Showing 372001 words to 375000 words out of 397328 words
kwana ashirin da ɗaya, saida ta saka mata ruwan da suka dace da ita ta kwanta kan gado sannan ta je ta sanar da Dr. Siddik, tun kafin ya sanar ma AA yake ta murna da farin ciki, dan ya san babu abinda Aswan zai so ji a duniya yanzu dai da zai masa daɗi kamar ya ji wannan labari.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
12/07/2024, 12:05 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*94*
*A* ƙasar waje kuma yau kwana goma sha ɗaya kenan da zuwan Bilal, sun nemi da ya zo ne dan ya samu sauƙin abinda ke damun shi, sai dai babu canjin da suka gani tunda ya zo garin, idan ya yi zaune yana tunani har sai a kusa sace shi bai sani ba, wannan walwalar da raha da yake da yanzu duk babu, duk yadda suke da aunty Intisar wajen raha da barkwanci yanzu babu, sai ya zama ita ke jan shi da hira da tsokana amma sai ya mata murmushi kawai, hakan sai duk ya fara damun su har suka zauna suka tattauna maganar ita da Yaya Mubarak, amma hakan ba yana nufin zai canza bane tunda ba mafita suka sama mishi ba.
Yanzu ma coffee ne a hannun shi da Intisar ta miƙo mishi tun yana da zafi har ya huce salam, ya tsurawa titi idanu ta saman benen yana kallo, tun mutane nata kai da kawo wajen tafiya sabgogin su da suka saba, har layin ya yi tsit ta yadda za'a iya kashe mutum wani ma bai fito wajen ba. Ita kanta aunty Intisar har ta gama kula da yara da mahaifin su suka fice, shi ya nufi wajen aikin shi daga nan ya sauke yara a makaran ta, ƙarasa kaye-kayen ta tayi ta sake leƙowa ta ƙofar ta ga yana nan yadda ta bar shi, ya share sama da awa ɗaya bai ma sani ba shi kan shi, girgiza kai ta yi a sanyaye cike da tausaya mishi, buɗe ƙofar ta yi ta hauro matakalar ta tsaya kusa da shi ta ɗora hannayen ta kan ƙarafen da aka zagaye wurin ya yi kyau tana kallon shi.
Bai san ta zo ba sai da ta ɗan bubbuga ƙarfen sannan ya ɗan zabura ya kalli inda take, yana ganin ta ya saki murmushin yaƙe ya kalli coffee hannun shi yace "Aunty."
Girgiza kai ta sake yi tace "Hmmm! Bilal ba dai za ka sauƙaƙawa kan ka ba ko? So ka ke sai wani ciwon ya same ka? Bilal komai fa da ka gani ya faru a rayuwa haka dama Allah ya rubuta zai faru, Bilal akan mace ɗaya, yarinya ɗaya ka saka kan ka a damuwa sannan ka sa duk wani dake tare da kai, ka dubi halin da Hajia take ciki a kan ka? Ba za ka rayu dan ita kawai ba Bilal?"
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ƙasan benen yace" Ba haka bane aunty, ba wai na kasa cire abun a rai bane ko ban yarda da ƙaddarata ba, sau da dama sai na manta da abun, amma sai na dinga tambayar kaina me ya sa Hajia bata mana adalci? Me ya sa wannan videon ba ta bayyana ba saida aka kusa auren mu? Sannan da na rasa Yusrah yanzu, shin a ina zan samu madadin ta? Wannan tambayoyin su nake yi wa kaina kullum aunty."
Murmushi ta yi tana ɗan bubbuga ƙafar ta dake mata mijirya tace" Bilal kenan, Hajia fa yanzu ta canza daga yadda ka san ta, kai ma shaida ne akan haka, mata kuma za ka samu Bilal, wallahi za ka samu wacce ma ta fi Yusrah."
Shi ma murmushin ya yi yace" Aunty Intisar, a ina kenan? Ina zan samu kamar Yusrah?"
Da sigar zolaya tace" To ka sani ko na samo maka ne?"
Murmushi ya sake yi ya ɗan kalle ta yace" Da za ki sama min matar ma da naji daɗi, dan in dai nine kam ban shirya ba yanzu, burina kuma shine na ga na farantawa Hajia ta hanyar samo wata matar na aura."
Irin fa da wasa ne kawai kamar kuma suɓutar baki ta sake cewa" Da gaske na maka mata Bilal, ai tuni nake maka ajiyar Nawal, dan ma suna karatun nahda ne ya sa ban ma kowa maganar ba, amma tuni na baka ɗaya daga cikin twins ɗin Anna."
Kallon ta ya yi da irin ba alamar wasa yace" Aunty, Nawal fa?"
