _" To ki daina kukan hakanan kin ji? Ba kin gani ba kamar yadda na faɗa maki da kika kirani da wayar ƙawarki? Mabruka innalaha ma'asabirin, komai rintsi kuma kar ki yada ibadar ki, kin ga Abanki bai taɓa sanin abinda kuke ciki ba, ni da kaina ban san abin har ya kai haka ba, ni dai ina ji a jikina cewar kuna cikin takura sai yanayinku da nake gani dake damuna, amma ban taɓa sanin cewa abin zai kai nan ba, ku yi haƙuri kun ji my babys, ga Akhi nan, ga kuma auntynku, duk abinda Akhi ya yanke a kaina ni da kaina mahaifiyar ku zan yi biyayya ne balle ku, duk abinda yace kar ku saki ku yi masa gardama, ku yi biyayya kun ji? Mu ma fa mun samu tahowa in dai wannan abin bai sa Akhi ya hana ni tafiya ba kwana kusa zamu haɗewar mu a cen kin ji in sha Allah."_

A hankali Yusrah ta ce _" Aunty, inaga fa da su zamu zo kamar yadda na ji ya faɗa."_

Aunty Intisar ta yi tsai na ɗan lokaci a hankali ta ce _" Shikenan ƙanwata, duk yadda ya yanke bani da ja, dan ko cewa ya yi ya katse auren nan wallahi bani da ja, dan na tabbata ba zai taɓa aikata aikin da ba tunani ba, dan Allah ki saka su barci ku huta zan yi kira da yamma."_ Daga nan suka yi sallama da wayar, tana ajiye wayar ta ga mijinta a tsaye hankalinsa gaba ɗaya ba a jikinsa ba duk ya fice a hayyacinsa.

Idanuwanta ta ɗauke, ta miƙe a hankali da nufin ƙarasawa wajen bed ɗin ta, a tausashe ya ce" Intisar."

Intisar ta dakata ta juyo tana kallonsa, a hankali ya ce" Idan Akhi yace zamana da ke ya ƙare kina nufin zaki barni?"

Intisar ta sauke idanuwanta ƙasa, a hankali ta ɗago tana dubansa ta ce" Aka yiwa ƙanwa biyayya ma balle Yaya? Ina ce a lokacin da tace a wajenta yara zasu zauna da na nuna maka bana so ka nuna min ba zaka taɓa hana mata ƴaƴanka ba, jininka ce, babu mai jin maganar nan karma na ɗaga rigimar da bani da riba a ciki, a haka na ɗinke bakina nake zaune, bani da damar jin ƴaƴana sai ƙarshen sati, shi ma] an sakanni an katse min, ban isa in tambayi ya ya suke ba sai ace ban yarda da riƙon da ake masu bane? In na nemi jin ya ya karatunsu sai a nuna min duk wannan ba hurimina bane suna karatu sosai suna lafiya, a haka nake rayuwa ina ganin tashin hankali a fuskokinsu amma ban isa in tambayi ba'asi ba, Mubarak an yiwa ƙanwa biyayya na ce balle Yaya? Idan ya ce ɗin zan yi biyayya ne kawai in yaso sai ka mayar da su can din ta riƙe, na tabbata wahala bata kisa duk rintsi kuma abinda Allah ya nufa ne kawai zai same su!" Ta ƙarashe idanuwanta a kansa tarr sannan ta shige bayi ta nufi wajen wanka ta barshi a sume a tsaye.

Tunda suke bai taɓa ɗaga murya ko ya yi kalar tashin hankali ta mayar masa da aniyarsa ba sai yau, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! A raba su? Lalle Intisar bata da hankali, to shi in ba muguwar ƙaddara ba wacce zata kai shi ƙiyama ai shi da matarsa sai mutuwa, tabbas ƙanwarsa ta saka shi a tashin hankali mai girman gaske, yanzu haka da ƙyar Hajia ta saurare shi, kuma yana zuwa nan ya tarda wani zafin? Ya so kiran Yusrah ɗin shi ma sai dai jin tace su huta ya sa ya bari ya nemi waje ya zauna yana jira ta fito daga bayin dan ya tabbata ba zata kwana a ciki ba.


