Showing 375001 words to 378000 words out of 397328 words
ta, kuma na san babu abinda zai canzawa Chef ra'ayi saboda nasan wanene shi, dan haka na baki wannan albishir ɗin a matsayin tukuici, ma'ana na baki tabbacin za ma naki ke kaɗai."
Tana tsaka da mamakin furucin shi bata kai ga jefo masa tambayar da ta yi niyyar yi masa ba Anna ta fara sanyo kai da sallama sannan Aba, da girmamawa Aswan ya tashi daga kusan Yusrah ya ma Anna alamun ta zauna yana musu sannu da zuwa, gaba ɗaya su kuma hankalik su na kan Yusrah da ta rufe fuska da hijabin ta saboda kunya musamman da Anna ta zauna daf da ita ta riƙe hannun ta tana faɗin "Ƴata, ya jikin naki? Zazzaɓi ne ko?"
Ba ta iya amsawa ba haka ma Aba dake tsaye yana duban ta ya tambaye ta jiki, amma ta kasa buɗe fuskar ta saboda gani take za su iya gane komai daga fuskar ta musamman ma Anna da ta san mace ce ita kuma uwa tsaf za ta fahimci abinda ke damun ta.
Aswan dake kusa da Aba ne ya dafa kafaɗar shi cikin raɗa yace "Jikan Anza, hala rashin lafiyar amare ce ta fara yi?"
Kallon Aba Aswan ya yi ya ɗan dafe haɓa, wato Aban shi ko? Sai fatan Allah ya ƙara mishi lafiya kawai, cike da kunya ya shafa ƙeyar shi ya jinjina masa kai yace "Ina ga hakane?"
Da raha Aba yace "Kana ganin hakane? Ko kana da tabbacin hakane?"
Shima cikin raɗa yana sadda duban shi yace "To wai Aba ba ni ne ɗan ka na fari ba? Kunya nake ji ko?"
Ɗan dukan kafaɗar shi Aba ya yi ya ƙyalƙyale da dariya a harshen buzanci yace "Hakane fa yarona, to ashe nine nake aikata aikin rashin kunya."
Girgiza kai Aswan ya yi yana ƴar dariyar shima yace "Ban faɗa ba Aba, ni kake saka wa ina jin kunya ai."
Gyara babbar rigar shi Aba ya yi ya kama hanyar fita yana faɗin "Bari in samu Siddik in ji me ke faruwa, tunda Allah ya fara karɓan addu'ata ka fara jin kunya jikan Anza."
Murmushi ya yi yana shafa kai yace "To Aba, idan ka same shi ka bashi har da tukuicina da ban bashi ba na goron albishir da ya min." Wani kallo Aba ya mishi sai kuma ya fice yana amsawa da shikenan, fitar Aba kuma su Manal suka ƙaraso suma.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
12/07/2024, 12:06 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️??🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*95*
Duka iyalan nan basu bar asibiti ba har saida aka sallami Yusrah bayan ruwan sun ƙare, dan kuwa ko da Aba ya shinshino wannan labari daga gurin Siddik ya zo yana baza riga baki har kunne ya ja hannun Anna ya shiga kora mata nasiha akan zunubin ta na baya wai duk ita ta saka mishi tunanin ko dai aljana ta aurar masa ɗa, to yanzu ga aikin sojan shi nan ya bayyana? Yanzu ta gane ɗan shi lafiya tai ƙalau kawai lokaci ne bai yi ba, dan haka daga yanzu in ya sake amsawa in ta kiran shi da wani suna da ba Kakan Haidar ba to ya kwana tsaye, ai fa haka Anna ta so korar shi a asibitin amma ya ce wa? Ba dai shi ba wallahi, shi yanzu ai ya wuce ajin da za'a dinga juya shi, dan haka tare da shi za'ayi wannan jinya, Anna da ta ga lamarin sa babba ne haka ta ƙyafaci Aswan ta masa raɗa akan ya ja Aba su fita wani wurin gaban suruka fa yake, amma wallahi Aba ya ƙwala musu harara ya rumgume hannaye yana kawar da kai yace "Ku yi ku gama, a cikin ku dai ba mai iya ɗaukata, Haidar na zuwa kuma duk zai rama min abinda kuka min in sha Allah."
Aswan kuma kallon Aba yake da nishaɗi yana son zaman nasa a nan, saboda gobe za'ayi zaman farko na shari'ar uncle Hamat da shi dai ba ya tunanin za'a sake na biyu saboda girma da tarin hujjojin da ya damƙa a hannun Chef, dan haka yake son ganin Aban cikin nishaɗi dan ya ce sai ya je kotu komai zai faru ya faru gaban shi.
