Showing 162001 words to 165000 words out of 397328 words
nauyin sa. Mukhtar dai na ƙyaƙyata dariya yace "Gaskiya kam, dan farashina babba ne, ban san ko za ka iya biyana ba iko?"
Shi ma da murmushi a fuskar sa yace "Faɗi na ji."
Lokacin ya ɗan tsagaita da dariyar sa ya dubi Aswan ɗin dake kallon gate ɗin gidan kamar yana wani nazari yace "Zama abokin ka, sannan ka zama shaƙiƙin da zai iya zaneni idan na yi ba daidai ba, sannan mai tsawatarwa ƙannaina, sai kuma ka ɗaukar ahalina a naka ko da kai za ka hana min naka ne, wannan ma ya wadace ni Oga, wayar gari da nayi ina kallon wanda ya firgita su Samir a tashi ɗaya, har ya saka yanzu sallah ba ta wuce su akan lokacin ta, sannan suke kama hanyar zuwa islamiyya, wannan ba ƙaramin gyara da sauyi ya kawo mana a gida ba, yanzu ƙiriniyar su ba babba bace, wacce zasu iya bari ce idan suka ƙara mallakar hankalin kawunan su, sai dai duk da haka da wasu ƴan matan biyu dake buƙatar saiti a rayuwar nan."
Da mamaki Aswan ya kalle shi da kuma jin kamar ma zai bashi haushi yace" Wai dakata, ƙannan naka har nawa ne marasa jin magana? Shin baka taɓa kwatanta ɗaure su bane a jikin bishiya ka zane musu jikin su? Ko nauyi suke maka da yake gagarar ka cira ƙafafuwan marasa kunya ka sadda kawunan su ƙasa ka jijjiga kowa dan hankulansu su dawo kawunan su madadin zuciyar su? Me ye haka wai?"
Tunda ya fara magana Mukhtar ke kallon shi da mamakin abinda yake faɗa har yana ayyana _" Shi yanzu kenan duk zai iya yin haka?"_
A zahiri kuma tausasa murya ya yi dan yaji kamar ya ɗan hau ne yace" Ka gane Oga? Wasu daga cikin su marayu ne da Hajia take ɗaukowa dan kulawa da su kuma ƴaƴan ƴan uwan ta, wannan ne dalilin da ya sa ita da Alhaji sam basa so a tsawatawa yaran, suna matuƙar ƙaunar su da gujewa ɓacin ran su, ni ne babba a gidan, amma kuma ban isa na tsawatar musu a gaban su Hajia ba, amma sosai da sosai nake son ganin sun kimtsu sun zama mutanen kirki suma."
Sai kuma ya yi dariya da irin gaggawar magana yace" Kuma ka san me? Yanzu haka tun ranar da muka dawo daga PG da su Hajia sai ta kalleni ta taɓe baki ta ce min wai idan ma zalin ƴaƴan ta naci Allah zai saka musu, amma gaba ɗaya ita tasan hukuncin da na musu ba ƙarami bane da ya sa suka canza haka, kuma wani lokacin idan sukayi wani abu sai ta min murmushi ta ce Allah ya maka albarka, dan ko da wasa basu faɗa kowa ya ji karon su da mahaukacin soja ba, haka kuma gamuwar su da makashin mahaukacin soja."
Taɓe baki AA ya yi ya ɗan buɗe motar ya zura ƙafar sa ɗaya waje yana faɗin" Zan samu lokaci kafin nayi tafiyar nan na kai ziyara wa waɗannan ƙannan nawa, kai kuma wallahi ka dinga jin tsoron Allah."
Dariya Barista ya yi yana faɗin" Ai kuwa ni dai da ka bani lokacin da nasan irin shirin da zamuyi dan tarban ka, bayan wannan, na gode da shawara."
Fita ya yi daga motar yana faɗaɗa murmushin shi yace" Zan kira Humed sai nayi ƙoƙarin haɗaku, zan sa shi ya same ka."
Da tsokana barista yace" Da dai ka bani lambar shi ni sai naje na same shi ai tunda ɗan uwan Oga ne."
