Showing 195001 words to 198000 words out of 397328 words

Chapter 66 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70069

ya ce zai je su haɗu a park yau, sun yi magana da ita, to yau ya je yana ta kira baya samunta shine na ji muryarsa dai wata iri kar aje ko ba lafiya."

Aba ya ɗan zuba mata ido na ƴan mintuna, yanayinta na so ya saka shi a damuwa da tunanin ko ƴaƴanta na cikin wani hali basu sani ba, ganin mijinta ya shiga kiran lambar ƴar uwar tasa sai ya ɗauke kai ya sauke dubansa a kan Anna da ta masa alamun kar ya ce komai dan Allah, sannan ya maida dubansa kan labaran da ake ta haskowa bai ce komai ɗin ba, sai Annar ce ta ci gaba da faɗin" To *maman Yusrah* kina bayanin gado da me ma? Kai amma Yusrah ƴar gatan Mamanta ce, ki ce suturun ma canzawa za'a yi?"

Intisar ta sauke ajiyar zuciya, suna ta shan kwasa ne da iyayen nasu ana ta shan dariya ta ce hatta penti sai an sake yiwa ɗakin da zata sauke Yusrah da su gado kai hatta suturu sai ta mata odern sababbi dan kar ta yi rigimar sai ta bi su dan ta kwantar da hankalinta sai kace ƴar goye Yusrahn, sai ga wannan kiran.

A ɓangaren yaya Mubarak kuwa shi ma ransa ne ya ringa ɓaci, kira ya kai huɗu ya yiwa ƙanwar sa amma bata ɗaga ba, ya yi kiran mijinta shi ma bai ɗaga ba, ƙarshe ya yi kiran Akhi tasa a kashe ma a dole ya kirayi Yusrah ya tambayeta ko lafiya? Suna ina ne?

Yusrah da suka ajiye mai taxi ɗin nan a gidan mai ya mashi trensfer ɗin kuɗi bata san adadin nawa ba ya sa mutumin bashi motar sai godiya yake masa suka amshi katin juna, AA ya amshi tuƙin ya falfala da gudu da ita ta kame a bayan motar nan zuciyarta ke harbawa da tsoron tabbas ta yiwu shiga cell ta biyu ta kamata a yau sanadiyar wannan bawan Allah, inna lillahi jama'a a ƙasar da ba'a gudun da ya wuce ƙa'ida yake wannan falfalatun da ita, a ƙasar da take haɗuwa da abubuwan mamaki da na tsoro ne yake wannan falfalatun da ita, duk a firgice take, ta masa bayanin abinda ta sani ita dai har ta ga sun ƙarasa wani madaidaicin gate ya sauka daga motar ya shiga ta sanarwa yaya Mubarak wanda ya ce" Gidan da su Mabruka suke ne, please ki bi shi."

Jiki a mace ta fito ta bi bayan shi bayan ta kashe kiran, tana shiga ta ganshi tsaye yana kallon wasu kyawawan ƴan mata, ɗayar na duƙe tana wanki, ɗayar kuwa da tiyo tana zubawa tarin kwanoni sai kace kwanonin da aka yi biki da su, yaran sun ɗago sun ganshi, sun ga wanene amma sun kasa tashi su zo inda yake sai su dube shi sai su dubi hanyar ɗakin hawaye tuni ya ɓallewa ƙaramar.

Idanuwansa ya rintse, hankalinsa na son tashi da gasken gaske, wanki da hannayenta? Duka nawa Mabruka take? Ita kuma wanke wanken nan sai kace na gidan biki? Shin basu da injin wanki ne? Ko basu da masu wanke wanke? Bai ce masu komai ba ya nufi ɗakin kansa tsaye.

Yana shiga ya tarda mijinta zaune saman kujera yana shan sigari, ita kuwa ta saka kiɗa sama sama tana ɗan juyi da wani gajeran wando tamkar zai tsage a jikinta, da sauri ta kashe kiɗan tana kallonsa ta ce" Yaya Aswan? Kai ne? Dama ka san gidan nan? Ka san abinda yasa bamuje da wuri ba jiya aka yi birthday ɗin prince, to basu wanke gidan da kayan aikin ba sai yau suka ɗauko shine nake jira su gama mu tafi, zauna mana bari in kirawo su."

Bai zauna ɗin ba ya dai bita da kallon da ya sakata jin tsoro a ranta, domin ta san waye shi farin sani, fita ta yi bayan ta raɓe shi ta kirayo su Mabruka, ƙasa ƙasa tana kashe masu warning ɗin su gaishe shi da sauransu.

Suna shigowa suka gaishe shi a raɓee kawunansu a ƙasa, nan ma ya bi su da kallo kafin ya buɗa bakinsa ya ce" Ku wuce mu je."