Haka aka sallame su duk suka ɗunguma gidan, kai tsaye Anna ta shiga ta bar Manal wajen Yusrah da faɗa mata ayyukan da za ta iya yi mata sannan suka wuce gida suma cike da mata fatan lafiya.
Wannan bari da aka ma Manal sai tayi nadama, ta ce za ta tafi gida tunda ba abinda take kuma ita ta gaji da ganin wannan rumguma da Aswan ke ma Yusrah da sam ba ta yi tunanin zai fara aikata haka yanzu yanzu ba, amma ya ce salon ta je ta ce ma Anna ya kore ta ko? Dan haka babu inda za ta je sai yamma ta yi kamar yadda Anna ta faɗa, haka ta laɓe a ɗakin Yusrah ta bar su a falo suna ta taɓeɓeniya da fitsarar su a falon.
*GIDAN CHEF*
Tun a wunin ranar aunty Fauzy ta zo gidan saboda Mus'ab da ya sanar da ita abinda ke faruwa, da ta zo ta samu maman su a rikice ta gama dukan Nabihat ta haɗa mata jini da majina da muciya, ba kuma komai ya janyo hakan ba sai ikrarin da Nabihat ɗin ta yi akan ita fa da a tsayar da auren nan nata a sabar wa da Imran, ta san zai amince ya aure ta tunda yana son ta, kuma ita yanzu da shi kaɗai za ta iya zaman aure, ko AA ɗin ya dawo ba za ta amince ba dan ita bata ga wani alfanu ga soyayyar shi ba.
Hakan ya hassala maman nata ta jibgi banza da wofi, yau kam dole ta saurari Fauzy da ta bayar da shawara a amincewa Imran ɗin saboda a fita kunya ma kamar yadda aka yi ga auren Yusrah wanda ita Nabihat ta lalata, ta gamsu da haka kuma take ta nuna to a samu Imran ɗin, amma sai Fauzy tace "To amma fa Mama ita kuma Nabihat ta amsa da bakin ta cewa sun kusanci junan su, idan hakane kuwa dole sai Nabihat ta yi istibra'i kafin a ɗaura auren su."
A gigice maman tace "Wane istibra'i kuma? Salon dai ki tona mana asiri? Ita Yusrah da haka ta faru ba take aka ɗaura auren da Aswan ba?"
Ajiyar zuciya Fauzy ta sauke tace "Hakane Mama, amma na tabbata Yusrah bata aikata aiki irin na Nabihat ba, kuma idan ma hakane ai bai fito fili ba, ita kuma yanzu za'ayo hakane saboda gudun kada ayi aure sa ciki, ƙa'idar shari'a zamu bi."
A kausashe ta sake cewa "Wane irin ciki kuma? Sau nawa ne ta ce sun haɗun? Kinga ni zan iya cire hannuna daga maganar nan wallaho, can na bar ta da uban ta ya mata duk abinda ya ga dama."
Da sauri Nabihat ta riƙe ƙafar ta tana rusa kuka tace "A'a dan Allah mama, mama ki ƙyaleta kawai kar ki cire hannun ki, ni zan ma Imran ɗin magana, wallahi na san ma ban da ciki."
Da tausasawa Fauzy tace "A'a Nabihat, wannan ba faɗata bace faɗan Allah ce, ko da ya amince dole ya kamata ki yi istibra'i kafin a ɗaur..."
Wata irin tsawa Nabihat ta daka mata cikin fitar hayyaci da manta cewa ita ke gaba da ita tace "Dallah ni ki rabu dani, ki cire hannun ki daga maganata malama, na gaya miki ban da ciki, ni ƙaramar yarinya ce ko sakarya? Haka kawai sai na ɗauki ciki daga zuwan da ya min da bai fi guda biyar zuwa bakwai ba, to ba zan iya ɗin ba."
Kallon ta Fauzy ta dinga yi da mamakin abinda ta mata, ta kalli maman su tana jira ta ga ko za ta tsawatar mata amma sai ta ga ta kaɗe kai tana faɗin" Aikin banza, ban da ma abinki ƙaddara da cikin, shin ciki dubu nawa kika san mata sun shiga da shi gidan mazaje kuma suka haife shi, kuma har yau babu uban da ya san da cikin aka shiga bare a yi maganar ɗaga maganar, ke dai kawai wata shari'ar ai sai a lahira, amma da a ji kunyar duniya kam gwara ta can da dama kowa yana ta kan shi ne ai ba mai kula da tsiyar da wani ke yi."
