Showing 159001 words to 162000 words out of 397328 words

Chapter 54 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70022

yi a yiwa Aba sharri?"

A tsorace ya ɗago yana dubansa, fuskarsa jage jage da hawaye ya ce" Akhi, wallahi ban san me saƙon ya ƙunsa ba, ni dai uncle ya nuna min ga wani ɗan aiki mai sauƙi da zai kawo min kuɗi masu yawa, shine na amsa, ban san meye a ciki ba, sai ma da na tambaye shi ina fatan ba ƙwaya bane yace a me na ɗauke shi ne? Shine fa nake masa hanyar ana shigar da saƙon."

AA ya kama hannayensa ya ja, amma Humed ya kuma naniƙe shi, sai da ya ɗago yace" Kai cikani mana magana ce zamu yi ai."

Humed ya sake shi ya zauna daf da ƙafafuwansa yana kallonsa, AA ya sauko ɗin shi ma ya zamo suna zaune saman cafet ne su duka.

A tausashe AA ya ce" Humed, da ilimin ka? Da hankalin ka, a kawo maka aikin da aka ce da kai kaɗan ne a baka maƙudan kuɗi ka karɓa? Humed ba zan tambayeka me zaka yi da kuɗaɗe bayan wanda kake samu ba dan kai namiji ne ban san girman abinda ke kanka ba na hidimar rayuwa, amma Humed ko me bawa zai yi sai ya ringa aunawa ya kuma ringa tuna ranar da zai kai bayani gaban Allah, Humed kana cikin irin ma'aikatan dake saka kansu a uku a cikin rashin sani ko gidadanci ne? Ya Allah! Humed ka duba ka ga kuɗin da aka rubuta maka a check ɗin nan, kuma ka amsa zaka je ka ci, faɗa min tun yaushe kake fitar masa da kayan? Faɗa min check ɗin kuɗi irin haka ƙwaya nawa ya baka? Idan zai baka meye shedar da yake ajiyewa ta tabbacin kun yi aiki tare da ya cancanci ya baka kuɗi irin haka?"

Humed ya ce" Akhi, babu wata sheda, check ɗin kawai yake bani, dan da farko ya nuna ya bani cach na ƙiya, kuma ni bai fi sau biyar da na fitar masa da saƙon ba, yace ne da farko a wani kamfanin yake turawa wai sun saka masa tsada ne ya ga gashi a gida bari ya yi abinsa a wajen mu, Akhi ni ban kawo komai a raina ba dan na ga ai Uncle ne, uncle Hamat ɗin mu ne, ba zai cutar da ni ba, shi yasa nake yi hankali kwance fa."

AA ya sauke ajiyar zuciya yana kallonsa, ya ɗan jima kafin ya ce" Gaba ɗaya shedun da ya baka nake so ka kawo min, ka kuma tabbatar min da maganar da ka yi cewar ba ka san meye a cikin saƙon sa ba, saboda da shi ne zan iya aiki in hana maka zuwa prison."

A tsorace Humed ya ce" Prison Akhi?"

AA ya gyaɗa kansa, ya ce" Prison, a kaɗan idan ka ɗauka ka ɗauki shekaru goma, garin shirme ka saka kanka a uku."

A rikice Humed ya ce" Akhi wallahi babu abinda na yi."

"Ka yi ɗan ƙaniya, ka yi tunda ka ci kuɗi, daga yau zuwa gobe nake son komai, dan fita zan yi da son harkar lafiyarsa, ka kula, na san matarsa zata gaya masa na same ku a falo da abinda ya faru, in dai ta faɗa ya tuntuɓeka kace rikici muka yi shine na bika, kuma da na je na ga check ɗin kuɗi a hannunka sai raina ya ɓace na yi abinda na yi, Humed ka san yadda zaka yi ka yi convincing ɗin sa ya yarda da maganar ka, ka kuma dage da addu'a Allah ya bani damar da zan wanke ka."

AA ya faɗa a tausashen sa, Humed ya ringa godiya yana ƙara jaddada masa babu abinda ya sani, har ya miƙe zai tafi AA ya dakatar da shi ya shige ciki, jim kaɗan ya fito da wani magani na shafawa ya shafa masa wajen da ya fasa masa sannan ya bashi takalmi ya kuma sarkafo hannunsa ya raka shi har kusan motarsa.

Da ya buɗe ya shiga ya sake dafe wajen ƙofar yana dubansa ya ce" Ka kula, ka yi taka tsantsan, inaga ƙarshen duniyar ne ya zo, ka cire maganar uncle ne ba zai cutar da kai ba a ranka, ka kuma kiyaye kar ka min ƙarya, Humed idan ka toni asirin abinda muke ciki a yanzu ko da a wajen Aba ne sai na jijjigaka fiye da tunanin ka, ka gaishe min da yarona."

