Showing 384001 words to 387000 words out of 397328 words
nan da ɗan kwali yana ta ihun azaba da ciwo, ta kuma kama Goggo ita da Safiya suka sakata adaidaita sahun suka ɗauki hanyar Anza mension saboda basu san gidan Yusrah ba, ko da sun sani da wahala a barsu su shiga haka kai tsaye.
Sun jima suna tafiya Goggo na ta faɗin Allah ya yafe mata har suka ƙaraso nesa da ƙofar kaɗan Aunty Khadi ta fita ta je wajen masu tsaron ƙofar ta gaishe su a mutunce sannan ta sanar musu ko su su wanene ta kuma roƙi alfarmar a barsu su shiga.
A dole suka barsu shiga saboda Aba ya jima da soke maganar wai in ba'a ba mutum damar zuwa kar a barshi ya shiga ba, ya nuna duk wanda ya zo nemansa a barshi ya shiga inda yake ko inda ahalinsa suke, ƙarshe ma gidan suka buɗe suka shiga da adaidaitar bayan yayi kira ya sanar cewa ga baƙi nan iyayen madame Yusrah ne kuma suna da marar lafiya ba zasu iya fita daga adaidaita sahu ba.
Anna dake zaune a filin gida ita da su Manal suna ta fama da shayi ta miƙe tana gyara mayafinta da kyau ta ce" Nawal tashi maza ki ƙaro abin shinfiɗar ta yiwu Furera ce, Allah ya sa dai ba ita ce bata da lafiya ba, tashi maza ki gani."
Suna nan mai aiki ta tarbo su aunty Khadi har wajen su Anna, suna zuwa su Safiya suka fara kama Goggo suka cirota da ƙyar suka nufi shinfiɗar da su Manal ke nuna musu, Anna kuwa ido waje take kallon Goggo, ƙwarai ta ganeta ta shedata.
Aunty Khadija ta koma ta ɗauko auta ta kawo shi ta shinfiɗar tana sauke ƙafarsa ƙasa bayan ta sake shinfiɗa ɗan kwalinta dan kar ya ɓata musu waje da mugunyar dake ɗiga, sannan ta koma ta sallami mai adaidaitar ta dawo ta tsuguna tana gaishe da Anna dake faɗin" Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, subhanallah wannan ai Goggon Yusrah ce? Ko ba ita bace?"
Unty Khadija ta sadda kai tana kallon irin kukan da Goggo ke yi, tana kuka kanta a ƙasa jikinta na rawa sosai ta shiga labartawa Anna abinda yake faruwa gaba ɗaya, ta ɗora da faɗin" Dan girman Allah Hajia ku taimakeni in ba ƴar nan haƙuri, ta yafe min abinda na yi mata tun kafin in mutu a haka in je ga ubangijina ƙasa ta ƙi ɗaukana, tabbas idan na tafi ƙiyama a haka ni da kaina na san menene makomata, dan Allah ku yafe min ku saka baki ta yafe min."
Manal hawaye take yi tana kallon Goggo, duniya kenan, tabbas tana tune da Goggo dan kuwa har ranar ɗaurin aure ai ita ce take maganganun nan har sai da Sulaiman ya koreta ta tafi, lalle duniya ko me kake tunani ta fi ka, gashi dai ta ɗauki Goggo ta kaita can can saman sama sannan ta saketa ta yi faɗuwar da ba daidai ba, ba abinda ya fi bata tausayi irin yaron nan dake kuka, yana cikin wani yanayi marar daɗi, ya salam.
Anna ta share hawayenta a tausashe ta ce" Ki daina kukan haka kin ji? Ki godewa Allah da ya baki ikon neman gafara da ranki, da yawa suna cikin tafka shagala ba tare da sanin yaushe ne ranar da zasu koma ga Ubangiji ba, sai mutuwa ta same su rana tsaka shikenan su tafi su bar abinda suke ta yaƙi a kan nasa, a je a tarda rayuwa bayan mutuwa wacce ita ce dawamammiya ba wai ta gidan duniya ba, ba komai bari direba ya zo ya kai ku gidanta, yau suna gida in sha Allah na tabbata zata dube ki, ku daina kukan haka ba komai kun ji? Allah ya yafe mana Allah ya sa mu fi ƙarfin zuƙatanmu mu kuma guji cin zalin bayinsa, domin ba wai tafiyar nan ta duniya ce abin duba ba, a'a babbar tafiyar ita ce ta bayan mutuwa domin *WATA TAFIYA* ce mai nisan gaske, wacce muke fatan Allah ya sanyaya mana ita."
