Showing 156001 words to 159000 words out of 397328 words
barni da raina!"
Aswan ya girgiza kai ya ce" To bismillah, wa kake yiwa aiki?"
Saida Sani ya ja majinar wahala dake masa zuba yana gunjin kuka sannan yace "Yallaɓai oga ne, wallahi shi ya sani na dinga bibiyar duk wani motsi na Mani dreba da iyalan sa, sannan shi ya sa muka masa barazana da iyalin sa, bayan wannan bansan komai ba yallaɓai, dan Allah ka min rai."
A shashance AA yace "Zan maka tunda ni ke yi, bayan wannan, ka sani dama tun zuwana na farko asibiti na fara dasa alamar tambaya akan ka, yau da dubun ka ta cika ina so na maka tambayar da na jima ina yiwa mutane kuma kaima na tanade ta dan yi maka, kuɗin da suka fito daga asibiti na waye? Kuma daga ina suka fito?"
Rarraba idanu ya shiga yi kamar ba zai amsa ba, amm da AA ya masa wani kallo sannan ya kalli inda wannan sharɓeɓiyar wuƙa take, sai kawai ya ƙara buɗe murya kamar zai yi kuka yace" Zan faɗa maka yallaɓai, wall..."
Ɗaga masa hannu ya yi rai ɓace yace" Kai dakata dallah! Ka daina cika min kunne, bana jurar hayaniyar nan, ka fahimta?"
Da sauri ya jinjina kai alamar e, dan haka ya ci gaba da cewa" Kuɗin Oga ne yallaɓai, ta ɓarauniyar hanya aka shigo da su ta Cotonou, daga nan shine aka kawo su asibiti dan kar a zargi komai, bayan an kaisu asibitin Saddi Ja naje na ɗauko motar na kai gidan Muntari Buza, daga nan ma shigar dare mukayi aka kaisu gidan Oga anan aka sauke kuɗin."
Irin kallon nan mai kama da zan iya cin naman ka ɗanye ya shiga jifar shi da shi yace" Kuɗin na me ye? A ina ya same su?"
A marairaice Sani yace" Yallaɓai, sanin ta ina wannan kuɗaɗen suke fitowa sai Allah sai kuma shi Ogan, amma wallahi ban sani ba, na san dai akwai abinda oga yake turawa ƙasashen waje sannan daga gare su kuɗin ke fitowa, amma bayan wannan ban san komai ba, wallahi na rantse maka."
Harara ya daka mishi saboda ya fahimci gaskiyar kenan ya faɗa masa sannan yace" Wane ƙasashe ne yake tura kayan?"
A sanyaye yace" Yallaɓai ƙasashen dayawa, amma dai nasan akwai Austria, akwai Chine da kuma Milan."
Da ɗan karan mamaki kamar zai kashe AA yake duban Sani ya ma kasa magana, ya jima haka kafin yace" Ka faɗa min me yake fitarwa mai tsada haka a ƙasashe mabambamta?"
Girgiza kai Sani ya yi yace" Yallaɓai sanin wannan sirrin sai waɗanda ke aiki ka'in dana'in a asibitin ne za su iya sanar da kai shi idan basu so rufewa ba, sai ka shi Oga da kan shi."
Ɗaga masa gira ya yi yace" Amma kuma kai baka san komai ba?"
Ɗaga kai ya yi alamar e yace" E yallaɓai, saboda koma menene ake fita da shi daga asibitin ake fitar da shi, ni kuma ba ma'aikacin cikin ta bane."
Tabbas! Ta tabbata dai yanzu dole zai shiga neman yarinyar nan mai ragowar hankali, dan maganar da Sani ya yi tasa ya ji tabbas wani abu ta sani mai mahimmanci da ya sa ta bar asibitin, dan haka zai fara neman ta dan kar a zo su jefa rayuwar ta a garari.
Miƙewa ya yi zai fita daga ɗakin ya kalli Sani yace "Me ye ka haɗin Buza da duk wannan? Bayan a zahirance tafiyar su ba ɗaya bace."