Humed sai ya zamo banda gyaɗa kai baya iya yin komai, yana kallonsa ya tayar da motar ya tafi, AA ya jima a tsaye, dafe da ƙugun sa yana tunani, a nutse ya juya ya koma ciki, saida ya buɗe ƙofar ɗakin Safwan cikin sanɗa dan kar ya tashe shi a bacci, ya ga har lokacin dai yana baccin shi a nutse amma ya gyara kwanciyar sa, murmushi ya saki sannan ya jawo masa ƙofar a nutse ya nufi ɗakin sa cikin sanɗa ya lalubo wajen takardunsa, ai kam ya ga takardar lambar Brs. Mukhtar yayan su Samir.

A nutse ya ɗauki lambar a wayarsa ya nemi waje ya zauna ya shiga bugawa, yana ji a ransa lokaci ya yi da zasu zauna da lauyan nan, lokaci ya yi da zai ɗaukarwa ahalinsa lauya da ya yarda da shi dan ya kare su a sirrance.

Dake dare ya yi gaisawa sukayi har AA na faɗa masa _"Sorry for disturb, wataƙila na tashe ka a bacci ma?"

Brs. Mukhtar ya amsa da _" Comon man, wanda bai da mata me zai kaishi bacci yanzu?"_

Murmushi AA ya yi yana auna kalar shaƙiyancin Mukhtar ɗin yace _" Well, dama ina so zamuyi magana ne da kai mai mahimmanci, a ina zan same ka gobe da safe?"_

Da sigar zolaya Brs. Mukhtar yace _" Ba damuwa dan wannan Oga, in dai kana gidan to da kaina zan zo in sha Allah, tunda babu inda zan je da safen, kaga daga nan ma sai na zo maka da ƴan ƙiriniyar ka."_

Murmushi AA ya sake yi sannan yace _" Ok, Allah ya kaimu safiyar."_

_" Ameen Ya Allah, saida safe."_ Mukhtar ya faɗa sukayi sallama daga nan.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
25/05/2024, 08:15 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*42*




Da mamakin yadda su Meem ɗin ke ta hawa jikin Safwan ya ƙaraso yana faɗin "Meem, Angel, ku barshi mana ya huta."

Tunda suka ji muryar shi duk suka zabura suka tunkare shi da farin cikin su, ɗaukar kowacen su ya yi har ya ƙaraso ya zauna kusa da Safwan yana kallon fuskokin su yace "Wannan fa yarona ne, ba shi da lafiya a yanzu, dan haka ku barshi yana samun hutu, nan da kwana kaɗan idan ya samu lafiya, zai yi wasa tare da ku, right?"

Yanayin da suka nuna masa da kukan da sukayi ya sa shi yin murmushi ya shafa kawunan su yace "Good girl's."

Sai kuma ya sauke su daga jikin shi yana maida hankalin shi kan Safwan da ya tsare su da idanu yace "Abba, suna jin me kake faɗa kuma?"

Murmushi ya yi yana shafa kan Safwan ɗin yace "Suna ji, kai ma idan kuka saba zasu dinga jin maganar ka."

Da mamaki dai Safwan yace "Amma Abba ta ya suke jin magana, kuma su basa magana?"

Ƴar dariya ya yi yana mai jin daɗin yadda yaron yake da tambaya akan komai, wannan alamu ne na hasken ƙwaƙwalwa da Allah ya bashi, kuma a haka yaro ke tara ilimi sosai, a sanyaye ya mayar masa da "Suna ji, su a haka suke, idan ka dube su ai zaka ga ba irin magunan da kake gani bane, sannan suna magana fa, ba ka ji?"

Ɗan zaro idanu ya yi tare da sakin baki irin mamakin nan yace "Ni kuma bana jin maganar su, ya suke yi?"

Da dariya AA yace "Bari ka gani to." Kallon su Meem ɗin ya yi da suke ta wasar su har wani tsalle suke kamar zasu tashi sama yace "Angel."

Mai ɗan ratsin baƙi baƙin ce ta kalle shi da sauri tare da sukwanowa ta nufo shi, remonte dake kusa da tv dake manne a bango daga ƙasa ya kalla yace "Bani remonte?"

Da gudu Angel ta juya ta nufi inda ya aike ta, da bakin ta ta ɗauko remonte ɗin ta juyo da gudu ta kawo masa ya karɓa yana faɗin "Thank you."

Farantin kayan marmarin dake kan ƙafafun Safwan AA ya ɗauka sannan ya ɗauki yankan lemu ɗaya ya miƙawa Safwan a hannu da ya saki baki yana kallon sarautar Allah yace "Ba ta, za ka ji ta yi maka godiya."