Yaran suka ɗago suna kallonsa, sannan suka kalli ƙanwar mahaifinsu, a kausashe ya ce" Nace ku wuce mu je."

Da sauri mijinta ya miƙe yana wani ɗan murza hanci ya ce"...




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
31/05/2024, 01:09 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*50*


Da sauri mijin ya miƙe yana wani ɗan murza hanci ya ce "Hi man, ina zaka je da su? Ko makaranta yau ba su je ba saboda sai sun gama aikin nan da aka saka su, shine dan su tafi park za ka wani fidda su?"

Ko dubansa bai yi ba, hasalima ba shi da niyyar duban nasa ya sake duban yaran wannan karon da duban ba magana zai sake yi masu ba jikinsu ne zai faɗa masu, da sauri suka juya sumui sumui suka fita da slipas a ƙafafuwansu jama'a sai kace a ƙauyen ƙayau suka nufi Yusrah dake ɗage tana leƙe ta dube su da son gane wai ana nufin sune ƴaƴan aunty Intisar ɗin?

Ya juya ya fito zai sauka mijin nata ya dafa kafaɗarsa da wani rainin zai masa magana, da ƙarfi ya juya ya damƙi hannun nasa ya haɗe shi da garun ƙofar ɗakin ya kama ƙeyarsa ya buga kansa da wajen ya riƙi bayan rigar ya yi cilli da shi.

Da ihu Yusrah ke tsale tana ɗora hannu a kai ta ce" Shikenan ya kashe shi, ya kashe shi, wannan kam ya kashe ɗan mutane, lahaula wala ƙuwata na shiga uku kar ka ja a rufeka mu shiga uku a garin nan, inna lillahi! Kai cewa ya yi ku je motar? Ku je gani nan ku je."

Ta idasa faɗa har tana tsale dan tashin hankali ta tura su waje gurin motar sannan ta shiga haɗa uku uku ta nufi ɗakin a guje ta auka hankali tashe tana faɗin " Gafara dai, ina kake?"

Turus ta yi ta zuba masa ido ganin yana tsaye a kansu ƙiƙam ƙanwar Yaya Mubarak sai ihu take yi na kuka tana faɗin a kan me zai dakar mata miji a gidan su? Ya san ai hukuncin haka, me suka yi masu? A kan me zai zo har gida ya dakar mata miji? Wallahi sai ta haɗa shi da hukuma, sai ta faɗa a gida sai ta kai ƙarar sa.

Shi kuwa yana tsaye a kansu yana kallonsu kallon da ta tabbata yana tunanin yadda zai sa su daina motsin kirki ne, dan haka da sauri ta ƙarasa daf da shi kaɗan murya a sanyaye sosai take faɗin" Kana ji? Kana ji mu je dan Allah mu tafi."

Shirun da ya mata ya sakata ƙara matsawa daf da shi hankalinta a tashe ganin ita ɗayar ta nufi waya ta ɗauko sai ƙara faɗi take ya bari ya gani sai ya je prison in dai a kan zuciyarsa ne a garin nan.

Ai a rikice ta kai hannunta da sauri wajen sajen haɓarsa ta kamo ta juyo da fuskar shi gareta, abinda sam da a nutse take ba za ta iya aikata haka ba, amma sai gashi ta yi wanda hakan ya bayar da wata irin ƙawa tamkar ta tsakanin miji da mata, duk da hannayen ta na jin laushi da sulɓin dake ga gashin da ta ɗora hannayen ta a kai ne, amma kuma idanun ta ƙyam a cikin nashi da take son ta samo kan shi kar ya ja a halaka su a ƙasar da ba tasu ba, yadda tsigar jikin ta ke tashi da sanyin da jikin ta ya yi sakamakon abinda ta aikata, ga kuma zuciyar ta da ta ƙara gudun harbawar ta tamkar za ta faso ƙirjin ta ta fito, hakan ya haddasa mata yin laushi laƙwas muryarta a sanyaye sosai ta ce" *Aban Safwan*, please lets go, dan Allah mu je kar ta kira mana police."