Kai tsaye ya amsa mishi da "Yana da wani kaso ne a duka harkokin, dayawan lokuta ni ake bawa kuɗin shi ina kai masa, kasancewar basa son harkar transfer bare a var wata shaida, bayan Buza ma akwai masu hannu a ciki, sai dai bai san dayawa ba."
Taɓe baki AA ya yi yace "Uncle Kofa, da sa hannun shi aka kama shi ko?"
Jinjina masa kai ya yi yace "Shi ya yi plan ɗin, su Buza ne suka aiwatar."
Da irin shashantar da zancen yace "Saddi Ja fa da kuka kai motar asibitin sa?"
Girgiza mishi kai ya yi yace "Bai san komai ba, kawai ana son ɓatar da sawu ne shiyasa aka kai motar can, amma da fari ma gidan Chef aka so kai motar saboda wani shiri da Ogan yake yi akan Chef ɗin."
Da mamaki ya ƙanƙance idanu yace "Wane Chef ɗin? Shirin me kuma yake yi a kan shi?"
Saida ya sauke numfashin wahala kafin ya ce "Chef dai, Chef naka aminin Elhaj (mahaifin Aswan), Oga ya gano cewa Chef yanzu shi ya fi kowa sanin sirrin Elhaj ɗin ka tunda aka rufe Kofa, kuma kasancewar mahaifin ka yana hushi da Kofa saboda shi y yarda ɗari bisa ɗari cewa ya aikata masa cin amana da yaudara, sai yanzu ya ƙara jan Chef a jiki a ganin shi shi kaɗai ne ba zai yaudare shi ba, shiyasa Oga ya so shi ma ya watsa masa baƙin fantin da ya fi na Kofa, kuma...kum..."
Shiru ya yi yana sassauke numfashi saida AA yace" Kuma me?"
Sannan ya ɗora da" Ya gano Chef shine ya baka aikin binciken nan, har ma ya gano shi yake taimaka maka akan komai, ya yi shiri sosai na ganin bayan Chef nan kusa, shirin da idan ya zartar da shi kuɓutar da Chef sai Allah kawai."
Duk da tsaye yake saida ya ɗan jimƙe hannun shi sosai a ran shi ya ayyana _" Hasbunallah wani'imal wakil."_
Juyawa ya yi ya fice saga ɗakin saboda kan shi da yake jin kamar yana sarawa haka ko juya masa ne ma oho! Amma dai baya jin daɗi gaskiya, kawun sa? Kawu Hamat? Uncle Hamat ɗin sa da idan ya kwana biyu basu haɗu ba yake kiran shi yana magiya ya zo ya gan shi? Kawun sa Hamat dai da ya rene shi a hannayen sa? Ya Allah!
Mota ya shiga sai dai ba gida ya nufa ba ya kama hanya saboda yana so kafin ya je yi musu sai da safe yanayin sa ya saku, dan suna ganin shi a haka zasu fara tambayar sa lafiya? Hanya ya kama zuciyar shi da ƙwaƙwalwar shi tunanin Hamat fal da su, wannan ya sa har ya ɗauki hanya da za ta kai shi gidan kawun bai ma sani ba, sai da ya zo kusa da gidan a can gefendake kallon ƙofar gidan ya ja ya tsaya yana hangen ƙofar... Tsoron duniya da mutanen cikin ta ya sake kama shi gaskiya, kawun sa, shine da wannan baƙar harƙalla haka? Ya salam! Me ya sa Colonel Garba duk ya zo masa da wannan batu na kuɗi ne da gashi yanzu suke neman ran sa, e mana suna neman ran sa, tunda yanzu haka ba ya jin daɗin jikin shi, gashi kuma har yanzu zaƙulon bai ƙare ba.
Jiki a mace ya ma motar ky sannan ya dafe sitiyarin zai bar ƙofar gidan, dan ba yanzu zai gana da kaw... Hamat ɗin ba, tabbas akwai lokacin da idan ya gama tara shi zai masa zuwan sa na musamman, kamar dai yadda ya ma Sani ɗin nan, a wannan ranar so yake ba wani tsumi ko dabara da zasu ƙwace shi, kawai zai miƙawa huk...