Da sauri Safwan ya kalli Angel ɗin ya miƙa mata lemun, da baki ta fara karɓa sannan ta aje shi ƙasan carfet tasa ƙafar ta ta take shi alamar ba mai taɓa mata fa sannan ta kalli Safwan tayi wani marayan kuka tana wani sissine kai da ƙoƙarin fara gwaguyar lemun dan babu abinda ba sa sha ko ci, ganin yadda Safwan ya yi tsuru tsuru da idanuwa ya sa AA bushewa da dariya ya tarawa Angel hannaye ya ɗauketa ya rumgume yana shafa ta har da sumbata sannan ya kalli Safwan yace "Ka gani? Ta ce maka thank you."

Shi ma Safwan sai ya bushe da dariya yana kallon Meem da ta wani yi kwance tana wani kuka miyau miyau tare da juya kanta bata kallon su, kallonta AA ya yi sannan ya kalli Safwan ya masa raɗa da "Kishi fa take ban kulata ba, bari ka gani?"

Sake dubanta ya yi yace "Meem." Shiru ta yi bata juyo ba, hakan ya sa ya sake jan sunan "Meeeeeeeemmmm."

Nan ma dai bata kula shi ba, sai kawai ya maƙalewa Safwan ido ɗaya alamar zai tsokaneta, da gangan ya fara atshawa kamar mai murar nan, ai da gudu Meem ta zabura ta yi kan table ɗin glas ɗin ta haye saman shi ta zaro tissue ta sauko da gudu har kwalin na biyota ya faɗi ƙasa ta zo kusan ƙafafun shi, saida ta fara zagaya shi sau uku sannan ta haye kujerar ta aje masa tissue ɗin saman cinyar sa, ɗaukar tissue ɗin ya yi ita ma ya ɗauketa ya rumgume a jiki yana faɗin "Cute baby, don't be jalous, kuna zuciyata."

Vibration da wayar sa ta yi ya sa shi zaro wayar ya duba, sai kuma ya kalli Safwan yace "My boy, zan fita farfajiya ina da baƙo, ka zauna da su Meem ku sha hira."

Turo baki Safwan ya yi yace "Abba bana so kana min nisa fa."

Shafa kan shi ya yi yace "Kar ka damu, ba fita zan yi ba ina nan, maganar tafiyar ka fa zamuyi, nan da kwanan da bai fi huɗu ba."

Dariya Safwan ya yi yana faɗin "To Abba, a dawo lafiya."

Saida ya sumbaci kan Safwan sannan ya amsa da "Ameen my boy, thank you." Daga nan ya fice ya bar shi da Meem shi kuma ya samu Brs. Mukhtar a farfajiya zaune cikin motar sa yana jira.

Maimakun ya bashi damar shiga ciki sai ya buɗe motar shi ya shiga ya rufe sannan ya juyo yana miƙowa Barister Muktar hannu ya furta " Barka da warhaka iko?"

Barista ya yi murmushi ya kama hannun nasa suka gaisa shi ma ya ce" Barka kadai iko."

AA ya yi ɗan murmushi sannan ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce" Na san ni ya dace in je office ɗin ka kan abinda ke tafe da ni, sai dai a yanzu daga bakin lokacin da na bar gidan nan ina kyautata zaton ana bin sawuna, shi yasa na zaɓi kiran ka, ka yi haƙuri."

Sauƙin kan dake bayyana a wajen mutumin da yake tunanin dariya ma na yi masa wahala na matuƙar bashi mamaki, a yanzun ma ya bashi mamakin ainun har ya zamo ya zuba masa ido kafin ya yi murmushi ya ce" Idan ka tuna, na nemi zumunci da kai, idan har da zumuncin in zo in sameka kan abinda kake son bani matsayin aiki ba wani damuwa Iko."

Aswan ya gyaɗa kai ya ciro takardar check ɗin nan da ta kwana a hannun shi, miƙawa Barrister ya yi yana dubawa.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana kallonsa ya ce" Ban san girman amanarka ba, ban kuma san irin ƙwazon ka ba, abinda na sani shine in dai Chef ya saka ka a lamarinsa ka kai ya saka kan ne, ina cikin hali na shirin tafiyar da zata ɗauke ni wataƙila kwana goma, gashi kuma wannan abin ya ɓillo min, Barista wannan takardar na ɗaya daga cikin abinda ke iya tsayar da bugun numfashina."