Jinjina masa kai tayi da irin dariyar nan ta tsokana tace" E Nawal, ko bata maka bane?"
Tsare fuskar ta ya yi da idanu, sai dai sam ba hankalin shi na kanta bane kawai ya tafi tunano Nawal ɗin ne, ƴan biyun nan dai, jajayen yaran nan masu kama da larabawa? Ƴan lukutaye ma sha Allah dumur dumur da su, gwanayen kwalliya da tsafta, sannan in suka gilma sai ka bi su da kallo ko dan ƙamshin jikin su? Ba su da wata makusa, ilimi suna da shi tubarkallah, a sanin shi ma ai da ƙasar waje zasu je su ci gaba da karatu, bai san me ya hana tafiyar ba?
Take ya ji wani murmushi ya suɓuce masa ya ɗan girgiza kai a hankali yace "A'a aunty, ni na isa nace bana son Nawal, ina so mana tunda kin bani, na ji kuma na yi biyayya."
Zuro aunty Intisar ta masa da idanu tana jin kamar zufa za ta keto mata tace "Kana nufin ka amince kenan?"
Da tabbaci yace "Na amince mana aunty, ba ke kika bani ba? Ai ko wanda ban sani ba ce kuma baki haɗa jini da ita ba kika bani wallahi zan karɓa, saboda na yarda dake aunty, bare kuma jinin ki, ƴar uwar ki."
Murmushin yaƙe ta sakar masa tare da share gumi daga ƙarƙashin hancin ta, sai kawai tace masa" Ina zuwa?" Da sauri ta bar wurin ta nufi ɗakin ta tana ambaton" Hasbunallah wani'imal wakil! Me na faɗa haka da bakina? Bilal fa ya ɗauka da gaske nake wallahi, ya zanyi yanzu? Su Nawal suna da samari fa, duk da dai nasan ba wanda ke zuwa wajen su, ni kam na shiga uku, yau ko ɗan da ka haifa ba za ka masa haka ba bare ƙanwa."
Tana wannan sambatun ta ɗauki wayar ta ta shiga dokawa Anna kira, ba jimawa Anna ta ɗaga suka fara gaisawa sosai kafin ta shiga sanar wa Anna abinda ya faru, da fari da zolaya Anna tace _" Kai ba fa na son iskanci, shi waccen Yayan naki haka kawai ya bayar da ɗaya autar tawa ga uncle Sul, yanzu kema kina so ki ce min kin bayar da ɗayar ga ɗan uwan ku ne?"_
A marairaice aunty Intisar tace _" A'a wallahi Anna, sam ba haka nake nufi ba, na kira ne dan ki faɗa min ta yadda zan faɗa masa da fa wasa nake masa, dan ni kai tsaye ba zan iya faɗa masa ba Anna, kinga har yanzu bai warware daga damuwar abinda ya faru ba."_
Ajiyar zuciya Anna ta sauke cike da dattako da nutsuwa da dattijantaka tace _" Mu mun isa tsayar da abinda ubangiji ya hukunta zai faru ne? Shin kika san me hakan ke nufi? Wataƙila abinda yake a rubuce ne tun kafin samuwar mu kika faɗa, ko kuma ita ubangiji ya zaɓa masa a yanzu bayan yayi haƙuri da ƙaddarar sa, shiyasa kika faɗi haka kuma mala'iku sun amsa, dan haka ba zan ce miki a'a ba, shawarar da zan baki kawai ita ce ki kira Nawal ɗin sai ki mata maganar cikin nutsuwa da hikima, idan ta fahimci ta kuma amince, sai mu ce Alhamdulillah, idan kuma tana da wanda take so da bamu sani ba, kinga sai ki bashi haƙuri ta wata sigar."_
Da jin daɗi da farin cikin samun mahaifiya kamar Anna Intisar ta dinga godiya da yi mata addu'ar Allah ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, kafin sukayi sallama ta kira Nawal kai tsaye dan hankalin ta ba zai kwanta ba idan har matsaya ta samu akan maganar ba, tana da naci irin na Yayan Aswan akan abu idan suka saka mishi rai, sai dai bambamcin su shine ita zata yi ta nacin abun ne har sai ta samu yadda take so, shi kuma yana iya shanye shi sai dai kuma gangar jikin sa za ta cutu da haka.