Direba aka saka ya zo aka kama musu suka shige mota ya tafi da su gidan Yusrah, Anna ta ɗauki waya ta yi kiran Yusrah ta sanar mata zata yi baƙi sannan ta ja mata kunne ban da ɗaga hankali saboda abinda ke jikinta, wato tsohon cikinta, sannan ta sanar mata duk hukuncin da ta yanke ba damuwa kuma duk taimakon da zata yi ta yi kanta tsaye Allah ne zai dubeta shi zai gafarta mata gobe ƙiyama ita ma.
Tana kashe kiran Nawal ta ce" Anna, why baki musu taimako tun kafin su tafi wajen aunty Yussy ba? Suna da buƙatar taimako, bale yaron nan."
Anna ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Yes, suna da buƙatar taimako sosai, amma nan zuwa gidan Yusrah babu abinda zai hana musu in sha Allah, ina so Yusrah ta taimake su, ina so ko me zasu samu ya zamo daga hannunta ne, ina so Goggon ta ta ƙara gane Allah ne gatan bawa ta kuma yi tuba na gaske, bana so gobe idan ta manta zafin nan ta yi tunanin ai ko yanzu ba Yusrah bace ta taimaketa nice, na fi so ta ringa tunawa cewar Yusrah ɗin nan dai da ta wulaƙanta ita ce ta zama gatanta a duniya."
Sun fahimci abinda take nufi suka tattara suka koma ciki dan fitar tasu gaba ɗaya sai ta zama ba daɗi, ƙwarai yanayin su Goggo ya ƙara saka musu tsoron Allah a zukatansu.
*Duk* yadda ta so hana kanta kuka gagara tayi bayan ta buɗe kafar auta ta ga irin yadda tsutsa ke yawo a jikin ruɓaɓɓen naman ƙafar da ya tarda ƙashi ya lalata.
Amsar akwatin aikinta ta yi bayan AA ya ɗauko mata ya koma ya zauna yana kallon yadda take hawaye ya ɗauke kansa yana sake kai zuciyarsa nesa saboda iyayenta ne ai bashi da yadda zai yi dole zai yi shiru yana kallon ikon Allah, maganin da ta zuba masa ta ga bai yi wani motsi ba ya sa ta zube nan ta fashe da kuka tana kallon Aunty Khadija dake riƙe da shi wacce ta sake shi da sauri ta zo ta kamata daidai da miƙewar da AA ya yi da ƙarfi yana kallonta ƙirjinsa na neman kasa ɗaukan yanayinta ya ƙaraso ya kamata daga hannun aunty Khadija ya miƙar da ita tsaye ya kama hannunta yayi ciki da ita ya zaunar da ita sannan ya duƙa a gabanta sosai yana riƙe da hannayenta ya ce" Idan ba zaki iya ba bani saƙon da zan sanar musu in je in faɗa in dawo, ki rufa min asiri ki dubi maraicina, Anza ya tafi ya barni da duniyar nan, in kika bi shi to kuma in yi ya ya ne? Haba mana *budurwata*."
Numfashi ta ja na abin kuka tana laƙace hancinsa ta ce" Kai ko? Ba zaka daina tsokana ba ko? Allah na barin wani dan wani ya ji daɗi ne *saurayina*?"
Kai ya girgiza a sanyaye ya ce" A'a, amma kuma... mu bar maganar ma, in je in ce mun yafe musu ko,shikenan ko? Kin ga Haidar fa baya son rigimar nan."
A dole ta yi murmushi tana kallonsa a sanyaye ta ce" Yaya zan yi? Rohi yaya zan yi? Ƙafar yaron nan fa cireta za'a yi, baya jinta a jikinsa, kukan ciwon da yake yi ba na ƙafar bane na jikinsa ne da ƙugunsa, ƙafar bata ciwo ta mutu murus fa."
Shi da kansa sai da jikinsa ya mutu a sanyaye ya ce" Allah ya bashi lafiya, babu yadda bawa zai yi da ƙaddarar rayuwarsa, daga nan a kai su asibiti su duka in kin shigo sai ki ɗora su a abinda ya dace su duka, ki daina kukan haka."
Ta sake sauke ajiyar zuciya ta ce" To shikenan, ina so ita aunty Khadija ta fara zuwa can gidan marigayi da aka gyara su zauna a nan kafin a saki su Goggon, kuma ina so a sauke musu kayan abinci da suturu Rohi, ka ga dole dai zan fita yau."
Ido ya yiwa micik micik ya rage murya sosai ya ce" Haƙƙin nawa fa?"
Da ƙarfi ta ce" Astagfirullah, wai ba zaka daina ɗanyan baki ba?"
