Showing 90001 words to 93000 words out of 397328 words

Chapter 31 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70070

yasan idan dai har ya ci wake minti goma ya yi yawa ya fita a hayyacin shi.

Yana gama sallah ya miƙe ya ɗauko waken nan ya zauna bakin gado ya fara ci, saida ya ci kusan rabin shi sannan ya ajiye ya wanke hannu sai kuma ya ƙi shan ruwa saboda dai dole yana so ya ga uncle Kofa a yau ɗin nan. Kafin kace kwabo yanayin shi ya fara canzawa, nan da nan AA ya rikice bai kuma sanin inda kan shi yake ba.

*01:00* cif aka shiga zagayen ɗakunan dan tabbatar kowa na ɗakin sa, nan ne mai shawagin ya ga AA a wannan halin, dan haka aka kira ambulance aka zo aka ɗauke shi da gaggawa sai asibitin dake cikin nan wacce guda ce tak, amma kuma daga ciki akwai ɗakin idan babba ba ya da lafiya aka ajiye shi ba mahalukin da ya isa ya gan shi saboda tsaurara tsaron da ake gare su, dan kowane lokaci za'a iya farautar rayuwar su a gidan ma.

Tabbas kuwa inda aka kai shi ba nan ne uncle Kofa yake ba, sosai likitan dake kan shi ya wahala kafin ya gane wani abun ya ci ko ya sha, nan ya masa allurar da za ta saka shi amaye abinda duk ya ci, dan tun aman da ya yi a daki bai sake wani ba, kafin wani lokaci kuma ya samu aman tare da wani irin gumi dake tsatsafo masa tamkar wanda ya haɗiyi bakin wuta, ai sai jikin shi ya saki har yana iya motsa jikin nasa, sannu sannu nutsuwar sa ta dawo jikin shi ya tuna abinda ya kawo shi wurin nan.

A hankali ya miƙe daga kan gadon ƙafafuwan sa har rawa suke irin zasu masa gardamar ɗaukar sa, haka ya dinga bin bango yana son fita daga ɗakin, haka a daddafen ya fita yana ta dube dube da leƙa sauran ɗakunan dake wurin, ya gamu da wasu likitoci biyu amma basu kula da shi, sai wani ɗaya daga cikin masu tsaron wurin yana tsaye ƙofar wani ɗakin da alama gadi yake yi, har AA ya ɗan giftashi ya wuce mutumin ya bishi da kallo yana wani shaƙiyin murmushi ya ce "Ka makara da kaɗan, idan kana son kai wa gaci ga wannan *tafiya*, to dole ka fara sammako, amma ka sani oga ba zasu bari ku haɗu ta sauƙi haka ba."

Juyowa AA ya yi ya kalle shi, amma sai ka rantse ba shi ya yi maganar ba, da wani takaici ya sake ɗaga ƙafa zai ci gaba da tunkarar inda ya sa gaba, amma sai jami'in nan ya sake duban ƙeyar shi yace" Wahalar da kan ka zakayi, an jima da canza masa ɗaki."

Nan ma juyowa ya sake yi, sai kawai ya tunkaro mutumin cike da ƙarfin hali dan jikin shi ba ƙwari sosai, saida ya tsaya gaban shi yana jin kamar suna neman yi masa rainin wayo ne yace" Yana ina yanzu? Me ya same shi? Ba likita zai gani ba kawai?"

Saida mutumin ya dudduba ko ina ya ga ba kowa sannan ya kalli AA yace" Wannan ba irin takon da zakayi bane dan ganawa da mutum kamar Sidi Kofa, ba dan ana tuhumar sa ko ya aikata wani laifi aka kawo shi nan ba, ta ya kake tunanin za su barshi sakaka haka har kowa ma da ya yi ganganci irin naka dan son ganawa da shi ya gan shi? Ka canza salo."