Kallon shi Aswan ya yi yana hango tarin farin ciki da shaƙuwar da zata iya shiga tsakanin su idan har ya sake masa yace" Kaga, bana so na fara safiyata da ashar, ka daure mu rabu lafiya mana."
Sai kuma ya rufo masa ƙofar motar sannan ya leƙo yace" A sauka lafiya."
"Nagode Oga." Barista ya faɗa yana wa motar ky da ƙyalƙyalewa da dariya, ciki Aswan ya koma ya ɗauki babbar wayar shi dan kiran Humed ya haɗa shi da Barista Mukhtar.
*YUSRAH*
Tsaye ta wuni tana aiki ba tare da gajiyawa ba dan babu gajiya tare da ita indai akan abinda ya shafi aikin ta ne ko aikin gida, zirga zirgan ba kaɗan bace, amma haka ta daure musamman da take so ta nunawa Dr. Siddik za ta iya aiki da shi, har ƙarfe takwas da rabi ta wuce tana sannan ne ta fara shirin tafiya gida bayan Dr. Siddik ɗin ya sallame ta yana mai yaba mata sosai, cire rigar ta tayi ta rataye sannan ta gyara zaman baby hijab ɗin ta kafij ta ɗauko jakar ta tawa Dr. sallama ta fito.
Tana saukowa daga kan matakalu za ta tunkari hanyar fita ta ji an yi oda a bayan ta tare da ɗan haska mata fitilar mota, juyawa ta yi da tunanin kawai dreba ne aunty Intisar ta sake aiko mata hala? Amma hasken da ya ɗauke mata idanu ya sa take hangen son gano wa ye a motar... Bilal da ya fahimci abinda take son yi sai ya kunna fitilar ciki sannan ya kashe ta waje, tana ganin fuskar shi ta ɗan sauke numfashi ta ayyana _"Da shi ne?"_
Takawa ta fara yi zuwa gare shi da tunanin ko me yake yi anan? Ba dai ɗaukar ta ya zo ba? Ai ko ba za ta so haka ba gaskiya, ƙarasawa ta yi fuskar ta ba yabo ba fallasa, buɗe mata motar ya yi mazaunin mai zaman banza yana sakar mata murmushi kamar ya ga watan ramadan.
Ba musu ta shiga ciki ta zauna ta rufo ƙofar tare da kallon shi tace "Yaya Bilal, me ya kawo ka asibiti? Fatan dai kowa lafiya?"
Wata ajiyar zuciya ya sauke yana tayar da motar da murmushi a fuskar shi yace "Yanzu ni da nake shirin zama mijin likita har za'a min wannan tambayar?"
Murmushin yaƙe ta yi tana kawar da kan ta, lokacin da ya fita daga harabar asibitin yace "Ya aikin madame? Gaskiya Yaya Siddik ya wahalar min da ke, takwas fa anan ta miki inji aunty Intisar, gashi sai yanzu tara na neman yi kike saukowa? Gaskiya zan tuhume shi fa."
Ƴar dariya ta yi ita dai tace "Aiki ne ya yi yawa a asibitin shiyasa."
Kallon ta ya yi da tausasawa sosai yace "Fatan aiki bai gajiyar da ke ba?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Da gajiya mana, sai dai kuma da sabo ma, dan haka gajiyar za ta bi ruwan wanka in sha Allah."
"Allah ya sa." Ya faɗa yana maida hankalin shi kan tuƙi, sun ɗauki shiru na kusan sakanni ashirin kafin ya sake duban ta yace "Yusrah."
Da kulawa ta dube shi ta amsa da "Na'am." Saboda yanayin da ya kirata ya nuna zai faɗi maganar da ba wasa, a nutse yace mata "Na ji duk abubuwan da suka faru da ke, tun kafin na ji ma dama nasan dalili mai ƙarfi ne zai iya fitar dake hayyacin ki, ina mai baki haƙurin rashin iyayen mu, Allah ya jiƙan su da rahama ya kuma gafarta musu."
Jiki a sanyaye tana jin wani irin abu ba daɗi haka na neman kunno mata tace" Ameen ya Allah, na gode sosai."