Magana ta fahimta sosai sukayi da Nawal tare da fahimtar da ita alfanun yin haka da kuma wa ye Bilal, sannan ta ƙara mata da za ta bata lokaci tayi tunani sannan ta yi shawara da half ɗin ta wato Manal haka ma da Anna, daga haka ta kashe wayar da tabbacin za t a sake kiran ta washe gari dan ta ji shawarar da ta yanke, daga haka ta kashe wayar tana addu'a da fata maganar ta ta tayi tasiri a zuciyar Nawal, duk da dai ta ji jikin ta ya yi sanyi kuma ta amsa mata a sanyaye da kulawa, amma dai tana fata har zuciyar ta hakane.
Gidan su Manal suka zo aka ce babu kowa, nan sukayi ta kiran wayar Yusrah tana ƙara ba'a ɗagawa, sai kawai Manal ta dubi Nawal tace "Ke ki kira Akhi muji ko tare suka fita?"
Nawal kuma da jikin ta ke mace murus game da maganar ta da aunty Intisar sai ta taɓe baki tace "Me na fiki da zan kira shi? Baki, kati a waya ko wayar?"
Abrar ce tace "Dan Allah sis ke ki kira, kin ɗan fi iya ji da shi ne ai."
A taƙaice tace "Kai, idan ba wacce za ta kira shi a cikin ku mu wuce mu tafi gida, haba."
Tsaki Manal tayi tare da fara duba lambar shi, tana aika kira saida wayar tayi kamar za ta tsinke bai ɗaga ba saboda lokacin ana ƙoƙarin sakawa Yusrah ƙarin ruwa ne duk hankalin shi na kan su. Daga wannan kiran bata sake ba kawai ta kira lambar Anna, Anna na ɗagawa Manal tace _"Anna, nace ko za ki kira mana babban ɗan ki muji ina suka je, gashi mun zo gidan basa nan har Yusrah ma, ko zamu iya bar mata saƙon a hannun masu gadi?"_
Da mamaki Anna tace _" Ba sa nan kuma? Amma ai bamu yi da su zasu fita ba."_
_" Nima shine abun ya bani mamaki."_ Manal ta faɗa tana gyara zaman ta cikin mota, dan haka Anna tace _" Kar ku ba kowa kayan ta, bari na kira shi naji."_
Saida Anna ta kira ne sannan ya ɗaga yake sanar da ita Yusrah ba lafiya suna asibiti, hankalin ta ya so tashi ta fara faɗan me ya sa bai kirata ba to? Dan haka gata nan zuwa yanzu ta kashe wayar, wayar kawai ya bi da kallo yana ayyana _" Matan Haidar ba dama."_
Anna kuma na kiran su Nawal ta sanar da su ta ce su koma gida kawai, sai suma suka ji ba zasu iya haƙura ba sai sun je sun ga jikin Yusrah, hakane ya sa asibitin karɓar baƙuncin su dan Anna ma da zata tafi lokacin Aba ya dawo, sai kawai Sk ya jasu a mota suka nufi asibitin.
*Bayan* ya gama waya da Anna ne ya sake zaunawa kusa da ita tana lumshe idanu bacci na son ɗaukar ta, a hankali ya ranƙwafa daga zaunen ya haɗa goshin shi da nata tana kallon idanun ta cikin tausasawa yace "My lady, kinga damuwar ki abinda ta haifar ko? Dan Allah ki saki ran ki *iyalina*, ni naki ne ke kaɗai, ba zan taɓa raba miki kaina da wata ba, kin fahimta?"
Idanuwan ta ne suka ci taf da hawaye a sanyaye ita ma ta kai hannun ta tana shafa gemun shi tace" Ya zan yi to? AA ba za ji maganata ba, bana so na zama marar adalci, yarinyar nan ta rigani shiga duniyar ka, me ya sa zan yi takaici dan za ta shigo gidan ka ita ma? Na so kaina dayawa, ka yafe min dan Allah?"
A nutse ba tare da ya ɗaga jikin ta ba ya girgiza kai yace" Babu wacce za ta shigo gi..."
Kafin ya faɗi abinda yake son faɗa Dr. Siddik ya ƙwanƙwasa ya shigo kai tsaye fuskar shi fal fara'a ya nufo shi yana faɗin" Oga, na ji daɗin ganin ka a nan."
A sanyaye Aswan ya ɗago daga jikin ta ya kalle shi bai bashi amsa ba, hakan yasa Dr. Siddik kallon Yusrah yace" Madame, ya jikin? Da dama ko?"
A hankali ta ɗaga kai sannan tace" Alhamdulillah."
Murmushi ya yi ya sake duban Aswan da hannunshi ke cikin nata yana ta murzawa cike da tausayin ta yace" Oga, ina ga fa zan sake ƙarawa madame wani hutun ne mai tsayi, a taƙaice dai ina ga har ta gama raino da goyo, ko kuwa?"