Daga faɗin haka ya shiga takawa ya bar ƙofar ɗakin har ya ɓacewa ganin shi, dafe ƙugu ya yi yana ayyana _" Lallai sai ya canza salo, canji ma kuwa babba, tunda gashi duk kasadar nan da ya ɗauka ba ta anfane shi da komai ba sai barazana ga rayuwar sa."_

Jinjina kai ya yi ya shiga takawa har ya koma ɗakin da aka kwantar da shi gudun kar a zo baya nan a zargi wani abu. *Abun* rikitarwar yana shirin kwantawa kan gadon shi dan ya fara tunanin wata sabuwar hanyar kawai ya ga ƙaramar takarda a saman gadon, da sauri ya ɗauka yana warwarewa tare da dussuba kusurwar ɗakin ko zai ga wulgin mutum amma babu ko da motsi, yana buɗe takardar ya shiga karanta rubutun ta a cikin zuciyar sa kamar haka _"Ka sameni ɗakin dake kusa da inda aka kwantar da kai yanzun nan."_

Ƙwarai mamaki ya kama shi har yake jin hakan na nufin wasu na bibiyar aikin nan kenan? Ko kuma dai wasu ne ke bibiyar shi? Idan hakane kenan dai tabbas aikin da ya ɗauko ma kan shi babba ne? Sannan zagaye da manyan mutanen da basa so a bankaɗo gaskiyar? Tabbas hakane, kuma kamar yadda aka faɗa masa ya canza salo, to kuwa zai canza salon ko dan ya basu mamaki tare da kai wa ga abin da ya soma.

Ba tare da tsoro ko shakkun wani abu ba ya linke takardar sannan ya sake ƙwarara gangar jikin shi da kuma zuciyar shi, dama dai ba tsoro gare shi na wata halitta a duniya face mahaliccin ta, kawai wani abun yana saka shi ɗar ne saboda rashin sabo a aikin, dan tunda yake zai iya cewa sau ɗaya ya yi aikin dake cike da sarƙaƙiya da tuggu kala kala, daga ƙarshe kuma basu sha wahalar warware matsalar ba dake yana da mataimaka a lokacin.

Da ƙarfin shi ya tura ɗakin dake manne da wanda ya fito daga ciki bayan ya duba lambar ɗakin, yana shiga ba wani abu da ya ɗauki hankalin shi a ciki kasancewar kamar dai ɗakin da ya fito ne sai mutumin dake zaune bakin gado ƙafar sa ɗaya a miƙe kan gadon ta yi sumtum tsabar kumbura, sai kuma ɗaya ƙafar akan wata ƙaramar kujera mai matakala irin wacce ake ajiyewa mata masu ciki idan za'a musu awo na kwance, ma sha Allah mutumin ko banza yana da jiki sosai, ga kuma kayan marmari a gaban shi yana faman ɗirka tamkar dai a gidan sa yake. Idan akwai abun mamaki da dasa alamar tambaya bai wuce yadda yake zaune asibiti ba bayan kuma ba alamar rashin lafiya a tare da shi, amma sai AA ya haɗiye duk wani mamaki dake shinfiɗe kan fuskar shi ya ƙaraso kusa da shi suna kallon juna musamman dattijon da har yake masa murmushi.

Kujerar da likitan da ya gama duba shi ya tashi ya nuna ma AA yana tauna ƴaƴan inibi yace "Bismillah, zauna."

Fuska a haɗe AA ya dubi kujerar sannan ya zauna yana ci gaba da kallon shi, cikin dakakkiyar muryar sa dake nuna ransa zai iya ɓacewa kowane lokaci yace "Kai ne kake son ganina a nan?"

Murmushi mutumin ya yi yana kallon shi amma har lokacin bai daina shan inibin ba yace "Ban tsammaci wannan tambaya daga gare ka ba, kamata ya yi tambayar ka ta kasance _" Wa ye kai? Ya aka yi kasan ina asibitin nan? Me kuma ya sa ka kira ni?"_

Wani malalacin murmushi AA ya yi saboda hango wani abu a tare da mutumin nan, gyara zaman sa ya yi cike da wata muguwar ƙasaita ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ɗora hannun shi na dama kan saman kujerar yana ƙarewa dattijon kallo yace" Idan na fara tambayar ka duk wannan, to me ye anfanin kasancewata *namiji* kenan?"

