Showing 273001 words to 276000 words out of 397328 words

Chapter 92 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70116

shi dan ba dukiya gare shi ba sai karatun, shi yasa ta sanar masa amma sai ta ga kamar shi bai ɗauki abin yadda ta ɗauka ba, duk da haka dai ta gyaɗa kanta tana faɗin" Eh Aba, dan Allah ka je ka mata wata addu'a ta samu barci ta yi haƙuri, auren nan nima ai zan samo mata mai kuɗin in aura ko?"

Kai ya dafe da hannayensa yana faɗin" Inna lillahi wa ina ilaihi raju'un, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, ke ƴar nan to shi mijin dama ke zaki ba kanki? Dama abin na Hinda har ya kai nan? To ai babu maganin da za'a iya yiwa Hinda, hassada ta gama cinye duk wani imanin Hinda, kin ga bari ki ji, wallahi wallahi ki sanarwa Hinda na saketa saki uku, ba zan kuma iya zama da ita ba, Hinda ta yiwa jininta haka balle ni? Idan ƙarfina ya ƙare na san a bola zata saka ni, wallahi ba zan taɓa ci gaba da zama da ita ba in mutu Allah ya ƙona ni saboda maƙotaka da ita, ki sanar mata zan ɗauki matata mu je inda Allah ya bamu, ku kuwa Allah ya raya duk inda nake zan zo in neme ku, amma Hinda kam a yanzu ta fi ƙarfina."

Yana gama faɗa ya sa kai ya tafi hankalinsa tashe ainun yana ji a ransa bashi da nadama a kan haka, wallahi ba zai kuma ci gaba da zama da ita ba, duk abinda take yi uzuri yake yi mata da tunanin zafin zama irin nata ne kawai ya sa, amma a yau ya gane banda zafin zama bata da imani, ba zai zauna ba wata rana ta kashe shi saboda naira ba, abin Hinda ya girmami tunaninsa, ita kuwa mutuwar tsaye ta yi tana kallon babanta har ya ɓacewa ganinta sai kuma ta zaro ido tana ɗora hannu a kai ta ce" Kai, an saki Mama? Tashin hankali, wallahi bari in faɗa mata tun kafin ka yi nisa ta neme ka ku sasanta abinku, saki fa?"

Ta runtuma ɗakin da mararsa lafiya ke kwankwance tana ta ɗumumuwa da niyyar zuwa ta sanar Goggon abinda ya faru, dan kuwa ita wallahi babu ruwanta da wannan abin su sasanta kansu can.

Tana zuwa ta samu Goggo na ta wani ciccira kai tana mimimi da baki, sai kuma kaga ta buɗe idanuwa tar kamar tana ƙidaya taurari, sai kuma ta koma ta rufe, ba ta damu da halin da take ciki ba ta daddaɓata tana faɗin "Mama, Mama tashi, Mama kin ji wai Baba daga na gaya mishi abinda ke faruwa da ke shine wai ya ce in gaya miki ya sake ki, wallahi tashi ki bishi gashi can bai yi nisa ba, wai har da ce..."

Wata zabura Goggo ta yi tare da buɗa idanu tar tar a saman siling ɗakin, sai kuma ta miƙe zaune har tana rintse idanu saboda girman jikin ta ya sa ta ji ciwon haka ta dai daure ne, wata irin damuƙa ta ma Safiya tana jijjigata tace" Me? Me kika ce? Malam ya sakeni? Yana ina? Ina malam ɗin yake? Muje maza ki kaini wajen shi, ni malam zai tozarta? Muje dan uban ki."

Da ƙyar Safiya ta ƙwace daga riƙon sannan ta yi gaba Goggo ta biyota daga baya ko hijabi bata ɗauka ba, mutanen ɗakin na kallon su wasu sun ji abinda ya faru, amma ba wanda ya damu da tsiyar su kallon su kawai ake yi. Haka suka kama hanyar fita da sauri, sai sukayi karo da Khadija ɗauke da kwanukan abinci ɗaure, da mamaki ta aje kwanukan ta rirriƙe Goggon da tun daga nesa ta gane ba lafiya ba ta dubi Safiya a tsawaxe tace "Ke lafiyar ki kuwa? Ina zaku je? Me ya sa kika bari ta fito?"

Turo baki Safiya ta yi tana kawar da kai, sai kuma Khadija ta zubawa Goggo idanu dake faɗin "Wai malam ne ya sake ni, ni malam zai saka yanzu? Wa ya gaya masa aurena da shi mai ƙarewa ne? Ai wallahi mutu ka raba, sakeni na je na same shi tun bai yi nisa ba."

