Showing 111001 words to 114000 words out of 397328 words
jin kin zagi babba, na rantse sai na tardo ki inda kike na zane ki, banza da ke ƙatuwar yarinya da ke baki iya kama bakin ki ba, wani yaro ƙaramin nema baya zagi amma ke ki kalli wannan ki zaga? Wuce ki je wankan da akace ki yi ki yi shi yanzu yanzu Ko ni da ke a gidan nan."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raj'un! Maryam ya haka? haba Maryam." Yusrah ta faɗa da ɗan ɗaga murya dan ta dawo da Maryam hayyacinta kar ta ja masu bala'i daga zuwanta.
Maryam da mamaki ta kalli Yusrah ta ce" Yusrah lafiyarki ƙalau? Yusrah yau ke ce da faɗin haka? Yaushe kika yi sanyi har haka? Haba Yusrah abin naki kar ya yi yawa mana, ke ɗin ce yau da faɗin haka?"
"Barka da zuwa Hajia, sannu da zuwa." Faɗar mai aiki ya saka Yusrah juyawa da sauri hankalinta na neman tashi.
Fatila da mamakin Maryam tana tsaye tana kallon ta wani courage na shigarta ta juya itama jin ana maraba da mamansu ta ƙarasa ta amshi jakar mahaifiyarsu tana yi mata sannu, Hajia ta ƙaraso tana sakin murmushi ta zauna tana fadin" A'a, ya haka kuke tsaitsaye, Maryam ko? Sannu da zuwa ƴata."
Maryam ta sosa kai ita ma kunya na ƙoƙarin rufeta ta duka har ƙasa ta gaisar da Hajia , cike da jin kunya ta ce" Hajia dan Allah ki yi haƙuri ba laifin Yusrah bane, hasalima bata san zan daki yarinyar ba, zagin Fatila na ga tana yi kuma ana ƙoƙarin kwatanta mata tana ƙi, dan Allah kar ku ga laifin Yusrah."
Hajia ta yi murmushi ta ce" Ke, tashi maza tashi, babu laifin wanda zan gani, ai dama zuma sai da wuta, dan kin daki yarinya ta yi rashin kunya sai a ga laifin ki? Bari in je in huta in baku waje ku zanta."
Daga haka Hajia ta nufi ciki, mai aiki ta je ta kai mata shayi da ruwa ta fito, tana fitowa ta yi waje dan kiran uwar ɗakin ta domin wannan bala'i ai yanzu yanzu zata sanar, kan uba lallai sai sun yi da gaske, wannan Yusrah dama ta san ba haka take ba, sanyi sanyin nan na munafurci ne, gashi ta yi gayya an daki Arifa, lallai za'a yi tashin hankali a gidan nan wallahi dan ko Hajia ai bata dukan Arifa.
Jiki a sanyaye Yusrah ta zauna ta zubawa Maryam ido da Fatila ke ta ƙoƙarin nuna masu lafiya lau, yarinya ai rashin kunya ta yi duka ta sha iya sha ba wata damuwa.
Murya a sanyaye Yusrah ta ce" Ba zaku gane ba, Arifa tana cikin yanayin da ba zata fahimta ta duka ba, yarinyar nan gaba ɗaya bata san soyayyar mahaifiya ba, bata san me ya dace ta yi da wanda ya dace ta kiyaye ba, bata iya bambance yadda zata yiwa babba magana ba, bata san yadda yiwa ƙarami magana ba, ƙarewa mahaifinta bata san ya ya zata yi magana da shi ba, ya ya zaki shige ta da duka Maryam bayan yaran nan abinda suke da buƙata su fara gane rayuwa su san su ɗin mutane ne masu daraja a cikin halittu, haka kuma basu fi kowa ba ko a wajen Allah sai in sun fi bauta masa, su fahimci menene mu'amala su iya bambance baƙi da fari, su koyi ba ɗan adam daraja koda yaro ne balle babba, a hankali ne yaran nan zasu gane abinda ake so su gane ba wai ta duka da zagi irin yadda suka saba ba, shikenan sai ki daketa?"
Baki Maryam ta saki tana kallon Yusrah, sai da Fatila ta gyaɗa kanta ta ce" Lallai aunty Yusrah, kin ga, ki gane, ba wai irin tarbiyyar da yaran nan suka samu ake yiwa haka ba, zuma fa sai da wuta, wallahi Yusrah duk abinda kika zayyano mun gwada amma in faɗa maki gaskiya babu wani result mai kyau kamar wannan na yau da na gani, dan tunda muke ba'a taɓa tanƙwarar da yaran nan suka tanƙwaru ba sai yau, kuma na gane idan suka samu wanda suke tsoro ko suke shayi tsaf za'a daidaita da su, ke uban fa ta fara zagi ko baki gani ba?"