Sai kuma ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya har da murmushi a fuskar shi yace" Ko da yake, gaggawa nake dan ina so na yi bacci, me kake so ka faɗa min *Baba*?"

Irin murmushin nan mai ciwon gaske ya yi dake nuna bai ji daɗin maganar AA ba, amma sai ya basar ya dube shi da kyau har da dakatar da shan kayan marmarin sa yace " Aswan, binciken da kake yi ka dakatar, idan ba haka ba za ka tono wuƙar da za ta yanka wuyan ka, ba komai bane mutum zai so ya bankaɗo shi, wani sirrin idan ka tono shi fallasa ka yake a yadda ka zo duniya, dan haka ka dakatar."

Ɗaga giraren shi biyu ya yi da mamakin nan yace" Au! Dama da kuka dinga tonawa kuna ajiye sirrin ba ku san da cewa akwai kazar da ke tonowa ba? Wannan sirrin naku kuma ba kaza ba ce ke tonon shi..."

Sai da ya haɗe duk wata dariya sannan yace" Zakara ne."

Sai kuma ya gyara zama tare da sauke ƙafar shi yace" Idan har kunsan kuna da tsoro ko hauhawar jini, ku nemawa kan ku mafita, ƙasata nake wa aiki, na kuma riga da na fara wannan aikin, ba wanda ya isa ya dakatar da ni duk faɗin duniyar nan muddin ina numfashi."

Miƙewa ya yi daga kujerar ya juya zai bar ɗakin, rai ɓace mutumin ya kalle shi yace" Ko da kuwa mahaifin ka ne Aswan?"

Ba tare da ya yi mamakin sunan shi da ya kama ba ya taɓe baki cike da tabbaci ya kalle shi yace" Ƙwarai, ko da Elhaj Aliyu Anza ne."

Hannun ƙofa ya kama zai fita cikin ɗaga murya mutumin yace" Kar kayi wasa da wuta Aswan, ka bi a sannu ko dan kar ahalinka su tagayyara, ka dakatar da binciken nan ka koma gida."

A gadarance ya juya yana kallon shi a tausashe yace" Nayi *tafiya* mai ɗan tsayi kafin na iso nan, kuma na jima da ɗaura niyyar yin *WATA TAFIYAR* in har zan gano daga ina asibitin mu ke fitar da bilyoyin kuɗin da duk yadda asibitin ta kai ga duba majinyata ba za ta haɗa kan wannan kuɗi a ƙananun shekaru, infact...me ma zai sa a dinga fitar da su a sirrance? Kuma a motar asibiti kamar wata gawa? Dattijo, ina so na sani, kuma zan sani da izinin Allah, ka faɗawa waɗanda suka turo ka kar a sake min irin wannan ganganci, ma'ana yi min barazana da ahalina ko abinda ya yi kama da hakan."

Daga haka ya fice daga ɗakin gaba ɗaya bai sake ko bi ta kan dattijon nan ba da ya ji wata irin nadamar karɓar aikin nan akan wasu kuɗi da basu taka kara sun karya ba marar kunyar yaro yana neman tayar masa da hawan jinin sa a banza a wofi. AA kuma tsabar takaici duk da zuwa lokacin ya fara fahimtar wasu abubuwa da daman gaske, amma haka ya dinga keta tsakiyar prison ɗin nan saboda ya san wurin duk da ba sosai ba har ya koma ɓangaren shi kaɗai ba tare da an sallamo shi ba.