Ya ƙarashe maganar yana ƴar dariya, dukansu basu gane me yake nufi ba, dan haka Aswan ya kalle shi sosai bayan ya kalle ta yace" Ban gane ba? Hutun ta ai ya kusa ƙarewa, dama ina so ne a gama hidimar nan sai ta fara zuwa."
Da fara'a dr yace" To ka kwantar da hankalin ka, yanzun ma na sake ƙara muku wani hutun har ku gama rainon unborn ɗin ku."
Rarraba idanuwa suka shiga yi har Yusrah dake kwance tare da dafe ƙirjin ta da ya ji ya mata wani rasss tana son gano abinda yake nufi dan da kaji likita na maka maganar nan akwai abinda ya gano a mahaifa, Aswan kuma a nutse ba tare da ya ɗauke idanun shi daga kan Siddik ba yace "What do u mean?"
Dariya Siddik ya yi ya miƙo masa hannu da sigar musabiha yace "Congrat bro, madame ɗin ka tana ɗauke da ƙaramin cikin da bai fi kwana ashirin da ɗaya ba, ina taya ka murna."
Wani irin abu da ya daki ƙirjin shi ya saka shi saurin rufe bakin ta da tafin hannu tare da ƙara jimƙe hannun Siddik gam gam da ƙarfi, ya kalli Siddik ya kalli Yusrah da ta dafe goshin ta da kuma marar ta tayi mutuwar kwance tana ta ayyana _" Ciki? Ciki? Ni? Cikin Aswan?"_
Wasu irin zafafan hawaye ya ji sun cika masa idanuwa wanda rabon da ya yi irin su har ya manta a rayuwar sa, abun kawai ya ji kamar zai fi ƙarfin iya ɗaukar zuciyar sa, sai ya ji abu wani daban haka ba kamar ba yadda yake jin Safwan ba, hakan na nufin dan wannan yana tabbas daga gare shi ne? Bai taɓa tunanin zai ji wani abu sama da yadda yake jin Safwan ba idan aka cire Yayar sa, amma ya yake jin yanzu haka wannan abu da Siddik ya faɗa masa da ko ganin shi bai da tabbacin zai yi kamar darajar shi na hawa kujerar mulkin da Y. Turaki take a kai.
A hankali ya buɗe bakin shi da tafin hannun yana share ƙwallar da ta gangaro masa ya dubi Siddik sosai yace "Na gode, na gode da wannan albishir, ba zan taɓa mantawa da wannan ranar ba."
Juyowa ya yi kan Yusrah da har yanzu bata motsa ba ya sake haɗa goshin shi da nata ya tallabota ya rumgume sosai a jikin shi, cikin nutsuwa ya raɗa mata "Jaanu, ashe har na yi wuff da ke? Y. Turaki da me zan saka miki?"
Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke ta saka hannayen ta tana shafa bayan shi, Siddik na ganin haka ya fita yana dariya cike da begen hakan, Yusrah ma a tausashe tace "Ai ka jima da yin wuff da ni, tun ranar da na zama taka."
Kallon ta ya yi sosai yace "Me kike so? Me kike so daga gare ni Y. Turaki? Ki faɗa ko menene zan baki shi indai akwai shi a gidan duniya."
Fuskar shi ta shiga shafawa ko ina da hannun ta na dama tana murmushi tace "Abun duk da nake so a duniyar nan...*bayan ka ne*, kai kaɗai ka ishe ni rayuwa Abban Haidar, kai kaɗai kawai *nake so*, kai kawai."
Wata irin matsa ya mata kamar zai ɓallata gida biyu saboda jin daɗi, rintse idanu ta yi tare da cije leɓen ta, amma dai bata ce komai ba tana sauraron shi yana cewa" Me kike so tukuici? Me kike so na baki?"
Saida ta ji ya sassauta mata riƙon kafin ta raɗa masa a kunne" Ka bani kyautar darare masu zuwa kafin ɗaurin auren ka ba tare da ka matsa daga kusa dani ba, idan ka min haka zan ji daɗi sosai."
Ɗaga fuskar shi ya yi ya zuba idanun shi a cikin nata yace" In baki wani tukuicin da ya fi wannan?"
Zuba masa idanu tayi ba ta ce komai ba dan bata so ya mata kyautar dukiya wallahi, dan wacce ta tara ma bata san ina za ta kai ta ba, saida ya shafa kumatun ta sannan yace" Fitar da nayi ɗazu, ban dawo gida ba saida aka soke aurena da Nabihat saboda Chef ya gano ita ce ta sa aka fara auren ki tun farko, maganar da nake miki yanzu Chef ya ce ko bayan ran shi ya haramta min auren