Showing 330001 words to 333000 words out of 397328 words
kuma sai yadda ta yiwu fa, tunda dai bashi da kunya da tsoron Allah.
Da fari sagale haɓa ya yi ya bita da kallon mamaki yana ayyana _'Me kuma za ta je ɗaukowa ta dawo?'_
Amma da ya ji daga ƙasan shi an zungure shi sai ya yi saurin gyara zama yana kallon kan shi ɗin, zaro idanu ya yi ya rufe baki da tafukan hannayen shi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ji jaraba, Y. Turaki dawo nan kin ji? Subhanallah! Ɗan Anna me ya same ka haka?"
Ya faɗa yana ɗan taɓa wajen ya ji wai da gaske shi ɗin ne a tsaye haka car kamar wanda ya haɗiyi taɓarya, gyara zama ya yi akan kujerar yana sake bin ƙofar ta da kallo ya taɓe baki ƙasa ƙasa yace" Aikin banza, ashe ma su Y. Turaki kuraye ne sai tsoro da ban tsoro, to wallahi dole ma za ki sauko ne yarinya ayi abinda ya dace, dan ɗan Muhammad Anza jika yake so nan da wata tara, nima kuma ina so na tabbatar masa da haka dan ya gane ba aljanar da ta aurar masa ni."
Tagumi ya zuba yana ta matse ƙafafun shi, ya kalli can ya kalli can ya rasa me zai yi, can ya ja tsaki ya sake dafe wurin yace" Ƙalau nake rayuwata, dan fin ƙarfi aka min aure, to kuwa wanda ya sa aka min aure dole a bar ni nima na ci...me ma su Arid ke faɗa da hausa...?"
Ya y maganar yana son tunowa ɗin da gasken gaske, sai kuma ya tuna dan haka yace" Yawwa, a bar ni naci ƙaniya nima, ahaf!"
Sai kawai ya kalli ƙofar ta ya maka mata harara yace" Za ki fito ne, wai har da wani ko tarewa ban yi ba, ko tarewa ta yaushe kuma? Ko kuma dai a mafarki ne naji maganar?"
Shafa kan shi ya fara yi yana tunanin ya zai yi yanzu? Ya jima nan zaune kafin ya miƙe da ƙyar har tafiyar sa ta canza ya nufi nashi ɗakin shi ma da tunanin ko Aban shi yake kira ya ce ya zo ya ma yarinyar can wa'azin sanin haƙƙin maraya, dan an ga kakan shi ba ya raye ai ba shi zai sa a dinga masa abinda aka ga dama ba, kai yo idan da Anza na nan wacece ta isa ta kunna ta gudu? Tsaf Anza zai jawo masa ƙafar ta ya kwantar masa idan ya gama ci ya sake ta.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
30/06/2024, 23:11 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*83*
Washe gari ya kama ranar tarewar Yusrah, ko in ce ranar wunin bikin tarewa domin tariya yau Yusrah ta kwana a gidanta, tunda safe Anna ke waya da ita ta sanar mata zata yi baƙi sosai, za'a zo da kayan girki a yi na baƙin da zasu zo ganin ɗaki da yamma, akwai aminiyar auntynsu wato aunty Fauziya zasu zo da su Abrar da masu girki a yi girki a kuma tayata zama har yamma ta yi ƴan ganin ɗaki su zo idan aka gama shikenan sai a watse.
Anna ta so yi mata maganar da Aba yace kan maganar Nabihat, sai dai ta ga gwara ta bari idan aka gama bikin nan na yau sai ta sameta ta yi mata maganar a tsanake, Allah yana gani sam lamarin Nabihat bai kwanta mata a zuciyarta ba, sai dai bata da yadda zata yi, kuma Yusrah da kanta ta san da maganar tana kyautata zaton ba zata wani ɗaga hankalinta ba ma, amma duk da haka zata same ta ta mata nasiha sosai, dan ta kula tana da barin abinda ya dace ta bari da wanda bai dace ɗin ba ma, irin su Nabihat kuwa idan har suka gama gane suna iya zubar da duk sharar da suka kwaso a kan ka, tabbas ka gama zama bola sai haƙuri, wayar da suka yi da ita kuwa na ɗan lokaci sai ga aunty Fauziya.
Tabbas aunty Fauziya bata so zuwan nan da wuri ba sai dai yadda suka yi da aminiyarta a dole ta zo da sassafe dan ta faɗa mata amaryar yaya Akhi ɗin ƴar ɗakin ta ce, tana so ta je ta yi tsaye a kan komai tamkar ita ce a wajen, a dole ta je ɗin kuwa dan zumuncinsu ba ne wasa bane gaskiya, Anna ta haɗa su da tarin kayan miya da komai da komai da masu girki suka yi gaba bayan ta faɗawa aunty Fauziya idan sun je fa dan Allah ta kula da komai za'a kawo kayan miyar ta da na abinci komai dai a shirya mata yadda ba zata wahala ba.