Ya dafe bakin yana kallonta yace" Ai kin san boy kawai nake jira ya dawo in kora shi gidan kakarshi,wallahi yau sai su Haidar sun samu madara iya madara bayin Allah, taso mu je a yi duk abinda ya kamata kya fita amma zuwa dare, ma je asibitin mu gansu sannan mu je mu ga duk abinda aka kai musu can gidan, tashi mu je kin isama ki hana min ƙaniya Allah na tuba."
A dole ta yi gum tana gaba yana biye da ita suka dawo ta zauna daf da Goggo sosai ta riƙo hannunta a tausashe ta ce" Goggo, ki yi haƙuri ki bar kukan hakanan kin ji, haka Allah ya hukunta kuma ni na yafe miki duniya da ƙiyama ina fatan Allah ya jaddada rahama a kabarin iyayena sanadiyar wannan, kin ga dole yanzu za'a kai ku asibiti, kema baki da lafiya, gashi ciwon auta fa babba ne, dole za'a je asibitin nan,ku daina kukan hakanan dan Allah, in sha Allah lafiya zata samu kuma hankali zai kwanta aunty Khadinmu."
Aunty Khadija ta kalleta
Yusrah ta ce" Ki daina kuka kin ji aunty Khadinmu, Allah ya ƙara sanyaya mana, idan aka je asibiti aka gama amsar su kin san can ba ma yarda da ƴan jinya, ku sai a kaiku gida ku huta, in sha Allah da dare zan shigo mu sake zaunawa, ki daina kukan nan haka aunty Khadi yaya aka yi kuka ɗauki lokaci a cikin wannan halin baku zo ba? Ni ban sani ba wallahi da ba'a kai har haka ba."
Aunty Khadija ta share hawaye zata yi magana aka buɗe ɗakin aka shigo da sallama, jikinsa ɗauke da uniform da jakar makaranta, mai aiki ta shigo masa da wata jakar mai ɗauke da computensa ya ƙaraso yana faɗin" Dady, wayyo Allahna yau mun daku."
Aswan ya tare shi kamar wani ƙaramin yaro yana faɗin" Come on boy, ai da gani yau ka sha wahala, zo in gani?"
Yusrah ta taɓe baki bayan ta bi su da kallo ta ce" Kai Safwan baka ga mutane bane? Su Goggo ne fa."
Goggo sai da ta zabura tana ƙara bin Safwan da kallo, aunty Khadi kuwa tana murmushi ta ce" Ka ga shagwaɓaɓɓe, malam zo nan mu gaisa, ko da yake ka san bama jituwa da kai."
Baki ya kama yana kallonta kafin ya yi dariya ya ce" Kai, aunty Khadi masoyiyar, ai baki isa ki sakeni ba, na faɗa miki ba kayan sallah ba? Allah ya kai mu sallar bana a Dubai zaki zaɓo sai in ga ta gori ko dad?"
Aswan ya gyaɗa kai ya ce" Tabbas in dai saboda kayan sallah za'a saka min ɗa a gaba, zaki je Dubai ki zaɓi kayan sallah."
Gaba ɗaya aka yi dariyar diramarsu sannan ya gaishe su sosai kafin su yi ɗakin sa shi da babansa yana faɗin " Kana ji boy, yi maza ka yi wanka direban ka ya kai wajen kakarka ka ji? Ɗan Anza ma ya ce ka je yau yi maza ka gama."
Ai kuwa da farin ciki yayi bayi bayan ya gama cire kayansa, shi kuwa ya fito yana nufar waje dan motar asibitin ce ta ƙaraso, wato ambulance nan likitocin suka shigo suka gaishe da Yusrah a matsayinta na mataimakiyar shugaban asibitin sannan suka ɗauki mararsa lafiyan, docter na rubuta abinda take faɗa masa duka wanda take buƙatar a yi na gwaje gwaje harda na auta saboda ba za'a cire masa ƙafa kai tsaye ba sai an tabbatar da gwaje gwaje sosai kafin a yi, sannan mai aikinta ta saka kayan abinci da su fruits kafff suka yi gaba bayan Safiya ta nunawa aunty Khadi ita fa ba zata bi su ba aunty khadi ta ce wallahi ta kiyayeta bata son iskanci ta wuce su tafi sannan suka tafin sai sakin baki take tana kallon gidan ta rafka tagumi tana kallon Goggo ba ranta ta ayyana _' Ina ma ace Goggo da malam ne suka sheƙa nima na samu wannan duniyar? Kai da an gama min komai.'_
( Duniya kenan budurwar wawa, wato duniya rawar ƴan mata, da ace Goggo zata ji fatan ƴar ta Safiya da ta idasa mutuwa da baƙin ciki a cikin ambulance ɗin nan, sai dai gado ƙarfin Allah. Allah ya sa mu dace)
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
12/07/2024, 12:06 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*98*
A gajiye sosai ta zuro ƙafafun ta da ƙyar kafin ta fito daga motar gaba ɗayan ta tana rataya jakar ta da kuma riƙe mayafin ta da kyau, kafin ta juya ta rufe ƙofar har dreban ya fito ya rufe ƙofar, a kasalance ta dube shi tace "To, na gode, sai da safe."