Ƙara ɗorawa ya yi da" Yusrah."
Wannan karan kallon shi kawai ta yi ba ta amsa ba, dan haka ya dube ta yace" Allah ya jarabceni da son ki, na san kuma kin fahimci haka, amma girmanki da ajin ki na ƴa mace ya sa kike basarwa, hakan ya min daidai, amma ina miƙo ƙoƙon barata, please Yusrah kar ki ce min a'a, rashin ki ma na wasu kwanaki ba ƙaramar jigatani ya yi ba, idan na rasaki na har abada Yusrah ba zan iya rayuwa ba."
Gaba ɗaya ya kashe mata sassan jikin ta har ta kasa buɗa baki ta ce masa komai, sai ta ji abun ya zo mata wani iri da shi haka, ba wai bata taɓa jin kalmar so daga bakin namiji ba, a'a sai dai yadda shi ya faɗa matan ne ya sha bambam da na saura, kalaman nasa sun tsaru, sannan sun tasirantu matuƙa a ran ta, kuma ma za ta iya cewa sun birge ta tare da jin cewa ai za ta iya waiwayar sa tunda har yana jin haka a kan ta. To amma fa... Yanzu ba ta ga Safwan ba, ita kuma rayuwar duniya ma ce bata so ta ci gaba da zaƙewa a cikin ta saboda ba ta tare da ƙanin ta da iyayen su suka rasu suka bari a hannun ta, idan ta mayar da hankali kan aikin ta yanzu sannan soyayya ta zo ta ratso mata, hakan zai sa ta ji kamar bata ɗauki lamarin Safwan ɗin ta da mahimmanci bane.
Bugu da ƙari aikin nan ta fara ne saboda kar cewa aunty Intisar a'a ya yi yawa, ta ce ta yi aiki asibitin su ta ce a'a, ta ce ta daina shiga madafa da masu aiki shima ta ce a'a, yanzu kuma an ce ga asibitin da za ta yi aiki ta ce a'a a jira har ta ga Safwan? Sai kawai ta amsa da babban fatan haɗuwa da ƙanin ta, abu ɗaya da ta saka a ran ta shine duk wani da ya shafi aunty Intisar ba za ta yarda wata ɓaraka ko raini ko rashin girmamawa da sakin fuska su fito ta ɓangaren ta ba, kamar yadda bata so rashin kyautatawa ya fara shiga tsakanin ta da su. Amma fa wannan lamari rayuwar ta ya shafa, tabbas ta fahimci me ye a ran Bilal game da ita tun ba yanzu ba, kula bata da matsala da hakan za ta iya bashi dama ya shiga rayuwar ta wala'Allah akwai sauyin da zai iya kawo mata, amma kafin nan... Za ta fara ɗan ja masa aji ta ga salon takon shi, haƙurin shi, juriyar shi, da ma yadda zai iya shanye duk wani abu da ya shafe ta.
Da wannan ta ƙi bashi amsa duk da ya so jin wani abu daga bakin ta, daga ƙarshe dole ya haƙura yace "Shikenan tunda ba zaki ce komai ba, amma ina neman alfarma ɗaya a wajen ki?"
A tausashe ta kalle shi alamar tana ji, ɗorawa ya yi da "Ina so ki bani izini na dinga ganin ki ko da sau ɗaya ne a kullum?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan, ba damuwa."
Da jin daɗi yace "To amsar tawa fa? Sai yaushe?"
Cike da kunya ta sunkuyar da kai tana jawo jakar ta ta ƙara rufe fuskar ta da ita tace "Zan faɗa maka amma ba yanzu ba."
Da zolaya yace "Nan da kwana ɗaya?"
Girgiza kai tayi tace "A'a."
"To biyu?" Ya faɗa yana leƙa fuskar ta, nan ma girgiza kai ta yi, da haka ya dinga tambayar ta har suka kai kwana biyar, sannan ta ɗan ce "Ummm! Wataƙila."
Da jin daɗi yace "To Allah ya sa na ji daddaɗar amsa."