*A* gidan kuwa sai ƙarfe bakwai ta fito daga ɗakin ta tana sanɗa dan zuwa kicin domin a jiya Allah kaɗai ya san a yadda ta yi barci, kunya, tsoro, tunani kala kala babu irin wanda bata yi ba da kuma tarin mamakin ɗa namiji, shi wai bashi da kunya a kan lamarin nan? Namiji a kan lamarin nan ya kan fito kansa tsaye ya nuna abinda yake da buƙata baya ɗan kara ma? Ai sai ya bari su saba, ai sai ya bari a kwana biyu ko? Ko da yake wani sabo? Ba dai sabon ba amma sai ya bari mata su tare fisabililahi.
Sai da ta zo daf da table ɗin diner ta ga ya ɗago daga wajen frij hannunsa riƙe da madara da kofi ya sauke dubansa a kanta, murmushi ya fara yi irin yadda ta wani zabura sannan ta sunne kai, hakan ya saka shi jin kamar ya yi dariya, sai dai ya maze yana kallonta ya ce" Ina kwana Y. Turaki?"
Da mamaki ta kalle shi, sai ta buɗi baki ta ce" Ina kwana Aban Safwan."
Ya yi murmushi yana kallonta ya ce" Lafiya, ke ma yunwar ta fiddo ki? Jiya zamu ci abincin mu kika hana kika sa muka je can, kuma za'a baki abinda kike so ɗin kika gudu, Y. Turaki ya ya maganar tsinuwar mala'iku da aka ce in muka so a bamu aka hanamu suna kwana suna yiwa mata? Ina zaki kai wacce kika kwaso?"
Yusrah ta yi saƙalau tana kallonsa ta ce" Tsinuwar?"
Ya ɗaga girarsa yana kallonta, Yusrah ta sadda kai jikinta ya mutu murus ta ce" Astagfirullah."
Aswan ya taɓe baki ya ce" Ai kin san Allah baya yafe laifin da ke tsakanin bayinsa sai idan bawa ya yafewa bawa ko?"
Ta ɗago idanuwanta tana kallonsa ta ce" Yanzu sai ka bari a sakani wuta?"
Ya ɗauke idanuwansa daga kanta ya sake ɗauko wata madarar ya haɗa a hannu guda ya ƙaraso inda take ya ja hannunta suka ƙarasa falon suka zauna saman cafet ɗin ya buɗe mata ya bata yana faɗin" Ya danganta, yanzu ai na yafe maki na farko ne, ma in ki ka ce zaki ringa cin zalina tsaf zan kwana saman sallaya bayan na mala'ikun nima in ringa sheƙa kuka ina faɗawa Allah, yo in ban da rashin mutunci ma so ake in je in ci a waje?"
Kan ta sai da ta ji ya sara mata dan kunya, ta sadda kai riƙe da madarar nan a hannunta tana tabbatarwa kan ta ta da shiga uku ta lalace, ta fa auri mijin da ba zai ji kunyar furucin bakinsa ba, sai dai ita kunyar ta kasheta, ganin abinda ta yi ya saka shi yin wata ƴar dariyar ya ce" Buɗe ki sha mana kafin in fita, an ce yau za'a yi wani zaman ko? Wai me suke yi a zaman nasu ne?"
Yusrah ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe madarar ta zuba a kofi ta shiga sha a hankali tana kallonsa kamar yadda yake kallonta, sai da ta sha ta ɗan sauke ajiyar zuciya ta ce" Saukar Alkur'ani ne muke yi."
Ya yi tsuru yana kallonta kafin ya yi dariya ya janyo ta jikinsa ta hanyar shamata ya rungumeta a jikinsa sosai a ransa ya ayyana _' Wa Billahillazi an bani daidai dani, wai saukar Alkur'ani, kwa dai sha magungunanku na mata da yi da mutane kamar me, Allah ya shirye ki matar jikan Anza.'_
A fili kuwa yana kallon yadda ta yi luff ya ɗan ƙara rungume ta yana jin nutsuwa na ratsa jikinsa, a hankali ya furta" Allah ya miki albarka, laifi na yafe maki wanda na sani da wanda ban sani ba, nima ki yafe min kin ji?"
Yusrah ta ɗago idanuwanta ta sauke a kan gemunsa dake matuƙar birgeta a duniya, a hankali ita ma ta ɗan shafa gemun nasa ƙasa ƙasa ta ce" Na jima da yafe maka, ba zan taɓa iya riƙe ka ba baban Safwan."