*U.S*

Sun yi barci sosai sun huta, sallah kawai ke tashin su sai abinci da take saka su ci a kai a kai, sannan ta ringa ɗaukan hankalinsu da yan firarraki waɗanda tun suna ɗari ɗari da ita har suka zo suka fara sakewa, balle da ta ɗauko masu game bayan sun yi sallar magariba suka hau bugawa nan suka hau gardama da ƙoƙarin ganin sai an cinye juna sai dariya ta buɗe a tsakaninsu har aka fara buga ɗakin da neman izinin a shigo.

Ɗan shiru Yusrah ta yi domin bata yi odern komai ba, abincin darensu kuwa basu buɗe shi ba ma sai an jima dan a ƙoshe suke, miƙewa dai ta yi dan ta gani ta yiwu masu gyaran ɗakin ne, ɗazu ma da suka zo ce masu ta yi sun yi aka bata kayan gyaran, to yanzun ma zata ce ne su je sa yi, shi kaɗai ne aikin da zasu iya yi su dan motsa jiki fa, in ba shi sai dai a wuni a waje guda.

Tana buɗewa kanta na kallon baya tana ji Mabruka na ihun "Aunty wallahi zo ki ga ta maida ni gida, sai na rama Anna ƙarama sai na rama bari ki gani."

Ta yi yar dariya ta ce" Bari in zo a sake, yanzu ba zan yarda ku fitar da ni da wuri ba."

Tana gama faɗa ta juyo dan ta sanar da masu aikin a bari fa sun yi, sai ta ganshi tsaye hannunsa ɗauke da fulawa da kuma wani kwali yana kallonta.

Ido ta ɗan ƙiƙifta a hankali ta ce" Au! Kai ne? Shigo." Ta faɗa tana bada hanya, kansa ya ɗauke daga duban nata ya sauke kan su Uka da suka taso suma suna gaishe shi daga ɗan nesa da shi haka, hannayen nasa ya miƙa masu bayan ya saki murmushi ya sakar mata fulawar da kwalin chocolat ɗin.

Ƙarasowa suka yi suka kama hannayen nasa suma da murmushin a fuskokinsu, ƙasa ƙasa ya ce" Kun yi kuka ko?"

Aslama ta gyaɗa kai a sanyaye ta ce" Dady 2, mun yi kuka amma aunty tace kar mu sake ba zamu koma can ba ko?"

A hankali ya gyaɗa masu kai, sannan ya ce" Zamu je wajen su papy ɗin ku, idan cousin brother ɗin ku ya samu lafiya kin ji?"

Sun so tambayar waye hakanan, sai dai har zuwa lokacin ba wai sakewa suka samu yadda ya kamata ba, suna dai sakewar a hankali a hankali ne, shi ma kuma bai takura su ba ya masu nunin fulawar da chocolat ɗin tasu ce, ai kam da farin ciki suka koma, ita kuma ta zo zata rufe.

Har ya juya ya ɗan dakata ƙasa ƙasa ya ce" Idan an buga ku ringa sanin waye kafin ku buɗe, nd gobe ku shirya da wuri zaku je clinic." Daga haka ya yi tafiyarsa.

Ita kuwa harda ɗan ɗage tana leƙawa ta ga ya rufe ta taɓe baki ta dawo ta ga sun saka fulawar a cikin base da ɗan mamaki ta zauna tana yi masu tambayar ita ma ta ci ce? Hakan ya basu dariya Uka ta ce" Aunty ba'a cin fulawa, kin san wannan fulawar irin tsadarta kuwa?"

Ita ma da mamakin ta ce" To fa, ban gane ba, me ake da ita da za'a saka maƙddan kuɗaɗe a siya in ban da almubazaranci?"

Aslama ta ce" Aunty, signe ne na ƙauna, ana bada ta ga wanda ake so, ko ƴaƴa, ko iyaye, ko abokai, ko yayu duka kaf dai."

Yusrah ta ƙarasa saman bed ta faɗa tana faɗin" Wani iya shegen sai nasara, ku zo na kama blue." Ai kam da gudu suka je suna rigaye rigayen zaɓar color na ƴaƴan lido ɗin da suke yi a wayarta.