Wasu zafafen hawaye suka gangaro ma Khadija a sanyaye tace "Ki yi haƙuri Mama, Baba ya jima da yin nisa, a can muka haɗe da shi ya ce in baki haƙuri kuma wai gashi nan zuwa, Safiya ba daidai ta gaya miki ba."

Wani kallo ta ma Khadija kamar mai son gasgatata, sai kuma tace "Da gaske?"

Jinjina mata kai tayi tace "E Mama, muje." Ta faɗa tana juyar da ita dan komawa ciki, alama ta ma Safiya ta ɗauko kwanukan abincin sannan suka koma ciki.


*NABIHAT*

Kamar yadda mahaifiyar ta ta kitsa mata suka kuma shirya haka ta sake kamo hanya ta dawo gidan na su AA, saidai wannan karon salon da ta zo da shi ya fi duk wanda take zuwa da shi a baya, dan tsabar sun yi niyyar yaƙi da Yusrah da kuma kawo ƙarshen auren ta da AA ko Chef bai san ta dawo gidan ba, ta zo ne da niyyar ita ko Yusrah, sannan ta kaɓe duk wani da ya nemi shiga gaban ta ya hanata cimma burin ta.

Sai dai kamar yadda komai ke canzawa hatta Anna wannan karon duk son ta da baƙo saida ta ɗan yi jim da ta ga Nabihat ɗin, a tunanin ta matsayin ta na uwa ita ba za ta bari ƴar ta ta dawo gidan nan ba ko da an so hakan, ba dan komai ba sai dan kunya da kawaici, amma sai ga Nabihat ɗin har fa sun yi shirin kwanciya, ba ta nuna mata komai ko a fuska ba ta ce ta shiga ta kwanta dare ya yi, nan ta wuce tana gatsine gatsine da jin haushin Anna kan ta, dan duk sune suka haɗa wannan auren ta sani ai.

Twins ta samu a ɗakin su dan su kam basa rabuwa dama ko a gurin bacci, sai dai bata shiga ba tunda ita ma yanzu ɗaki gare ta a gidan, daga bakin ƙofa tace da su "Hi girls."

Ba ta kuma jira amsar su ba ta jawo musu ƙofar ta fita tana bankawa ɗakin harara, ɗakin Abrar ta kalla ta ja tsaki ta ayyana _'Yar wahala.'_

Sai kuma ta tura ƙofar ɗakin ta ita ma, tana tsaye bakin gado tana ɗaure zarigar rigar baccin ta iya guiwa fara sol da ta mata kyau, saida Nabihat ta ji kamar za ta suma dan wani sabon baƙin ciki da ya taso mata, tun daga ƙasan ƙafafun ta ta kalle ta fatar nan a kwance take sumul fara tas, zuwa rigar da ta ɗan bayyana surar ta sai dai ba sosai ba, zuwa gashik nan na Abrar da bata ƙaunar ganin shi, ita kullum a fama da gashi na ƙari, amma ga dubi Abrar har wani tattare sa tayi ta zuba cikin hula bayan ta gama jan tsaki kamar ma abun ya dame ta? Da ƙyar ta daure ta dubi fuskar Abrar din da ta zuba mata idanu tana kallo da mamaki tace "Sannu, *ƙanwar my Aswan*?"

Haka kawai yau Abrar ta ji dariya ta fara kubce mata bisa shirmen na Nabihat, da irin shaƙiyanci ita ma ta amsa da "Yawwa, sannu *ƙawar ƙawayen matar AA*."

Haɗe fuska Nabihat ta yi da mamakin Abrar ce yau ta faɗa mata haka? Sai kuma ta saki ƙofar ta shiga tana takawa da ɗaiɗaya tana faɗin "Aikin banza, ke da duk wani mai tunanin an yi wannan auren dan ya jima ne, to ki sani ba zai kai ko ina ba zai lalace, dan AA nawa ne ni kaɗai, ƴar wahala kawai mai bautar so a banza"


Karon farko da maganganun Nabihat basu mata zafi ba, dan haka ma ta murza tafukan hannayen ta tare da shafawa a fuskar ta sannan ta zauna bakin gadon ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallonta tace "Ƴar wahala? Ko kuma ƴan wahala? Ko da yake, zan iya cewa dai ƴar wahala ɗaya ta rage mana yanzu, wacce bata gaji da yankawa kare ciyawa ba, tunda ko ba komai ni yanzu na kama dahir ɗina, wanda yake sona ya ke kuma bani kulawa iya ƙarfin sa, kuma fa yana da lambata, dan har waya munayi da shi, nima kuma na riƙe lambar sa a kaina yanzu."