Ya sakar mata murmushi kusan kunnenta ya ce" Zan wuni da kewarki fa, i swear, amma idan na zo yau sai na ci..."
A tausashe ta tambaye shi" Me za ka ji?" Saboda shiru da ya yi, a kunne ya raɗa mata cewa" Sai na ci ƙaniya, haka naji su Arif na faɗa, kin san ƴan iska ne su."
A zabure ta ɗago daga ƙirjin nasa ta sakar masa harara tana kaiwa hannunsa dake mata lalube ta ture ta miƙe da sauri tana girgiza kai ta rufe kunne ta yi gaba da gudu tana faɗin" Na shiga uku, sai ya lalatani."
Ya saki dariyar da bai shirya ba ya rakata da kallo har ta ɓacewa ganin sa, sai kuma ya yi tsuru yana dafe haɓa a ransa ya ayyana _' Ta tabbata sittin saba'in kake bi da kallo ƙato, sai ka tashi ka tafi kar ka auka mata bayan baƙi zata yi ai.'_
Murmushi ya yi ta miƙe ya je ɗakin sa ya ɗauko ky ɗin mota ya fito ya sake leƙawa wajen ɗakin ta ya bubbuga, ya ɗan yi jira ta buɗe ta ɗan leƙo kamar wanda zai mata fyaɗe ya mata sallama sannan ya tafi yana faɗa mata za'a zo mata da abincin kari dan kar ma ta ce zata yi girki.
Addu'a ta yi masa sosai tana kallonsa har ya fita a babban falon, sannan ta fito ta dawo falon ta zauna tana lumshe idanuwanta haɗi da sakin murmushi mai tsada tana jin wata nutsuwa na ratsa mata zuciya, ƙwarai yanzu take jin nutsuwa mai sunan nutsuwa, har yanzu ta gaza tambayar kanta ya ya aka yi auren sa bai ɗaga mata hankali ba sai ma kwantar mata da ya yi? Ya ya aka yi idan ta tuna ba fa ita kaɗai bace a duniyar sa take jin kamar hankalin nata a nan ne zai ɗagu? Ya Allah! Kai ka san damuwar dake cikin zuciyata, ka yaye min ya rabbb.
Kiran da wayarta ke yi ya sa ta nufi ciki ta ɗauko ta ɗaga tana ganin sunan uncle Sulaiman, da fara'a ta ringa gaishe shi, uncle Sulaiman da ya kwana bai yi barci ba tun binciken da ya tsananta ya ga abinda ya gani yake jira safiya ta yi ya sanar mata abinda ya gani bayan ya ba mutumin maƙuddan kuɗi ya bashi numbar wacce ta aikata aikin nan hankalinsa ya tashi sosai ne ya amsata shi ma yana faɗin" Daughter, ina fatan ban tasheku ba? Ina yan uwan ki?"
Kasantuwar bai san ta tare ba, a tunaninsa yau dai aka ce zata tare, ita ma sai bata sanar masa ba kawai ta amsa a tausashe cewar " A'a uncle, lafiya ƙalau, ya karatu?"
Uncle Sulaiman ya ce" Alhamdulillah karatu, uhum kin san me ye ? Na fa gano wanda ya yi haɗin bala'in nan fa, kin san da Nabihat ce ta sa aka yaɗa ku a Tiktok?"
Sai da Yusrah ta zabura dan jin tashin hankalin maganar, kuma da ba dan uncle ɗin ta bane ya faɗa mata maganar nan tabbas da sai ta ce a'a, da yanayin tashin hankalin ta ce" Uncle Nabihat kuma? Amma me yasa ta yi haka? Me na yi mata a lokacin? In ka kula a lokacin ai ba wani abu tsakanina da mijin....da mijin....da shi Yayan namu ko?"
Uncle Sulaiman ya yi dan murmushi dan irin yadda ta yi ta maimaita mijin mijin, a tausashe ya ce" Ina ga kawai haka Allah ya halicce ta, kin san akwai mutanen da ba sa jurar ganin farin cikin wani, gaya nan ai ta yiwa kanta, dama Allah ai ba azzalumin sarki bane."
Yusrah ta sake sauke ajiyar zuciya ta furta" Lalle ma, wannan matar sai na yi ta addu'a saboda ban san me zata iya aikatawa ba a yanzu kenan, a da ma ta yi haka balle yanzu?"
Uncle Sulaiman ya ce" Kina ji? Babu abinda ta isa ta yi, kuma ni zan sanarwa Aba fa, dan wallahi duk abinda ta aikata gabanan ba zan ƙyaleta ba ko wanene babanta kuwa sai na ja da shi."