*Washe gari* haka suka ɗugunzuma suka tafi baki ɗayansu suka isa asibiti, sun ɗauki lokaci a wajen sa Yusrah na danna commande ɗin kujerarsa a hankali tana ɗan yawatawa da shi sunna ɗan fira da su Uka da shi, shi kuwa AA yana cen gefe zaune yana binsu da kallo har suka gama ya mayar da su ya yi shigewarsa cikin gari dan ya gama ƴan bige bigensa a ƙasar da yake da mutane sosai dan a nan ya yi karatu.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
31/05/2024, 10:44 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*51*




Lallai Anna ta ga aiki da cikawa, dan ita dai wankan kaɗai ta yi da ƴan shafe shafen ta da kuma sallah, ta je madafa ne dan ɗaukar abincin Aban da ta girka da kan ta su Nawal suka ƙarasa duba mata kawai ta samu Chef a falon suna hira ta kwana biyu basu haɗu ba, tabbas jikin ta ya bata maganar nan zai masa, amma sai ta yi gum suka dai gaisa ta tambayi Aba a zuba musu abincin? Da ƴar tsokana yace "To maman twins idan ba laifi nayi ake so a min horon yunwa ba ai yau tsohon naki ya yi juriyar yunwa ko? A zuba tunda ga Chef ai ba ya ƙin tayin madame ɗita."

Ita dai da dariya a fuskar ta ta shiga zuba musu cikin nutsuwa har ta kammala ta zuba musu jus ɗin da ta haɗa naturel sannan ta musu a ci lafiya ta fice daga ɗakin tana jin kamar ta kwaɓi Aban yaran, amma ta san ba zai dakata ba sai ya shirifta musu wani shirmen daga baya ya koma tambayar ta kin gani ko?

Bayan fitar ta sai da suka ɗan yi nisa da cin abinci sannan Chef ya ce "Elhaj, ka ce na zo kuma baka ce komai ba, ina fata dai lafiya ko?"

Kallon shi Aba ya yi ya ɗan sauke ajiyar zuciya ya ce "Hakane Chef, na san kuma kana uzirin ka na taso ka, ka yi haƙuri, magana ce akan ɗan nan naka da kullum yake caza mana kai, shin ko dan yana ɗan fari ne?"

Maganar Aban sai ta ba wa Chef dariya har ya dara kam sannan yace "Me ya sa ka ce haka Elhaj? Me kuma ya aikata yau? Ina ce ma ba ya ƙasar?"

Girgiza kai Aba ya yi yace "Chef, jikan Anza ko ba ya gari ai yana kawunan mu."

Murmushi ya yi yana jinjina kai yace "Hakane, me ya faru to?"

A tsanake Aba ya dubi Chef ɗin sannan yace "Chef, ina nemawa Aswan *auren* Nabihat, idan har baku mata miji ba sannan babu damuwa game da hakan?"

Tashi ɗaya Chef ya ƙurawa Aba idanu, kallon mamaki ne? Tsoro ne? Al'ajabi ne? Bazata ce? Sai ya rasa wanene a ciki kawai ya ke ta kallon shi saida Aba ya sake cewa" Nasan za ka yi mamaki dama, amma ka fi kowa sanin yadda na damu da ya yi aure, sannan ka san yadda ya ɗauko maganar yaron nan Safwan, Chef ta ya zai riƙe babu mata a tare da shi? Sannan wacece za ta yarda farat ɗaya ta aure shi ta zauna da yaron tsakani da Allah ba dan abun duniya ba? Ni a ganina sai dai ta gida, shiyasa na nemi wannan haɗin, amma fa idan ka ga ba wata damuwa?"

Da sauri Chef ya girgiza kai yana faɗaɗa fara'ar sa yace" Ah haba dai Elhaj wata irin damuwa kuma? Ko ma an ma Nabihat miji ka zo da maganar nan ai kasan za'a baka, kai ma fa ubane gare ta mai ba wasu, wallahi ba wata damuwa, Nabihat ai yanzu haka tana gidan ka, san haka na ɗauki wannan kiran a matsayin karramani ne kayi dan na zama wanda ya fara sani, sauran aiki kuma ya rage naka, ni nawa aiwatarwa ne kawai."

Da farin ciki Aba ya shiga jinjina kai yana faɗin" Alhamdulillah to, na ji daɗin jin haka, amma duk da haka zan so ka shawarci mahaifiyar ta, sannan ita ma Nabihat ɗin zan sa Annar su ta mata maganar, idan ta amince ka ga shikenan."

Da wannan tattaunawa suka ƙarasa cin abincin su. *Sai dai* a cikin gida tunda Nabihat ta koma ciki da Anna ta dakatar da ita ta kira Maman ta tana wannan kukan, dan haka hankalin ta ya tashi tana tambayar ta _" Ke Nabihat lafiya? Me ya same ki? Me kuma aka miki a gidan kike kuka? Ko mutuwa aka yi?"_

Cikin kukan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login