*ANZA MENSION*


Kasantuwar yau ta faɗo week-end ya zamo gaba ɗaya ahalin gidan Anza suka ɗugunzuma zuwa asibiti wajen Safwan, domin tunda Anna ta samu Aba da maganar a faɗa mata waye yaron ya zayyane mata ita ma ta ji yaron ya shiga ranta ainun har ya zamo a yanzu da Babansa yace zai yi tafiya na ɗan lokaci take ji anya zata iya bar masa yaron? Duba da shi ba mazauni bane, Safwan kuwa iyaye yake da buƙata masu kula da shi da dukkan motsinsa, sai dai zata bari har ya dawo sai a yi maganar, ita in ba ma rigima irin ta Aswan ba, kai da ba mace gare ka ba ya ya zaka ce wai yaro naka ne ɗan ka? Ka kula da shi ta ya ya? Yau ko aure ya yi ai sai an yarda da cewar matar zata iya haɗawa ta riƙe za'a bar mata dan ba kowa ke iya riƙe ɗan wani ba gaskiya, balle Safwan ba zata so ya ga rayuwa irin ta matsi ba, ba zata taɓa so ba gaskiya.

Kuma cikin ikon Allah yaran gidan ma sai yaron ya shiga ransu, ko yau da ta fito a shirye ta same su har da Abrar sun shirya zuwa asibitin, amma duka kaf wannan sintiri da suke yi Gwaggonsu bata ce ku ci kanku ba, hasalima faɗa ta yi sosai da mamakin halayyar su har faɗi take sai sun ɗauko mugun iri ya gama da su baki ɗaya kowa ma ya huta.

Tunda suka zo suka saka Safwan a tsakiya, ba ma kamar Abrar da ta fi jin yaron a ranta saboda tunda aka ce Yaya AA ne ya kawo shi kuma yana masa inkiya da ɗan sa ta zo masa da ice cream take bashi a baki da cokali tana yi masa fira a dole yaron ya saki jiki da su, su ɗin ma yana ta bin su da kallo da dariya idan suka yi masa abin bada dariya, dama Anna ta jima da jan shi a jiki, ya zamo idan ta zo a fuskarsa take gane ƙwarai ya yarda uwa take a wajensa ko kaka, domin da fara'a da sakin fuska sosai yake tarbanta ita kuwa takan wuni tare da shi ko ta yi rabin wuni idan likitoci suka nuna ya dace ta tafi, hakan ya sa a hankali a hankali damuwarsa ke tafiya abinka da yaro har ya zamo a yanzu damuwarsa biyu ne kawai, zaka ji yace Anna yaushe Dadyna zai dawo? Ko kuwa ka ji yace Aunty Yusy nima na maki fushi..., haka dai ire iren haka kan faɗo masa suma Anna na da amsar bashi da zarar ta bashi sai ka ga ya shiga lamuransa, amma kuma a kwance da yake sai dai a dan dagon shi, a ɗan juya shi kaɗan a jinginar da shi, dan bayansa na nan ba warkewa ya yi ba.

Sai da suka kusan wuni sannan suka koma gida, suna zuwa suka tarar da su Meem da Angel ɗin Aswan na inda suka bar su, abincin su wuni guda yau basu wani ci abin kirki ba, hankalin Anna ya tashi, mai kula da su ta tabbatar masa babu abinda bata kaɗa masu ba kuma a launin abincinsu na ci na dangin nama du ta gwada masu sun ƙi ci, a dole ta yi kiran Aba ta sanar masa, ya saka a kai su asibiti ko basu da lafiya ne? Ta ƙare da faɗin ta yiwu kuma mai su suke so, ai sun ma yi ƙoƙari su da basu saba da kowa ba, kai tsaye ya sa aka ciro su aka kawo su aka ajiye.

Da sigar damuwa Anna ta ce" Abansu, wai ina ya je ne? Wayarsa bata shiga? Anya ba ya koma aikin sojan nan ba kuwa? Ni fa lamarin yaron nan na bani tsoro, mutun sai ɓoye abu a ciki, bai sanar maka inda zai je ba?"

Aba a waya ya yi tsammm, sai kuma ya ce" Bari in yi kiran masu tsaronsa, su kam dole su san inda yarona ya je, maganar komawarsa aikin soja bai isa ba, bai isa ya koma ban sani ba, ina zuwa." Daga nan suka yi sallama ya kashe kiran ita ma ta kashe ta zauna jiran wanda zai zo ya kai magunan asibitin dabbobi a dubo lafiyarsu, dan kuwa ba zata taɓa yarda ta yi wasa da lafiyar magunan nan ba, ta san zuciyar yaronta ne.