A tausashe Yusrah ta ce" Uncle, Abanta mutumin kirki ne, wallahi mutumin yana da kara sosai a rayuwa da kuma tsoron Allah, ka yi haƙuri kar ka faɗawa Aba, ban san me zai faru ba, ni dai na san Allah na tare da mai gaskiya kuma ko me ya faru ka sani Allah zai kareni uncle."
Haka dai ta yi ta lallaɓa uncle, har bakinta suka ƙaraso suka yi sallama ta tafi wajensu, ai kuwa tana ganin aunty Fauziya daga ita har ita suka zaro ido suka ruƙumƙume juna da ihu da mamakin ganin juna a nan.
Da mamaki aunty Fauziya ta ce" Wai, wai dama ke ce ƙanwata? Amma ta ya ya? Yaushe? Kin san irin neman da na maki kuwa?"
Yusrah na dariya ta liƙu da aunty Fauziya ta ce" Aunty, labarin akwai tsayi, amma tunda kin zo zan faɗa maki komai, aunty ina wajen su uncle? Wai dama ke ce aminiyar aunty Intisar?"
Aunty Fauziya ta zauna da kyau tana faɗin" Ni ce, ƙanwata bani labari in sha?"
Daga nan suka baje suka shiga labari da aikace aikace, domin a yau ne ake saka duk wani abu na ci ko sha a gidan kuma fauziyar ce a kan komai.
***AA na fita ba gida ya nufa ba, tafiya ya yi wajen wasu aikace aikacen sa, nufinsa daga nan zai je gidan ya ga Aba da jiki sannan ya wuce asibiti, tabbas yana so ya je ya ga Hamat ido cikin ido a yau, dan yana matuƙar son ya ga idanuwan sa ya faɗa masa abubuwa sosai da sosai, hakan ya sa bai shiga gidan Aba da wuri ba.
*A* gidan Aba kuwa Aba kusan ƙarfe tara na safe da ya ji garas sosai kawai ya fito a shiryensa ya yiwa Anna sallama cewar zai je gidan Chef, duk yadda ta so ya bari mana a kwana biyu sai ya nuna a'a yana son fita kuma can ɗin yake son zuwa, a dole ta raka shi da addu'a ta ci gaba da shige da ficen ta cikin kwanciyar hankali bayan ta ƙara yin addu'ar idan har auren nan na Nabihat ba alkairi bane Allah ya kwaɓe shi cikin ruwan sanyi.
Ba tare da Chef ya daina mamakin nan ba ya fito riƙe da wayar sa a hannu yana kallon motar ta Aba dake jingine a motar ya rumgume hannaye yana ta doka masa murmushi, yana ƙarasowa Chef yace "Elhaj, da gaske ɗin dai kai ne? A wannan safiyar Elhaj, ina fata dai lafiya?"
Aba ya gyara tsayuwar sa ya bashi hannu suka yi musabiha yace "Mamakin me ka ke wai? Zuwan safen ko ganina a gidan? Kamar yau na fara zuwa."
Murmushi Chef ya yi yace "Ba haka bane Elhaj, zuwan ne naga kwatsam, sam ban yi tunanin haka ba, ina fata dai lafiya?"
Yadda ya ji ya sake maimatawa irin duk ya damu ya san ko lafiya ya sa Aba komawa ya jingina a motar yace "Lafiya ƙalau Chef, na zo ne akan maganar yaran nan, ɗan ka da kuma ƴar wajena Nabihat."
Ƴar ajiyar zuciya Aba ya sauke yace "Oh, to bismillah mu shiga ciki sai mu zauna."
Da sauri Aba ya dakatar da shi da cewa "A'a Chef, ba sai na shiga ciki ba, a ganina mun yi mai wahalar, to yanzun ma na zo ne bisa abinda ya faru kwana biyu da suka wuce, shiyasa naga gwara na zo na ji ya batun tsayar da ranar nan ne wai? Gwara a saka ranar suma ayi a ɗaura musu auren mu bisu da addu'ar zaman lafiya."
Jinjina kai Chef ya yi yana jinjina abun a ran shi, idan ya faɗa ma Elhaj mata yake jira su saka ai ya zama marar anfani ma kenan, dan haka kawai ya kalli Aba kan shi tsaye cike da nuna jarumta kasantuwar sa namiji yace" Elhaj, ina ga tunda kai ne mahaifin yarinyar nan, kawai ka tsayar da ranar, ni kuma matsayina na uban ɗana sai na sanar masa tare da ƙoƙarin fara shirye-shirye."
Da gamsuwa Aba yace" Hakan ma ya yi, to ina ga me zai hana a saka..." Saida ya ɗan yi tunani kafin yace" Ina ga a saka sati uku mai zuwa in sha Allah, kaga kenan za'ayi hidimar gaba daya a wuce wurin, kana ganin ba wata matsala daga gare ku?"
Girgiza kai ya yi yace"