Ya dakatar da maganar yana dafe goshinsa, a tausashe ya ce" Na fara binciken nan ne dan kawai in daidaita abubuwan da basu min ba a gidanmu da kuma daidaita abubuwan da nake tunanin suna faruwa da sunnan mahaifina, a yanzu na kai gaɓar da nake jin kamar na dakatar domin a jiya da ace ban gane cewar mahaifina ne ake son ɗaurewa ta kowace fuska, a ɓata masa suna, a aikata laifi da sunansa, a yi anfani da sunansa a tara dukiya ƙarshe a kai ƴaƴan sa a rufe a wulaƙance wanda ni na san hakan ba zai barshi da lafiya ba ko da kuwa ya samu ya tsira da ransa, uwa uba mahaifiyata, na gane cewar na fa shiga sai na ƙarasa ko da ni zan shiga a wani halin ne."

Ya amshi takardar yana sake kallon ta yana nuna masa ya ce" Wannan kuɗin da kake gani ƙanina aka ba su, ba kuma wannan bace kaɗai akwai guda huɗu a hannun sa irin wannan, na faɗa masa yau ya kawo min su dan na ci gaba da tara hujjojina, abinda bani da damar sani shine menene babbar shedar da zata iya saka shi a matsala, wacce in wanda ya bashi kuɗin ya ajiye a wajensa, kai dai kuɗin nan ana bashi su ne a rufe, bai ma san aikin da yake yi mai hatsari bane kuɗin dai yake amsa, na fahimci cewar a yanzu ina da buƙatar wanda zai bani shawara, har ma in ta kama shiga kotu zan so ace na gama shiryawa shine na tuntuɓeka, ban wani sanka sani ba, amma haka kawai na tuntuɓeka."

Duguwar ajiyar zuciya Brs. Mukhtar ya ja sannan ya sauke yana duban AA ɗin bayan ya sake zura hannu ya karɓi takardun yace "Lallai wannan babbar magana ce, kuma har ban san godiya zan maka ko jajanta maka ba akan faɗa min wannan abu da ya shafe ka, wannan kuma ya sa na ƙara tabbatarwa kai na lallai ba'a banza ka shiga prison ba, wel..."

Gyara zama ya yi ya ɗora da "In sha Allah in dai har ƙanin ka bashi da laifin, to ba zamu rasa hanyar da zamu bi ba wajen nunawa alƙali da kuma duniya haka, abu mai mahimmanci shine takardar dake nuna an bashi kuɗi, ko da ma ace wanda ya bashi kuɗin yana da wata hujjar da tafi wannan dan tozarta ahalin ka, je t'assure, wannan ma shaida ce da za ta ɗaure dukkan su."

Jinjina kai Aswan ya yi tare da sauke ajiyar zuciya a tausashe yace" Na gode da ka ɗauki lamarina da daraja haka, ƙwarai na je prison ne duk saboda wannan, kuma yanzu haka zan iya ce maka aikin farko ma da nake so ka fara min shine ƙoƙarin fito da wanda naje gani a wurin nan...bashi da laifi ko kaɗan, an kaishi can ne kawai saboda ana so ya yi nesa da Abana dan a ji daɗin ruguza shi, sannan mutum na biyu Arif, Arif Sani Galadima, zai taimaka min sosai saboda yana da confidence fiye da zaton ka, idan ka min haka zan ji daɗi sosai, sai kuma magana akan farashhh..."

Bai ƙarashe ba Brs. Mukhtar ya girgiza kai yana murmushi yace" No wahala Oga, amma da fari zan so ganin ƙanin naka, akwai tambayoyi masu mahimmanci da nake son yi masa, sannan wannan check ɗin na baki dukansu original ne, dan haka zamu sake buga wasu a ƙalla guda biyu ko uku, ni da ƙanin ka zamu riƙe na bogin, kai kuma Oga sai ka adana mana na gasken har zuwa ranar da komai zai zo ƙarshe, saboda nasan ba taƙadarin da zai yi gigin tunkarar nan saboda wannan fallen takardar..."

Ya faɗa yana sake kallon ginin gidan da kuma murmushi a fuskar sa kamar mai son yin tsokana, shi kan shi Aswan murmushin ya yi ya ɗan girgiza kan shi yace" Ba damuwa, amma kafin ka fara min aiki ai yana da kyau na san farashin ka ko? Dan kar ka zo daga ƙarshe ka nemi karya min tattalin arziki, dan kasan ku manya ne, kuma tsaf za ka nunawa alƙali shaidar da za ta saka har Annata sai ta siyar da gwalagwalanta dan kawai mu tarkata mu biyaka."

Sosai ya yi maganar da zolaya sosai a yanayin nasa da ya fara nuna ya ɗan saku, abinda ya danne masa ƙirji na damuwa akan abinda ka iya faruwa da su Aba da kula halin da Humed ya jefa kan shi a ciki ya ji ya fara rage


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login