Motar Humed da ya ga ta danna hancin ta cikin gidan na kawu Hamat ne ya saka shi dakatar da tunanin ya shiga tambayar kan sa _"Shi kuma me ya kawo shi nan? Me ya zo yi ma wannan mutumin a yanzu dare ya tafi haka sosai ƙafa ta fara ɗaukewa?"_
Wani sabon takaici ne ya ji ya kunno masa, sam bai zargi Humed da komai ba daidai da yankan farce, ɓacin ran kawai na kawu Hamat ɗin ne da yake jin shi fa yanzu daf yake da yanke alaƙa da shi haka ma ya sa duka ahalin shi su yanke alaƙar su da shi, baya ga wannan sai yake ganin Humed ai yaro ne, tunda ba shi ba Intisar ma ai gaba take da shi, to tsoron shi kar fa a zo yadda yake mugun nan yana cutar masa da ɗan uwa ne, ko kuma yana wani shirin akan sa ko...ko kuma *mahaifin su*? Tabbas, dan idan ma ya fahimci komai daidai kamar da mahaifin sa ne yake yaƙi, gabar sa ba da kowa bace face da mahaifin su, shiyasa yake nesanta shi da duk waɗnda ya ga suna zaune da shi dan Allah.
Ai da sauri ya kashe motar ya fito da tako irin na ɓacin rai ya tunkari gidan, tun da mai gadi ya gane waye ya shiga yi masa sannu da zuwa da kirarin da ya saba, amma dake ya hau ma'aunin da basa so suna haɗuwa da shi idan ya hau, ko irin barka ɗin nan bai ce masa ba, gagara haƙuri ma ya yi ya buɗe masa ƙofar sai da kanshi ya tura ƙaramar ƙofar ya shiga gidan, take alamu suka nuna masa kawun ma ba ya gidan, tunda babu motar sa sai ta matar shi, sannan daga nan yana hangen falon ɗirim yake da duhu alamar ba kowa ciki, amma da ya ga falon matar da haske yake kuma kyautata zaton nan Humed ya nufa, kai tsaye sai ya nufi can shi ma da jin lallai za'a yi ta yau.
Kamar dai ɗin yadda yake ta tunanin ba wani abun tashin hankali, shi kawai yana so kar ya zalinci Humed ne tunda ya ga yaro ne, dan haka kawai ya tura ƙofar falon tare da yaye labulen dake shara shara ya shiga. Dukansu babu wanda alamar tsoro da firgici bai bayyana a jikin sa ba musamman ma Humed da ya san shi ne ya kaɗe a tafiyar, dan kuwa ya ɗauresa anan ya zane sannan ya kaishi gidan sa ya kwana ba kaya ba kuma cin abinci ai ƙaramin aiki ne, to wai dama ba dan baya so ya ji daɗin rayuwa bane ya yi aure da wuri? Ai ya gwada fara yin rayuwar ta holewa kasancewar sa ɗan mai kuɗi sannan matashi, amma fa, shisha kaɗai bawan Allahn nan ya ga yana sha cikin abokanan su ya ɗauko shi, a zahiri dai ya cewa su Aba ai yana gidan shi ne yana masa nasiha ya yi karatu, har da fa karɓan litattafan shi wurin Anna dan kar su zargi komai, amma a baɗini, a wani keɓantancen gida da su dai basu san ma nashi bane ya dinga masa horon bala'i bayan ya zane masa jikin sa da bulala, kashedin da ya masa ne baya mantawa a rayuwar shi, kashedin da kasan an faɗa ne dan a cika, ai ba zaka yarda ka sake yin wasa da rayuwar ka ba kuma.