Leɓenta dake bayanin ya zubawa ido a hankali, sai kuma ya lumshe idanun shi yana jin suna neman tara masa ruwa saboda zai iya rantsewa Anna kaɗai ke masa irin wannan taɓe taɓe ya ji shi normal, amma yanzu sai ya ji duk jikin shi ya amsa, daga kan babbar yatsar sa zuwa tsakiyar kan sa sai ya ji wani irin sanyi ƙalau, bugu da ƙarin wani irin fat fat da yaji zuciyar sa ta kwasa lokaci ɗaya. Har ransa ba ya son kusancin sa da mace, kuma yana tsawatar wa idan aka masa wannan haukan, amma me ya sa? Garin ya ya? Saboda me? Sai wannan da ta kai hannun ta inda shi kawai ke iya kai wa, dan ko Aba da Anna ma fi aksari kan shi suka shi shafawa, amma sai ya ji ta kashe masa jiki kamar ta zane shi da wayar lantar ki, sai ya zama kamar gunki kawai ya tsare leɓunan ta da kallo dake motsawa.

Bugu da ƙari ta ƙara daɗaɗa masa rai da sunan da ta kira shi da shi wato *Abban Safwan*, sai ya ji kamar abinda yake ta kitsawa ya wa ƙanwar Mubarak ɗin nan da mijin ta yana sauka, kafin daga bisani ya ɗauke dubansa daga nata ya saka hannunsa ya sauke hannunta da ya riƙe haɓarsa saboda ji da yake kamar hakan ne ya gajiyar da shi ya dubi ƙanwar yaya Mubarak a hankali ya ce" Idan kika kira police ɗin ga adireshin hotel ɗin da nake, ɗaki na dubu biyu da goma sha ɗaya, idan baki haɗani da police ba ma kin shiga uku, dan ta yiwu idan muka zauna da su aka san abinda kike yiwa yaran can aka yi mana maslaha in shafa maku lafiya, in ba haka ba daga prison ɗin zan halaka ku! Gida kuwa dama ki shirya zuwansa dan kaf danginki sai na rufe ba Yayanki ba kafin ki zo in zane ki, sai na zane ki! Mahaukaciyar banza da wofi."

Daga nan ya damƙi hannun Yusrah ya juyo da ita a hannunsa dan kawai zuciyar sa ya ji tana raya masa matsananciyar so yake ta take masa baya sosai yayin fitar tasa. Baki Yusrah ta saki ta shiga bin shi ba gardama amma tana kallon hannayen su dake sarƙafe da na juna, uwa uba kayan su da suka yi kala ɗaya sai abun ya zama wani gwanin birgewa, suna fita ya zagaya da ita ya buɗe mata gaban motar, da mamaki ta shiga kallon shi har ta shiga ta zauna bata daina kallon fuskar sa ba duk da ya ƙi haɗa idanu da ita kuma fuskar a tamke, tana shiga ya saka hannunsa ya gyara abayarta dake ƙasa kaɗan sannan ya saka hannu ya ja kallabin ta da ya yi baya gashinta suna waje ya rufe mata ya zagaya ya shiga motar ya tayar ya ja ya harba kan hanya,

Har sun kusa isa hotel ɗin ya tsaya wani babban boutique, sai da ya ɗan shafa kansa a hankali dan ya sake control ɗin ɓacin ransa sannan ya ciro katinsa ya miƙawa Yusrah da wayarsa matsakaiciyar, a hankali ya buɗi baki ya ce" Ku shiga ku siyo dukkan abin buƙatar su da naki na kwanakin da suka rage mana, cod ɗin mtn ɗin........., na bankin kuwa........." Ya sanar mata cod ɗin gaba ɗaya sannan ya sake gyara zamansa a cikin motar ya mayar da idanuwansa ya rufe.

A hankali ta dubi yaran sannan ta buɗe motar ta fita ta zagaya ta buɗe masu a tausashe ta ce" Ku zo mu je, wacece Uka wacece Annarmu?"

Mabruka ta nuna kanta ta amsa da ita ce Uka, ɗayar kuwa ita ce mai sunnan Anna wato (Asalama), suka fito suka bi bayanta suka nufi wajen siyayyar wacce da farko security ɗin ya so hana yaran shiga domin har ga Allah sun yi datti sosai ga yanayin shigar su, sai da ta nuna da su take sannan suka shiga ɗin.

Siyayya ta masu na kayan buƙata hatta pant da bruch da sababbin towel sai da ta ɗaukar masu, takalma kuwa tun a nan ta siya masu wasu suka cire na ƙafafuwansu suka saka, sun dai ɗan ɗauki lokaci kafin su fito tana riƙe da hannayensu suka dawo motar suka shige baya su duka aka loda kayansu a bayan motar sannan aka rufe.

Jan motar ya yi ya je wajen parking ya fita ya yi gaba ko katinsa da wayarsa bai karɓa ba ya je ya sa ma'aikatan hotel ɗin zuwa suka kwaso masu kayan sannan ya hayewarsa da ky ɗin sa ya shige ɗakin sa suma suka shiga kokowa da nasu tarkacen suka shige ɗakin Yusrah wacce ta yi tsaye a kansu suka fara shigewa wanka, duk a tsorace suke, yanayinsu abin tausayi, kafin su fito ta sa a kawo masu abinci da sunan Aswan.