Ta ƙarashe maganar tana bushewa da dariya, ganin ta cika Nabihat ɗin fam saboda ta san magana Abrar ta faɗa mata kuma tabbas ta yarda ta yanketa sosai, tunda harafi ɗaya bata sani ba na lambar bawan Allahn nan, kai Allah wadaran wata zuciya ma wallahi. Miƙewa tsaye Abrar ta yi fuska a haɗe tace "Ke Nabihat kike ko? Kar ki ɗauka can da bana maida maki magana rashin iya hausa a bakina da kyau ne ya jawo haka, ko ɗaya, kawai dai bana son biyaki ne akan wanda bai san dukan mu munayi ba, kinga kuwa zamu tabbata ƴan wahala ne yaƙin soyayya akan wanda ko kallon fuskokinmu ba ya yi, amma yanzu da na haƙura na sallamawa Yusrah Akhi AA, sannan na samu wanda zai iya nunawa duniya har ma nace amini ne ga Akhi AA, to ba ke ba ko gyatumar ki zan iya maidawa magana idan ta nemi takani, ki sani ni fa haihuwar Tidin ce, idan baki san wacece ita ba ki tambayi Maman ki, ba arzikin Aba kawai muke ci ba a gidan nan, Mamana ma ba zaman banza take yi ba, idan ta so za ta iya ƙera nata gidan da ya fi naku ko da bai kai wannan ba, amma rashin dacewar hakan ya sa muke zaune anan, dan haka ni da hujja nake zaune a gidan nan, kar ki ƙara cewa za ki takani son ran ki, dan ba zan bar ki haka ba."

Tana gama faɗa mata ta sake komawa ta zauna ta jawo wayar ta, Nabihat na tsaye kamar wacce ta suma sai da ta ji muryar Mukhtar da Abrar ɗin ta kira kuma da gayya ta saka a speaker yana faɗin" My cute angel, dan Allah me ya sa kika kirani? Ki bari na kiraki ta WhatsApp mana dan in dinga kallon fuskar ki."

Murmushin mugun ta Abrar ta yi ta kalli Nabihat da ta ƙura mata idanu ta mata alama da gira kan ta fita mana cikin shagwaɓa sannan tace" Uhum uhumm! Ni dai wallahi bana so, na saka kayan bacci fa, sai ka kalleni kuma Yayana."

Rintse idanu Nabihat ta yi sannan ta yi ƙwafa ta juya a hassale za ta fice tana jin muryar Mukhtar na faɗin" Wayyo Allahana, habibaty za ki kasheni da komai naki, please ki sanar a gida zan kawo gaisuwa dan na gabatar da kaina a kuma bani ke."

Cikin jin haushi Nabihat kamar da ita yake ta banko ƙofar tana faɗin" Banza wahalalle."

Abrar na ganin fitar ta ta rufe fuska kamar tana gaban shi dan maganar nqn ma da ta yi dan ta ba Nabihat haushi ne, amma ba sa irin haka da shi ko kaɗan har yanzu.

Tana fita ɗakin ta ta nufa duk da ta wuce ta ƙofar ɗakin Yusrah kuma ta ji wani sanyayyan ƙamshin turaren wuta dake fitowa mai daɗin gaske, tana kuma kyautata zaton anan aka sauke ta, amma ai ba damuwa zuwan ta ne dama wannan karon, dan haka zasuyi ta haɗuwa ne har sai sun gaji.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
21/06/2024, 22:07 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*68*




*Safiyar* yau ɗin ma an waye ta ne da burin ƙarasa sauran abubuwan da al'ada ta tanada za'ayi kamar yadda ake ma kowace ƴa, musamman ma zuwa gaishe da iyayen Yusrah da yi musu godiya na basu ƴa da aka yi, sai kuma haɗuwar ango da amarya wajen Aba dan yi musu tashi kalar nasihar da gaba ɗayanta ya shirya yin ta ne akan bijimin ɗan nasa da yasan dole sai sun tanƙwarashi ko da Yusrah za ta ji daɗin zama da shi. Haka kuma a wajen su Anna ma rana ce da suka ware dan gabatar da kyaututtukan su ga Yusrah, wanda dama tun asali sun shirya yi wa duk wacce Aswan ya aura ko su ce duk wani ɗa ɗan ahalin su da ya aura, duk da kyautar ta kan zama ne bayan tarewar mata da miji, amma sai Anna ta canza tsarin musamman da lokacin kai kuɗin shi gidan su Nabihat ya nuna ga yadda yake so kuma suka yi, to yanzu su ma zasu yi gaban kan su ne saboda ba Nabihat bace wannan Yusrah ce.

*Da* fari Arif ne ya kira Aswan ya tambaye shi inda yake, buɗar bakin sa yace masa "Friend, gani a ƙofar shiga falon Aba, please ka tayani addu'a na shawo kan Aba, wallahi ban san me zan ce masa akan aikin da ya kaini prison ba."