Tuni hannun shi ya fara rawa rawa takardun dake hannun shi suka nemi kubcewa su zube, AA da tuni ya ƙarasa kusa da Humed ɗin bayan ya ma matar kawun irin kallon tatas ɗin nan bai kuma ce da ita komai ba dan dama ba yinta suke ba bare yanzu da ko mijinta da yake ƙauna ba zai saurara masa ba ya figi takardun dake hannun Humed, hakan ya sake ɗaga hankalin shi yana ma matar kawun kallon dan ya rasulillah aunty ki fara bashi haƙuri, amma sai ta kawar da kai bayan ta masa kallo irin na _"Iya ruwa fidda kai."_ Sannan ta ɗan sadda kan ta tana tunanin wai shi Aswan ɗin nan uban me yake taƙama da shi ne? Ita wallahi yaron nan bai mata ba ko alama, gashi kuma ita ba wani girman sa tayi a shekaru ba bare ta dinga tsawata masa, ko da yake... Tidin ma ya ta iya da shi bare kuma ita? Kawai tunda an samu ma yana jin maganar kawun nasa ai shi za ta faɗa ma ya masa magana kar ya sake diro mata gida haka gaskiya, dan wallahi idan hawan jini gare ta wannan tsaf zai kasheta a rasa me ye silar tafiy...
Da ƙarfin masifa ta ɗaga kai ta kalle su, ashe sanda ya karɓi takardu ya duba ɗaya check ɗin banki ce kawu Hamat ɗin ya rubutawa Humed ta wasu milyoyin daloli, sai ɗaya takardar dake nuni da Humed ɗin ya sa hannu ne wasu kaya sun fita ta ƙarƙashin office ɗin da Aba ya damƙa masa yake kula da shi na kamfanin shi na sufirin jiragen sama, dan har juragen ƙasa Aba yana ɗaukar hayar su suyi jigilar su su dawo sai a raba riba, yanzu ne ma da yake ta fafutukar ganin ya mallaki ko guda biyu sai ya daina karɓa.
Kallon Humed ya yi da wani razanannen kallo amma da wata irin sanyayyar murya da a dole baya so ya fara nuna halin sa anan bare kawu ya samu labari har ya ankara da wuri yace "Na menene wannan?"
Saida ya kalli matar ta kawun da lokacin tana kallon gefe tana ta yatsina fuska da tunanin to ita ina ruwan ta? Saƙo ne aka bata fa kawai, rashin madafa ta sa ya rarraba idanu ya kalle shi da rashin gaskiya yace "Aaa..ammmmm...tttta..."
Irin marin nan na bayan hannu ya sauke masa a lafiyayyen kumcin shi da ko gemu irin na matasan yanzu ba ya tarawa, faɗuwar Humed ɗin ce ta sa matar kawun kallon su da sauri ta miƙe tsaye ita ma cikin ta na wani irin juyawa kamar za ta ɓarke da zawo, musamman yadda ta ga Humed saida ya hantsila daga kan kujerar sannan ya daidaita faɗuwar sa. Kafin ya ankara da abinda ya faru da shi kuma AA ya damƙe takardun a hannun shi ya shaƙo wuyan Humed ta baya sannan ya ja shi zuwa fita, takalmin shi ma ɗaya da ya fita ba wanda ya bi ta kan shi sai faman bashi haƙuri da yake yana kiran sunan shi da Akhi Akhi, bai tsaya da shi ko ina ba saida ya kaishi ga motar shi sannan ya buɗe da ƙarfi ya watsa Humed ɗin ciki a mazaunin matuƙi, ranƙwafawa AA ɗin ya yi ya dafe kujerar da ya zaunar da Humed ɗin sannan ya sa ɗaya hannun shi ya tallabo haɓar sa ya tilasta masa fuskantar shi sannan a tsawace yace "Kalleni nan?"
Da mugun sauri Humed ya kalli fuskar AA yana ɗan ja baya, saida AA ɗin ya ɗan lumshe idanu da kawar da kanshi a take saboda jinin da ya ga yana ma Humed ɗin zuba ta hanci, ɗan uwan sa, ko wani ya cutar da shi zai iya ɗaukar masa fansa, amma akan me Humed zai sa kan shi a ƙazamar harƙallar kawun su? Yaushe ya zo duniya da zai fara yin abu ba shawarar kowa? Da sanin Aba ne ya yi haka? Ko kawai sun yi niyya ne? Shi dai ya tabbata haramtattun kaya ya wucewa kawun da su ta jiragen su, shiyasa har suka iya biyan shi ma da daloli, me ye haka wai?