Shi kuwa yana shiga ya samu ɗayar wayar tasa babba da tarin miss call ɗin lambar Aba da Anna, zama ya yi bakin gadonsa ya yi kiran Anna dan ya tabbata tana tare da Aba domin lokacin sallar azahar bai shigo ba tukunan bai fita masallaci ba, ita kuwa idan yana gida tana tare da mijinta.

Ɗagawa Anna ta yi a nutse ta amsa sallamarsa kafin ta shiga mitar ina ya ajiye waya, me yake faruwa? Sai kuma ta ba Aba wayar dan ya ƙi bari ta idasa tambayoyin ta ma, Aba na amsa Aswan ya sauke ajiyar zuciya.

A tausashe Aba ya ce" me yake faruwa ne baban Safwan?"

Aswan ya buɗe idanuwansa bayan ya sake sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Yaran wajen Intisar, dama a irin wannan halin ta tafi ta barsu? Daɗi miji ne ya sa ta yi shiru take zaune a nan ta bar yaran nan a wannan halin? Yau ko mutuwa ta yi muma muka mutum a tunanina ƙanwar mijinta mariƙiyar ƴaƴanta ce, sai gashi yara a irin wannan halin ana zaune ƙalau? Aba, a yanzu ba zan yi kira Intisar ba, amma dan Allah ka sanar mata idan na zo ta tanadi amsar bani daga ita har mijinta a kan maganar yaran nan, in ba haka ba ran kowa sai ya ɓace, kuma in dan soyayar miji ce yasa ta je ta bar yaran nan a hannun matar nan take zaune a can sai na raba auren in ga ƙarshen soyaya!"

Irin yadda ya ƙare yana huci ya sa Aba ɗan yin jim kafin ya ce" Ka yi haƙuri jikan Anza, yanzu ina yaran suke? Ka san zuwan da ta yi dan ta sanar mana ne sun samu takardun da suke jira zasu tafi nan da kwana goma, ka san halin ƙanwar ka kaf cikinku Allah ya yi mata zurfin ciki mai wuyar fassara, kana gani fa ko rashin lafiya take yi yarinyar nan sai mamanku ta gane ta tambayeta sai tace eh, yanzu haka abu da yawa sai ka ji tace ta bari ne har ta zo sai ta sanar, mahaifiyarta ta jima da tuhumarta da zancen yaran, sai kawai ta fashe mata da kuka da ta yi ta ƙoshi sai tace wai bata da lafiya ne yara lafiyarsu ƙalau, kar ka ga laifinta a kan maganar yaran nan, kar kuma kace zaka raba aurenta, biyayya zata yi maka ko da kuwa mutuwa zata yi da cutuwa, ni na san zurfin cikinta ne ya sa ta kasa sanar da kowa halin da take ciki ko ƴaƴanta suke ciki, please ka yi haƙuri ka ji?"

Anna na zaune kamar ta amshe wayar take ji, ita ma a cikin damuwar take tun ɗazu, su Mubarak kuwa damuwar ta sa suka nufi gida ya ce bari yaje ya yi kiran ƙanwar tasa da lambar mamansu ya tabbata zata ɗaga ne,
Aswan ya ɗan yatsine bakinsa a hankali ya ce" Aba, zan yi wanka, yaran gasu can da Y. Turaki suna ɗakin ta, idan na fito zan yi kiran ka, amma ka sanar da Intisar ba zan bar yaran nan a hannun mahaukaciyar can ba, kuma idan rashin hankalinta ya kawota inda nake ban san a wace asibiti ce za'a iya ɗora ƙasusuwan ta ba."

Daga haka ya kashe kiransa ya ajiye cike da jin haushin Mubarak ɗin kansa da familly ɗin sa baki ɗaya, baya jin zai iya basu ƴaƴan nan ta daɗi, ashe a wannan halin yaran nan suke ciki? Sai kace bata da wanda suka tsaya mata? Ba laifi daga ita har shi zasu gane akwai manya a gabansu.

*A* wajen Yusrah da yaran kuwa tana tsaye a kansu bayan sun yi wanka sun yi bruch sosai ta basu sababbin pant da turare suka saka sannan ta basu riguna mararsa nauyi suka saka ta saka su zama cin abinci sannan ta shige wankan ita ma, bayan ta fito daga wanka ta saka ita ma rigar marar nauyi ta sa hula a kanta ta zumbula hijabin ta ta kabarta sallar azahar.

Sai da ta gama ta dubi inda suke ta ga har yanzu basu gama ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login