*BILAL YUSUF*


Bawa bai san ƙarfin da zuciya ke da shi a gangar jiki ba sai idan zuciyar nan ta haɗu da jarabawa mai ƙarfin gaske a filin da babu sake, a irin wannan lokacin ne bawa zai san cewa lalle zuciya mugun nama ce mai ɗauke da sinadarin tarwatsa duk wani yunƙuri na farin ciki ko akasin haka

A yanzu Bilal na cikin halin bege fiye da misali, ta zamo a cikin tunaninsa, a cikin mafarkansa ta zamo abinda ya fi nema fiye da kuɗi idan ya saka ƙafa ya fita daga gidan su, matar Yayansa ta zamo wacce ke tausarsa da bashi baki, Yayunsa sun zamo masu dubansa da mamakin lamarin, mahaifiyarsa kuwa ƙwarai ta tausaya, amma a nan ta tashi ta bar zancen, domin ita dama mutun ce mai riƙe da nata ra'ayi, damuwar ɗan wani damuwa ce amam a wajen uwar sa ko a wajen ahali nasa ko a wajensa, ita ta ta damuwar ta nata ƴaƴan ne, shi yasa tashi ɗaya ta nuna masa cewar Allah ya sawaƙa, ta yi addu'ar bayyanuwar yarinya ta ƙarashe da faɗin "Bilalu Allah ya baka mace ta gari kawai, amma kar ma ka saka damuwar nan a rai kuma kar ka nemi ɗagan hankali a kan wannan damuwar dan gaskiya ba zan lamunta ba."

Daga wannan lokacin ya gane shi ma yana iya shiga sahun Yayunsa tun kafin ya yi auren, sai kawai ya naɗe damuwarsa ya barwa cikinsa, amma a zahiri neman ta yake yi ido rufe, burinsa ya ganta, kuma in sha Allah ya aure abinsa, so halitta ne, Allah ya dasa masa, bashi da wani abin yi sai bautawa so ɗin, kai ko da *WATA TAFIYA* zai yi dan ya ganta, sai ya nemo muradin zuciyarsa.


*NABIHAT*

"Nabihat, Nabihat! Ba kya ji ne ana ta kiran wayar ki?" Mahaifiyar Nabihat ke faɗa dake gefenta tana shan fruits salat hankalinta a kan Nabihat ɗin dake zaune wayarta sai ringin take yi amma ta ƙi mayar da hankali ta ɗaga, kuma ta gani ta kalla amma ta ki ɗagawa.

Wayar Nabihat ta danne ta kashe gaba ɗaya tana fitar da siririn tsaki na jin haushin mai kiran nata, to ita mahaukaciya ce zata yarda ta ɗaga kiran nan su cewa juna me? Da ace ba soja bane sojan ma yaron sa da sai ta kula, amma haka kawai salon sanadiyar wannan a yi mata sakiyar da ba ruwa?

" Wanene?" Mahaifiyarta ta tambayeta da kula,
Nabihat ta sadda kanta a hankali ta ce" Mum, sergent Auwal ne fa, bayan na faɗa masa ba zan taɓa iya kula shi ba ya yi haƙuri amma ya kasa ganewa... Mumy wai dan Allah ya ya labarin Yaya Aswan? Ba zaki yi kiransa ya zo ya gaisheki ba? Ya jima bai zo ya gaishe ki ba."

Mumy ta yi ɗan tsai tana kallon Nabihat, har sai da Nabihat ɗin ta tsargu ta ɗan sosa kai zuwa gaban goshi sai kuma ta miƙe tana sinne kai ta yi sama da sauri cike da jin kunya.

Ido mahaifiyar ta ta zarro sai kuma ta shiga tafa hannu tana faɗin "Allah mai alkhairi, ke Nabihat zo ki faɗa min me yake faruwa? Kai kai kai lalle da nice zan kaiwa Babanki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login