"Bama wannan ba, duk na gane me Yusrah ke nufi, kuma na yarda ƙwarai idan suka samu haka za'a ji daɗin su, abinda ban yarda da shi ba daya6 ne a yanzu, ƙwarai a yanzu sai sun gane ba su kaɗai suka iya rashin kunya ba, ba su kaɗai suka iya ɗaga murya ko duka ba in har za'a ji daɗin su, koi yi haƙuri Yusrah amma bari in tuna maki yaron da kika zane har aka kai ƙarar mu polise station a ƙofar makarantar su inda muke zuwa mu sayi awara mu karya, wanda ya cira jakar Yayarsa ya kuma mari Yayarsa, dan kawai ta ƙi bashi cenjin mamansu, kika daki yaro kamar an aiko ki, me yasa kika dake shi? Kin san shi? To abinda kika ji a lokacin shi na ji a yanzu, kin san inada ƙannai mata idona ya haska min ace husna ce ta aikata haka, ta zagi babba, ko ta yi zagi gaban babarmu, taɓdijan, kin ga kawai ki yi haƙuri na zo dan mu ji sanyi mu jajanta rayuwa na ɓata maki rai ki yi haƙuri my kawa." Maryam ta faɗa tana sakarwa Yusrah murmushi.
Yusrah ta girgiza kai, domin an gama ai, an riga an yi, sai fatan a kiyaye, ita bata so ta dakar masu ƴa ba, daga zo mu ci tuwo sai ka fi mai tuwon loma? Bai dace sam ace dalilinta an daki yaran nan ba, dan bata son fitina, bata son abinda zai haɗata da mamansu sam, ba dan bata cike da son make bakin yaran ba, kawai kawar da kai take yi dan a zauna lafiya, dan bata san yaya girman kaunar ƴaƴan nan a zuciyar kakarsu ba, wasu basa so a taɓa masu yara fa, ko me suka aikata, sai ga Hajia baba ta aikace ƴar mutane daga zuwa.
Fira suka shiga taɓawa, yawancin firar kuwa a tsakanin Fatila da Maryam ne, Yusrah ta shiga kaye kayen kayan abincin nan ta shiga zuba masu, Fatila kuwa gaba ɗaya fira ta baje dan a duniya tana son zumunci da mai irin ƙarfin halin Maryam, domin itama tana ji tana gani gidan mijinta ya fi ƙarfinta saboda ƙannensa dake zuwa su zageta tassss su wulaƙantata, aka nuna ta ƙwaci kanta, ita kuma ta rasa ta yaya zata ƙwaci kan nata? Ta ina zata fara? Tsoro suke bata fiye da tunanin bawa, yanayinsu kaɗai ke tsoratar da ita, har ta kasa zama tana son mijinta yana son ta sai haƙura ta yi da shi, ko yanzu yakan zo zance , amma ta kasa bashi dama dan bata ga yadda zata iya zaman aure haka ba, idan ba zai iya tsawatarwa ba bata tunanin ita zata iya, auren su ko zaman wata huɗu na kirki basu yi ba ya rabu.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*30*
Zuwa karfe goma sha biyu na rana Fatila ta ɗaukowa Maryam kayan kitso suka saka Yusrah a gaba kan sai an yi mata kitso.
A rashin yadda zata yi da su dole ta buɗe kan nata ta zauna Fatila da ba iya kitson ta yi ba sosai, kawai dai a dole take so ƙawar ta ta ta ƙara sakewa ta shiga cazar kan tana tsagawa da yi mata manyan kitso tamkar mai takaba, ita kuma tana jin daɗin yadda take yiwa kan domin kamar tana sosa mata amaddari ne, mai aiki kuwa na kicin tana girki na alfarma kamar yadda Hajia ta umarta, yaran Jafar kuwa suna baya tare da sabon malamar islamiyar da Hajia ta ɗaukar masu , maƙociyar su hajiyar ce, shekara kusan biyar da mijinta ya rasu ya zamo tana bada lesson na boko da islamiyya a gidajen masu buƙata da kuɗi mai ɗan yawa domin bata wasa da aikinta, kuma duk yaron da ya zamo ita ce malamarsa zaka ga masha Allah yaron akwai mayar da hankali da hazaƙa sosai.