Da ƙyar ya kalli fuskar ta Humed yana jin zafi a zuciyar shi yace "Ka tayar da motar ka sannan ka biyo bayana, idan kuma ba haka ba..."
Takardun nan ya nuna mishi yace "Aba ya san da wannan?"
Girgiza kan da ya yi na alamar a'a saida AA ya sauke numfashi mai tattare da nutsuwa a cikin sa, dan haka ya ɗora da "Idan ba haka ba, ni zan tayar da tawa motar yanzu, idan ka yarda na sha gaban ka, to Aba zai ga wannan takardun."
Sai kuma ya gyara tsayuwar sa kaɗan yace "Na san komai dake faruwa Humed, kar ka layance min."
Yana fada ya miƙe daga ranƙwafawar da ƙarfi sosai ya tura masa murfin ƙofar sannan shima ya nufi motar sa, a gigice Humed ya lalabi makullin mota da dama ya bar shi ga motar ya tayar, da sauri ya fara fita daga gidan yana share jinin dake hancin shi kafin ya fara daidaita zaman motar har AA ya tayar da tashi dake nan waje sannan ya dinga bin bayan shi sau da ƙafa.
Wannan shine tashin hankali goma da gomiya tara, bayan firgicin da yake ciki sai ya sake tsunduma shi a wani ta hanyar nufa gidan shi wanda shi baya son haka, amma ya zai yi da kishiyar uwar sa, haka suka cilla motocin cikin gidan sannan ya dinga bin shi a baya ba takalmi ɗaya a ƙafa kuma sam bai lura da haka ba har ya masa alamar ya zauna kan kujera a falon sa'ilin da yake ta shafa kan su Meem da angel da suka tarbe shi, abun mamaki cikin wata sayayyar murya yake musu magana da "Cute baby's, kun ci abinci?"
Kukan da Angel ta yi da yanayin da Meem ta yi ya sa yace "Ba kwa jin nasiha kenan? Ba na ce ku dinga ci ba idan Kabir ya baku, and...bayan shi kar ku yarda da kowa."
Sai kuma ya miƙe ya shiga ɗakin sa duk suka rufa masa baya, Humed dai na kallo' ikon Allah yana ta addu'ar Allah ya sa su rabu lafiya da mutumin nan, Allah ya sa yau ba a gadon majinyata zai kwana ba.
Bayan ya gama zubawa su Meem abinci ya shige wanka, domin kansa yake ji ya yi masa mugun nauyi, ba zai so ya fuskanci ƙanin nasa a irin wannan yanayin ba, ya jima sosai a ɗakin sa domin sai da ya yi sallah ya riƙe carbi yayi ta istigfari da ambaton sunayen Allah ɗari ba ɗaya sannan ya miƙe bayan ya ajiye carbin ya fito falon.
Inda ya bar Humed nan ya same shi kansa a ƙasa ya yi shiru tamkar baya nan, zama ya yi a kujerar dake facing ɗin sa, hakan ya sa ya ɗago a firgice yana dubansa, idanuwansa ya rintse, baya son ganin jinin dake jikin Humed, ko kaɗan baya so.
A tausashe ya ce" Meye anfanin wannan lamari da ka saka kanka? Yanzu fa kai magidanci ne harda haihuwa, so kake yi in ci gaba da saka hannu a kanka? Humed kasheni kake son yi?"
Humed ya girgiza kai da sauri ya sauko ya rungume ƙafafuwan AA ya fashe da kuka kansa a saman ƙafafuwansa, shi ma ya yi shiru idanuwansa a rintse, bai hana shi kukan ba, bai kuma saka shi ƙarawa ba, shi dai shiru ya yi yana sauraron kukansa dake dukan zuciyarsa.
A hankali ya iya buɗar bakinsa ya ce" Me kake aikatawa? Ka san me saƙon ya ƙunsa? Ka san lamarin na iya saka mahaifinmu a uku? Ka kuwa san so ake a saka Aba a cikin halin ƙaƙa naka yi? Ka san so ake