Ba ta dai amsa mishi da ameen ba haka suka ci gaba da tafiya yana jan ta da hira, amma ita sai dai ta bashi taƙaitacciyar amsa ko gajerruwa da haka har suka isa gida, tare suka rankaya ɓangaren na aunty Intisar, da kulawa sosai ta yi ta ma Yusrah sannu da zuwa tana kuma mayar wa da Bilal martanin faɗi da yake ya je ya dawo mata da ƴar ɗakin ta dan haka ta bashi abinci ya ci, ita kuma ta ce ai ba aikin shi ta yi ba, da ta san ma zai je da ta riga tura dreba dan bata son gorin nan dama, Yusrah dai na jin su tana dariya ta shige ciki dan yin wanka mai sunan wanka sannan ta fito ta ci abinci kafin ta kwanta kuma ta sha maganin ta.
*BAYAN WASU KWANAKI*
Ba ƙaramin takaici da ɓacin rai Nabihat ɗin ta tsinci kanta a ciki ba tunda ta zo gidan nan, idan ta maƙasudin zuwan ta ba wai iya yadda za ta ƙara siye zuciyar kowa dake gidan bane, har fa da yadda za ta dinga ganin Oga kwata kwata, amma yau kwana huɗu da zuwan ta har yanzu ba ta ganshi ba sai dai hana rantsuwa sau ɗaya ta ji ƙamshin turaren shi a corridor ɗin ɗakin Aba da zasu shiga gaishe shi Manal ke cewa har Akhi ya zo ya gaishe da Aba ya tafi, ta ce ta ya ta gane ta ce daga turaren da ya bar musu anan.
Sau biyu kaɗai yake zuwa gidan sai kuma idan buƙatar zuwan ta taso wanda tunda ta zo buƙatar hakan bata taso ɗin ba, da safe ta wata hanyar yake shiga ya gaishe da Aba da Anna babu mai sanin ya zo sai idan katari ya haɗaku. Gashi kuma ba kowane lokaci Anna ke basu damar shiga wajen Aban ba gaishe shi bare ta dinga yin sammako ko za ta dace da haɗewa da shi. Da dare kuma ko da yake zuwa sun riga da sun kwanta ko da ma basu yi bacci ba, idan ma bata kwanta ɗin ba ta ina tasan zai bi bare ta je ta kasa ta tsare? Wannan abu shine ke matuƙar bata haushi da ɓata mata rai har ta ji gidan ya fita ranta duk da kuwa gatan da take gani da more rayuwar da ta fi ta gidan su.
Shiyasa yau tunda sassafe take zaune ƙarƙashin flawowin da suke fuskantar ƙofar shigowa sannan suke bayan ɓangaren Humed, yanzu haka ita da matar Humed Wa'at ne zaune suna hira kasancewar Humed ɗin na bacci bashi da fitar safe, sai Saiful Islam dake buga ball shi kaɗai suna kallon shi suna taɓa hira sama sama amma hankalin Nabihat ya fi karkata ga ƙofa musamman idan ta ji kamar an yi oda.
Fitowar Nabihat daga filin da suke motsa jiki ya sa hirar tasu ta canza, sanye take da riga da wando kana ganin ta kaga sak wata balarabiya ko baturiya, ƙafafun ta sanye da takalmi ƙafa ciki, cikin mitumci kuma sai ta ɗoro baƙar abaya a kai irin mai buɗaɗɗen gaba da kallabin ta saman kan ta sai ruwan roba dake hannun ta. Tana isowa gare su ta ɗan dafa kai Islam dake wasar sa tace "Ɗan Tata, barka da safiya."
Sai kuma ta kalli Wa'at dake mata murmushi tana tambayar ta har an dawo tace "Na dawo aunty Wa'at, ina kwana?"
Da fara'a ta amsa mata da "Lafiya lau Abrar, antashi lafiya?"
"Lafiya lau." Ta faɗa tana ƙoƙarin wucewa, sanin kai da ka samu na zaune kai zaka fara gaishe shi ya sa Abrar yi wa Nabihat kallo ɗaya da takaicin ko me ye na fitowa da wannan matsatsun kayan a taƙaice tace da ita "Barka."