Muryar mai gadi dake tare hanyar shigowa yana magiya sama sama kamar haka ya saka su miƙewa gaba ɗayansu suna kallon ƙofar" Hajia dan girman Allah ki yi haƙuri ki koma kar ki ja min matsala da aikina, kin ga tun jiya Hajia babba ta min kashedi a kan irin haka, wallahi na zata Elhaji ne da motar nan ya sa na buɗe, Hajia ki bani galan ɗin nan kar ki yi aikin dana sani da girman ki da darajar ki da ƴaƴanki ki rufawa kanki asiri kar zuciya ta kai ki ta baro, Hajia dan Allah ki juya kar ki sa in taɓa ki dan in hana ki shiga falon nan."
Irin faɗuwar da gaban Yusrah ya yi sai da ta rintse ido, lokaci ɗaya wani irin zafi ya nemi rufe hancinta da ƙofofin fatar jikinta, hakan ya sa ta ringa neman layi tana fitar da huci a hankali a hankali idanuwanta a kan Fatila da ta ɗora hannayenta saman kanta ta ce" Yau mun shiga uku da masifar wannan mata, meye kuma ya kawota bayan jiya Hajia ta mata kashedi? Ai ba zata taɓa barinmu mu shaƙi iska ba tunda ta yada ido ta ga Yusrah, dan masifa a haka mijin nata bai ma ce yana son Yusrah ba fa? Ku wuce mu je ciki kar ta iskomu nan ta jinyata wata a cikinmu dan kuwa in bayan an jinyataka aka baka haƙuri kai aka cutar."
A ƙofar falon kuwa Tasneem ta ƙarewa mai gadi kallo ta gyaɗa kai da wani mahaukacin ɗaurin ture ka ga tsiya hannunta na hagu da baya riƙe da galan ɗin fetur din da ta ciko dan litter biyar ta nuna masa ta ce" Da kaf danginka sai na ɗaure su idan ƙazamin hannunka ya taɓa lafiyar jikina, ka san wacece ni? Ka san mijina sarai a kaina zai iya ɗaure har babarka, dan Allah matsa min ni in shiga ƙazamin banza da wofi algungumi ai da kai ake haɗa bakin ana cin dunduniyata, to wallahi sai dai duk wacce za'a yi a yi a kan mijina sai in yaƙi duniya."
Tana gama faɗa gadan gadan ta nufo shi, hakan ya sa ya kauce ya bata hanya da sauri ya juya ya ciro wayarsa dan kiran oga Jafar domin ba zai taɓa yin shiru matarsa ta shiga da galan ɗin fetur ta yi wani haukan ba, kai yana tur da halayyar matar nan kuma yana ganin laifin Jafar, domin duk a ganinsa shi ya bata dama take wannan iskancin, yo shi da yake talaka in matarsa ta isa ta zagi ko ƙanwarsa Allah ya tsine masa, koda yake ƙanwar tasama tana girmama matar tasa kamar yadda take girmama shi, kai shi bai ma ga isa a wannan lamari ba, mace kamar ƴar tinkiya, sam bata da alƙibla, sai hauka kala kala, bata girmama mijin nata balle mahaifiyarsa.
Tana shigowa ta ajiye galan ɗin tana binsu da kallo su ukun. Fatila da jikinta ke rawa ganin galan ɗin ta haɗe hannayenta ta ce" Aunty Tasneem dan girman Allah ki yi haƙuri, wannan fitinar da kike yi fa babu abinda zai sa ki yi, kin ga Yusrah dake zaune a gidan nan babu abinda ya haɗata da mijin ki, ki tambayi Hajiya ki ji, dan Allah ki yi haƙuri ki barta ta yi rayuwarta ita ma babu abinda ya shafeta da ke."
Sai da ta yi ƙas ƙas da cingan tana kallon Fatila ta yi wani murmushin duniyanci da tarin masifa ta ce" Nan ɗin gidan ubanta ne? Fatila nace nan ɗin gidan ubanta ne?"
Fatila da sauri ta ce" Aunty, ki daina zagi dan Allah, duka abin nan bai kai cen ba, tunda ba gidanki ta je ta zauna ba dan Allah ki yi haƙuri ki barta haka."
Wata shewa ta yi tana dafe ƙugu ta ce" Wannan karuwar ta isa ta je gidana ta zauna? Ke ko ke ban yarda ki zauna min a gida ba saboda ai mace ce ke, mijina kuwa namiji ne, a wannan zamanin da uba ke danne ƴa ai sai da kakkau balle wata gardiyar yar wiwi da ta fito daga maɓoyarta ta naniƙewa mijina? Ke ko ke aljana ce sai kin bar gidan nan, bari ki ji bana gajiya da masifa, bana gajiya da balaki, bana gajiya da kai kawo, in tare ki a hanya in tare ki a cikin gidan nan in ba barin gidan nan kika yi ba sai na zama ajalinta, banza marar usuli, ki fita a gidan nan ko kuwa wa Billahillazi in sauye maki galan ɗin fetur din nan in ƙona ki na ƙona banza!"