Jin magana ce serious yake yi yasa Arif aje duk wata wasa a gefe yace "Friend, da fari ka nutsu sannan ka nunawa Aba ka yarda ka yi laifi, sannan ka nemi yafiyar sa iya iyawar ka, tare da nuna masa ka yi amanna da hukuncin da suka yanke a kan ka kuma za ka ci gaba da biyayya, in sha Allah ina tabbatar maka Aba zai fahimce ka."

Wata bazawarar kubtacciyar ajiyar zuciya ya sauke a tausashe sosai ya sake cewa" Allah ya sa, amma Y. Turaki fa?"

Da mamaki Arif yace" Me Y. Turakin ta yi?"

A ladabce kamar yana magana da Aba yace" Shikenan, ba komai."

Da sigar tsokana Arif yace" Kana jin faɗuwar gaba ne?"

Kamar Aswan zai yi kuka ya furta" E wallahi, haka nake ji tun jiya."

Sai kawai ya bushe da dariya yace" Matan kenan friend, matan kenan ai, sai ma kun haɗu."

Shashaƙai Aswan ya yi yana kallon ƙofar shiga falon Aba da yanayin waskewa yace" Tsoran ta nake aka gaya maka? Mtsssss! Dallah malam sai anjima."

Da gaggawa Arif yana ci gaba da dariya yace" Gamu nan zuwa gidan Aba mu tisaka gaba ka je godiya akan mata da aka ba ka, kuma dolen ka kaje wallahi ko Aba ya ji labari."

Taɓe baki ya yi ya kashe wayar yana ayyana _'Ba zan je ɗin ba, na ga mai ɗaukata, ni da aka wa auren dole, godiyar me zan je nayi to? Haɗani da sukayi da taɓaɓɓiyar?'_

Kawai ya soka wayar shi aljihu yana tunkarar falon Aba da salatin annabi da hailala da fatan bakin Aba ya ɗauru kar ma ya tayar masa da maganar komai.

Anan ya tarar da Humed yana faɗawa Aba wasu daga cikin baƙi da zai sallama yanzu, da farin ciki Aba yace mishi "Ka yi ƙoƙari jikan Anza, Allah ya saka maka da alkairi, ka gani dai kaine ƙarami, amma kaine ke ta ɗawainiya a sabgar Yayan ka da kake kallo kamar uba."

Murmushi Humed ya yi tare da ɗan sunkuyar da kai saboda idanun Aswan da ya ji a kanshi suna yawo, sai dai bai sani ba hararen shi ne yake yi ko kallon sa? Da kulawa sosai Aba ya sake duban Humed ya shafa kan shi yace" To ya, akwai cash hannun ka ko na ƙara maka wani abu dan sallamar baƙin namu?"

Da sauri ya girgiza kai a tausashe yace" A'a Aba ka barshi ma akwai, ai dake mun shirya ma bikin Akhi ne dama ba tun yau ba."

Wani kallon in ba mare ka ba ya mishi ɗan ƙwal uba nake wanda ya sa Humes na haɗa idanu da shi dan ya masa dariya irin ta tsokanar nan sai kawai ya miƙe yana faɗin" Aba bari na je kar su fara jirana, sai na dawo."

Da kallo Aba ya bishi bayan ya ga kallon da Aswan ɗin ya masa yace" To Allah ya tsare, amma fa kar ka manta anjima akwai bayar da kyauta ga amaryar Yayan ku, ka sani?"

Da fara'a ya juyo yace" Aba ai ba zamu taɓa mantawa ba, in sha Allah zan zo akan lokaci."

Saida ya fita Aba ya yi murmushi irin shaguɓan nan yace" Yaron kirki kenan, nan da watanni kaɗan fa uba zai sake zama a karo na biyu, hmmm! Allah dai ya maka albarka."

Sadda kai Aswan ya yi kamar mai raɗa yace" Nima da kun haɗani da mai hankali ai da nan da wata tara kun karɓi jikan ɗan Anza, mun fa san hanyar da ake bi ana yin abun nan, kawai take sanin ne mukayi saboda mun fi son halaliyar mu Aba."

"Magana ka ke?" Cewar Aba da ya ji kamar yana magana, da sauri ya ɗago ya girgiza kai alamar a'a da cewa "A'a ba komai, albarkar nace a saka mana mu ma, sai muyi irin ta su ko?"

Girgiza kai Aba yayi irin Allah ya shirya ka ɗin nan tare da danna wayar sa ya kara a kunne, Anna na ɗagawa a taƙaice yace "A turo min ƴata."

A ran shi ya ayyana _'Ya fi kyau dai ku zama ƴa da uba Aba, amma da abinda nayi tunani ya faru? Hmmmm!


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login