"Wal'iyazubillah!" Fauzy ta faɗa tana kallon maman ta a tsorace da yanayin ta dake neman fin ƙarfin ta, sai kawai ta miƙe tsaye tana ɗaukar jakar ta da gyalen ta ta kalle su sosai tace "Shikenan, na cire hannun nawa Nabihat, Allah ya kyauta."
"Ameen." Nabihat ta faɗa tana ƙara matsawa kusa da Maman su tana ci gaba da rarrashin ta Fauzy kuma ta fita tana kuka na jin jahilcin dake damun su dukan su da kuma wautar da suke shirin aikatawa.
Maman kuwa Nabihat ta kalla tace "Ki kira min Imran ɗin a waya, ki ce ya zo nan ya sameni ina son ganin shi, amma zan sanarwa da masu gadi cewa ɗan aminiyata zai zo dan su bar shi ya shigo, kuma ko da mahaifin ki yake jin labarin ma an yi baƙo zasu sanar da shi ɗan aminiyata ne."
Aka ce da zafi akan daki ƙarfe, take Nabihat ta zura masa kira, kuma kiran farko ya ɗaga da tunanin zai sake samun ƙaniya ya ci ne, amma da ga ce wai maman ta na son ganin shi sai ya ji lamari fa ya ɓace, duk tunanin duniya ya gama shi bai ga dalilin da zai sa maman Nabihat ta so ganin shi ba, sai kawai ya ce to ya yanke kiran tare da basarwa ya shiga wasu harkokin, bai zo ba, bai kuma kira ba, haka bai da niyyar zai zo tunda dai ya san ai auren ta da an ga gobe to jibi ne in sha Allah.
*WASHE GARI*
A babban kotu aka yi zaman shari'ar uncle Hamat, a dole dai ya sauko daga matakin haukan da ya ɗora ma kan shi dan ya girbi abinda ya shuka, ba ma iya shi kaɗai ba har da duk masu hannu a ciki, dama ba zama bane da aka tsara za'ayi dan mutane dayawa su halarta, hakan ya sa bayan waɗanda ake tuhuma masu taya shi aikin sai lauyoyi da kuma shi alƙalin da magatakarda.
A wajen uncle Hamat ne ma Aba da Anna da kuma Goggo Tidin duk suna nan cikin jimami Goggo Tidin ma na kuka, sai matar sa ita ma da take kukan a saman fuskar ta amma zuciyar ta fal farin cikin ɗaukar fansar wulaƙanta ta da ya yi akan wata Yusrah, da kuma ƙudurin ana gama zaman nan za ta tattara abinda ya rage mishi ta yi ƙasar waje ita da ƴar ta su canza rayuwa. Sai Aswan da shi ma ya zo ba dan ya so hakan ba sai dan Aba ya ce ya zo, sai kuma uncle Kofa shi ma yana wurin.
Suna ji suna gani ba yadda suka iya aka yanke masa hukuncin shekaru ashirin cif da diyya kuɗi masu zunzurutun yawan da dole sai dangi sun agaza wajen biya, dan abinda ya mallaka ma ba zai biya mishi wannan tara ba, sanda dangi suke kukan baƙin ciki matar sa kuma kururwa take yi, abinda kawai take faɗa shine "Na shiga uku na lalace, bani ga tsuntsu bani ga tarko."
San kuwa ta gane laifin na mijin ta babba ne da har ya yi sanadiyar ba za ta samu ko tsinke ba, tunda gashi take alƙali ya bayar da umarni ga hukuma da a tsare duk wata kadara ta shi da dukiyar sa. Haka jami'ai suka sako shi gaba za'a tafi da shi babban prison din da ya yi silar zuwan uncle Koca ba tare da laifin komai ba, kan shi na ƙasa a sadde cike da nadamar wannan rana, an zo za'a shiga da shi mota ya nemi alfarmar ganawa da Aba na minti biyu, ba su hana shi ba dan yana da wannan damar, haka ya taho kanshi ƙasa inda Aba da Anna ke tsaye duk sun yi jugum.
Yana zuwa ba zato suka ga ya zube guiwoyin shi ƙasa yana fashewa da kuka ya riƙe rigar Aba yana cewa "Akhi, Akhina ka gafarceni, dan girman Allah ka yafe min laifin da na maka a rayuwa, tabbas na gane hassada ga mai rabo taki ce, domin kuwa ni nake maka da son ganin ka ci baya, amma Akhi kullum gaba ka ke yi, hatta ƙasa idan ka taɓa kai da ahalin ka sai kun ci ribar milyoyin kuɗaɗe, Akhi na gane arziki na Allah, dan da ace zan yi shi wallahi da na jima da fin ka kuɗi saboda irin gwagwarmayar da nake yi, kan halak kan haram babu wacce bana yi Akhi, dan Allah ka yafe min ko na samu salama idan ajalina ya zo..."