Da girmamawa ya amsa ta da sai da safe kasancewar dreban su Anna ne ya dawo da ita gida, a nutse ta shiga jan ƙafafu zuwa cikin gidan ta buɗe ƙofar da empreinte ɗin ta. Tana buɗewa ƙarar radio ta daki kunnuwan ta wanda aka cika falon da shi, dake ƙofar ba ta wasa bace shiyasa daga waje ba zaka ce an kunna radio ba kamar dai a studio.
Riƙe haɓa ta fara yi tana wara idanun ta da son tabbatar daga falon ta ne kiɗan nan ke tashi? Ko da yake ko ba ta tambaya ba ma ai daga ɗakin ta ne, saboda waƙar dai ta sojawa ce wacce ita a wajen ta kamar ihu ne suke dan wasu kalaman ma ba fahimtar su take yi ba.
Abu ɗaya da ta fahimta game da wannan ƙarar anan shine, matsala yake so su samu da ita tunda dama ta san a cike yake da ita na laifuffukan da ya jeran ta mata ɗazu wai ta masa, haka fa ya yi tsayuwa kamar wanda zai yi huɗuba yana faɗa mata tunda aka shiga satin sabgar bikin ƴaƴan Anna ta daina bashi kulawa, sannan a gaban shi ta jibgawa ɗan shi dundu a baya tare da katsa masa tsawar da shi kan shi uban ba jura yake ba, sannan wai kwana biyu ba ta ba su Meem abinci da kan ta ba.
To, wwataƙila hakan ne ya sa ma ta yi ta kiran shi ya zo ya ɗauko ta sai a ce waya a kashe, ashe casu yake yi a gidan ta dan bata nan, ya sani ne wannan hayaniyar bata son ta, tunda ta samu cikin nan har zuwa yanzu da ya bayyana kan shi magana ma ba cika son ta tayi ba, to amma bari dai ta ƙarasa ta ji me ye dalilin shi na son tara mata iskokai a gida.
Za ta yi sallama sanda take cire takalmin ta daf da carfet ta ja baki ta yi shiru saboda ganin shi zaune ƙasan carfet ɗin ƙafar sa ɗaya miƙe ɗaya kuma a tanƙwashe yana cin indomie da soyayyar kaza, sai wayar sa a hannu yana dannawa, mamakin lamarin na shi ya sa da ba za ta yi sallama ba, amma da ta tuna falalar sallamar sai ta yi ƙasa ƙasa tana takowa a sanyaye tana kallon shi.
Irin kallon nan na ka dai yi wa mutum ya sakar mata shima daga iya ƙasan ƙafafun ta, take kuma ya cira kan shi ya mayar kan sabgar gaban shi yana kai wata loma a baki tare da shiga jijjiga kai shi a dole rawa yake daga zaunen nan. A hankali ita dai ta zauna kujerar dake duban shi tace "Sannu da gida Rohi."
Bai kalle ta ba ya fara jinjina kai sannan yace "Sannu da ƙoƙari."
Murmushi ta yi ta shiga waigawa da son hango inda za ta ga magunan shi amma shiru, Safwan kuma tun jiya da ta jibge shi ya kai shi wurin Anna, ashe bayan ya kai wa Anna shi sai da ya ce mata wai ita shirin kashe masa ɗa take yi bayan Haidar bai zo duniyar ba, to ko Haidar ya zo ai ba zai yarda a taka masa babban ɗan sa ba, dan haka shi fa baya son ɗaukar alhaki, ita ba dakuwa za ta yi ba, kuma harare ma idan ka wa mutum sai ya kwana yana kuka ya ce wai Haidar baya son hakan, to kenan sai a yi ta zaluntar shi dan yana maraya kawai?
Kallon shi ta yi tace "Wannan kiɗan fa? Dan Allah a rage mana ya yi yawa."
Ba tare da ya kalle ta ba yace "Nishaɗi nake ji, lakuru nake fa."
Ɗaga murya ta yi sosai saboda ƙarar na shiga kunnuwan ta tace "Amma ai ni yana takurani."
Ƙasa da sama ya kalle ta kafin ya taɓe baki yace "Ko za ki kira yarinyar (Intisar) nan ne ta bani umarni na kashe?"
Murmushi ta yi dan yanzu kam ta gano waɗanda ke saman kan nashi, dan haka ta girgiza kai tace "A'a, uwata na zamanta