Ba ta kuma jira me za ta ce mata ba ta fice abun ta zuwa babban falo, hakan ya sa Nabihat binta da kallo na takaici kala kala sannan ta ja tsaki tana taɓe baki tace "Mtssssss! Wannan Abrar ɗin wallahi sai ta dinga abu kamar wata kidahuma, yanzu wannan wa zai gan ta ya ce a nan gidan take?"
Da tsananin mamaki Wa'at ta kalle ta tana ƙara hasko shirin da Wa'at ta wuce da shi, me ye aibu a jikin ta? Abrar ba ƙaramar yarinya ba ce, sannan ba raguwa ba saboda a hannun Anna ta tashi, dan haka tare da twins babu aikin da basu iya ba, Abrar ta yi karatu, ko su Manal da suka gama jami'a suke shirin shiga university shekara ɗaya ce tsakanin ta da su, ba kuma koma baya ta samu a karatun ta ba a'a dan sun ɗan girme ta da wannan shekarun, uwa uba kuma islamiyya da suke zuwa, Anna bata yarda dan suna ƴaƴan masu kuɗi ba su zauna mata haka kawai ba sanin Allah da manzon sa, a taƙaice ma wannan islamiyyar da suke zuwa AA ne ya saka su ya kuma tsawatar kan zuwa ɗin idan ba da ƙwaƙƙwaran dalili ba. Sannan, Abrar bata wasa da tsaida sallah sai idan tana fashi, sannan bata da wulaƙanta mutane, hasalima kaf gidan nan idan ka cire Goggo Tidin babu mai wannan halin, to me ake da buƙata ga ɗan adam bayan wannan? Ɗan adam ɗin ma mace, macen ma kamar Abrar da bata wuce shekara 21 ba, bayan nan kuma Abrar ta haɗa da kyau, jar fata, gashi har gadon baya saboda gaba da baya buzuwa ce, to amma shi ilimi ai kogi ne, dan sanin wannan ilimi ya sa Wa'at da mamakin nan a fuskar ta tace ma Nabihat "Me ya sa kika ce haka?"
A yatsine ta fara kallon hanyar da Abrar ɗin ta bi sannan ta kalli Wa'at tace "Sis, ba ki ga dan ƙauyanci daga nan wajen motsa jiki zuwa cikin gida har wani abun ɗora abaya ne a kai? Sai ta yi ta fama da dogayen riguna a gida kamar wata ƴar saudiya."
Saida murmushi ya suɓuce ma Wa'at dan ita kawai sai ta hango tsabar hassada a maganar ta Nabihat da kuma jahiltar mecece mace, hakan ya sakata sake bin shigar dake jikin Nabihat ɗin da idanu, sai kawai ta girgiza kai tana mai ɗauke duban ta tace" Ni kuma ban ga laifin haka ba, kowa da yadda yake ɗaukar daidai, ita ta rufe jikin ta haka ta fi jin ta a daidai ɗin."
Wani kallo ta ma Wa'at ɗin, sai kuma ta taɓe baki tace" Hmmmm! Har da rashin wayewa dai."
Ita ma cewa ta yi" Hmmmm! Amma dai kin san Abrar bata da duhun kan da ba'a fata a ce mutum yana da shi."
Daga nan ta ɗauki hankalin ta kacokam ta mayar kan wayar ta dake hannun ta dan bata son ma su ci gaba da hirar nan, ita ma, ita ma Nabihat da ta fahimci haka sai kawai ta miƙe tana faɗin" Ni zan shiga ciki."
Ba ta jira me zata ce ba saida ta bada baya ta ji Wa'at ɗin ta amsa da" To." Kawai ta ɗan saci kallon ƙugun Nabihat ɗin, sai kawai tayi murmushi tana ayyana _" Da rufe shi kike yi ai yafi asiri rufe, anan ina abun kallo a wannan ƙugun kamar an ɗaure sisi?"_ Tsaki ta yi ciki ciki ta ci gaba da harkar ta da kuma sa ran ganin kiran mijin nata da zai nuna mata ya tashi kenan.