Sai kuma ya kalli Anna ma yace" Dan Allah Hajia ki sa baki ya yafe min, ku yafe min dan Allah."
Kama hannayen shi Aba ya yi ya miƙar da shi tsaye yana faɗin" Hamat, ai ni tun ranar da na gano abubuwan da kake aikatawa na yafe maka, saboda ban san ko na jima a duniyar ba da zan yi ta riƙon ka a zuciya, wallahi na yafe maka duniya da lahira, abinda nake so da kai kayi ta istigfari Hamat ko Allah zao gafarta maka zunuban ka, muna fata kuma Allah ya sa diyyar nan ta zama silar karkarewar zunuban ka, sannan ka yi magana da matar ka, shin za ta iya jiran ka ko ba za ta iya ba? Idan ba za ta iya ba kar kaga laifin ta sannan ka sawaƙe mata, saboda kar a shiga haƙƙin ta, Joli kuwa na maka alƙawarin zan riƙe ta, daga yanzu da nake maka magana ta zama ƴata, in sha Allah ba za ta yi kukan rashin uba a kusa da ita ba, Allah ya gafarta maka Hamat, Allah ya yafe maka kurakuren ka."
Kuka sosai uncle Hamat ya dinga yi yana godiya kafin ya ƙarasa kusa da Aswan da ke tsaye kamar bai san tsiyar da suke yi ba, kusan shi ya tsaya yana kallon fuskar shi a raunane yana kuka yace" Son, son..."
Sai kuma ya yi murmushi yace" Da gaske ina son ka har cikin raina, son da ko ƴar da na haifa bana mata irin shi, na gode son da ka cece ni tun a nan gidan duniya, wataƙila da baka fara binciko wa ye ni ba da har yanzu ina nan ina aikata ta'asa da tarawa kaina zunubin da ba zan iya ɗauka ba, na gode sosai son, sannan ina neman yafiyar ka abisa komai, dan Allah ka yafe min, kuma ina neman wata alfarma a wajen ka idan zai yiwu?"
Aswan da ko kallon inda yake ba ya yi da ƙyar ya ɗan cira kai ya saci kallon inda su Aba suke, ai kuwa gaba ɗayan su shi suke kallo da gargaɗin da ya fahimci me suke nufi, a dole ya ɗan saki fuskar sa ya kalli uncle Hamat ɗin, murmushi ya yi bayan ya fahimci komai da ya faru yana jan majina yace "Ina so dan Allah ko sau ɗaya ne a shekara ka dinga zuwa dubani a cikin gani biyu da aka bayar za'a min a kowace shekara, dan Allah son?"
Abu ne mai girma ya nema a wajen shi, amma saboda iyayen shi dake wurin sai kawai ya jinjina kai tare da ɗan saka hannun shi ya bubbuga damtsen uncle ɗin alamar ya amsa kenan amma dai bai buɗa baki ba ya ce masa komai, wajen Goggo Tidin ya ƙarasa ita ma tana ta kuka, rarrashin ta ya yi daga ƙarshe kuma yace mata "Kar ki yarda ki auri Muntari, ba mutumin kirki bane ƙanwata, amma ina baki shawara da ki samu nagartaccen namiji ki yi aure bayan kin aurar da ƴar ki, hakan zai sa ki ɗauke idanuwan ki daga rayuwar Aslama a gidan ta, sannan ina baki shawara ki daina hassada da rayuwar da take ciki, a shekarun da kika ɗauka kina mata ƙyashi har yanzu babu wani abu da ya sauya, dan haka ki daina kafin ke ma kiga ɓacin rana kamar dai ni."
Daga haka ya kalli matar shi da take masa wani irin kallo kamar tayi ta ɗura masa ashar yace" Na san ma ba zaki iya jirana ba, abinda ya sa kika aureni yanzu babu shi, dan haka ki bar min ƴata a wajen ɗan uwana zai kula min da ita, ke kuma ki je na sake ki saki ɗaya."
Wani wawan tsaki ta ja tare da maka masa harara tace" Gayyar tsiya."
Nufa motar ta tayi hakan ya ba Goggo Tidin mamaki ta bita da kallo, daga haka jami'an nan suka tisa ƙeyar shi gaba aka saka cikin