"Wai wacece ke?" Maryam da ta yi mutuwar tsaye ta amayar da tambayar dake cikin zuciyarta ba tare da ta shirya ba.
Da sauri Fatila ta ce" Yanzu tsabar rufewar ido da baƙin kishin ki ne yau har ni kike yiwa wannan mugun fatan da mijinki uban ƴaƴanki? Wai ke kina da hankali kuwa ko kishin ne ya rufe maki ido? Yanzu aunty Tasneem ni zaki ce ba zan zauna a gidanki ba saboda kar wani abu ya shiga tsakanina da Yayana uwa ɗaya uba ɗaya? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Hajia zainab ta rintse idanuwanta jikinta na kwasar mujirya ta dafe bango da sauri jikinta na ɗaukan rawa na tashin hankalin abinda ke faruwa da furucin Tasneem da kuma galan ɗin da take gani da idanuwanta.
Tasneem ta gyaɗa kai ta ce" Ok, ok, ke waccen kece kika dakar min ƴa kenan? Ai tafiyar ta ku biyu ce na yi dama, nufina sai na ƙare da karuwar in yi da ƙawar karuwar, tunda kin riga kin shigo zancen da ba naki ba zan haɗa da ke in ci uwar ku! Ke kuwa Fatila ko fitila ke ta gano, idan kina so ki ɗauki lasifika ki bi duniya ki ce nace, eh na ce in da ubanda zai ɗaure ni saboda wannan bismillah, ai ba ƙarya na yi ba ana yi, dan na yi kaffa-kaffa kar ta faru da ni ai ba laifi bane."
Tana rufe bakinta ta ƙarasa da takalmin ƙafarta plate ta tsinke Yusrah da mari, tana neman damƙar gashin kanta wuta ta ɗauke mata sakamakon tsinketa da Maryam ta yi da wani gigitaccen mari sannan ta saka hannunta ta fincike nata da ta damƙi gashin Yusrah, rai ɓace ta hankaɗa Yusrah da ƙarfi ta ce" Yusrah idan baki dawo hayyacinki ba na rantse da Allah ni zan matse maki wuya, gwara in san ni na maki illa da wata ƙatuwar banza ballagaza jaka ta maki, na rantse da Allah in baki dawo hayyacinki ba nice nan zan maki illa... "
Sai kuma ta juya kan Tasneem da hannunta ke kan kumcin ta kamar ta suma tace" Ke kuwa ƙaramar ballagaza ƙaramar shashasha bismillah, dan Allah bismillah abinda kika faɗa aikata, sai dai a koremu a gidan nan amma ƙarya kike ki zage mu marar ilimi, to ke ƙaryar banza ma kike yi, namijin da zai fita ya je nema ya dawo shi kaɗai ai abinda ya dawo maki shi kika gani sai wanda ya faɗa maki, Allah ya sa yana da wata macen a ɓoye da ƴaƴa masu tarbiyya baki sani ba mu ga ta iskanci, ke ɗin me da zaki hana namiji kallon wata? Wacece ke? Kyan kirkima baki da shi balle hali, dan yau na fara ganinki amma sai in saka hannuna a wuta kan baki da tarbiyya baki da hali shima mijin sai ki zage shi, an daki y'ar taki ki rufe ni ko ki dake ni bismillah, nace bismillah."
Maryam ta idasa tana cire hijabinta ta ɗaure a ƙugunta ta kuma tardo Tasneem da kanta ta ce" Gani taɓa hannuna ko ki dake nin in gani, ke nan har wani abu kika iya sama da fitsara? Ko fitsarar ce na dame ki na shanye ki yi abinda kika ce."
Tasneem da marin nan ya ɗauke jinta na yan daƙiƙu dan zuwansa a ba zata a wajen da ta gama yarda cewar ko yankawa take yi sai dai a rarrasheta a bata haƙuri dan ta riga ta gama da kowa a gidan nan, a gidan da take zuwa ta yi wulaƙancinta har uwar mijin nata ta wanke sumul ta je gida ta kwana lafiya ta tashi, a gidan da zagi ba komai bane ta ɗura maka zagi baya ce mata komai aka ɗauki hannu aka wanka mata mari jama'a, ita Tasneem? Hakan ya gigitata ainun har ya sakata zaro ido da rurruko su rai ɓace ta nuna kanta ta ce" Ni kika mara? Kin san wacece ni?"
Hajia dake jingine da bango ta samu da ƙyar ta rabu da jikin bangon a hankali ta ƙaraso falon wajen da Yusrah ke tsaye da Fatila da tunda aka yi marin ita da Yusrah suka ɗora hannayensu saman kawunnan su ido waje ,